WACECE NI Complete Hausa Novel
Ta qarashe mgnr cikin kuka da sarqewar murya itama Zahran kuka takeyi me tsuma zuciya mamakin wannan kwamacala da kwado takeyi a hankali tace “ innanillahi wa Inna ilaihir raji’un Allahummah ajjirni fi musibati wa’akalifni khairin minha” abinda taketa nanatawa kenan jin yana qoqarin bude qofar ne yasata miqewa da sauri ta shige bathroom ta sakarwa kanta ruwa saboda zafin da taji zuciyarta tanayi.
Ta jima sannan ta fito suka hada ido yana kwance da Ukteeh a jikinsa yanda yake kallonta ya bata tsoro tadai dake taci gaba da shiryawa har yanzu idonsa na kanta tayi ajiyar zuciya qoqarin danne damuwarta takeyi don haka tana gamawa tayi ficewarta ta shiga kitchen ta fara qoqarin girki.
Ji tayi ya rungumeta ta baya ya saqalo weast dinta ta sauke ajiyar numfashi tare da dagowa ta kalleshi idanunta cike da hawaye tayi saurin janye idonta daga nasa tace “yaushe zamu tafi 9ja everlasting?” Tambayar ta bashi dariya yace “kin matsu mu tafine?” Ajiyar numfashi tayi tace “matarka tana buqatarka sosai tanada abinds zata fada maka don Allah idan zai yuwu yau mu tafi inason ganin Hajiya Ra’isah”
Dago kanta yayi ya sanya harshensa cikin bakinta ya tsotsa sosai sannan ya saki yace “babu matsala ki shirya mu wucce kawai yanzu nayiwa abokina waya yace akwai jirgin da zai tashi qarfe biyu zai sama mana 2 sit” murmushi tayi tace “na gde mijina” suna gama aikin sukaci abinci suka fara shiri cike da qaunar juna daya da kwata suka gama shirinsu suka fita driven yajasu zuwa airport suna zuwa suka shiga jirgi ya lula dasu zuwa qasarmu ta gado wato Nigeria.
Bakwai na dare suka dira a airport suna sauka drivensa na office yazo ya daukesu tunda suka iso takejin gabanta yana faduwa kai tsaye driven gidan Abuh ya nufa Colonel Marwan yace “gdana zaka kaini naga ka nufi wani gurin daban” sunkuyar dakai yayi yace “ba dabi’ar soja bane saba umarnin shugabansa amma wannan umarnin na dole ne Alh ne yace idan kun iso na wuto daku nan”
Colonel Marwan bai qara cewa komai ba saboda jikinsa da yaji yayi sanyi suna isa gidan suka tarar dashi cike da mutane gaban Zahrah ya qara faduwa taji jiri yana neman daukarta da gudu ta shiga gdan yana Kiran sunanta amma Ina tasan babu lfy suna shiga dukka sukayi turus ganin mutum kwance mimmiqe da alamun gawace, da sauri Zahra ta zube a gaban gawar hanunta na rawa ta bude fuskarta dukkansu sukaja da baya ba kowa bace face Hajiya Ra’isah ta zuba mata ido jikinta na rawa mgn takeso tayi amma ta kasa sai rawar baki yanda jikinta yake rawa kona marwan bayayi, da sauri ya riqota jikinsa ta kuwa rushe da kuka tace “itace Colonel da gaske Ra’isah ta mutu innanillahi wa Inna ilaihir raji’un meyasa kika mutu Ra’isah meyesa kika mutu meyasa baki jira na dawo na mallaka miki Mu’azzam ba wlh naci buri da alwashin mallaka mikishi halak malak, ashe dama dazu wasiya kike barmin wayyoh duniya kaico rayuwa da bakida tabbas Allah ya gafarta miki Ra’isah Allah ya karbi tubanki Allah ya baki tubarakin wannan rana ta juma’a….”
Amsawa mutanen dake gurin sukayi da “amin” janyeta mahaifiyar Ra’isah tayi daga jikin Marwan da ya qanqameta abokinsa Colonel Mahfuz yajashi suka fita sukayi alwala aka gama shiryata itadai Zahrah kuka kawai takeyi saboda tunawa da wannan rana itama tana zuwa kanta da kuma tuna kalaman Hajiya Ra’isah gareta dazu, bayan an gama shiryata zaa dauketa a fita da ita Zahran taja hannun Inna mahaifiyar Ra’isan sukaje sukayi mata addu’ar bankwana aka dagata aka fita da ita qanqame Inna tayi tana kuka me ban tausayi hakanan Inna itama ta qanqameta sukayita kukansu har zuwa wani lkc da Zahrah ta miqe ta shiga wani daki ta kwanta saboda kukan da yaja mata ciwon kai.
Bayan isha suka dawo gada jana’izar Ra’isah ya shigo parlourn idanunsa sun kada sunyi jawur mutanen dake parlourn sunata yi masa ta’aziyya amma hankalinsa baya gurinsu Ukteeh ya karba a gurin maqociyarsu ya dubi Inna yace “Inna ina Zahrah?” Dakin da take ciki ta nuna masa ya shiga ya taddata zaune saman sallaya da qur’ani a hannunta tana karatu tana kuka, zama yayi kusa da ita ya sanya hanunsa ya rufe qur’anin ta dago a sanyaye ta zuba idanunta da suke cike da qwallah akansa shima qwallar ce a idonsa yace “meye yasaki kuka?”
Murmushin qarfin hali tayi tace “ya hqr?” Shima murmushin ya qaqalo yayi mata ya janye qur’anin ya ajiye yace “inajin yunwa everlasting bazan iyacin komai ba ki samomin coffee nasha ko zanji sauqi” miqewa tayi ta ta fita ta shiga kitchen din dake saman ta hado masa tea ta soya masa chips ta dawo ta kawo masa ta hada masa zuba mata ido iska ta hura masa yaja numfashi tare da karbar cup din ya fara sha tana bashi Chips din yanaci har ya qoshi ya zame ya kwanta a qasan carpet din yana qoqarin janyota ta zame ta gudu parlourn sukaci gaba da zaman tagumi har zuwa wani lkc sannan kowa ya nemi makwanci itama ta tashi ta shiga dakin ta lallaba ta haye gado ta kwanta yanajinta kasancewar bai rintsa ba saboda dukan da mutuwar takeyi masa a hankali.
Da hijjab dinta ta kwanta tanata juyi bacci barawo ma ya saceta yaqi taji ya miqe ya hauro gadon ya riqota jikinsa ta sauke ajiyar zuciya tasan ta kade har ganyenta ita bata taba ganin mutum jarababbe irin Marwan ba matarshi ta mutu a yau dan baqin naci kuma so yake ya kwanta da ita, tanajin yanda yake yawo da hannunsa a jikinta tayi kamar me bacci shima sanin ba baccin takeyi ba yasashi yaci gaba da yamutsata har saida ta saki jikinta ya cita son ransa sannan sukayi wanka suka dawo suka kwanta yanayin bacci ta miqe ta tayar da sallar nafila tana roqawa Ra’isah rahamar ubangiji.
Haka suka wanzu a gdan har akayi kwana bakwai tun a kwana na biyu Ummuh da Mu’azzam suka dawo ranar da akayi bakwai suka koma gdansu suka gina sabuwar rayuwa cike da so qauna da tattalin juna rayuwa me cike da ban sha’awa, tsohuwar amana Baba Zulai itace take kula musu da yaran rayuwa cike da albarka.
Kwanaki sukayita turawa abubuwa masu dadi da akasinsu sunata faruwa.
*******
Watanni bakwai tsakani Marwah ta sake samun ciki wannan cikin har yafi na Mu’azzam bata wahala hakadai lkc ya rinqa shudewa har cikin ya isa wa’adin haihuwa saboda girman cikin da wahalar da yake bata ai sai gdan Ummuh ta koma taci gaba da rainon cikinta idan tasa ta ciyosa kuwa anan zai kwana suna kashe arna.
Satinta biyu a gdan nasu Ummuh ta fara labour cikin dare suka tafi Asibiti wannan karon ma taci baqar wahala likitan tace bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai Cx aka kumayi mata aka ciro mata yayanta biyu mace da namiji, wayyoh zo kuga murna gurin Colonel Marwan gdansa ya cika da yara likitocin sunso suyi mata planning amma yaqi yace zasuyi na musulumci.
Kwananta hudu a asibiti aka sallamota suka bata hutun wata uku batare da tayi wani aiki me wahala ba kwana hudu tsakani akayi didimar suna yaran sukaci sunan Fatimah da Aliyu inda Ra’ess da Ra’eesah daqyar Marwan ya bari ake cewa yarsa Ra’isah, hakanan yanaji yana gani ya qyaleta saida tayi wata uku sannan ya koma gareta aikuwa tanacin uwarta don duk wani missing da yayi na watanni ukun nan saida ya sauke matashi tass.
Bayan watanni takwas Zahrah an zama manyan mata ta koma makaranta tana digree dinta a fannin miscommunication A daidai lkcn ne labari me dadi ya isheta Mrs Hellin Moses ta musulumta har tayi aure sosai Zahrah taji dadin wannan lamari suka kuwa dinki da Raliya wato Hellin a baya tare sukeyin komai nasu.
Lkcn da ta sanar da Marwan saqon Ra’isah gareshi yayi kuka sosai daqyar ta lallabashi ya daina yimata Allah ya isa yace ya barta da Allah yayi duk yanda yakeso da ita zai iya yafe komai amma banda cin amanar aure, sun dade suna tufkawa kafin ya yafe mata tasasshi ya shige gaba wajan gina masallacin da tabar wasiyyar a gina matashi a matsayin sadaqatul’jariyyah sannan ta sanya aka gina boihol a gdan marayu da nufin Allah ya rinqa kaiwa mahaifiyarta da Hajiya Ra’isah ladan ta sake gina makarantar islamiyyah a cikin gdan wannan domin mahaifiyarta kawai tayita.
Shekarar data gama karatunta tayi service shekarar ta samu cikin auta Aisha wadda taci sunan Granny daga haka suka dakatar da haihuwar gaba daya saboda itama aikin akayi mata, sukaci gaba da bawa furensu ruwa yadda yadda ya kamata.