NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 44

     Sam Meenal batasan wainar da basiru ke toyawa ba, dan ba zaman gidan takeba, kullum abun natama ƙara gaba yakeyi, mantawa ma take da waji aure dake a kanta kwata-kwata.
       
           Gobe ta kasance valentine day, dan haka Meenal tazo gida ta kwana a tsarinta da shirinta gobe su fita yawon shakatawa itada Basiru, su more ƙuruciyarsu saboda muhimmancin wannan ranar a garesu (ƴan Boko zalla kenan????????, da zaka tambayesu rana mai muhimmanci a musulunci bazasu faɗa maka ko ɗaya ba????????‍♀, amma kowacce rana ta yahudawa sun santa, ALLAH ka rabamu da koyi da abinda zai halakar damu????????????).
           Kafin ta iso gida sukai charting sosai da Suhailat da Lubna, duk kuma akan valentine day ɗin, shikuma duk ɗaukarsa Meenal ce, (ɗan daƙikiya kenan????????).
      Haka itama zulfah ta turo masa massege, da yake yanzu yana ɗan kulata sai suka gaisa.
        Sai yamma Meenal tazo gidan, suka rungume juna itada basirun ta, tare da faɗawa wata sabuwar duniya, baiyi zaton samun yanda yake soba, amma a mamakinsa sai gashi ta basa kanta cikin sauƙi suka more.
     Ranar haka suka kasance cikin farin ciki a har wayewar gari. Da safe ma bayan sunyi sallar asuba a makare suka dawo falo suka baje suna hutawa da ɗanyin hira, daga nan aka fara canja salo, daɗi ya kama basiru ganin yanzunma dai Meenal ta saki jiki……
      Knocking ƙofa da akaine ya katse musu hanzari, Meenal dake a samansa ta sauka tana gyara igiyar rigarta, ta zata ko saƙon da ta bayan ai matane ya iso. Har Basiru zaice tabarsa ya buɗe sai kuma yay shiru..
     Koda ta buɗe sai taci karo da baba mai gadi riƙe da ƙatuwar rose flower and quisqualis da akaima shiri na musamman a cikin farar leda, sai ɗan kwali na alamar gift????.
       “Wannan fa?” tafaɗa a yatsine ba tare da ta amsa gaisuwarba.
     Cikin ɗan rawar jiki yace, “Hajiya watace ta kawo tace a bama Alhaji”.
       “Wata?!!!!!”
Ta faɗa cikin matuƙar hargagin da yajawo hankalin Basiru gareta.
   Karɓa tayi dan son tabbatarwa, ta juyo cikin falon sukaci karo da basiru daya taso, bangajeshi tayi ta zubar da flowers ɗin a falo ta fara ƙoƙarin buɗe????…..


????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????⛹????‍♀⛹????‍♀⛹????‍♀⛹????‍♀⛹????‍♀masoyan basiru.????????


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

            Cikin nasara su Ummukulsoom suka kammala exams, farin cikin data tsinci kanta a ciki ɓata lokacine, a randa suka gama a ranar da daddare su Attahir suka dawo, sai dai idonta baiga Amaan ba.
    

*_WASHE GARI_*

       Sanin gidan babu kowa ya saka Ummu fitowa kanta tsaye, sanye take da kayan barci farin wando dogo da riga pink wadda ta lafe a jikinta mai gajeren hannu, sai hula, wata baƙar yunwa ta tashi da ita kasancewar jiya tayi barci da wuri bataci abinci ba, gashi har takai kusan 11 tana barci tunda tana fashin salla.
        Kicin ta nufa kanta tsaye da addu’ar samun abu mai sauƙi, ganin babu wani abinci ta dafe kanta, yau maman Ahmad tea kawai tasha ta fita aiki, dama inhar Attahir baya gida bata zaman haɗa breakfast, tana zaton kuma shima tunda safe ya fita, Bily ma ta fita wankin kai.
      Tukunya ta ɗaukko zata ɗora noodles, gabanta ya faɗin jin ƙamshin turarensa, gakuma alamar tsayuwar mutum da taji tabbas a ƙofar kicin ɗin, tamkar mai ciwon wuya haka ta juyo dan tabbatarwa.
      Tsaye yake a sojansa, ya harɗe hannayensa duka a ƙirji, fuskarnan tamau babu alamar fara’a, busashen yawun daya tsaya mata a maƙoshi ta haɗiye tareda ɗauke kanta tamkar bata ganshiba, tahau ɗauraye tukunya.
        Cigaba yay da kafeta da mayun idanunsa, a ransa yana ƙara wadatuwa da mamakinta, wai ƴar tatsitsiyar yarinyar nan da aka kawo masa legos ce a gabansa haka?, ya lumshe fararen idanunsa ya buɗe akanta, kafin ya taka a hankali zuwa inda take a gaban gas tana shirin kunnawa.
       Jinsa dab da ita yasata rimtse idonta zuciyarta na ƙara gudu, amma sam ta dake a fili taƙi nuna masa hakan, saima cigaba da hidimarta da take.
       Tattausan hannunsa taji a saman nata dake ƙokarin murɗa gas, numfashinta dake neman ƙwacewa tai azamar fisgowa tareda yun ƙurin barin wajen.
      ya sake matse mata hannu a cikin nashi tareda fisgota ta dawo ƙirjinsa, idanu ta rumtse kafin tafara tureshi, “Wai miyasa kakemin hakane? Nace maka banaso niba ƴar iska baceba”.
      Ko motsi baiyiba, har yanzu kuma fuskar na nan tamau, sai dai a ƙasan ransa dariya ƙarfin halinta ke bashi……
      “Sakemun hannu”. Ta faɗa cike da tsiwa.
       Banza yay mata, sai ma kuma mannata da jikin dirowa ɗin kicin ɗin da yay, yasa hannu ɗaya ya ɗago haɓarta, yayinda ɗayan kuma ke rike da duka hannayenta a baya, kallon ido cikin ido sukaima juna, wasu abubuwa yake zuba mata dake neman karya garkuwar jarumtarta, tai azamar lumshe idonta tana tura masa baki da ƙokarin ƙwace hannunta………..✍????


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863


*_ƴan Niger kuma_*

_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*

*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*

 _TA NUMBER;_
 *+22795166177*   


Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button