Al-Ajab

Wata mata ‘yar shekara 18 ta jefa dan tsohon mijinta a cikin rijiya a Katsina

Jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina sun kama wata Maryam Habibu a ranar Juma’a.

 

An zargi yarinyar mai shekaru 18 da jefa dan tsohon mijinta mai suna Jamilu Rabi’u mai shekaru hudu a cikin rijiya.

 

Matakin da matar da ‘yar asalin kauyen Leko da ke karamar hukumar Danja ta jihar Katsina ta aikata, ya kai ga mutuwar dan.

 

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce wadda ake zargin ta je gidan tsohon mijin ta ne ta lallaba yaron zuwa wani wuri da ke kusa, ta jefa shi cikin rijiyar, ta kashe shi.

 

Maryam yayin da take zantawa da manema labarai ta ce tun da farko ta yi amfani da fartanya kan matar mijinta ta farko kuma har yanzu shari’ar tana nan a kotu.

 

Ita ma matar ta ce ta taba kona katifar da mijinta ya siyo ma ta saboda, ya kasa saya mata.

 

 

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button