WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 2

Cikin rawar murya irin na tsoro ta ce “Anty wasu abubuwan? 

Gasu can kusa da bango, waɗanda na kashe, basu zo sun kwashe abin su ba”

“Na shiga uku, ni banga komai ba, waiyo shi yasa fa ban cika son shigowa dakin ki ba”

Ɗan dariya ta yi,”to ai sun mutu,kuma sune masu zuwa suna jamin riga kullun wai in zo  mu tafi,shi yasa kike ganin ina ɗaukar tsanda kullun dashi kuma nake kashe su,kin gansu ma su kan mutane amma jikin su irin na Ƙadangare,kin ga can guda shidda ne waɗanda na kashe”

Kuka ta fara”waiyo Allah ni dai zan wuce ”

“Ke ba abin da zasu miki”

“Kin tabbatar”

“Eh, kar ki damu”

Ajiyar zuciya ta sauke,sannan suka ci gaba da hiran su,

Zawa can kuwa sai ga yaro ya yi sallama a ƙofar ɗakin, amsawa suka yi, shigowa ya yi “Anty Asma’u gashi wai in ji Malam a kawo maki” Ansa ta yi “na gode Abbati, yana ina ne? 

” Ya wuce, ni ma har ya bani Sweet ”

“To ka gode,” Juyawa yayi ya fita, yayin da ita kuma ta buɗe ledan, gasasshiyar Nama ce wanda aka barbade shi da garin  yaji, buɗe masu ta yi,nan suka shi ga  ci suna hira”ni kam Antyna me yasa a da kika auri Malam,bancin na  san abaya ma ki nada masoya masu son ki da yawa, duk da ke ba wata mai kyau ba ce,,amma mutum bai isa ya raina maki ta ko ina ba? 

Dariya ta yi tana tura tsokan nama a bakin ta”Hafiza ke nan, na Aure shi ne kawai saboda ina son shi, kuma a lokacin ina ganin shi yafi dacewa da ni,, kasancewar shi Malami, ya san duk wani abu mai kyau da mara kyau da ke tsakanin Aure,”tsayawa ta yi da taunar Naman, a lamun abin na ci mata rai”sai dai ashe banan gizo ke saƙa ba,a kwai abin da ban sani ba,ki duba fa saboda tsabar rashin tausayi da imani,in dauki ciki tsayin wata tara da kwana tara, amma ace ranar dana haihu, a ranar aka kashe min jariri,ba a barni haka ba,shi harda niman rayuwa ta,a gaskiya na yaudare kai na,amma ba komai hakan ƙaddara ce, kowa da irin na shi “ta karasa fada tana share guntun hawayen ta. 

” Karki damu Antyna Allah zai saka maki,kuma zai baki miji wanda sai kowa yayi mamakin irin shi,sai maƙiyanki sun girgiza da jin koda suna mijinki aka kira”

Dariya ta yi “taya hakan zai kasance kuwa”

“Karki damu Antyna cikin ikon Allah, ba gashi ba an samu nasara bayan uwar gwagwarmaya an samu Malam ya sake ki da kyar”

Ajiyar zuciya kawai ta sauke ba tace komai ba. 

Daganan hira suke yi jifa-jifa har huɗu ta yi, sannan tai mata sallama ta wuce dan zuwa Islamiya.????WATA TAFIYAR????

       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                  Free Page    

               02

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

  Nasiha sosai ya yi masu,wanda sai da ya tabbatar da jikin su ya yi sanyi sannan ya ma Nanne sallama ya fita. 

Share guntun hawayen ta ta yi “Nanne ni zan koma, sai zuwa anjima”

“To Fettel Allah ya ƙara kare ki”

“Amin Nanne”shiyan su ta koma,cikin natsuwa ta kammala karyawa,ta dauraye kopin,sallama ta yi dakin Inna Saude wacce har zuwa lokacin suna zaune suna hira da Baba duk da sun gama karyawa, yara kuma duk sun tafi makaranta. 

” Inna ga kofin”

“To ajiye nan Asma’u”

Kasancewar ta ga takalmin Baba a ƙofar yasa ta ce “sannu Baba” Banza ya yi da ita kamar bai jita ba, 

Ƙara mai matawa ta yi “sannu Baba”

Cikin hasala ya taso mata “haba mana ke wacce irin yarinya ce,kin ce sannu na kyale ki,kin kuma cewa, to ba sai ki rabu da ni ba, aikin banza kawai, 

Dukar da kai ta yi bata ce komai ba,dan indai wannan ne ta riga ta saba gani daga wurin Baba Ɗan Nanne,tashi ta yi ta koma daki tana tunanin me ta tsare mashi haka cikin waɗannan watanni gaba ɗaya ya sauya,dama ba wani dasawa suke sosai da shi ba,amma kuma abin be kai  haka ba. 

tana ganin ta wuce,ta dawo da kallon ta kan shi, 

“Hana Ɗan Nanne, me yasa kake ma yarinyar nan haka ne,bayan ta kasance amana ce a wurin ka”

“Da yaushe ta zama amana a wuri na,to ban dai sanan ko a wurin ki take amana ba,? 

“kar ka manta Asma’u ƴa ce a gareka ko ka ki,ko kaso,domin ɗiyar ƙanwar ka ce,uwa daya uba daya, dan haka dole a kira ta da taka, ni sam wallahi ba na jin daɗin irin yanda kake da yarinyar nan,dan Allah ka dunga sassauta mata”

Turbune fuska ya yi “ina fatan dai kinsan da cewa Uwarta ba mutuwa ta yi ba,kinsan duk abin da ya faru,haka kawai muna fama da kan mu zata kawo mana jinjira ta tsallake ta yi tafiyar ta,yau  kusan shekara nawa ke nan,shekara ishirin da biyu,dan ba zan taɓa mantawa ba,menene dalilin ta nayin haka,shi ne har zaki ce na rinka tausayin ta, ina tsinannun dangin Uban ta,tunda abin ga ya faru kin ga kafar wani acikin su, dan haka ki kamamin bakin ki,nasan abin da nake kuma baƙi isa  ki sa na canza daga yanda nake ba”yana kaiwa nan ya tashi fuww ya bar mata ɗakin, shiyar Nanne ya nufa domin zuwa ya gaishe ta, dan bai samu shiga da suka dawo masallaci ba. 

Da “Allah ya kyauta” Kawai ta bi shi, dan ita kan har ƙasan zuciyar ta,Asma’u kamar ƴar take a wurin ta,kuma tana son yarinyar sosai kamar yan da take son Uwar ta,dan sun yi abotar arziki sosai da ita, shi yasa a koda yaushe take matukar tausayin yarinyar a duk lokacin da ta kalle ta,gaskiya Asma’u ba ta yi dacen aure za tace ba,ko kuwa yama zata saka abun oho, tun da miji na bala’in son ta,kai wannan abin sai dai muce Allah ya mana maganin shi. 

Ganin ta gaji da zaman ne yasa kawai sa Hijabin ta ta fita,lekawa ta yi ta ce ma Inna ta leka gidan su Asiya, a dawo lafiya ta mata, 

  Da sallama ta shiga gidan, Maman Asiya ce ta amsa mata dan haka gaishe ta ta yi “Mama Asiya na ciki kuwa”

“Ban sani ba amma bari in duba”daki ta shiga, zaune ta tadda wata ƴar budurwa wacce za ta zo tsara da Asma’u, tana ganin shi gowar Maman ta, da sauri ta rike mata hannu” Mama dan Allah ki taimake ni,ki rufa min Asiri,ba zan ina ko da zama kusa da Asma’u ba, dan wallahi tsoron ta nake ji, kar tazo  muna hira ta shaƙe ni,kan a kawo min dauki na mutu”

Saura kaɗan Maman ta ta fashe da dariya, ganin yanda Asiyar ta rike mata hannu gam kamar ta ce dole sai  ta je, gashi sai wani zazzare ido take yi, 

“Amma ai naga ƙawar ki ce,tun da tare kuka tashi,ko ba komai akwai kauna a tsakanin ku”

Da sauri ta katse Maman”a da kenan, amma ba yanzun ba,Mama har kin manta irin zanan da na sha da daddare,daga abin arziki,dan kawai na ce zan amso mata tai mako wurin Kawu na,shi ke nan cikin barci a ka min dukan tsiya sai da na tashi ranar jikina duk a farfashe,ni ce har dasu karin ruwa, 

Kuma Mama kun san ba ni kaɗai suka ma haka ba,duk wanda suka ji ya ce ya san wani mai magani ranar sunan mutum Sorry dan ba karin duka da matsa zai sha a hannun suba, to Mama ina dalili, haka kawai ba su samu damar kashe taba, kai dan kallo su wuce da kai, dan haka ki taimake ni, ki ce mata kawai bana nan ”

 ‘Shi kenan “ko da ta fito a tsaye ta same ta in da ta bar ta, nan take Shai da mata Asiya bata nan ” To, Mama sai anjima, in ta dawo ki gaishe ta”tana gama fadar haka ta juya ta fita,dan tsaf ta ji komai da Asiya ke faɗi,ita kuma har ga Allah bata ganin lefin mutane dan sun guje ta,a ganin ta da gaskiyar su, tun da bamai son wahala a rayuwar shi,balle Aljannun ta su wahalar da shi,kasancewar Asiya irin matan nanne masu buɗaɗɗen murya,sha yasa ta ji  duk abin da suke faɗa.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button