WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 4

 ????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                  Free Page    

               04

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

   Yana fita daga falon,mota ya shiga ya ce ma direban ya kai shi gidan shi na London Street dan yana son ya huta, 

 To a haka dai wannan taron ya tashi,su na masu sa dukkan yardar su da yaƙinen su akan Haris Zamir domin ya zamo masu tsanin da zasu hau domin cikar muradin su.

Shima a na shi ɓangaren hakan ne, tabbas ya kamata ya jajirce a wannan karan,lokaci ya yi da ya kamata ya fuskance shi,kuma tare da kyakkyawar Albishir,gaskiya kan su Uncle Ahmad na ja,wannan shawara ce mai kyau,abin ba karamin ƙayatarwa zai yi ba,kai wa yaga su Oh Oh da Amarya,dariya da bai shirya mashi bane ya fito,kuma bai hana kan shi yi ba ya shiga kyakyatawa,sai da yayi mai isan shi harda share guntun hawaye, nan take kuma ya kara ɗaure fuska kamar bashi ya gama wannan dariyar ba. 

Shi dai direba bai ce komai ba duk da irin dariyar da ya ji uban gidan shi na yi, wannan ba abun mamaki ba ne idan ya tuna waye HARIS ZAMIR,

tuna wani shudadden zamani da ya wuce,yasa ɗan guntun hawaye suka sauko mai,da sauri yasa hannun shi ya share,Allah sarki wani kaya sai amale,Allah dai ya kai rahama gareka a duk in da kake ZABIHULLAH ZAMIR,an ce mana ka mutu shekara uku da suka wuce,amma har yau ba a samu gawarka ba,,

har cikin madai-daicin gida suka shiga wanda kallo daya zaka ma gidan kasan ba ƙaramin baje fasaha aka yi a wurin gina shi ba.

   Gidan Ɗan Nanne

“Me haka kuke yi ne, maza zo ku fita”

“Baba mun zo ne fa gaida Nanne” Cawar  Salma. 

“To in kun gaishe ta  ku zo ku wuce” fita suka yi suna turo baki, dama ba kunya ya ishe su ba.

Juyoda kallon shi ya yi kan Asma’u,ganin abin da take yasa kawai ya girgiza kai,sannan ya dawo kusa da Nanne,hannu ta ya riƙe “me ya faru kike kuka haka Nanne? 

Fyace majina ta yi” yanxun ɗan nan baka ganin abin da Fettel ke yi,kana gani kuma haka zamu sa mata ido? 

Ajiyar zuciya ya sauke, Allah ya gani yana iya bakin ƙoƙarin shi akan wannan lamarin na Asma’u,to ya za su yi har yanzu basu dace da wanda yafi karfin waɗannan shaidanun ba,”Nanne ki kwantar da hankalin ki,insha Allah za a dace idan aka ci gaba da addu’a,sannan ki daina mata kuka tunda ke ma Nanne kinsan da kan ki wannan ba halin Asma’u ba ne, ba daɓe arta ba ce, duk wannan abin da ki kaga tana yi ba yin kanta ba ne, dan haka ki kwantar da hankalin ki,komai zai yi dai-dai ”

Gyaɗa kai ta yi “shi kenan Allah yasa a dace”

“Amin Nanne”tashi yayi ya tsiyaya kunu a cofi da yawa,sannan ya je ya zauna kusa da Asma’u,kallon shi take amma ba ta ce komai ba, domin duk rashin kunya da take yi da zaran Baba Mudansir zai zo wurin to an gama magana,dan tsaf za ka ga ta natsu,kamar dai yanzun, 

“Je ki yi Alwala ki yi sallah” ba ta ce komai ba ta tashi ta fita,zuwa can kuma sai gashi ta shigo a jike a lamun ta yi Alwalla, Hijabin Nanne ta dauka,sallah ta yi duk suna kallon ta,tana idarwa ta dawo kusa dashi ta zauna, mika mata Kunun ya yi wanda ya dan sha iska saboda zafi,a hankali take sha har ta kammala sannan ta mika ma shi kofin, 

Murmushi ya yi “Allah ya miki Albarka, ya baki lafiya, ya kuma nuna min sanda za kalle ni ki yi dariya kamar da,ki ce Baba  Mudansir ka yi kyau yau,ko kuma idan ki kaga ina fushi ki ce yau waya taɓa min Baba na”

Saukar hannun ta kawai ya ji a fuskar shi tana share mai hawaye, wanda bai masan da zubar su ba,tana gama share mai ta tashi ta fita,shiyan su ta koma.

        Bayan kwana uku

Zaune yake a bayan mota, yayin da Habu  direba ke jan shi,gidan Uncle Ahmad za shi dake unguwar El-Amin, tun dazu ake kiran wayar Habu amma ya kasa ɗauka saboda sarai ya san  halin Haris,jin ƙarar wayar ya dame shi ne yasa ya ce “ka ɗauka mana kana damuna”

Da sauri ya ɗauka dama tsoron shi ne ya hana ya ɗauka, dan yaga sunan Baba Mudansir a rubuce, “Ayi min afuwa yallabai”

Shi dai bai ce komai ba. 

Sallama yayi,bayan ya ƙara wayar a kunne,can kuma da ɗan ƙarfi ya ce”Baba wata Asma’u ne ba a gani ba”dan shiru ya yi, sai kuma ya ci gaba da magana”ka yi hakuri Baba yanzun ina wurin aiki ne,amma dana tashi zan biya in dubota,shi kenan”

Sauke wayar ya yi a kunne yana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi

“Me ya faru”

“Wallahi yallabai wata ƙanwa ta ce dake da dan matsala,to wai sun fita ita da ƙanne na wurin walima amma basu ganta ba”

“Har ina ne wurin,kuma sun duba da ƙyau kuwa? 

” shi ne ban sani ba yallabai,gashi kuma dama yarinya ba ta da lafiya”

“Shi kenan juya motar mu je a duba ta”

Dan juyowa ya yi ya kalle shi da mamaki,wanda har ya ja ya ƙasa yin shiru, sai da ya ce “da gaske yallabai”

Banza ya ma shi, ganin hakan ne yasa da sauri ya juya kan motar,suka nufe unguwar Limawa,dan a can suka je walimar,dan tsakanin unguwar Daji, da Limawa babu nisa,dan da kafa ma mutum zai je, dan babban Titi ne kawai ya raba tsakanin unguwanni biyun.

Kiran Baba ya yi ya ce a tambaya su Maimuna wani Layi ne suka je, da kuma kalar Hijabin da Asma’u ta saka,wayar Baba ya ba Maimuna ta mai bayani,

Duk inda suka samu camba yakan fita ya tanbaya,a haka har suka kusa zagaye Layukan dake cikin unguwar,ganin kamar yana batawa Haris din lokaci ne,yasa kawai ya yanke ya kai shi in da zai je, in ya so shi sai ya dawo yaci gaba da niman ta,tunda su waɗancan sun ki,wai sun gaji,fisabililah in da daya daga cikin dan ɗakinsu ne hakan ta faru da shi da tuni sun hargitsi gidan Ɗan Nanne,amma da yake Asma’u ce, shi yasa kowa yayi likimo,harsun kusa fita layin ƙarshe ya hango wata yarinya na niman tsallaka Titi, har zai wuce sai kuma yaga kalar kayan da Hijabin,da sauri ya faka motar. 

Jin motar ya tsaya,yasa ya go kai”lafiya ”

“Yallabai kamar ga ta can,amma barin in tabbatar” da sauri ya fita ya nufi in da take tsaye sai faman leken titin take amma ta kasa tsallakawa, 

Kiran sunanta yayi”Asma’u ”

Jin yanda aka kira sunan ta da ƙarfi ne yasa ta juyo,ganin me kiran ta ne, yasa ta shiga washe mashe baki”laa Yaya Habu”

Tsabar haushin data ba shi,yasa yana karasowa tun a nan ya hau mata matsifa kamar zai mareta, 

Turo baki gaba tayi “bancin wucewa suka yi suka barni, wai ba zasu jera dani ba, shi yasa na zauna a ta baya da ake walima,kuma koda aka tashi ina ta niman su ban gansu ba”

Tsaki ya ja”wawuya kawai! Dalla zo mu je,in Oga na ya yarda ki shigar mashi muta to sai in sauke ki bakin Joction ke karasa gida”

Ita dai ba ta ce komai ba ta bi bayan shi,a bayan shi ta tsaya,, shi kuma ya dan ƙwanƙwasa Glass din windo kaɗan. 

Tun daga lokacin daya fara mata masifa ya ke kallon ta, yana kuma nazarin ta a takaice, masha Allah ya furta a hankali saman labban shi,cikin natsuwa ya ke ƙare mata kallo yayin da suka tun karo in da yake, 

“Yallabai in ba damuwa ɗan Allah zamu iya ajiye ta bakin joction”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button