Mai gabatar da kara, Aliyul Abidin ya shaida wa kotu cewa tun farko sabani ne ya barke a tsakanin abokan biyu, Abbah Isah da Nura Ado Gaya a kan kudin wiwi Naira 200 inda Abba Isa ya dauki almakashi ya soka wa Nura a wuya lamarin da ya sa ya samu mummunan rauni Aminiya ta rawaito.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa na yin mummunan rauni, laifin da ya saba wa Sashe na 159 na Kundin Shari’a na Pinal Kod.
Mai gabatar da karar ya nemi kotun ta sanya wata rana don sake gabatar da wanda ake zargi a gaban kotun.
Alkalin Kotun Mai shari’a Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali, kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Yuli, 2022. An tsare wata kan ba bata gari mafaka a gidanta.
A wata shari’ar, Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gama PRP, ta bayar da umarnin tsare wata mata mai suna Rahma Hassan a gidan gyaran hali a kan zarginta da bayar da mafaka ga barayi da sata da kuma samun kayan maye a gidanta.
Mai gabatar da kara, Aliyul Abidin ya shaida wa kotun cewa, al’ummar Unguwar Na’ibawa ne suka yi kara a gaban kotun cewa Rahma Hassan tana bayar da mafaka ga wadansu mutane da ba su yarda da dabi’unsu ba, inda bayan binciken ’yan sanda aka samu kayan maye a gidanta da kuma wasu kayayyaki da ake zargin na sata ne.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa Rahma ta musanta laifuffukan, wanda hakan ya sanya mai gabatar da kara ya roki kotun ta ba su wata rana don su fadada bincike.
Sai dai lauyanta Barista Salim Mohammed ya roki kotu ta bayar da belinta rokon da kotun ta ki amincewa da shi.
Alkalin Kotun Mai shari’a Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin a tsare wacce ake zargin a gidan gyaran hali, kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Yuli, 2022.
[ad_2]