BABU SO HAUSA NOVELNOVELS

BABU SO 10

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

10

BABU SO….!! AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

Shin ko kunada labarin Yar Zuru mamar ZEE ZEE Mai maida tsohuwa yarinya wadda ta shahara wurin hada kaya kamar haka ❤️kamar su
Kaza
Zabo
Zakara
Ciccibi
Zuciya
Tsimin kankana d rake
Tsimin tabaje
Zumar dabino d kwakwa
Zumar gorun tula syrup
Garuka masu kama jiki kamar su ❤️
Bita zai zai
Dan wata bakwai
Madarar mata
Bata????????????
Ba kishiya ba Ko mugun mutan d mugun aljani sai sun barki
Matsin kinfi budurwa
Kalolin gumba dsauransu
Address maberar jariri bayan FGC sokoto
Phone 08068526455
Instergram Yar Zuru mamar ZEE ZEE kayan mata


………Ido ya ɗan tsura ma atm ɗin hanunta cike da nazari, kusan mintuna biyu harta ƙosa da tsaiwar sannan yay magana.
     “Ina zakije?”.
  Yanda yay maganar babu alamar wasa yasata ɗan ɗagowa a marairaice ta dubesa. “Abu zan siyo”.
      “Shi abun bashi da suna?”.
   Ƙasa tai da kanta tana tura baki batare datace komai ba.
“Kin kurumuce ne?”.
      Kamar zatai kuka tace, “Sirrine fa Yaya MM, kuma acan shagonne bada nisa bane”.
            “Koma ciki”.
    “Yaya zanfayi amfani da shine yanzu”.
      Ƙoƙarin zagayeta yay zai wuce da faɗin, “Idan kin matsu da koma miye sai ki faɗa kafin ki fitan”.
     Ƙafarta ta ɗan buga a ƙasa kamar zatai kuka sai kuma ta nufesa da sauri tasha gabansa. “Yaya Shareff dan ALLAH. Wlhy important ne”.
     “Inda important ɗinne da baki tsaya raimin wayo ba. Tashimin a hanya ko nabi ta kanki”.
    Matsawa ta ɗanyi ya raɓata zai wuce. Ganin da gaske tafiyar zaiyi tace “Audiga zan sayo”. Cak ya tsaya daga yunƙurin barin wajen, kamar wanda akaima tilas ya juyo yana kallonta. Sai dai ita nata kan a ƙasa sai faman ɓata fuska take dayin muy-muy da baki alamar akwai abinda take son faɗa koma take faɗar a zuciyarta. Harga ALLAH abinda ya fahimta zatai da audigan da ban. Dan haka ya dalla mata harara.
       “Duk audigan dake cikin First aid box’s ɗin gidannan kirasa audigan amfani sai kin fita saya? Bar nan kona mareki, mu nan ba’a mana fitan dare”. Kukane kawai ya rage bata saki ba. Har tayi niyyar yin zuciya sai kuma ta tuna halin da take ciki da wanda zata iya tsintar kanta kafin anjima kaɗan. “Yaya Please zanyi amfani da shine ALLAH”. Ransane ya ɓaci, ya ƙaraso inda take a fusace kamar zai kai mata mari ta zabura gefe. “Ina miki magana kina faɗamin zakiyi amfani da shine”. Ganin ya ƙaraso kanta ta zabura da gudu sai sashen Mom. Baiyi niyyar binta ba, sai dai kawai zuciyarsa ta kitsa masa ya amshe atm ɗin hanunta shiyyasa yabi bayanta. A falo ya sameta tana kumbure-kumbure Mom da su Salim zagaye da ita ana tanbayarta lafiya? Dan babu wanda yasan tama fita.
         “Wai bazakiyi magana bane Anam ana tambayarki kinyi shiru?”.
     Shigowarsa ta hanata bama Mom amsa, duk suka maida hankalinsu garesa yaran na gaishesa. Amsawa yay idonsa a kanta. Batare da yayi magana ba ya miƙa mata hanun fuska a tsuke. Ta fahimci mi yake nufi ta bashi dan haka ta zabura zata gudu.
     “Kika tashi a wajen nan sai kinyi kukan da baki taɓa yin irinsa ba bani”.
     Mom ta kalla idanunta cike da ƙwalla. Mom data kasa fahimtar inda suka dosa tace, “Babana miya faru ne?”.
    A taƙaice ya faɗama Mom abinda ya faru. Cikin mamaki Mom ɗin ta kalleta dan tasan dai Anam da tsoron dare, itada da dare yayi ko’a cikin gidan akace taje wani sashin aika saita nema ƴan rakiyya. “Anam”. Mom tai kiran sunanta. Ɗagowa tai ta dubeta sai kuma ta maida kanta ƙasa.
     “Ina zakije?”.
   A hankali tace, “Audiga zan siyo”.
Ɗan jim Mom ɗin tayi na nazari. Sai kuma ta girgiza kanta “Yanzu Anam har sai kin tafi siyen audiga basai ki tambayeni ba, idan ma babu ai za’a bada a sayo miki. Amma ko fitama bansan kinyi ba”.
    “Kiyi haƙuri Mom naje naga kina salla”.
    Girgiza kai kawai mom tayi, ta maida kallonta ga Shareff, “Ƙyale shashancin wannan Babana, nasan yanda zatai maka bayanin ne yay mata nauyi”.
     Janye idanunsa yay daga harar Anam ɗin, komai bai sake cewa ba ya fice. Binsa tai da kallo tana taɓe baki, sai dai shi baima san tanai ba.

                     ★★★★★★

   Kamar yanda Daddy ya faɗa game da matso da auren Shareff ɗin hakane ta kasance. Dan shirye-shirye aka cigaba da yi babu kama hannun yaro. Dama ankai komai gidan su Fadwa, sai gidansa daya rage a ƙarasama ayyuka wanda dama kamfaninsa keyin ginin shi kuma ya zana kayansa da kansa. Sosai yay busy a tsakanin, Anam ma wataran sai Ya Khaleel take bi ya sauketa ya kuma ɗakkota. Tana dai shan masifa idan ta makara. Ita dai yitake kamarma batasan hidimar da akeba a gidan, ko anko da aka fitar nata cewa tai bataso ita batason kayan zafin nan sai da Mom ta mata faɗa sosai randa zasuje wajen tela sannan ta yarda tabi su Aysha tanata kumbure-kumbure.

       ★Yau data kasance alhamis daya rage 1week bikin Shareff ƙarfe sha biyu ta baro wajen aiki sakamakon mura da take fama da shi. Dama cikin dauriya ta fita aikin har Khaleel na mata faɗa. Zazzaɓi daya rufeta ya hanata sukuni ga ciwon kai, Yaseer ne ya samu shugabansu yay complain aka bata damar zuwa gida. Karan farko data yarda ta shiga motarsa, dan tayi ƙoƙarin zame masa amma ya ɓata rai. Maimakon ma gida sai ya fara nufar asibiti da ita, taso masa magana ciwon da kanta keyi yasata hakura ta zuba masa ido kawai.
    Basu wani samun tangarɗar ganin doctor ɗin ba, kasancewar akwai sanayya tsakaninsa da Yaseer ɗin. Da ɗan mamaki Dr Jamal ke duban Anam ɗin, daga ƙarshe dai ya kasa daurewa ya jeho mata tambaya. “Anam baki ganeniba ko?.”
       Ɗagowa tai daga kwanciyar datai akan desk nasa ta ɗan dubesa, sai kuma ta maida kanta ta kwantar tana ɗan girgiza masa kai. Shiru yay yana kallonta na wasu daƙiƙu kafin ya cigaba da rubuta musu maganain ya bama Yaseer da tun tambayar da yayma Anam ɗin ya shiga tunani. “Babu wani damuwa Yaseer murane kawai kuje a sai waɗannan drugs ɗin tasha insha ALLAH fiver da headache ɗin zai sauka”.
   Godiya Yaseer yay masa da basa hannu sukai musabaha. Ya bisu da kallo lokacin da suke fita kansa a matuƙar ɗaure. Jiyay bazai iya haƙuriba ya ɗauka wayarsa domin lalubo abokinsa dan tabbatarwa. A kiran farko dai ba’a ɗaga ba, duk da yasan daliline ya hana hakan sai ya kasa daurewa ya sake kira….
      “Ai harna fara tunanin bazaka ɗaukaba nai tracing naka ninazo inda kake”.
      Daga can aka amsa da “Saikace wani ɓarawo”.
    Dariya Dr Jamal yay dakai hannu ya shafi gemunsa. “My Man ai baka da maraba da ɓarawon da ake nema ruwa a jallo yau a wajena. Dan nasan bazan iya haƙuriba”.
        “Ai dama koda yaushe kai ba haƙurinne da kai ba. Miya faru?”.
     “Muje a hakan bani da haƙurin. Wai dama mutuniyar ta shigo Nigeria amma ko labari?”.
            “Malam jeka kai tsaye kan maganarka waye mituniyar? Dan na kula kai baka gajiya da kwashe-kwashe”.
    “Oh ALLAH shaidar da kai min kenan? To Anam nake nufi. Dan yanzu suka bar wajena ita da wani yaro Yaseer ya kawota a dubata”.
          Ɗiff yayi kamar wanda ruwa ya cinye har Dr Jamal na tunanin kota yankene, wayar ya cire a kunnensa ya kalla, ganin yana online ɗin dai ya shiga faɗin “Hello! hello! Bakajina ne?”.
     Ɗin! Ɗinn! kiran ya yanke, bai wani kawo komai a ransa ba ya ajiye wayar da tabbacin bayaji ɗinne, shawarar daya yanke a zuciyarsa na anjima zaije har gida kawai ya sashi ƙin sake kira.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button