WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 5

“Nanne me ya faru a  wancan ranar? 

Ajiyar zuciya ta sauke” zan faɗa maki amma ba yanzun ba”

“Dan Allah Nanne ki faɗa min,ina son in san me ya faru da iyayena,wani irin abu ne ya faru haka, ina so in sani”

“Zan faɗa maki Fettel amma ba yanzun ba”

Shiru ta yi dan ba haka taso ba,

“Tashi ki je ki huta Fettel”

“To Nanne”tashi ta yi ta fita, 

Tashi ta yi ta shiga ɗaki, wani dan Aƙwati ta buɗe,wani  hoto ta ciro tare da wani takardar, zama ta yi bakin gado,a hankali take shafa hutun tamkar mai shafa fuskar mutun,hawaye ne ke  zubo mata,wasiƙar ta warkare tana kallo,ƙara fashewa ta yi da kuka”ba zan taɓa yafe ma Azzaluman da suka ai kata maku wannan abin ba,Allah kuma ya ƙare min ku aduk in da kuke,in kuma muna da rabon saduwa da juna to,in kuma na tafi a lokacin ina dai fatan ku haɗu da ƴar ku,cikin aminci “sosai ta yi kuka a wannan ranar na tuna abubuwa da yawa,Asma’u ƴa ce a wurin ta wacce ta ke matukar so fiye da komai na rayuwar ta,in da a wancan ranar da suka biyo ta zasu nime ranta ya zama fansa a kan Asma’u to da wallahi ta bada na ta ran ba tare da tunanin komai ba, ko dan ta zauna ta rayu da ƴar ta da kuma Ahalinta, yanzun ko a ina suke ko suna raye ko kuma! kai wannan tunanin kadai  idan tayi yana matukar girgizata da daga mata hankali,shi yasa har yau ta kasa yarda ta yi shi, duk da ta san hakan na iya faruwa tunda abu kusan shekara Ishirin da biyu kenan, kuma ko sau daya basu taba waiwayan gida ba,Allah dai yasa kar wannan tunanin ya zama gaskiya,Allah dai ya daura ta a kan hakan.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button