NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 49

_NO. 49_*
*_Bilyn Abdull ce????????_*

 …………Koda maman Ahmad ta maido Ummukulsoom sashensu basu iske Amaan ba, ita takuma ɗan mata gyara kafin ta ƙara mata nasiha ta wuce akan sai sun haɗu a legas. 

       Tun Ummu na ɗari-ɗarin shigowar Amaan har ta saki jikinta, dan kuwa ko alamarsa babu har bayan sallar isha’i, kiran Bily tayi suka gaisa, tai mata yaya jiki?. Basu wani jimaba suka yanke wayar dan Muhsin na tare da ita, wayar Aziza ta kira, sai dai kuma a kashe, “A lallai amarcin naki mai lasisine Aziza” Ummukulsoom ta faɗa a fili, dan tun safe take neman Number Azizan amma a kashe, da su murja zasu wuce har saƙo ta basu akan su cema Azizar ta kirata, dan sunce can zasuje daga nan su kama hanyar gida.
         Buhayyah ce ta kawo musu abinci, bata wani zauna ba ta koma sashensu, dan tana shakkar Amaan yazo ya isketa a sashen.
     Tun dai Ummukulsoom na kawaicin rashin shigowar Amaan harta gaza ta fara kallon agogo, amma kamar almara har 10pm tama gota, jiki a sanyaye taje tai wanka ta fito, ko kallon abincin da Buhayyah ta kawo bataiba.
    Ganin fa wankin hula zai kaita dare sai ta fara lalubo Number ɗinsa daya bata a amatsayin Abdul-Waheed, sai dai tana kiran wayar sai taji ring ɗinta a ɗakin, waige-waige ta farayi tana kasa kunne wajen gane inda take, saman gado da take jiyota ta nufa, ta ɗaga filo sai taga wayar a wajen.
     *_Noorulain_*.
    Tsirama sunan ido tayi har kiran ya yanke, sai maimaitawa take a zuciyarta tamkar ta samu karatun salla.
      Amaan dake bayanta ya miƙo hannu ya zare wayarsa, a ɗan rikice ta waigo ta kallesa, tamau fuskarsa take babu alamar sassauci, ba tare da ta shiryaba idanunsu suka shige cikin na juna.
    Shine ya janye nasa cikin salon nasa na lumshe ido yana barin wajen, ta bisa da kallo ƙasa-ƙasa harya shige bathroom.
     Kaɗan ta sauke ajiyar zuciya, ta zauna bakin gadon tamkar wadda ƙwai ya fashema a ciki, ɗan sake matan da yayi daga jiya zuwa yau sai taji babu daɗi yanzu da fuskarsa ke a ɗaure matuƙa, ta ɗauki tsawon lokaci a wajen zaune, kamar yanda shima ya daɗe a bayin bai fitoba.
      Ɗaure da towel ya fito a ƙugunsa, yayinda hannunsa ke riƙe da ƙarami yana goge wuyansa zuwa ƙirji, kallo ɗaya yay mata ya lumshe idanu yana sauke numfashi da ɗan nauyi. Ko kaɗan bayason ganinta a yanayin damuwa, ya tako a hankali zuwa gareta, batare da Ummukulsoom tasan da zuwansa ba taji an janye hannun datai tagumi da shi.
    Kaɗan ta kallesa ta kauda ido saboda wata faɗuwar gaba da taji, ganinsa gabanta gingirin babu kaya ba ƙaramin harbawa zuciyarta tayiba dan tsoro, dama ga firarta da Bily ta ɗazun da safe ta kasa barin ranta, musamman ma furucinsa data yini dashi a arai tana tunani.
    Baice da ita komaiba yabar wajen zuwa gaban mirror, tamkar munafuka haka Ummukulsoom ta miƙe zata fita, harga ALLAH bazata iya zama yay shiri a gabanta ba, duk yana kallonta ta cikin madubin amma ya basar.
     Harta kama handle ɗin ƙofar zata murɗa yay magana da ƙyar, wadda Ummu ma sam bata jisaba.
      Kanta a ƙasa saboda batason kallonsa a yanayin da yake ta ɗan turo baki gaba tana faɗin, “Nifa banji mi kace ba ALLAH”.
      Juyowa yay ya kalleta sosai na wasu seconds, sai kuma ya ɗauke idonsa yana takawa gaban Wadrobe ba tare daya maimaita mataba.
   Takaici ya kama Ummukulsoom, ita kanta tasan zama da irinsu Amaan saika daure, dan takanji firar halin miskilamcinsa ga Attahir, duk da itama taɗan zauna dashi taga wani.
     Sai da ya ɗauko kayan barcinsa sannan ya koma gaban mirror inda ya ajiye wayarsa yay gajeren rubutu ya tura mata a waya.
    Wayarta tai ɗan motsi alamar shigowar saƙo,  Sam batai zaton shi baneba, dan haka ta kalli wayar zatonta ko Bily ce ko maman Ahmad.
     *_Coffee nakeso_*
Iya abinda ya rubuta kenan kawai, Kasa daurewa Ummu tayi, sai da ta ɗago ta kallesa, shima kallon nata yakeyi, dan haka ya ɗan langaɓe mata kai alamar “Please”.
     Batace komaiba ta girgiza kai kawai, dan wannan gayen addu’a kawai yake buƙata akan wannan halin nasa da babu mai rabashi dashi sai ALLAHN daya haliccesa da kayansa.
    Kusan Mintuna talatin ta dawo ɗauke da mug a saman ƙaramin tire da ruwa, da alama dai har sashen su Momcy taje ta haɗo masa, dan kayanta na nan babu abinda aka haɗa tunda ba zama zasuyiba, andai jibgesu a kicin ɗin ne kawai.
      Tashi yay daga kwanciyar da yayi a saman gadon, taɗan saci kallonsa saboda ya mata ƙyau cikin kayan barcin nasa marasa nauyi da suka lafe masa a jiki, ga wani ƙamshi na musamman yana fitarwa. Taja Copy table ɗin dake gefe ta ɗora tiren.
    Harta yunƙura zata bar wajen yay azamar cafko hannunta, rumtse idanu tayi ba tare da ta juyoba. “Mikake buƙata kuma?” ta faɗa a haka.
     Bai ce da ita komaiba ya jawota baya ta zauna saman gadon rabin jikinta a nasa. Gaba ɗayansu turaren junansu ne ya daki hancinansu, kowa ya shaƙa yana jin wani nishaɗi na musamman da saka ƙwanciyar hankali.
      Ganin bashi da niyyar magana bare sakinta sai ta ɗago ido ta kallesa, hakanne ya bashi damar janye hijjab ɗin jikinta, tai saurin riƙe hannunsa tana ɓata fuska, amma sam bai bata damar dakatar da shiba sai da ya cire shi. Ƙyawawan kayan barcinta pink suka bayyan, wandone iya gwiwa sai rigarsa itama dai bata da girma da hanunta siriri, sosai kayan suka zauna mata a jiki kasantuwarta mai cikar halitta da murjewar jiki. Babu shiri Amaan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yayinda ƙasan zuciyarsa shawarar Attahir ke dawo masa dalla-dalla.
    Ummukulsoom kam fuskarta ta ɗora saman damtsen hannunsa saboda harga ALLAH taji kunya ta kamata, zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa jin ya saƙalo tattausan hannunsa ta bayan ƙugunta ya ɗorasa saman cikinta.
      Duk yanda taso ta fuske saita kasa, ta kama hannunsa zata janye ya kuma ƙanƙameta, murya na rawa tace, “Dan ALLAH ka bari, wlhy hakan bashi da ƙyau”.
    Taso bashi dariya, amma kasantuwarsa gwanin ɗaurewa saiya fuske yana ɗaukar coffee ɗinsa da ɗayan hannun ya hau shan kayansa a hankali yana wani lumshe ido.
     Ita kam ta gama sakankancewa da halin Amaan gaskiya, sai kace wani kurma…?
     Haka kawai yaji a ransa gulmarsa take da zuciya, dan haka yaɗan mintsini gefen cikinta.
     Babu shiri ta ƙankamesa tana sakin kukan shagwaɓa da kiran sunan Ummi, dan ta ɗanji zafi.
     Kofin ya ajiye ya maido dukkan hankalinsa gareta, “Kinci abinci?” ya faɗa a hankali kamar bayaso.
     “Ni na ƙoshi, ka sakeni barci nakeji wlhy”.
     Baice mata komaiba ya jawo ledar daya ajiye da hannu ɗaya, kallonta yay yana mata alama data buɗe ledar.
    Kamar zata sharesa sai kuma ta kasa, dan ta tuna nasihar Inna laraba ta ɗazun a gareta.
      Gasashshen kifine irin na musamman ɗinnan, ya haɗu iya haɗuwa, dan babu shiri yawun bakin Ummu ya shiga tsinkewa, a ranta kuwa rayawa take shi ango na zuwa da kazar amarci shi da kifi yazo, kai wannan bawa lamarinsa sai shi…….
       Tunaninta ne ya katse jin yatsansa saman laɓɓanta tare da kamshin kifin da yasha gashi, kauda kai taso yi zatai magana ya tura mata kifin a baki. Duk yanda Ummu taso zamewa kar taci kifinnan Amaan ya hanata kowacce damar kufcewa, dole ta haƙura ya bata da kansa iya yanda yaso.
    Shiko ko kaɗan bai ciba, ya kama hannunta zuwa bayi wai zai mata brush, yanzun kam ƙin yarda tayi sam, sai shima kawai ya barta yay alwala ya fito.
     Da harara ta raka bayansa, sannan itama tai alwalar kasancewar ta riga ta saba a duk dare idan zata kwanta sai tayi koda kuwa tana prioud ne.
       Zaune ta iskeshi bakin gado sanye da jallabiya saɓanin kayan barcin, ta ɗauke idonta zata nufu gado ya dakatar da ita da faɗin, “Tashi muyi salla”.
      Dakatawa tayi da yunƙurin kwanciyar ta zuba masa ido jin yanda yay mata magana murya a dake, sannan fuskarsa babu walwala. Wani kwarjini na musamman taga ya sake mata, ta sakko domin bin umarninsa tamkar yanda addini ya koyar da ita da tarbiyyar musulinci.
      Hakan yasaka Amaan jin daɗi da karajin kaunarta, ya kuma aminta da tarbiyyar Ummukulsoom hundred percent, ita ɗin ƴar ƙwarai ce mai bin umarnin iyayenta da aiki da ilimin islama ba wayewar boko ba dajin itama ta isa akan komai, musamman ma dashi ya kasance mai laifi a gareta, ashe dai ƙaryar mutane dakema mata kudin goro wajen faɗin dasun samu zurfin ilimi saisu zama bijirarru masu ra’ayin kansu saboda sunajin kansu dai-dai da kowa, wato abin ba’a bokon yakeba atarbiyya yake, tun farko daga yanda tarbiyyar mutum ya tashi to haka dukkan rayuwarsa ke wanzuwa koda shine yaga karshen biro kuwa.
    Sun gabatar da salla raka’a biyu, Amaan ya juyo ya dafa kan Ummukulsoom yana ambaton addu’ar nan da duk wanda yay sabon aure ya kamata yayita ga iyalansa.
    “اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.
*_Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha ‘alayh, wa-a’oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha ‘alayh._*
       _Ya Allah ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi’antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi’antar da ita a kansa._
        Kan Ummukulsoom a duƙe harya kammala ya janye hannunsa yana ɗaga hannunsa sama da cigaba da jero addu’a, sai dai kuma a ɓoye ba’a filiba.
      Itace ta fara miƙewa ganin sun kammala, gaba ɗayan jikinta a sanyaye yake, shi kansa ya gama lura da ita tsaf, amma sai ya basar kawai. 
    Can ƙarshen gado ta kwanta ta juya masa baya bayan ta cire hijjab da zanin jikinta, uffan baice mata ba, sai baima hau gadonba yaja wayarsa yana danne-danne tsawon lokaci har barci ɓarawo ya sace Ummukulsoom. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya tashi ya kwanta shima.
     Tamkar yanda suka kwana jiya yauma hakane ta kasance, da asuba yau ta rigashi tashi, motsinta a bayine ma ya tashesa.
     Koda ta fito bata amince sun haɗa ido ba ta raɓa gefensa ta wuce inda abin salla yake. Shima alwalar yayi ya fice.

     Yau kam har gari ya fara haske bai shigoba, ga hadari daya ɗaure garin kasancewar damuna taɗan fara zama, sai zuwa can lokacinma Ummukulsoom ta gama gyaran ko’ina tasa turaren wuta ya shigo, har iskar hadari mai fidda ƙamshin ƙasa ta fara busawa a hankali.
     Shigar Ummu bayi kenan Amaan ya shigo, da alama dai motsa jiki ya zarce saboda ganin hadari, dan jikinsa sai zufa yake dukda iska mai sanyi da saka jiki kasala da akeyi kuwa, duk da yasan tana ciki saboda neman magana sai ya cire kayansa ya nufin bayin. Murɗawar farko ƙofar ta buɗe, Ummukulsoom dake zubama jikinta ruwan dumi wani daɗi na ratsata taji an buɗeta.
    Yanda ta ɗago kawai zai tabbatar maka tashiga ƙarshen firgita da ruɗani, musamman datai tozali da wanda bata taɓa zato ko tsammanin ganiba, ta dunƙule jikinta waje ɗaya bayan ta duƙe zata kwalla ƙara…
      Ko’a kwalar rigarsa shikam, amma ganin zatai ihu ne ya sashi isa gabanta cikin taku biyu kacal ya dora tafin hannunsa akan bakinta.
     “K lafiyarki kuwa?” yay maganar cikin kunnenta a hankali.
     Hannunsa ta fara turewa hawaye sun cika idonta taf, sai dai yaki bata damar cirewar, saima towel ɗin jikinsa daya saki ƙasa tare da sakar musu ruwan yana zuba a jikinsu.
        Yau kam Ummu takuma ƙara tabbatar da rashin ta idon Amaan, shi komai nasa kai tsaye yakeyinsa, babu ruwansa da dai-dainsa ga waninsa ko akasin haka, indai shi yay masa dai-dai to dole yazama dai-dai ga kowama da abin ya shafa.
        Da kansa yay mata wankan idonta arufe, hakama hannunta ta rufe ƙirjinta dashi ruf, duk dai yanda yaso ta saki jikinta ayi wankan ƙi tayi, dole ya wanke mata iya inda zai iya ya ɗaurayeta tare da ɗaukar bathrobe kalar ruwan toka ya saka mata, ko sashen da yake bata kallaba, tai azamar fitowa ta barsa a bayin saboda wani kuka da taji ya taho mata ba tare da tasan dalilin yinsa ba.
         Amaan ya lumshe idanu ya buɗe a hankali fuskarsa na fidda wani ɓoyayyan annurin murmushi.
     Koda ya fito saiya iske Ummukulsoom kwance a gado rufda ciki tana shashshekar kuka..
     Sosai ta bashi mamaki, to miye abin kuka anan? Sai kace wani abun ashsha suka aikata, Cike da nutsuwarsa yazo bakin gadon ya zauna yana ɗora hannunsa saman bayanta, ko motsi ƙinyi tayi duk da tanajinsa.
    Jikinta ya kwanto sosai ya sakar mata nauyinsa har numfashinta na fita da ƙyar.
      “Yanzu nan dan kin samu ladan yin wanka da mijinki shine abin kuka? Indai hakane to bara na kawo ƙarshen komai kawai ki kuma tabbatar da cewar Usman mijin kulsoooom ne”.
      A yanayin daya karasa sunanta da yanda yake mata raɗa a kunne sai gaba ɗaya tsigar jikinta ta tashi, ta haɗiye kukanta babu shiri jin yakuma sanyaya murya da narketa yana cigaba da faɗin, “Ki karɓa, ALLAH ya riga ya baki indai Amaan ne”.
    Haushi ya kama Ummukulsoom, an faɗa masa damuwa tai dashine, “Ai ni bana amsar abinda bai minba” ta faɗa cikin gatse.
      Birkitota yayi ta dawo rigingine, ya zuba idanunsa cikin nata dake zabga masa harara tana yunƙurin kwacewa, iya ƙarfinsa ya matseta tare da canjama kallon nasu sabon salo ta hanyar ɗora fuskarsa kan tata ya  haɗe b…..”
        A salon da yake binta duk jaruntarta kasa jurewa tayi sam, dan tariga da takai age ɗin da  jikinta yasan ma’anar saƙonsa, tun tana ɗaukar lamarin da wasa harya fara caja mata kai, dan tuni ya canja layi ma gaba ki ɗaya zuwa abinda sam bata kawo a ranta ba, musamman a yanda yay biris da ita a kawanki biyunnan, ko jiya daya nuna mata take-takensa daga ƙarshe ai basar da ita yayi.

★★★★★
       Sabon salo kenan, anguna na angwanci da daddare shi da safe yay nasa.
    Ummu kwance luf a jikinsa tana tsiyayar da hawaye masu ɗumi dake sauka a saman ƙirjinsa, shiko har cikin zuciyarsa yake jin saukarsu, sai dai sam yakasa buɗe baki ko sau ɗaya yay mata magana, sai faman shafar sumar kanta daya hargitsa yakeyi a hankali yana sauke tagwayen ajiyar zuciya shima.
       Wani so na haƙiƙa mai ratsa zuciya da ɓargon jiki yakeji akan Ummukulsoom, ji yake kaf duniya yafi kowa sa’ar mace ta gari, dama a ko yaushe cikin ƙyautata mata zato yake, sai gashi kuwa ya zama na farko a gonar da ALLAH yay masa ƙyauta ba tareda wayonsa ba ko dabararsa, kuma ƙanƙameta yayi a ƙirjinsa, yakai bakinsa saman goshinta ya sumbata sau biyu zuwa hancinta yana cigaba da sauke ajiyar zuciya tamkar shike kukan ba Ummukulsoom ba.
      A tare barcin wahala ya kwashesu, dai-dai sannan kuma ruwa ya kuma ɓallewa tamkar da bakin ƙwarya, yayinda garin ke kuma ɗaukar wani sanyi mai saka zuciya nutsuwa musamman idan kana tare da abin sonka.
  
     Barcinsu sosai sukasha, ita Momcy duk ta damu ba’a kawo musu breakfast ba, haka ta taso Bassam cikin ruwan ya kawo musu breakfast ɗin, tsit yaji falon, dan haka ya ajiye ya juya ya fita gudun aikata wani laifi.
         Kamar wasa barci yaja su Ummukulsoom har ƙarfe ɗaya na rana, kuma har lokacin ba’a daina ruwa ba …………..✍????



*_Insha ALLAHU akwai Bonus zuwa anjima, amma bazanyiba sai naga yanda team Amaan da team Ummu zasu kwashe yau????????????⛹????‍♀️_*

_A kwankinnan duk wanda ya turamin massege ta pc yayi hakuri da rashin ganin reply, kunsan haƙori da ɗaukar hankali, typing ɗinma ina daurewane kawai saboda inada pages biyu dama a ajiye, shine naɗan muku editing ɗinsu na tura shekaran jiya da ranar litinin, nagode sosai da addu’oinku gareni, ALLAH yabar zuminci, so irin trillions ɗinnan my kankanatis????????????⛹????‍♀️????._

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button