Leonardis din yana da matan aure guda tara, amma uku daga cin su kadai ya yarda da su, basa cin amanar sa.
Tsohon ya bayyana dalilin haka kabarin sa
Da yake magana da kafar Afrimax English, tsohon ya bayyana dalilin sa na yanke shawarar ginawa kan sa kabari, duk da cewa hakan bakon abu ne.
Ya bayar da labarin cewa, da akwai wani mutum attajiri wanda yake da mata shida, kuma mutane da yawa suna kaunar sa, a kauyen da yake.
A fadar sa
,” Wata rana sai wannan attajirin yayi tafiya domin kasuwanci, amma cikin rashin sa’a sai ya mutu a can. A maimakon iyalan sa su yi masa jana’iza irin yadda ya dace, sai suka bige da wawaso akan dukiyar sa, shi kuma suka sanya gawar sa a cikin buhu, daga karshe dai, sai matasan kauyen ne suka binne shi ba tare da akwatin gawa ba. “
Leonardis din bai ji dadin abin da ya faru ga wannan attajiri ba, shine ya sanya, ya fara sayo akwatin sa da kayan shaye-shayen bikin binne shi.
Har kayan da za’a sanya masa idan ya mutu ya tanade su
Ya shirya komai hatta kayan da za’a sanya masa, lokacin kawai yake jira, inda yace shi maza ne kadai zasu binne shi banda mata.
Asali LabarunHausa
[ad_2]