BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 11 to 20

Bata kai ga magana ba dogarai ke sanar da shigowar sarki falon sirikan nasa , daman da baba tsoho ma shi ke fasara tsakaninsu domin ba komai yake ganewa ba shi kuwa sarki ya zauna da tubawa Tunda ya shigo Anna ta sada kanta dan kunyar siriki, shima du a wani takure yake inda Gaishat ke binsa da kallo tana tambayar kanta me ya kawo shi ko bakinsa ne?

Gyaran murya ya yi ya ce” Anna, ina fatan kin san baba tsoho, wanda Agaishat ke zuwa wajensa babanta kennan

Daga inda yake ya daga murya da irin abin haushi haushi ya ce” ya zata manta kwartanta uban yarta? Ai ni dama na san dubunki sai ta cika munafuka, yau dai ga zance zai bude

Da wani irin yannayi Wardugu ya kai dubansa daga inda ake maganar, wa ke magana ta rashin da.a haka? Shine abinda yake tambayar kansa din wardugu na jin yaren buzanci kai bama buzanci kadai ba wardugu irin mutanen nan ne masu kwakwaluwar kwashe yaren da ba nasu ba, yana jin yaruruka da dama, hakan ya bashi damar jin abinda ake fada harma wanda Algabiit ke aikowa daga daka

Sarki ya girgiza kansa kawai, ya san wanene Algabiit farin sani, kuma fa ya san harma gudumuwarsa wajen Algabiit ya tsula tsiya a garin aman ba komai zai dauki mataki ne tun kafin ya saka a tarwatsa su baki daya

Anna da ta kasa hada ido da shi ta gyada kanta, ya zata kasa gane mutun mai daraja a idannuwanta? Wannan mutumin ko dan tsufansa a girmama shi aman Algabiit ke aiko masa da zagi haka? Ta yi imanin ba ita ba ko Algabiit din baba tsoho ya haife shi

Bak’a kuwa tunda ta kyala ido ta ga baba tsoho ta samu ta rakube jikinsa tana dan jefo masa tambayoyi a hankali da alamun tsegumi

Hannunsa ya saka ya dungure mata kanta yana murmushi, a ransa ya ayyana idan kika tafi,….nishadina, murmushina, zai tafi da ke

Sarki ya ci gaba da fadin” wadinnan mutanen da kike ganni, wannan baiwar Allahm mahaifiyar wannan bawan Allahn ce, sannan ta taso tun daga garin da kuka kai Fatimata rashin lafia ta zo Agadez daga nan sun dauki hanya sun zo garin nan dan neman baba sofo da ya baiwa dan nata maganin huka tun yana yaro bisa alkawarin idan an samu lafia sai ta bashi abinda ya samu

Toh Sai aka tashe su Allah bai yi sun kara haduwa ba, tun daga lokacin take nemansa domin mutun ce mai son cika alkawari abin na tsaye a ranta sai yau Allah ya yi

Dan numfasawa ya yi, ya ci gaba” kin ga, ba a niger ba, ko a kasar waje masu fada a ji ne, 

Sun zowa Baba sofo da alkhairi na mamaki sai dai abin mamaki baba ya ce sam shi yanzu ba ta abin duniya yake ba, ya yafe sai dai damuwarsa *AGAISHAT CE*  

Anna ta dago da sauri ta ce ” AGAISHAT? 

Sarki ya ce” kwarai kuwa, Baba ya nemi alfarmar………………………………………………gaba daya sarki ya kwashe yanda suka yi baba da su Wardugu ya fadawa Anna dake zaune kanta na kallon kasa sauran yayanta na zagaye da ita Bak’a kuwa na jikin Baba sofo

Da sauri Bak’a ta dago ta kai dubanta wajen Anna da Sarki, ta maida dubanta wajen baba Sofo, 

Baba Tsoho ya yi gyaran murya ya ce” shakuwa, da tunani ya hana ni sakun nutsuwa Annar Agaishat, na sani bani da ikon zartar da hukunci kanta domin ban haifeta ba sannan ni ba wani shakikikin dan uwa ba

A duniya adu.ata biyu ce, Allah ya sa in gama da duniya lafia Aljanna ta zamo makomata , fatan Allah ya nuna min ta zama mutun mai cikaken inci, ta samu nutsuwar zuciya , ta samu zama itama mutun,

Anna Agaishat ta yaya hakan zai faru? A timiya mu duka bamu fi kirgo da yatsu ba, nan da kike ganina har limamin garinnnan na nemi alfarmar ya aure man ita mana aman ya nuna aa ba zai iya ba

Almajirina ma ya kiye min,

Gashi yau da gobe sai Allah, Agaishat girma take, mu kuwa gajiyawa muke kara yi,

Idan ta fito daga nan ina ta fada? Me ta ci? Ya ta yi ta samu Allah ne masanin gaibu, ni kam a matsayina da wanda take zuwa wajensa sannan ta daukeni tamkar uba nakan yi mata nasiha, nakan tsoratar da ita, nakan nuna mata karara rayuwa da abinda Allah ya bani ikon sani

Annar yara , Ba zan tirsasa maki ba, ba zan saka ki daukan abinda zaki yi ta nisawa zuciya bata da tabas, aman ina so ki yi tunanin gaba da bayan lamarin, in da hali ki dauki Agaishat ki baiwa wannan mata riko da zuciya daya, ki yi kyakyawan zato, ki saka a ranki alkhairi ne sannan ki bi da adu.a, na yi imanin koda mugaye ne Allah zai saka mata kaunar yarinyar shari ya juye wa khairi 

Wardugu ya yatsina fuska ya dubi Ayya dake zaune tana kallon su, da yaren tubanci ya ce” Ayya, yarinyar nan fa wannan mahaifiyarta ce , kuma ina jin shegiya ce shi ya sa wancen yake zazaginta haka! Ayya me ya sa suke faman rabuwa da yarinyar? Ayya 

Wardugu ya isheka haka , Ayya ta fada tana zaro masa idannuwanta, murya a kausashe ta ce” baka lura da abinda ke faruwa ne? 

Ba zato ba tsamani muryar Anna, cikin yaren Tubanci ta ce” ba shegiya bace, wannan da ka gani ya shige daki ya labe shine ubanta, yana kyamatarta ne dan ta zo duniya *BAK’AR FATA* 

Da mamaki du suke kallonta, 

Ayya ta taso ta karasa kusa da ita, hannunta ta kamo tana kallonta ta ce” batuba ce ke?????

Anna ta lumshe idannuwanta sai ga hawaye sharsharshar ta dan jijiga hannun Ayya ta ce” ban sani ba, ban san ko mecece ni ba,

Damko hannun Ayya ta yi da dan karfi ta saka idannuwanta cikin nata ta ce” ban san ko dan ina jin yarenki ba? Sai kawai nake ji zan iya sadaukar da y’ata wa ke, zaki rike mini yarinya da gaskiya?

Ayya ta ji gabanta ya dan fadi, matar na tare da wani banban lamari, Ayyan ta jijiga hannayenta itama tana kallonta ta ce” mudin raina

Algabiit dake ciki sai zaro ido yake, ya shiga ukunsa, ya aka yi Anna bata manta yaren nan ba? Aman abinda ya yi mata *Harta sunnanta ta manta*! Domin kafin ya lulo timiya da ita sai da ya tabata ta iya yarensa, ta iya saka kaya irin nasu, ta iya yan dabi.unsu, shigewa ya yi ciki ya zauna jikinsa na dan rawa rawa 

Anna ta lumshe idannuwanta, ta ce” thank you, 

Wardugu dake tsaye ya kalo su , Inglish kuma? Inglish ta yi? 

Hai san ya karasa shigowa dakin da kyau ba sai da ya karasa, inda shigowarsa ya saka du yan matan suka tsaya kallonsa da mamaki, Bak’a kuwa ta lafe da tsoro jikin baba tsoho jikinta du yayi wani sanyi tana son fahimtar maganar tafiya da wa wai ake? Ina ai ita ba inda zata, ba zata bi wasu mutanen da bata sani ba bata taba gani ba ta je a kasheta, ya zata iya tafia ta bar yan uwanta da annarta da baba Sofo? Wa zai ringa kawo masa ruwa? Wa zai ringa saya masa gogo yana gurza masa a karfen gurje goro? Wa zai ringa koya mata karatu? Wa zai ringa ce mata itama mutun ce dan tana baka Haka Allah yake son ganninta ? 

Wardugu yana karasowa ya dan duka yana kallon Anna ya ce” di u speak Inglish?

Anna ta dago ta kale shi, ta amsa masa da kanta, a ranta tana nanata inglish? Wani yare ne shi kuwa? Ba irin wanda suke yi da matar bane kennan?

Wardugu da mamaki ya ce” ya aka yi kika iya inglish? A ina kika koya? Wa ya koya maki? Daga wani gari kika zo? 

Anna da kanta ya fara sarawa ta dafe kanta da sauri , muryarta ya fara rawa rawa ta ce” i…i…i don’t know ! Ta fashe da kuka tana rungume hannayenta da sauri Gaishat ta karasa tana rungumo Annarsu itama tana kukan za.a kuma raba su da yar uwarsu? Domin ta sani ne , a yanda anna ke jin zafin irin abubuwan da ake yiwa Agaishat , a yanda aba ya tasota a gaba da man bleating kan sai ta shafa ya yi kudinta itama , anna na neman koma waye ta bashi aurenta ta tafi ta huta, ta gwamace ta tafi ta auri koma waye da aba ya yi kudinta itama kar a je ta fada irin rayuwar da fatimata ta fada ko ma wace ta fi ta

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button