WUTSIYAR RAKUMI 40

*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_NO. 40_*
……….Abba ya ajiyev wayar yana sauke numfashi, taajiyevxfaɗin akira Ummukulsoom ta shigo da Abdul-Waheed dake a ƙofar gida.
Itace ta fita tai masa jagora suka shigo, sai dai haka kawai ta tsinci
kanta cikin matuƙar sanyin jiki, bayan sallama da gaisuwa babu abinda ya sake shiga a tsakaninsu har suka shigo yana biye da ita.
Tunda ya shigo falon Dad da Attahir suka zuba masa ido, yayinda Abba shi sam bai kawo komai a ransa ba ya nuna masa wajen zama.
Abba zaiyi magana Dad ya katsesa cikin tsantsar takaici da ɓacin rai.
“Kai kaine Abdul-Waheed ɗin?”.
Cikin mamakin furucin Dad Abba ya kallesa, “Eh wannan shine kam nake gani, dan dashine mukai waya, ke Ummukulsoom ai shine wanda kuke taren ko?”.
Kan Ummukulsoom a ƙasa ta ɗaga kanta alamar eh.
Ƙwafa Dad yayi, cike da kakkausar murya yace, “Fodio kai ƙaramin mara kunya ne, tunda iya fuska ka iya canjawa banda gangar jiki, wato ni ban isaba ko? Shine ka koma ta bayan fage kana yaudararta……”
“Alhaji Mahmud wai mike faruwa? Wannan fa Abdul-Waheed sunansa ba Fodio bane ba”.
“Humm Alhaji Abubakar kenan, idan ya gama raina muku hankalin sai ya cire Mask ɗin fuskarsa”.
A matuƙar firgice Ummukulsoom ta kalli inda yake zaune kai a sunkuye, hakama Abba, Attahir kam da tun shigowarsa ya ganeshi takaicine kawai ya gama kumesa, sai dattijai biyu maƙwaftan Abba suma dai abin ya zame musu kamar almara, dan basu fahimci komaiba”.
Abba ne yace, “Kai ba kace sunanka Abdul-Waheed baneba yaro?”.
Hannu yakai saman fuskarsa, jiki a matuƙar sanyaye ya zare facemask ɗin da ya sanya, ainahin fuskarsa ta *_USMAN MAHMUD USMAN AJIWA (Amaan, fodio)_* ta bayyana ga kowa.
Gaba ɗaya Ummukulsoom takasa koda motsi daga inda take a durƙushe, sai kafesa tai da idanu tamkar wani butun butumi.
Attahir kam kallo ɗaya yay masa ya ɗauke kansa cike da tsantsar mamakinsa, sai maimaita sunansa yake a cikin zuciyarsa tamkar ya samu karatu.
Abba ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya yana kallon Amaan baki buɗe, “Fodio da kanka wannan aikin haka? Minene amfanin hakan ko ma’anarsa?”.
Jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu, hakama idanunsa jajur suke alamar tsantsar damuwa, ya ɗago ido a hankali ya saci kallon Dad, kafin ya maidasu ya risinar yana faɗin, “Abba ku gafarceni, banida wata mafitar data wuce hakan……..”
Cikin katsesa Dad yace, “Tashi kabar falon nan dan ubanka, inba hakaba duk abinda yazo harshena na jefeka dashi wlhy kaine kaja, mara mutunci kawai”.
Saurin riƙe hannun Dad Abba yayi, “Alhaji Mahmud Please Calm down, mubi komai a sannu dan ALLAH, shima ƙila akwai tashi hujjar….”
“Hujjafa kace Alhaji Abubakar? Usman bashida wata hujja, kuma koda yana da ita shi yasan har abadan bazata karɓu a wajena ba, wlhy kuma kai masa gargaɗi ya fita a idona, idan yabari nakai bango akan maganarsa da Ummukulsoom narantse da ALLAH har abada bazan sake waiwayarsa ba…”.
Yana gama faɗa ya tashi ya fice yabar falon.
Kowa kasa koda motsi yay a cikin falon, Amaan kam yay ƙasa da kai kawai ya kasa koda numfashi mai ƙarfi balle kallon wani.
Attahir ya fara farga da Ummukulsoom bata a cikin hayyacinta, ya miƙe da sauri zuwa gareta, yana taɓata ta zube a wajen alamar numfashinta baya tare da ita.
Kafin kace mi komai ya kuma rikicewa, Ummi ta duƙufa akan Ummukulsoom, gaba ɗaya hankalin kowa a tashe yake, musamman Yaa Amaan daya kasa zaune ya kasa tsaye. da ƙyar aka samu numfashin Ummukulsoom ya dawo, sai dai fa dole akai mata allurar barci.
★★★★
“Wannan ranar itace naita jiye maka Ajiwa, amma sam sai kaƙi saurarena, saboda shaiɗan na ɗoraka akan kekem ɓera, a zatona aure ya wuce abin wasa a garemu, musamman daya zam wannan wata babbar ƙyautace daga iyaye.
Bansan dalilinka na dawoma Ummukulsoom ba a karo na biyu matsayin wani, sannan bansan dalilinka na bibiyar rayuwarta ba, sai dai abinda zan sanar maka duk wanda ya baka gurguwar shawarar sakin Ummukulsoom da dawo mata ta wannan hanyar to lallai bai baka ƙyakykyawar shawara ba, dan koni nan bazan taɓa amince maka ba, wannan alwashinane”.
Attahir na gama faɗa ya barsa tsaye a harabar gidan ya koma cikin gida inda kowa yake jigum-jigum akan lamarin Ummukulsoom.
Hajijiya yaji tana ɗibarsa, yay saurin dafe motarsa yana sauke wata irin sarƙaƙƙiyar ajiyar zuciya, kansa yay masa jingim, babu wani abu da yake fahimta a halin yanzu, dama yasan dolene wannan ranar tazo kamar yanda Attahir ya faɗa, sai dai sam baiyi tunanin zatazo a juye baneba…
Mota ya shiga ya tuƙa kansa, ALLAH ne kawai ya kaisa gida lafiya amma badan yasan a wanne yanayi yay tuƙinba.
Ameer ne da suka shigo kusan tare yazo ya fiddashi daga moto ɗin ganin halin da yake ciki.
Hannu ya ɗagama Ameer alamar ya barsa kawai, Ameer baiyi musu ba ya sakesa, da kansa ya taka zuwa sashensu Momcy, ba tare da ya amsa gaisuwar su Buhayyah da Bassam dake falon ƙasa ba ya haye sama.
Da kallo suka bisa kowa baki a hangame, dan sun gansa tamkar baya cikin hayyacinsa.
Falon Dad ya nufa, Dad dake zaune rai a ɓace ko kaya bai sauya ba yay masa kallo ɗaya yana ɗauke ido. “Usman karka shigo min nan”.
Cike da mamaki Momcy dake fitowa daga bedroom ɗin Dad tace, “Miya farune Abban Fodio?”.
Wani banzan kallo ya watsa mata yana ɗauke kansa kafin ya miƙe tsaye hannunsa goye a bayansa.
“Kamar yanda na alƙawranta ma kaina hukuntaku a yau zan cika insha ALLAHU, Usman badai umarnin wannan yasaka bijirema nawa ba? To ta tattara ta barmin gidana itama, ince dai shikenan, jamila kije na sakeki saki ɗaya…..”
Ƙara mai ƙarfi da razanarwa Momcy ta ƙwalla.
Fodio kam tun yana fahimtar kaɗawar iska har komai ya fara masa nisa a kunne da ƙwaƙwalwa da zuciya, a hankali yaci gaba da tsintar kansa a wata duniya dake da banbanci data mutane.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Komai fa ya dagule musamman a gidansu Amaan, dan bai tashi buɗe idoba sai a ɗakinsa, baisan ya ya akai yazoba, miya biyo baya bayan furucin Dad akan Momcy da shuɗewar abubuwa daga jinsa da ganinsa tare da fitar numfashinsa.
A hankali ya buɗe idanunsa da sukai nauyi jingim ya saukesu akan Momcy dake zaune gefen haggunsa tana ta faman sharce ƙwalla, sai Buhayyah da Bassam da Ameer daga gefen damarsa suma da alama kukan suka sha, sai Ummayya a kusa da ƙafafunsa itama tana nata.
Idanunsa ya maida ya lumshe a hankali ƙirjinsa na sake ɗaukar nauyi sosai. Kukan Momcy yafi komai sukar zuciyarsa, yau shine yazama silar guntile igiyar auren iyayensa guda ɗaya bayan kusan shekaru talatin da takwas da ƙullata, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, shi Usman Mahmud ne dai sila da gaske? Sam bai taɓa tunanin Dad ya ɗau zafi har irin hakaba akan lamarin.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Ummukulsoom ma dai sai yamma liƙis allurar da Momcy tai mata ta saketa, sai dai abinda zai baka mamaki gaba ɗaya hawaye sun ƙafe a idanunta, sam taƙi kuka alamar zuciyarta a dake take.
Koda Maman Ahmad ta kawo mata kunun gyaɗa da Momcy tasa aka dama mata karɓa tayi tasha abinta, sannan bily ta haɗa mata ruwan wanka mai ɗan ɗumi. Bayan tayi wankan kaya kawai ta canja ta koma ta ƙwanta, dan tana fashin salla.
Anan kam hankalinsu yaɗan kwanta ganin Ummu tana cikin nutsuwarta, sai dai halin da Amaan yabar gidan shida Dad yasaka su a cikin jin nauyi.
Da daddare Zaid yakai Abba gidansu Amaan, dan yanason suyi magana ta fahimta da Dad, amma saiya iske babban tashin hankalin da yafi na farko. Sakin Momcy da Dad yayi, sannan yama bar gidan babu wanda yasan inda ya tafi, saboda harda kaya ya ɗauka.
Sai kuma Amaan da kowa ya rasa gane kansa a gidan, yaƙi magana ma kowa, sai dai kallo ɗaya zaka fahimci yana cikin matsala ta ciwo da babu wanda yasan na miye. Doctor dai yazo ya saka masa ƙarin ruwa wanda da ƙyarma ya amince aka saka masa.
★★
Wannan yini dai na Asabar a rashin daɗi jama’ar waɗannan gidaje biyu suka yisa. Shirin da akayi na farin ciki saiya juya zuwa wani al’amari mai rikitar da zuciya da walwala.
Kowa ya kasa fahimtar dakewar Ummukulsoom, dan sam taƙi nuna abin ya taɓeta a rai, ko shigarta ruɗani bayan ta fahimci Abdul-Waheed shine Amaan, shine yaketa yawo da hankalinta a kusan tsawon watanni bakwai da suka gabata.
Babu wanda ya matsa mata da tambayar komai a kaf gidan, sai dai kowa kaffa-kaffa yake da ita, musamman ma Attahir da yafi kowa jin zafin Amaan.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
“Wlhy Basiru yau saika sanar min inda ka samu kuɗi har ka sai waɗannan kayan masu tsada haka”.
Ransa ya kai ƙololuwar ɓaci da Meenal yau, ya ƙura mata idanun sa da sukai jajir saboda cin kashin da take masa tun shekaran jiya akan kayan da suka siyo shi da Abu.
“Wai Meenal wane irin rainine a tsakanin mu har haka? Ya kullum ina miki abu dan gudun ɓacin ranki amma ke sam baƙya ganin hakan, ni banida hurumin sayen abu sai kinbi ƙwaƙwƙwafina….?”
“To ya bazanbi ƙwaƙwƙwafin kaba tunda nasan bakada kuɗin sayen abun, idan har ba kuɗina ka ɗiba ba ta ina kake da kuɗin sayen waɗannan kayan masu tsadar tsiya da kaketa sakawa?”.
“Meenal! Ni kike faɗa ma wannan maganar? Ni ne zan miki sata?”.
“To waya sani abu a duhu”. ‘ta ƙare maganar da murguɗa masa baki tana dalla masa harara, ta bar wajen’.
Ko motsi kasa yi yayi, sai ma mamaki dake ƙara girmama a zuciyarsa akan lamarinta, wato dai su mata zumane sai da wuta, ɗaga mata ƙafar da yay tun farkone yajawo wannan rainin a tsakaninsu, yau harshi mace ke kira da ɓarawo dan kawai ta gansa da kaya masu nauyin kuɗi. Da ƙyar yaja ƙafa yakoma saman kujera ya zauna, dan ita meenal tama daɗe da barin gidan.
Tunda suka dawo Nigeria kamar itace mijin, kullum bata yini a gidan tana gidansu na gwamnati, idanma bata gadama ba saitai kwana biyu acan. Shine ke yini a gida, saboda iskancin tama kulleshi take a gidan, ta wata dabara yake samu ya fita kullum batare da ta saniba. Ko kaɗan bai taɓa zaton haka meenal takeba sai yanzu, dan a tsawon shekara biyar da sukayi a paris babu wannan rainin mai tsanani irin haka a tsakaninsu, duk da dama takan masa wasu abubuwan marasa da ɗi yana shanyewa ne tun suna can.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
A kwanaki biyunnan misalta tashin hankalin da gidansu Yaa Amaan suke ɓata lokacine.
Tashin hankali uku ya taso Momcy, barin Dad gidan, sannan duk inda ake tunanin samunsa abun ya gagara, ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya.
Sai sakin da yay mata wanda ko a mafarki bata taɓa tunanin hakanba, duk iya shegen da take masa tun sunada ƙuruciya bai taɓa kwatanta hakanba sam, sai dai yace taje gida ta huta, amma sai gashi yau da rana tsaka, da girmansu ga jikoki ya yanke igiya ɗaya acikin igiyoyin aurensu.
Sai damuwar da Fodio yake ciki, wadda ta tabbata itace tushen komai, laifin ta yafi na kowa yawa akan kuskuren daya tafka, duk tunaninta yarinyar ƙauye ta koma tai aure, ashe tana nan tana karatunta a kusa dasu batare da tasaniba, ashema tanada alaƙa mai ƙarfi dasu, ashema ahalinta sunfisu komai, wannan wane irin murɗaɗɗen yanayine ya riskesu a lokacin da basuyi zatoba.
Ita kanta kwance take rijif babu lafiya, hakan yakuma tada hankalin iyalansu, dan duk yaran suna gida har aunty Nurse da aunty Ummi.
Baya yima kowa magana a gidan, bawai dan miskilanci kawai ba ko jin haushin wani, a’a tsantsar damuwace tattare dashi, ta sanadinsa komai ya rikice a gidansu, kullum cikin yawon neman Dad suke shida Attahir da Ameer da Zaid.
Abinda ya kuma dagula masa lissafi shine sam Attahir baya ko kallonsa, bayan iyayensa bashida kowa da yake iya sakewa dashi sama da Attahir, Attahir yasan cikinsa fiye da kowa a duniya, shike saukar dashi idan ya ɗau zafi, ya sashi farin ciki idan ya tsinci kansa a damuwa, ya share masa hawaye a lokacin da yaga idaniyarsa na kawo ruwa, amma sai gashi a yau sam baya ko kallonsa, ya juyama komai nasa baya, ko a neman Dad ɗinnan yini suke bakinsu bai saɓa da juna ba. Dama shi inba Attahir ɗinba ba doguwar magana yake da wani ba.
Yau data kasance rana ta huɗu da faruwar komai Abba ya hasaso inda Dad yake, ya tabbata bayan nan babu inda Alhaji Mahmud zaije kuwa.
Bai sanarma kowa ba ya saka Attahir tuƙasa suka nufi Ajiwa.
Ilai kuwa Dad yana a can hankalinsa kwance, koda yaga Alhaji Abubakar sai ya kuma ɓata fuska.
“Alhaji Abubakar! Karka roƙeni akan abinda bazan iya maka shiba dan ALLAH”.
Murmushi Abba yayi, “Alhaji Mahmud kenan, ka kwantar da hankalinka bazan roƙeka ba, kamar yanda bazan maka tilas ba, amma sai daifa ka sani, barinka gida ba shine mafita ba, dan ba duka ahalin gidan sukai maka kuskure ba, aganina ka hukunta masu laifin, to mizaisa sukuma sauran kai musu hukunci da ƙaurace musu, nasanka da saurin fushi, amma kai mutum ne mai haƙuri da kawaici komai zafi da yay maka, sam banyi zato daga gareka ba zaka aikata ɗanyen aikin datse igiyar aurenku da hajiya Jamila, da kayi shawara dani dabaka aikata hakanba, mu manyane yanzu Alhaji Mahmud, mun wuce ajin yin hallayar yara ai, dan ALLAH ka tashi mu koma gida, kakuma janye sakinnan, gara kai mata hukunci da wani abun amma ba wannanba….”
“Alhaji Abubakar bazaka fahimci ƙunar da nake jiba akan lamarin nan, nifa nabama Fodio dama tafi shurin masaƙi akan ya fidda matar aure amma yaƙi, nazo na shige masa gaba akan yarinyar nan da ALLAH yayma rasuwa, ALLAH baiyi zasu rayu matsayin ma’aurata ba ta rasu, kai shaidane nabasa lokaci yakuma hutawa sannan na tuntuɓesa akan batun aure, amma ya nunamin shi bai samu ba, kafin na aura ma Fodio Ummukulsoom saida na sanar masa fa, dukda na isa dashi amma na fita haƙin yaron nan, yakuma cemin ya karɓa, ka tuna ko ɗaurin aurennan zamewa yay yaƙi zuwansa, nakuma barsa duk dan dai a zauna lafiya, na kuma karya ƴancina na ɗauki yarinyarnan da kaina nakai masa har inda yake, yakuma nunamin ya amsa hannu biyu, amma saboda banida daraja a idonsu shine ita ta sakashi ya saketa”…..
“Alhaji Mahmud ban katseka ba, amma dai karmuyi zargin ita ɗince, ƴaƴane na yanzu ka haifesune baka haifi halinsu ba….”
Murmushi Dad yayi mai ciwo, “Alhaji Abubakar Jamila itace ta sakashi sakinta, duk da dai shi yaƙi sanarmin gaskiyar abinda ya faru, amma ni na bibiyi komai naji yanda yake, Fodio yanada wani hali na shanye damuwa komai ƙuntatashi da zatayi, ni kaina ba kasafai nake fuskantar damuwarsa ba kai tsaye saina nutsu akan lamarinsa, sannan kaga maganar sakinnan, koda zata kasheshi arai bazai faɗin ainahin abinda ya faru ba da bakinsa, bakomai zai sashi yin shirunba sai dan kar mahaifiyarsa tai baƙi a idona, wannan ne yasa na biyo masa ta bayan gida ai na saketan a gabanshi, kuma dama nayi alƙawarin yanda ta sa ya saki Ummukulsoom itama sai ta ɗanɗani wannan tabon taji inda daɗi, karka ɗauka Ummu ce kawai ke fuskantar wannan bakin halin na jamila, yanzu haka matar Ameer cikin wannan ƙangin take, yarinyar sam bata sakewa a gabanta, shi Fodio zai iya mata kawaici ne, amma Ameer bai iyayi saboda kaf halayyarsa irin tatace, shiyyasa ma bata isa sakashi rabuwa da matar tashiba ko ƙuntata mata, narasa wannan wane irin banzan kishine, ita wanene ya sanya mata ido a nata lokacin? Sannan itama fa tanada ƴaƴa matan a gidan wasu, rayuwar da Jalilah tayi a gidan miji kaɗai bata isa zame mata izina ba ashe? Ka barsu Alhaji Abubakar, sai Fodio ya magantu da bakinsa ya sanarmin miya faru sannan”.
“Humm sam dai abin baiyi daɗi ba, sannan bata ƙyautaba itakam, dan wannan rayuwace irinta jahilci, duk sonka da ɗanka dolene kabarsa yayi aure, tunda ba kaine zaka auresa ba, amma dan ALLAH kayi haƙuri mu koma, komai fa ya birkice fiye da tunaninka wlhy”.
“Ka barni kawai anan Alhaji Abubakar, sa gaji su daidaita ne”.
“Dan ALLAH kar muyi jayayya dakai Alhaji Mahmud, muje koma mi za’ayi sai ayisa a can”.
Badan Dad yasoba ya kimtsa suka dawo KD a ranar.
Duk da ya iske dukan iyalan nasa a gida bai kalli kowa ba ya shige ɗakinsa ya sharesu. Har washe gari basu sake ganinsa ba, sai da rana da Abba yakuma zuwa gidanne ya lallaɓashi ya fito falo da ƙyar.
Babu abinda su Aunty Nurse sukeyi sai kuka da roƙonsa akan yayi haƙuri ya maida mahaifiyarsu.
Itama kanta hawayen take, dan tama kasa zuwa gidansu ta sanar, amma Abba yaje yay musu bayanin duk abinda ke faruwa akan lamarin, sunkuma ce babu abinda ya damesu, Dad yay musu dai-dai da hukuncinsa, dama saki Ukun yay mata lokaci ɗaya.
Gyaran murya Dad yay fuskarsa a matuƙar ɗaure, ya sauke kallonsa akan Yaa Amaan da tunda ya shigo falon kansa a sunkuye yake shi kam, duk ya zabge a tsaye, sai haske daya ƙara yay fayau, “Kai da kai zan fara Fodio, kamar yanda mukai dakai a shekaru biyar da wasu watanni da suka shige yanzu zuma shine zan maimaita, inhar wannan matsalar kana buƙatar ganin ƙarshenta to saifa ka sanarmin dalilinka da kuma ainahin abinda ya faru da har ya saka sakin Ummukulsoom, inba haka ba kuwa, hummm”.
Hankali Momcy yakuma matukar tashi, sai zufa take zabgawa dukda kuwa AC na aiki a falon, ta raba hankalinta biyu wajen kallon Alhaji Mahmud da kuma Fodio.
Har yanzu kan Yaa Amaan a ƙasa yake, sai da yaja kusan minti ɗaya sannan ya ɗago ya kalli Dad, idanunsa sunyi jajur matuƙa gaya, jijiyoyin kansa kam sunyi ruɗu-ruɗu, da ƙyar ya buɗe baki yace, “Dad ka gafarceni, a duk duniya ina ƙaunar abu biyu fiye da kaina, ina girmama abu biyu fiye da buƙatuna, zan iya sadaukar da komaina saboda abu biyu kuma. Ba komai bane abunnan guda biyu Dad sai kai da Momcy, kamar yanda na roƙeka da farko Dad akan kabar maganar nan a yanzuma ina ƙara roƙonka, dan girman ALLAH abar maganarnan, ka ɗauka ƙaddara ce kawai ta katsa igiyar aurena da ita”. ‘Ya ƙare maganar da dafe kansa da yakejin ya masa nauyi kamar zai tsage gida biyu’.
Murmushin takaici Dad yayi yana miƙewa, “Kamar yanda ban canja ba a shekaru shida da suka shuɗe a yauma bazan canja ba Fodio, daga yau inhar ka kuma bibiyar Ummukulsoom AL……..”
“Alhaji Mahmud karka ƙarasa dan ALLAH”.
Abba dake shigowa shida Ummi ya faɗa da sauri.
Kallonsa Dad yay ya ɗauke kai, “koda ban ƙarasa ba ya tabbata na masa katanga da ita na har abada”. ‘Dad yay maganar yana hayewa samansa’.
Da kallo duk suka bisa har Fodio dakejin falon na fara juya masa, miƙewa yay dafe da kansa yana haɗa hanya tamkar mashayin giya.
Ƙarar zubewarsa a wajen ce ta maido hankalin kowa na falon kansa a matuƙar tashin hankali………….✍????
Ga na jiyanan da ban samu yin posting ba bisa wani uzuri.
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
*_ƴan Niger kuma_*
_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*
*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*
_TA NUMBER;_
*+22795166177*
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????