BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO… 14

Typing????

❤‍????BABU SO….!!❤‍????
(Miya kawo kishi?)

      *_Bilyn Abdull ce????????_*

14

……….Ko parking bai gamayi ba da ƙyau a ƙofar gida ta buɗe motar ta fice. Ya bita da kallo harta shige gida. Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya saki tare da murmushi. Ikram ta fito tana masa bye-bye. Hanun shima ya ɗaga mata har lokacin da murmushin a fuskarsa. Motarsa ya tada tare dayin reverse yabar anguwar dan baizo da niyyar shiga ko’ina ba tunda ko wanka baiyiba. Ga Fadwa dake buƙatar taimakonsa ya baro tana barcin gajiyar daya tara mata a daren jiya wadda shi kansa barcin bawai ya ishesa bane ba, kawai dai sawun giwa ne ya take na raƙumi.

       Anam batai magana da kowa ba ta haye sama, tasan ɗakinta zai yuwu su Amrah na ciki yanzu, na Mamie ma tana jiyo maganar mutane a ciki. Dan haka tai wucewarta falon Abie. Nan kam kowa bata samuba, hakan ya bata damar kwanciyarta ta saki kuka mara sauti. Kuka tayi sosai bana wasa ba har barci ɓarawo yay awan gaba da ita batare data sani ba. Wajen sha biyu Abie daya shigo ya ganta ya shiga taɓa goshinta da tunanin ko zazzaɓin nata ne ya dawo. Amma sai yaji babu zafi jikinta. Idanu ta buɗe da suka maita nauyi dan kukan data sha. Ta dubi Abie ɗin dake mata murmushi. “Sleeping beauty na ta tashi”.
      Murmushi tai da tashi zaune. “My Abie good morning”. Ta faɗa a marairaice. “Morning Darling duk gajiyar bikince ta saki zuwa nan ɓuyan barci?”. Fuska ta ɗan ɓata. “Abie su Amrah basa barina nai barci mai ƙyau dan surutunsu. Gashi ƙasa nake kwana dan bana son kwana da kowa ɗakin ma ya mana kaɗan”.
    Murmushi kawai yay da shafa kanta. Sai kuma ya dubi idanunta da suka sake fitowa da ƙyau. “Mamana idanun nan kamar anyi kuka da su?”. Da sauri ta girgiza masa kanta. “Abie rashin barcine fa”. Bai gamsu ba. Sai dai baice komai ba. Itama mikewa tai da faɗin, “Bara naje nayi wanka”. Tai maganar da zuwa ta kama hanunsa ta sumbata. Da kallo kawai ya bita, dan yasan tayi hakane dan karya cigaba da tuhumarta akan kumburin idonta daya tabbatar kukane ya sakasu komawa hakan tunda ba yau ya santa ba.

        Ta fito wanka tana shafa mai Amrah ta shigo ta sanar mata tayi baƙo. Da mamaki take kallonta sai dai batace komai ba. Amrah ma ta juya ta fita abinta. A nutse ta ƙarasa shirinta ranta fal tunanin wanene?. Ba ta da mai bata amsa dan haka ta fesa turare da ɗaukar wayarta ta fito. Tayi ƙyau sosai cikin wando da rigar jikinta, sai siririn mayafi data yana a kanta. A wajenta wannan shigace normal saboda a inda ta tashi, sannan rigar bata kama jikinta ba ta kuma sakko har kan mazaunanta. A falo ta samu su aunty Mimi, har zata zauna Mamie ta harareta. “Bake naji ance anzo nema ba?”. Cikin ɓata fuska tace, “Ni banyi da kowaba fa zai zo Mamie”.
     Aunty Hamida tai dariya. “To ɗiyata kika sani ko a ƴan biki ne wani yay sau da baya?. Tashi kije dan da alama mun kusa dawowa wani shagalin insha ALLAHU”.
       “Hu’um aunty ALLAH ya kiyaye ni karatu ma zan koma”.
    Daƙuwa aunty Hamida tai mata. “Karatun gidan ku, a wannan shekarun naki ai aure ne ya dace ko dan kina ganinki ƴar ficika da ƙaramin jiki? Maza tashi kije ana ɓata masa lokaci”.
     Badan taso ba ta fito, Mamie na kiranta tazo tasa hijjab bama taji ba dan a fusace take da taikaicin koma wanene.
    
       Dr Jamal dake daƙilar waya ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonta. Itako kallo guda tai masa ta kauda idonta. Kujerar dake gefensa ya gyara mata, ta ƙaraso fuska babu walwala tana masa sallama. Amsawa yay murmushinsa na sake faɗaɗa. “Barka da fitowa gimbiyar mata”.
       “Ina yini”.
Ta faɗa a takaice.
  “Lafiya lau. Bismillah ki zauna mana”.
          Kamar zatace a’a sai kuma ta zauna.
    “Kiyi haƙuri nazo babu izini. Sai dai karki manta dama nace zan zo dubiya”.
     Ɗan murmushin yaƙe tayi, a taƙaice tace, “Babu damuwa”.
    Idanu ya ɗan kafeta da shi, a ƙasan ransa yana tattaro abinda ya dace ya faɗa. Ɗagowa tai ta dubesa itama fuska a murtike. Ya kauda nasa idon. Cikin zolaya yace, “ALLAH ni sai ma naji ina jin tsoronki kamar”.
      Haka kawai yanda yay maganar ya bata dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa shiko ya kafeta da idanu yana murmushi. A dai-dai nan aka buɗe gate ɗin gidan mota ta shigo. Su duka sukabi motar da kallo har lokacin kowanne da dariyar kan fuskarsa. Dr Jamal ya faɗaɗa tasa ganin Shareff, itako haka kawai sai da gabanta ya ɗan faɗi.
      Ya kai kusan mintuna huɗu bai fitoba idonsa kafe a kansu, sai dai shi basa ganinsa kasancewar tinted glass ne da motar. Murfin motar ya buɗe ya fito da nufin shigewarsa ya nuna bai gansu ba kawai. Sai dai Dr Jamal daya taso fuska ɗauke da murmushi ya hana hakan. Fara’ar dole ya ƙaƙaro yana mika masa hannu kamar yanda shima ya miƙamasa. “Ango! Ango!! Ƙyallinka dabanne”.
     “Haka dai kace”.
Shareff ya bashi amsa hankalinsa nakan Anam data ɗauke kai kamar bata gansa ba.
    “Haka ɗinne ma abokina. Dan ko kamshinka yau ya sake bunƙasa fiye da kullum. Muma dai gamu nan fara kafa foundation mukai matsayin nan naku haka nan”.
         Gabansa ne ya fadi, amma sai ya dake ya saki gajeren murmushi. “ALLAH yasa haka to.”
     “Insha ALLAH wannan karon da gaske nake abokina”.
   Nan ɗin ma murmushin yayi kawai da faɗin, “Bara na shiga na gaida su Mamie”.
       “Okay to a fito lafiya”.
Ido suka haɗa da Anam ya wulla mata wani mugun kallo data jima bata gani daga garesa ba ya wuce. Dr Jamal daba lura yay ba ya dawo ya zauna yana dariya. “Kinga Yayan nan naki da gaske angwancin nan fa ya amshesa. Kwana daya kacal harya canja kamar bashi ba”.
       Ƙin cewa komai tayi, sai dai tayi ƙaramin murmushi. Shima murmushin yayi yanaji kamar ya haɗiyeta. Sallamar Amrah ta katsesa daga kallon da yake mata. Duk suka dubeta. Gaishe da Dr Jamal tai, ya amsa cike da fara’a da tambayarta gajiyar biki. Tace masa Alhmdllhi tana maida kallonta ga Anam. “Anam Yaya Shareff yace yana jiranki zai amshi ajiyar daya baki”.
      Kallon Amrah take cike da mamaki da rashin fahimta, sai dai ta rasa abin cewa. Sai Dr jamal dake kallonsu ne ya katse shirun da faɗin, “Inaga jeki kawai ki basa saƙon sai na jiraki. Dan da muhimmiyar magana nazo”.
          Kamar zatace ita babu wani saƙonsa a wajenta sai tai shiru kawai. Ta mike zuciyarta na mata kaikawo da mamakin Yah Shareff ɗin. Yaushe ma har suka fara shiri dazai bata wani ajiyar abu..? Ita kaɗai ta nufi hanyar falon, dan Amrah fita tai dama cikin gida zata ya bata saƙon. Ta shigo ɗan lungun dazai sadata da ƙofar falonsu ya kuma zama hanyar dake tare data garden taji an fusgota. Ihu tai niyyar yi yay azamar rufe mata baki. Sai da ya maida ƙofar ya rufe sannan ya saki mata baki yana binta da wani shegen kallo data kasa fahimtar na minene.
     Baki ta tura tana gyara mayafinta. Ya sake harararta da binta da kallon sama da ƙasa fuskarsa a tsananin ɗaure. “Daga yau na ƙara ganinki da wannan banzar shigar gaban kowane ɗan iska ki tabbatar saina ɓaɓɓalaki na zubar. Ki kuma koma ciki, kona haɗa k da shi na zafafa. Tashi min anan kona kashe fuskarki da mari stupid”.
      Da gudu tabar wajen hawaye na silalo mata. Yaja tsaki mai kauri yana furzar da zazzafan huci daga bakinsa. Fitowa yay daga garden ɗin ya nufi falon shima dan dama ko shiga baiyi ba. Zama yay suna gaisawa da su aunty Mimi da ƴan uwan Mamie dama Abie ɗin. Kasa haƙuri sukai sai da suka tambayesa ko lafiya? Dan yanayinsa ya nuna ransa a ɓace yake. Ya kaƙaro murmushi yaƙe yana shafa kansa. “Bakomai fa auntys karku damu. Gajiya ce kawai da bata gama sakinmmu ba”.
      Mamie dake fitowa a kitchen tai yar dariya.  “To banda abun babana aida basai mun gankaba yau, sai kai zamanka ka huta sosai a gida ko”. Kansa ya shafa yana ƙara risinarwa. “A’a Mamie gara dai nazo na dubaku kuma hankalina zaifi kwanciya ai”.
     “To shikenan ALLAH yay maka albarka yaya ɗiyar tawa itama?”.
    “Lafiya lau tana gaisheku da muku bangajiya.”
          “Duk muna amsawa”.
Bai wani jima sosai ba ya fito, a waje ya sake samun Dr Jamal. Ya nufesa fuskarsa kadaran kadahan. Shiko Dr Jamal tasa kawace da murmushi. “A’a ango mijin amarya Fadwa har ka fito kenan?”.
       “Eh, ina so na ɗanje na sake hutawa kasan gajiyar biki. Kaima nayi mamakin ganinka anan kai da ya kamata ace kana can kana kwasar barci”.
       “Tab barci ai sai ku angwaye. Muko kwanciya mutum yayta rungumar fillos ai da gajiya. Gara mu fito farautar namu kayan kamar zaifi”.
            “Hakane, amma sai naga baka tafi farautar ba ai”.
     “Kajimun ɗan iska mi kazo kaga inayi? Inama take? Tunda kai akace kana kiranta”.
              Fuska ya ƙara tsukewa da ƙyau yana kallon Dr Jamal ɗin. “Yaka kafeni da idanu kamar naci bashinka?. Tunda kace babu ruwanka ni nazo da kaina na kafa gwamnatina”. Kansa ya kauda yana jan karamin tsaki. Kafin ya dawo da kallonsa garesa. “Jamal amma kasan bana son jan raini ko? Duk manyan mata dake garin nan da suka amsa sunansu mata karasa wa zaka so sai wannan ƴar abar haihuwar jiya”.
      Dariya sosai Dr Jamal keyi, “Oh badai an haifeta jiyan ba? To ni wlhy ko yanzu aka haifota ina son kayata a haka. Yarinyarnan ta haɗa duk abinda nake so ga matar da nake fata ta zama abokiyar rayuwata. Ni bana ganin waɗancan manyan matan sam a idona. Kai dai tunda ka ɗauka taka barni nima lokacina ne”.
     Tsaki yaja mai karfi da barin wajen. Dr Jamal ya bisa da kallo yana murmushi. “A gaishe da amarya sai munzo cin cin-cin”.
     Bai tanka masa ba, bai kuma juyoba ya shige motarsa ya fice. Agogo shima Dr Jamal ɗin ya kalla. Ganin lokacin da Anam taci babu alamar zata fito yay tunanin bara kawai ya wuce ya dawo anjima da dare. Yaran Aunty Hindu dake can gefe suna wasa ya kira babban. Leda dake dauke da kayan ciye-ciye na kwaɗayi ya bashi yakaima Anam ɗin shi kuma ya nufi motarsa…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button