WUTSIYAR RAKUMI 51

*_NO. 51_*
………..Ummukulsoom na zaune a inda tai sallar isha’i tana duba massege ɗin da Bily ta turo mata Amaan ya shogo.
Kaɗan ta ɗago idanu ta kallesa ta maida ta sunkuyar, sosai take jin
kunyar haɗa ido dashi tunda abin nan ya faru a tsakaninsu, shiko tuni ya harbo jirginta, amma da yake gwanine na basar da abu sai bai taɓa nuna ya fahimta ba.
Ya zaune a bedside drawer da Ummu ke gab da ita zaune, dan har ƙafarsa na gogar jikinta, waya yake tunda ya shigo, amma inba ka saka kunne a wajenba bazaka taɓa jin abinda yake faɗaba.
Idonsa na akan Ummu data tsirama waya ido tamkar gaske karatun take, sai dai a baɗini tuni ta bar karatun ta koma kallon ƙafarsa da sauraren wayarsa.
Kusan mintuna biyar kafin ya yanke wayar yana sauke ajiyar zuciya, “Please ɗan bani ruwa”. Yay maganar idonsa akan wayarsa.
Duk sai Ummu taji kunya, dan a ganinta baima dace ace saiya roƙa ba, wayarta ta ajiye ta miƙe, ya bita da kallo ƙasa-ƙasa, dan ash color hijjab ɗin ya mata ƙyau sosai, sai da yaga ta fice ya ɗauke idonsa yana miƙewa, kayan jikinsa ya hau zarewa dan wanka yakeson yi.
Ummukulsoom data shigo da sallama kallo ɗaya tai masa ta janye idanunta zuciyarta na wata iriyar harbawa da ƙarfi, itakam dai batason wannan rashin kunyar tasa, banda rashin ta ido minene abin cire kaya ya zauna mata da ga shi sai boxer da best a ɗaki.
Yanzunma waya yake dannawa, ta ajiye ƙaramin tiren data ɗoro ruwan gabansa ba tare da ta yarda ta kallesa ba, gabansa ta durƙusa ta zuba masa a cup tare da miƙa masa idonta a ƙasa.
Tattausan hannunsa ya ɗora akan nata dake riƙe da kofin ruwan, jin yanda ya riƙe ɗinne ya tilasta ta ɗago fararen idanunta taɗan kallesa. Caraf idanunta suka shige cikin nasa daya kafeta dasu, saurin janyewa tayi tana shagwaɓe masa fuska.
“Dama haka ake ba miji ruwa?” ya faɗa a hankali.
Shiru bata iya amsawa ba, sannan ta kasa sake kallonsa, shima bai sake cewa komaiba ya janye kofin gudun kar sanyin ruwan ya cutar da ita, har zata miƙe tana hamdala a zuciyarta taji caraf ya riƙo hannunta. Kasa juyowa tayi, shikuma baice komaiba har sai da ya gama shanye ruwan data zuba masa. Kofin ya ajiye gefe yana ɗan girgiza hannun nata, dole ta juyo ta kallesa, kasancewar shima ita yake kallo suka sake haɗa ido.
Lallausan murmushin daya narkar da zuciyarta ya sakar mata, mai tsadar da kafin yayisama aikine, ita kanta yaune ta fara ganinsa a fuskarsa, dan kuwa fararen haƙoransa saida suka bayyana. Kasa janye idanunta tayi daga garesa, sai ta tsinci kanta da kafesa da ido ba tare data shiryama hakanba. Kusan minti biyu suna a haka, ring ɗin wayar Ummu ne ya dawo dasu hankalinsu, kowanne ya sauke ɓoyayyar ajiyar juciya, Ummu ta zare hannunta a nasa ta ɗauki wayar dan duba wanene.
Shima miƙewa yay ya nufi toilet zuciyarsa na wani irin harbawa, tabbas yau ya hango soyayyarsa a idanun Ummu sosai, sai dai baisan miyasa take ɓoye masa ba, kokuwa har yanzu bata huce bane oho?. da waɗannan tunane-tunanen ya fara wankan.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }()); Ummu kam ficewa tai falo tana amsa wayar Bily dake mata dariyar shaƙiyanci, dama tun a asibiti take mata idan ta kira jin yaya jikinta? Sai dai acan bata kulata, yau dai ta biye mata sunata kwasar rashin arziƙinsu da suka saba, daga ƙarshe suka shirya tare da faɗawa hirar yaushe gamo.
Koda Amaan ya fito bai iske Ummukulsoom a ɗakinba, shirinsa yayi mai sauƙi cikin wandonsa dako gwiwa bai kaiba, sai riga mara hannu, yasa turarensa mai ratsa zuciyar mai shaƙa. lap-top ya ɗauka da wasu takardu ya fito falon shima, dan yasan dai nan Ummukulsoom ta gudo.
Har yanzu Ummu waya take, tana kwance cikin doguwar kujera.
Kujerar dake gefen inda kanta yake ya zauna, ya ɗora kayan hannunsa a table ɗin gabansu yana mai miƙa hannu ya zare wayar daga kunnenta.
Da hanzari ta miƙe zaune zatai masifa sai taji ƙamshin turarensa, ALLAH ta zata ko cikin ƙannan sa ne, dan ba ƙamshin turarensa data saniba taji…
Wayar ya saka a kunne bayan yaga bily ce, “K ina kika bar mijinki? Kika zo nan zaki ishemu”.
Jikin Bily har ɓari yake daga can wajen fadin, “Afuwa yaya Amaan, sai da safe”.
Shi baima jira amsarta ba, dan tuni ya ajiye wayar yana zubama Ummu dake kumbura baki mayun idanunsa, gira ɗaya ya ɗage yana lumshe ido da buɗesu kan table ɗin daya ajiye lap-top ɗinsa.
“Karki ce ban sanar mikiba, daga yau idan ina gida dukkan hankalinki nake bukata gareni, bana bukatar raba dai-dai ɗin lokacina da kowa”.
Cike da mamakin ƙarfin hali irin nasa ta ɗago ido ta kallesa, lip ɗinsa na ƙasa yaɗan ciza alamar tabbatar da gargaɗinsa.
Ummukulsoom ta janye idanunta kawai ta maida kan yatsun hannunta da take lanƙwasawa suna ƙara.
Shiru babu wanda ya sake magana, shi yanata ƙokarin dai-daita system nashi, itako tana juya maganar dake son fitowa bakinta.. Ganin bata da mafita tace, “Abinci fa?”.
Kallonta yayi ya janye idonsa, sai kuma ya maida lap-top ɗinsa sama table ya ajiye, “Zonan” yay maganar yana miƙa mata hannu.
Kamar bazata motsa ba, sai kuma ta muskuta kaɗan alamar son tashin amma ta rasa abinda ya hanata yunƙurawa.
Hannunsa ya miƙa sosai ya kamo natan cikin nasa, yay mata alamar ta miƙe da ɗayan hannunsa, koda ta miƙe ɗin jawota yay ta zauna a cinyarsa, yasa hannu ya zare hijjabin jikinta, duk yanda taso hanashi sai kuma ta kasa, ba komai bane ke taka mata birki ga aikata wani abun sai nasihar iyayenta da tsoron saɓama ALLAH.
Yanda ya zubama ƙirjinta idone abin ya matukar bata kunya, sai dai shi ko a kwalar rigarsa, dan babu alamar wani jin kunya tare da shi.
“Mrs Amaan wai har yanzu dai?”.
“Har yanzu dai me?” ta faɗa tana kallonsa ido cikin ido ba tare da tasan ta yaya ta samu jarumtar hakanba.
Shima haka ya kafeta da nasa, “Daga yanzu haka nakeson ki ringa min magana kai tsaye”.
“Murmushi taɗanyi tana janye idanunta cikin nashi”.
Shiru sukai su duka, shi dai ya fara ƙosawa da yawan maganar ne, a hakanma yasan yayi ƙololuwar ƙoƙari, dan so yake Ummu ta saki jiki dashi sosai. Daurewa yay ya kuma cewa, “Yanzu baƙya tsoron ki bani abinci naci ki kasa ɗaukata Beauty?”.
Sarai ta fahimci inda ya dosa, amma tsabar son ta manna masa shorme sai itama ta yatsina fuska da cewa “kamar ya?”…….
Kafin ta rufe baki ya mannata da jikinsa sosai ya haɗe fuskarsu waje ɗaya, duk yanda taso ƙwatar kanta ta kasa, sai da ya sumbaceta iya yanda yake so sannan ya saketa da faɗin, “Kamar haka”.
Cusa kanta tai cikin ƙirjinsa, lamarin Amaan sai addu’a, dolene ta ajiye komai ta rungumi mijinta dan yana bata farin ciki sosai, miskilancinsa ne kawai matsalarta gaskiya, wannan kam tasan sai dai haƙuri, dan bata isa canja abinda ALLAH ya gina ba.
Hannunsa na saman kanta yana shafa gashinta dake fidda ƙamshi mai daɗi, harga ALLAH yana ƙaunar wannan halitta, harma baisan yanda zai musalta ba a fahimta, babban fatansa ALLAH yasa itama tai masa koda rabin son da shi yake matane.
Da kanta ta tashi daga jikinsa, ba tare da ta yarda sun haɗa idoba ta nufi dani inda Buhayyah tazo ta ɗaura abinci.
Da kallo kawai yaɗan bita yana janye idonsa, ya ɗauki biro da takarda yay ɗan rubutu.
Ummu da taga abincin bamai nauyi bane saita zuba masa dai-dai misali ta dawo falon, lokacin harya ɗauki system ɗinsa ya ɗaura akan ƙafa ya fara aikinsa, zama tai a kujerar kusa dashi da take zaune da, kasancewar hannun kujerar ya haɗu waje daya sai ta ɗaura abincin saman hannun tana faɗin “Ga abincin”.
Ba tare da ya kalleta ba ya nuna mata takardar daya ajiye saman table. Ɗauka Ummu tai tana dubawa.
*_Gobe idan ALLAH ya kaimu zamu koma lagos, ana mini neman gaggawa a Office_*.
Da mamaki a fuskarta ta kallesa, kamar zata share sai kuma ta tanka, “Gobe da wuri haka? Kofa gidan yaya Zaid da Bily banjeba, ga Inna harira ban mata barka da tashin baƙiba. Indai dan tanice kaje kawai ni daga baya saina taho k…….”
Kallon daya zuba mata ne ya hanata ƙarasawa, ta haɗiye sauran maganar a hankali. Shima sai ya fasa maganar dake yawo a maƙoshinsa kawai yana ɗauke kansa.
Bata sake magana ba, saima wayarta data ɗauka ta shiga danne-danne.
Shima Uffan bai sake tofawa ba ya cigaba da aikinsa, kusan mintuna Uku Ummu taga idan ta biye masa sai bakinta yay wari, duk da itama bamai yawan magana bace amma idan tana gaban Amaan zata iya zama Aku.
“Wai nikam abincinfa kawu?”.
Ta kare maganar cike da tsokana, dan goge laifinta.
Kallonta yayi jin wai shinema Kawu?, hannu yakai saman kunnenta ya ja da murɗawa.
Babu shiri Ummukulsoom ta riƙe hannunsa tana fadin, “Wayyo ALLAH yaya Attahir zai kashe muku ni”.
Bai saki kunnenba, sai dai fuskarsa ta rage rashin walwala alamar maganarta ta bashi nishaɗi dai….
“Dan ALLAH kayi hakuri, wlhy akwai zafi fa”.
“Sake maimaitawa” yay maganar ciki-ciki da sake murɗe kunnen.
“A’a na tuba aminin yaya Attahir ”.
Yanzu kam dai kasa daurewa yay saida ya murmusa, Ummu ta rigada taga gadon barcinsa ai dama tuni, daga ita sai Attahir ne suke masa yanda sukaso ya ɗaga musu kafa, dan sunriga da sun zama wani sashe na rayuwarsa mai ƙarfin gaske bayan ahalinsa.
“Hukuncin ki shine bani abincin nan a baki harna koshi”.
Azabar da Ummukulsoom keji ce ta sata saurin amsa masa da eh zatayi, babban burinta dai ya saki kunnen.
Saki kuwa yayi, ita kuma tahau kumbura baki da faɗin zata ramane, baice da ita uffanba ya kawo hannu zai sake damƙar kunnan ta tare tare da ɗaukar cokali ta ɗiba abincin, baki ya buɗe ta zuba masa yana kashe mata ido da ƙyafta idanu.
Haka dole taita bashi abincin yanaci yana aikinsa, saida yaji ya ishesa ne ya ɗaga mata hannu alamar ya isa.
Harta fara murna zata gudu taga ya tsareta da idanu yana mata alamar wai itama taci, kai ta girgiza masa, ya harare ta yana haɗe fuska tamau.
Dole dai taci itama dai-dai misali. Sun jima a falon yana aiki itako tana danna waya har aka maido wuta, lokaci-lokaci Amaan kan amsa waya koshi ya kira da kansa ma. Sai da Ummukulsoom taji ta fara hamma ta miƙe ta barsa, dan ita tariga da ta saba barcin wuri.
Bai hanata ba, ta shige abinta tai shirin barci tai kwanciyarta da addu’ar ALLAH yasa kar Amaan yace zaizo mata. Babu jimawa kuwa barci ya kwasheta saboda tana bukatarsa sosai.
Wajen 12 Amaan ya miƙe, yasan dai Ummukulsoom ta jima da yin barci kam, ilai kuwa yana shiga ya isketa tayi barcinta. Bai tasheta ba shima yay shirin barcin ya haye gado, hadari nata cida alamar ko yaushe ruwa zai iya sakkowa.
Jikinsa ya sanya Ummukulsoom yana gyara musu bargo, ko alama bai yunƙurin mata komaiba, yay Addu’a shima ya kwanta. Cikin barci yaji Ummu tana kuma lafewa a jikinsa alamar ɗumin jikin nasa ya mata daɗi sosai, dan har an fara ruwa.
*_Washe gari_*
Su Ummukulsoom suka tashi da shirin komawa legas, duk yanda taso zuwa gidan Bily da Aziza Amaan ya kafa ya tsare, danma karta damesa sai ya miskile fuska, dolenta ta hakura tai musu sallama a waya ranta na ƙuna.
Sabuwar nasiha Dad daya dawo daren jiya yay musu, tareda jera musu kalmomin addu’ar zaman lafiya da gargaɗin Amaan akan Ummukulsoom. Itama Momcy ta dora nata bayan ta nemi gafarar Ummu, hakama yaran gidan su Aneesa da zasu wuce gidajensu suma duk sai da sukazo suka roki gafar Ummukulsoom akan abinda sukai mata a baya da, Jud kam dama tunda ta tare gidan yake mata wani ladabi na musammam, dan a rayuwarsa yana matukar ganin girman Amaan a gidan, sam babu ruwansa ko taka haƙƙin wani da akan sani, sai dai idan da kuskure.
ƙarfe huɗu suka baro gidan, Momcy harda ƴan hawayenta, dan taso Amaan yabar Ummukulsoom taɗanyi wata ɗaya anan su sake sabawa, taima Ummu gatan data gaza mata a baya, sai dai sam yaƙi yarda da hakan, ta juyashi dambu da takiya yace ai Ummukulsoom bata kammala abinda ya shafi karatun ta ba, ko yaushe za’a iya nemanta a makaranta. Babu yanda Momcy ta iya ta barsa da matarsa tare da binsu da addu’ar fatan alkairi.
Sai da suka biya gidan Abba da gidan Hajiya yaya, sai dai duk basu jimaba suka fito. Ameer ne ya kaisu airport, bai taho ba kuma sai da yaga tashinsu.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Tsawon lokaci babu wanda ya sake jin ɗuriyar basiru, iyayensa tun suna kauda kai har abin ya fara damunsu, dan kuwa tun zuwan da yay so ɗaya bayan dawowarsu bai sake waiwayensu ba.
Inna tun tana jin zata iya jurewa harta gaza, dama lokacin da suka tafi faransa haka taita ciwo a tsaye na damuwar rashin basirunta.
Baba da kansa ya shiryo shida wani yaron innar basiru daya zauna a wajenta sannan yana karatu a zaria sukazo katsina kozasuji labarin basiru.
Kai tsaye gidan gwamnati sukayo, sai dai fa wane mutum inji mutuwa, sam sun kasa samun damar koda ganin mai gadin gidan ballema mutanen ciki, tun suna zarya da marmari har suka fara jigata……
Meenal kam duk da son da takema Basiru a baya zuwa yanzu sai taji ta gama tsanarsa, dan kuwa tanada tsananin kishi, sai da bayan an kama basiru ne ma taga ɓarnar kuɗi da yay mata ba tare data saniba, wasu maƙudan kudinta data ajiye agidan zatai amfani dasu akan wani muhimmin abu basiru yay sama da fadi dasu ashe.
Hakan saiya sake bata takaici, ga ƴan iskan ƴanmatansa koda yaushe cikin kiransa da turo masa saƙo suke na rashin mutunci dake neman saka zuciyarta bindigewa, har sawa tai ai mata tracking numbers ɗinsu sai dai babu wani abinda aka samu daga garesu, da alama dai da shirinsu suma.
Wannan abu sai ya nemi zarar da Meenal, ga su Suhailat data ɗauka aminanta yanzu suna kuma tunzurata a gefe da yake ta sanar musu komai, taso ƙona wayar basiru mom nata ta karɓe akan cewar wayarsa hujjace babba a garesu koda anan gaba wani abu ya taso, dan haka ta ɓoyeta ta hana Meenal ƙonawa.
Maganar auren basiru dake a kanta kuwa babu wanda yabi ta kansa, ita kuma bata fasa dukkan abinda tai niyyaba balle tuna akwai wani aure a kanta.
A haka aka shari tsawon lokaci Basiru na jail yana cin gabza, tsabar zalinci irinna manyan mu saima aka ɗaukesa aka saka cikin gagga-gaggan ɓarayi waɗanda aka yankema hukuncin kisa, basiru duk ya koɗe ya jeme cikin lokaci ƙankani, babu abinda ke tada hankalinsa da cin zuciyarsa a halin yanzu irin iyayensa da basusan halin da yake ciki ba, duk wanda yasan basiru ɗan gayu ɗan ƙwalisa, mai ɗaukar mata ya yada tamkar laidan ruwa, bayan ka shanye ruwan ciki ya gama maka amfani ka yarda ledan, to yanzukam ka gansa sam bazaka ganesa ba, wahala ya ke sha a cikin waɗanda aka sakashi, har dukansa sukeyi sosai. Kuka kullum babu fashi sai basiru yayisa, tun yanayi da hawaye harya koma da zuciya da ƙwanji.
To dama masu iya magana kance *ɗan hakkin daka raina shike tsone idonka*. _wanda ya taka rawar wani kuma watan wata rana shi zai rasa filin taka tasa_. *Tsuntsun da yaja ruwa shine ruwa ke doka*. _Duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba tashi ko ɗumi ma baza tayiba_. *Duk abinda ya saka dariya wataran shine zai saka kuka*. _Yau dai ga matan da Basiru ya raina sun zame masa *WUTSIYAR RAƘUMI…*_????????
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Su Ummukulsoom sun isa lagos lafiya, inda Attahir da kansa yazo ya tarbesu, a fakaice Attahir keta tsokanar Amaan da idanu dan kar Ummukulsoom ta gani.
Tun yana basar dashi harya kai masa duka. Gocewa Attahir yay yana dariya da faɗin “Kai malam nifa yayanka ne yanzu wlhy”.
Amaan ya hararesa yana yin gaba ya barshi shi da Ummukulsoom dake musu dariya kasa-ƙasa, wannan abota ta dade tana birgeta, dan cike take da ƙaunar juna da tsantsar amana.
Cikin ɗaga murya kaɗan Attahir yace, “Badai kayi gaba ba, to sai kazo bikon ƙanwata gidan babban yaya”.
Cak Amaan dake shirin shigewa falonsa ya tsaya.
Attahir ya kalli Ummukulsoom yana faɗin, “ƙanwata shiga mota muje”.
Cike da son ganin yanda za’a kwashe Ummukulsoom tai yunkurin komawa motar da attahir ya ɗakkosu…
Ji kawai tai an ɗauketa cak, saita rikice sabo tsabar al’ajabinsa da mamaki, sam batai zaton zaiyi hakan gaban Attahir ba.
Dariya Attahir ya shige mota yana yi, Ajiwa nashi kenan, mai abubuwan birgewa dana mamaki, harma da takaici.
Duk da Amaan yanajin Ummun bata wasan yara bace wajen ɗan nauyi hakan baisa ya direta ba sai da ya shiga falonsa da komai ya canja. kai tsaye bedroom nashi ya nufa da ita, ya direta akan gadon shima yana kwanciya da sauke numfashi, sarai Ummukulsoom ta fahimci ya gaji ne, amma tsabar neman tsokala sai catai “Ya kamata na ƙara ƙiba kodan ka bar gigin min irin wannan ɗaukar amaryar a gaban yayana gaskiya”.
Juyowa yay ya kalleta, sai ta basar tana maida kanta gefe dariya na tsunkulinta.
Shima ɗauke idonsa yay daga kanta ya tashi zaune, tasan shirunsa na nufin ba yanzu zai maida murtani ba, sai ma ta gama mantawa da anyi sannan????………✍????
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
*_ƴan Niger kuma_*
_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*
*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*
_TA NUMBER;_
*+22795166177*
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????