Labarai

Wata budurwa ta kone takardar degree dinta bayan ta kammala makaranta

Wata budurwa ‘yar kasar Malawi ta kakkabo kwalin shaidar digirinta inda ta banka masa wuta saboda kasa samun aiki da shi da tayi

A bidiyon kai tsaye da tayi a TikTok, Bridget Thapwile Soko tayi rera waka tare da zunden wadanda suka kasa bata aikin bayan shekaru hudu da kammala digirinta.

Sai dai kuma, Desmond Bikoko, shugaban jami’ar Exploit inda Bridget tayi karatu yayi hanzarin martani inda yace sun kwace digirinsu. Jaridar legit tace;

Bridget Thapwile Soko, budurwa ‘yar kasar Malawi wacce tayi digiri a fannin kasuwanci ta fito bainar jama’a ta bankawa shaidar digirinta wuta.

Ta matukar fusata ne saboda shekaru hudu da ta kwashe da kammala karatu amma bata samu aiki ba.

A bidiyon kai tsaye da tayi a TikTok, matashiyar budurwar ta rera waka tare da zunden duk wanda ya gaza bata aiki ko kuma ya ki gayyatarta tantancewa.

Tace gara ta kone kwalinw digirin amma ta adana satifiket don aurenta. Muryoyi da aka ji a bidiyon sun tabbatar da cewa akwai mutane a tare da ita kuma sun yi mamaki.

Jami’ar Expoit tayi martani

Sai dai, makarantar da tayi ta gagauta yin martani bayan labarin abinda Bridget tayi ya kai mata.

Kamar yadda shugaban jami’ar Expoit, Desmond Bikoko ya bayyana, yace budurwar tayi hakan ne don zunde tare da zolayar jami’ar.

A wasikar da aka rubuta ranar 21 ga watan Oktoban 2021, makarantar ta kushe abinda budurwar tayi tare da kwace kwalin digirinta.

Wani bangare na wasikar yace:

“Cike da takaici muka gane cewa kin nadi bidiyon ko a digirin da muka baki bayan kin kammala karatu a jami’ar Expoit kuma kika wallafa a soshiyal midiya.

“A fassarar da muka yi, kin yi hakan ne don tozartawa tare da bata sunan jami’ar.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button