WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 2

Tana fitowa ƙofar din,samari ne zazzau ne a ƙofar gidan su,wato kofar digan Ɗan Nanne,wasu daga cikin su wadanda ta girma suna ganin suka shiga gaishe ta,yayin da ita kuma ta gaishe da wadanda suka girmeta a wurin,cikin  wasa daya daga cikin su mai suna Muntari “Anty Asma’u mai zan samu ne,dan wallahi ko ƙari ban yi ba”

Murmushi ta yi tana fito da hannun ta daga cikin Hijabi “zoka amsa” Ta faɗa tana mika mashi Naira ɗarin data kwana da shi.

Amsa yayi yana dariya”to bari in cire Hamsin sai in baki canji”

“Ka barshi kawai” Ta ce tana shi gewa cikin gidan. 

Sauran Samarin dake wurin ne sukai mashi caaa a kai”haba Muntari,baka da tausayi ne,yarinya na fama da kanta amma zaka raba ta da ɗan kuɗin ta, kai baka ɓata ba amma shi ne har da wani amsar mata”

“Kar ku manta Asma’u kamar yaya take a wurina,kuma da kuke cewa haka na tabbatar da kun san halinta,in dai zaku faɗa gaskiya,ko da ace na amsa Hasim din nan ko ban amsa ba zata kyautar da shi ne,dan ita abin ta baya tsole mata ido, ko da kuwa shi kaɗai ya rage mata,kuma ma tabbatar koda ku kuka tambaye ta in tana dashi zata baku, bare ni,”

Duk shiru suka yi dan sun san gaskiya ya faɗa,kai Allah dai ya bata lafiya, da Amin suka  amsa. 

 Tana shiga gida ɗakin ta ta koma,zama kawai ta yi,daga nan sai gyangyadi, dan kamar yadda take kwana ba bacci haka ta ke yini bata yi,sai dai gyangyadi, dan bata isa ta kwanta ba,dan tana kwanciya za su hau damun ta,da iyayyaku dole ta tashi,rashin bacci masifa ce,shi yasa idan abun ya ishe ta koda rana zaka ji tana kuka tana ihu,”waiyo  ku ƙyale ni barci nake ji”to ranar haka take yini,sai in Baba Mudansir zai zauna yana mata karatu shine fa zata samu damar bacci.

zuwa ƙarfe uku kuwa sai ga Hafiza ta shigo,,cikin jin daɗi kuwa ta tare ta, 

Zama ta yi kuwa suka fara shan hira, zuwa can daɗin hira yasa ta mike kafa har yana kusa taɓa bangon dakin,,kallon ta Asma’u ta yi “Hafiza ki yi a hankali kar ki taka waɗancan abubuwan da na kashe” wani uban tsalle ta daka sai gata manne da jikin Asma’u. 

Cikin rawar murya irin na tsoro ta ce “Anty wasu abubuwan? 

Gasu can kusa da bango, waɗanda na kashe, basu zo sun kwashe abin su ba”

“Na shiga uku, ni banga komai ba, waiyo shi yasa fa ban cika son shigowa dakin ki ba”

Ɗan dariya ta yi,”to ai sun mutu,kuma sune masu zuwa suna jamin riga kullun wai in zo  mu tafi,shi yasa kike ganin ina ɗaukar tsanda kullun dashi kuma nake kashe su,kin gansu ma su kan mutane amma jikin su irin na Ƙadangare,kin ga can guda shidda ne waɗanda na kashe”

Kuka ta fara”waiyo Allah ni dai zan wuce ”

“Ke ba abin da zasu miki”

“Kin tabbatar”

“Eh, kar ki damu”

Ajiyar zuciya ta sauke,sannan suka ci gaba da hiran su,

Zawa can kuwa sai ga yaro ya yi sallama a ƙofar ɗakin, amsawa suka yi, shigowa ya yi “Anty Asma’u gashi wai in ji Malam a kawo maki” Ansa ta yi “na gode Abbati, yana ina ne? 

” Ya wuce, ni ma har ya bani Sweet ”

“To ka gode,” Juyawa yayi ya fita, yayin da ita kuma ta buɗe ledan, gasasshiyar Nama ce wanda aka barbade shi da garin  yaji, buɗe masu ta yi,nan suka shi ga  ci suna hira”ni kam Antyna me yasa a da kika auri Malam,bancin na  san abaya ma ki nada masoya masu son ki da yawa, duk da ke ba wata mai kyau ba ce,,amma mutum bai isa ya raina maki ta ko ina ba? 

Dariya ta yi tana tura tsokan nama a bakin ta”Hafiza ke nan, na Aure shi ne kawai saboda ina son shi, kuma a lokacin ina ganin shi yafi dacewa da ni,, kasancewar shi Malami, ya san duk wani abu mai kyau da mara kyau da ke tsakanin Aure,”tsayawa ta yi da taunar Naman, a lamun abin na ci mata rai”sai dai ashe banan gizo ke saƙa ba,a kwai abin da ban sani ba,ki duba fa saboda tsabar rashin tausayi da imani,in dauki ciki tsayin wata tara da kwana tara, amma ace ranar dana haihu, a ranar aka kashe min jariri,ba a barni haka ba,shi ne harda niman rayuwa ta,a gaskiya na yaudare kai na,amma ba komai hakan ƙaddara ce, kowa da irin na shi “ta karasa fada tana share guntun hawayen ta. 

” Karki damu Antyna Allah zai saka maki,kuma zai baki miji wanda sai kowa yayi mamakin irin shi,sai maƙiyanki sun girgiza da jin koda suna mijinki aka kira”

Dariya ta yi “taya hakan zai kasance kuwa”

“Karki damu Antyna cikin ikon Allah, ba gashi ba an samu nasara bayan uwar gwagwarmaya an samu Malam ya sake ki da kyar”

Ajiyar zuciya kawai ta sauke ba tace komai ba. 

Daganan hira suke yi jifa-jifa har huɗu ta yi, sannan tai mata sallama ta wuce dan zuwa Islamiya.

   Tana shiga shiyar su ta haɗe da Maman ta,, Inna Ladi”ke daga ina kike tun dazu na aika yara su dubo min ke, amma sun dawo basu ganki  ba? 

Dariya  ta yi “laa Mama ai ina wurin Anty Asma’u, harma Malam ya aiko mana da Nama da yawa muka ci”

Wani irin finciko ta Inna Ladi ta yi, ta shiga duka kamar ta samu kayan wanki,tana yi tana haɗawa da kai ma bakin kulli”amma dai ba  kiɗa hankali Hadiza, yanzun har Malam din ne zai kawo mata abu ciki, dan ba kiɗa hankali, an faɗa maki shima  Malam din ya bar ta haka ne, yar banzan yarinya, duk abin da kika ga yana ba ta sai yayi mata barbade a kici,in ba haka ba taya za ayi bayan an raba auren su, da zaran ta gama ci zuwa anjima kaɗan zaki ga ta kwaso kayanta tana ma mutane hauka zata koma gidan Malam, wato so kike ki Jaza mana bala’i ke ma ki ce sai Malam din ko, to baki isa ba ”

Baba Sani ne wanda shigowar shi kenan ya tadda ana dukan Hadiza, nan ya ke tambayar dalili, nan Ladi ta faɗa mashi abin da ta yi, ran shine ya ɓaci,, cewa yayi Inna Ladi ta ƙara mata ta yanda gobe ko hanyar shiyar ba zata gane ba.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button