MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 56

 

*Page 56*

……….Sai da ya tsaya yay sallar azhar a hanya sannan ya ƙarasa gidan. Tun daga falon farko yake jiyo dariyar su Meenal da Jamal. Ya ɗanyi shiru na wasu 

sakanni a wajen amma baiji muryar Zinneerah ba ko sau ɗaya, firar tasu kuma dukta makaranta ce Nawaf na basu labarin makarantarsu ta Turkey shima. Kamar zai 

nufi can sai kuma ya fasa ya ɗauka hanyar sashensa.

         Khalipha dake zaune yana kallon television a falon nasa ya ɗago yana amsa masa sallamar da yayi. Cikin falon ya ƙaraso yana faɗin, “Am sorry besty 

na barka jira ko?”.

     “No babu damuwa Yayanmu, nima ban wani jima da zuwanba sai da na biya ta asibiti”.

      “Thanks”.

Yace masa kawai yana nufar hanyar bedroom ɗinsa. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito sanye da ƙananun kaya da alama waɗan can ɗin sun damesa. Yana zama 

Khalipha ya miƙe ya buɗe fridge ya ɗakko masa ruwa.

    “Thanks Darling”.

Murmushi Khalipha yay kawai ya koma wajen da yake ya sake zauma. Sai da AK yasha ruwan sosai dan ƙishirwar yakeji dama. Kofin ya ajiye yana gyara zamansa 

ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ƙara komawa serious.

      “Khalipha akan maganar da muka farone ranar, inason ka amsa min wasu tambayoyi”.

      “Okay Yayanmu kaimin, inhar na sani zan baka amsa insha ALLAH ”.

    Kansa ya jinjina masa da kai hannu yaɗan shafo sajensa zuwa gemu. “Yanzu idan nace kamin bayani akan dashen cikin gaba ɗayansa zaka iya?”.

      “Zan iya Yayanmu, sai dai zai cimana lokaci matuƙa, kai kuma nasan bakason a cinye maka lokutanka”.

     Sassanyan murmushi yayi yana ɗauke kansa daga Khalipha ɗin. “Ai wannan nine na bashi lokacin da kaina, sai dai kuma barsa kawai muje ga tambayoyin zasu 

wadatar dani insha ALLAH ”.

      “Okay Yayanmu ina saurarenka to”.

      Ɗan jimm yayi na wani ɗan lokaci kamar mai nazari, kafin ya duba Khalipha da ƙyau, “Bani bayani a taƙaice ta yanda za’a iya dashen cikin?”.

      Zama sosai Khalipha ya gyara da nutsuwa. “Abunda kake magana ana ce mishi artificial insemination Yayanmu. Ana daukar maniyyi namiji (semen) a tace, a 

ɗauki sperms sai a haɗa da Kwan mace (ovum). Shi Kwan mace sai an shirya ake ɗaukan shi shima, anabada magunguna kafin ayi hakan, sannan ba haka kawai ake 

ɗauka ba sai an duba lokacin da matar take ovulation, ma’ana Kwan yayi girma sai ayi amfani da na’urar scanning a ɗauka. Ta Mara ake ɗauka bata al’aura ba, 

sai a haɗa a Laboratory (invitro fertilization). Idan anyi sa’a an samu fertilization sai a ɗauki abunda ake cewa fertilized ovum kamar guda biyu a sa a 

mahaifar matar wannan ta vagina ɗinta za’a saka sai a jira a gani idan dashen ya kama. Idan ban mantaba kuma na fahimci tambayarka wannan itace amsar”.

        Sosai AK ke ɗan jinjina kansa yana taunar lip ɗinsa na ƙasa a hankali da haƙiri. “Okay Thanks. Next, za’a iya ɗaukar sperm daga wani ƙasa a kawo 

wani ƙasa batare daya lalace ba?. Misali kamar daga london zuwa Nigeria?”..

      “Eh to Yayanmu za’a iya ɗaukar semen akai wani wuri, amma gaskiya yanada matuƙar wahala saboda sai an sashi a ma’adani na musamman  (Google: transport 

sperm from one place to another). ba kowanne likita banema  zai iya maka wannan juriyar kai tsaye”.

       “Lallai kam. To amma za’a iya ɗaukar sperm ɗin namiji bada saninsaba aje a aikata dashen?”.

       “Yayanmu idan na fahimceka kamar ace matarsa ta ɗauka a ɓoye bada saninsa ba? Dan ko likita sai dai ya saka a kawo, bawai ya ɗiba kai tsaye ba tunda 

ba kamar jini bane ko fitsari da sauransu”.

      “Good, haka nake nufi?”.

               “Gaskiya Yayanmu kamar ba zai yiwu ba, saboda idan za’ayi irin wannan abun shi namijin shine zai bada maniyyi asa a kwalba na musamman a tace 

sannan ayi, ba zai yiyu ayi irin wannna kuskuren ba, kamar yanda na faɗa maka sai an shirya ake ɗaukan Kwan mace, sannan akwalba ake haɗawa sai ya haɗu 

sannan za’a ɗauka a dasa a mahaifar macen. Sai dai a sakashi ya bada da kansa ta wata sigar batare da shima ya san mi za’ai da shi ba nakega”.

     Ɗan jimmm AK yay yana wani tunani da ƙiyasta shekarun Zinneerah a ransa. Kafin ya duba Khalipha ɗin,

     “Okay, kenan za’a iyama yarinya ƴar 14years dashen cikin?”.

      “Eh Yayanmu za’a iya yi, sai dai kamar yanda na faɗa maka kafin ayi sai an shirya, ma’ana akwai lokacin da akeyinshi sai an duba menstrual cycle ɗin 

matar, sabida haka idan bata fara al’ada ba, ba zaiyi wuya ba, idanko ta fara zai iya yuwuwa”.

        “Akwai ta hanyar da ku likitoci kuke iya gane ɗan na dashe ne?”.

     “A iya sanina babu yanda za’a iya gane dashe ne, bandai saniba ko ga wasu manyan likitoci da suka fini ƙwarewa kasan har yanzu ni ɗalibin ilimi ne”.

       Ɗan murmushi AK yayi yana sake gyara zamansa. “A nawa tunanin idan har dashen ciki akai ma yarinya, ya kuma kasance cs akai mata bata haihu da kanta 

ba, kenan zata iya cigaba da kasancewarta cikkakkiyar mace dazai iya bada dukkan amsoshin ko hujja akanta tunda babu wani dalili dazai iya gusar mata da 

budurci”.

       Murmushi ne ya ɗan suɓucema Khalipha, dan sai yanzu ya fahimci dai Yayansu yana magana ne kamar akan Zinneerah, ya dai ƙi fitowa fili ne, zama ya 

ƙara gyarawa da ƙyau yana faɗin. “Eh to Yayanmu idan dai mace ta haihu ai babu zancen virginity ya kare nake gani ko kuwa?. Sai dai kuma da kace idan ya 

kasance an mata cs ne. Abunda mutane ke cewa budurci abun ba haka bane, virginity shine idan bata taba saduwa da namiji ba ko an zura wani abu a vagina babu 

yanda ake ganewa saboda mata da yawa wannan abun mai kama da yaɗi da yake ɗan rufe bakin vagina ba kowa keda shi ba, hasalima idan mace tana manyanta abun 

yana raguwa, sannan tsallle-tsalle da irinsu hawan doki ko Keke duk yana sawa a rasa shi, haka kuma Koda mace tana dashi ba kowa ke zubar da jini lokacin 

saduwar farko da ɗa namiji ba. Shi yasa yanzu duk ake hana abubuwa kamarsu vaginity testing. Kaga nauyin ciki zai iya sa ta rasa wannan yaɗin kenan itama 

inhar tanada, amma ba haka na nufin ta rasa budurci ba, dan dole a kirata virgin inhar bata taɓa sanin ɗa namiji ba, ko kuma wani abu makamancin haka kamar 

haihuwa bai ratsata ba”. 

       AK ya ɗan sauke numfashi, “Sannu da ƙoƙari Khalipha. to amma za’a iya yin dashen batare da ta saniba kuwa? Kamar a bugar da ita ko something hakan?”.

       “Tabbas za’a iya bata maganin bacci ayi, amma bazai yuwu ayi a gida ba ko ɗakin likita ba, a ɗakin theater akeyi, bai kuma zama lallai a samu nasara 

ba a yin farko, wasuma sai kaga sunyi sama da sau hudu biyar goma ma basu daceba, ƙwayayen sukan mutu kafinma a dasa ko bayan an dasa cikin yaƙi zama. Idan 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button