CociLabaraiPosto

​Wahayi aka yi Mani cewa na baiwa mabiya na ruwan sabulu su sha___Fasto

Daga Barista Nuraddeen Isma’eel

“Wani shahararren malamin addinin kirista mai suna Rufus Phala dake kauyen Makgodu Limpopo ta Afirika ta kudu, ya bayyanawa mabiyansa cewa! An yi masa wahayi kan cewa! Duk yabi ilahirin mabiyansa dazaran suka zo wurin ibada a ranar lahadin, da nufin ya baiwa kowa ruwan sabulu na kamfanin ” Dettol” a domin ya karama masu kaimi na wurin mai da hankali na kulawa da ibada tare da karfin ruhin kishin addinin kirista, da kuma wanke masu duk wani dattin zunubi.”

Fasto Rufus, fitaccene kuma sananne a wannan kuyen Makgodu a matsayinsa na babban malamin addinin kirista, rana tsaka an hango fasto din ya Shiga wata katafaren kasuwa yana cinikin wannan ruwan sabulun na “Dattol”, a domin yayi safara zuwa cocin dayake jagoranta dake Makgodu kusa da Polokwane a garin Limpopo a Afirika ta kudu.”

Bugu da kari, bayan kwana biyu da aikata wannan babban ta’asan dashi fasto din yayi ga mabiyansa na yin masu Duren ruwan sabulun na kamfanin “Dettol” din, bisani kamfanin “Dettol” din sun kirashi ta akwatin tafi da gidanka kan cewa lallai yadakata da baiwa mabiyansa wannan abun. Domin kuwa yana illatawa, ba’ayi ruwan sabulun da sunan asha bane an yi ne don a wanke jiki da wuri haka.”

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button