Al-Ajab

Wani magidanci ya cinnawa matarsa wuta, ƴan sanda sun bazama nemansa

Hukumar ƴan sandan jihar Legas ta bazama neman wani magidanci ruwa a jallo bayan ya cinnawa matarsa wuta.

 

Magidancin mai suna Akpos ana zarginsa da cinnawa matarsa mai suna Risikat, wuta wacce tayi sanadiyyar rasuwarta a mazaunin su dake kan titin Ayide Osolo, Divine Estate, a yankin Ijanikin na jihar Legas. Shafin LIB ya rawaito.

 

Lamarin ya auku ne a gidan ma’auratan

Shaidun gani da cewa sun tabbatar cewa Akpos da Risikat suna tare a cikin gidansu lokacin da rigima ta ɓarke a tsakanin su.

 

Rigimar tayi ta ruruwa wanda har ya kai ga Akpos ya ɗauko jarkar man fetur ɗin su ya ƙwararawa matar sa sannan ya banka mata wuta.

 

Bayan ya fahimci girman aika-aikar da ya tafka, sai magidancin ya ranta a na kare wanda har yanzu ba a san inda yake ba

 

Makwabta sun garzaya da Risikat zuwa wani asibiti mafi kusa da su inda daga bisani ta rasu yayin da ake duba lafiyarta bisa ƙunannakin data samu.

 

Ƴan sanda na neman magidancin ruwa a jallo

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa:

 

“An shigar da wani ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Ijanikin cewa wata mata mai suna Risikat, mai shekara 48 a duniya, sun yi rigima da mijinta wanda suna cikin rigimar ya ƙwarara mata man fetur sannan ya cinna mata wuta.”

 

“Lamarin ya sanya ta samu munanan raunikan ƙuna sannan an garzaya da ita zuwa asibiti domin duba lafiyarta amma ta rasu. Ana ƙoƙarin ganin an cafko wanda ake zargin tun bayan tserewar sa.”

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button