WUTSIYAR RAKUMI 55 & 56

Ɓangaren Ummukulsoom kam kamar yanda ta gana da Suhailat tai mata jagoran ganinsu Lubna a wancan karon, wannan karonma Suhailat ɗin ta kuma nema, dukda kuwa tayi nauyi da cikinta tsoho haihuwa yau ko gobe, lubna kuwa harta juyo, hakama Fannah dake da biyu.
Randa aka halarci zaman kotun da Ummukulsoom take fata da addu’ar ya zama na ƙarshe da ƙyar ta kawo kanta saboda rashin jin daɗin jiki, dama saida Dad ya saka baki Amaan ya bari ta baro lagos, shi bama ya ƙasar kusan sati biyu kenan, amma yaso hanata saboda yasan batajin daɗin jikinta.
Sai da Dad yay masa magana sannan ya haƙura, amma ita kanta tasan badan yaso hakan bane, dan haka kafin su shiga kotun ta kirasa tace yamata addu’ar nasara karta shiga bada son ransa ba komai ya lalace.
Guntun murmushi yay daga can wanda har tana jiyo sautinsa, waɗannan halayyar na Ummukulsoom ne ke ƙara masa ƙaunarta a zuciya, komanta yanada tsarinsa bisa ga bin dokokin addininta na islama, sam bata da ra’ayin jeka nayika irin na wasu matan yanzu dake jinsu kafaɗarsu dai-dai data miji, takan kalli mi addini yazo dashi bawai ra’ayin kaiba ko ƴanci.
Cikin sanyin murya yace, “ALLAH ya bada nasara Mrs Ajiwa, in har kika samo na sara a wannan shari’ar zan miki ƙyauta mai tsoka insha ALLAHU”.
Wani farin ciki taji ya kamata, ta lumshe ido tana sakarma wayar sumbar data saka jikin Amaan dukya saki daga can, Bily ta riƙe haɓa tana kallon ikon ALLAH, soyayyar Ummukulsoom da yaya Amaan abar birgewace da tarin sha’awa ga kowacce ƴa mace dake gidan miji, a duk lokacin da ɗaya ya ɗau zafi a cijinsu saikiga ɗayan ya kwantar dakai, basu taɓa yarda su ɗau zafi a lokaci ɗaya, wannan ne ya ƙara girmama zaman lafiya a tsakaninsu, koda saɓanin yazo saikiga yazo da sauƙi.
Tsokalema bily ido Ummukulsoom tayi tana faɗin “Kallonfa madam?”.
Bily da taji zafi taima Ummu dundu mara zafi a baya, “Wlhy yau badan babyna dake cikinki ba dasai na rama, muguwa kawai, duk salon muguntar yaya Amaan kin gama kwasheta.
Dariya Ummukulsoom tayi tana ɗaukar ƙatuwar rigarta ta lauyiyi ta ɗora saman rigar abayarta oxblood, ta ɗora hular saman baby hijjab ɗin dake wuyanta, tayi ƙyau sosai, dan saida Bily tai musu hoto, suna shirin shigewa dan angama shari’ar da bayan ita za’ai tasu sukaci karo da A’i tana kuka.
Sam A’i bata gane Ummukulsoom ba, sai ita Ummukulsoom ce ta gane A’i ɗin.
“Wanake gani nikam kamar A’i?”.
A’i dake share hawaye da bakin zani ta fyace bajina ta goge da gefen zaninta tana kallon wannan haɗaɗɗiyar mace dake gabanta tana mata magana, jikinta har karkarwa yake wajen ƙarema Ummukulsoom kallon tsaf.
Murmushi Ummukulsoom tayi tana gyara tsayuwa, “A’i nayi mamaki da baki ganeniba, Ummukulsoom ce fa matar Amaan da kuka zauna a lagos tare cikin dodan Barrack”.
A matuƙar razane A’i tayi baya, sai kuma ta zube ƙasa jiki na ɓari tana zare ido tamakar ɓarawon gwamnati a gaban efcc (naga idi kar ai farfesuna????????????⛹????♀️????).
“Dan ALLAH hajiya da gaske kece?”.
Bily dake zubama A’i harara tace, “Inba ita bace zata baki wannan dogon bayanin da kikajine? Halan salon annamimancin nakine ya kawoki kotu?”.
Kuka A’i ta fashe dashi mai ban tausayi, cikin sarƙewar halshe zata fara bayani Ummukulsoom ta kalli agogonta, “kinga A’i yimin afuwa na fito shari’arnan inhar ban takuraki ba, dan saurana minti goma kacal”.
Mamaki ya kuma kashe A’i, anya kuwa wannan yarinyarce ƴar ƙauye da ko magana batasonyi a gabanta?, cikin rawar baki tace, “A babu komai hajiya, ai wlhy ko ca kikai nanda wata ɗaya na jiraki zan jiraki, a fito lafiya”.
Gaba Ummukulsoom tai tana murmushi, da mamakin yanda A’i dukta lalace ta tsofe tamkar ba’itaba.
★★★★★
Kasancewqr yau kowa ke fatan kawo ƙarshen shari’ar su basiru kotun ta cika maƙil ga duk wanda ke ƙwaɗayin ganin ƙarshenta, hatta da A’i bata bari an barta a baya ba saida ta shigo burinta kawai taga micece Ummukulsoom a wajen.
A mamakinta saiga Ummukulsoom Buhari ɗilau na gabatar da kanta matsayin lauya mai kare wanda yay ƙara, wato Basiru.
Tunda aka fara zaman shari’ar shi kansa Basiru sai yaune za’a kawosa kotun, saboda Alhmdllh jikinsa yayi ƙyau, zuwa yanzu yana fahimtar mi akeyi saɓanin da daya zama kamar wani dolo-dole sha giri girbau.
Sunansa Ummukulsoom ta fara ambata a matsayin wanda zataima tambayoyi, dan haka kotu ta buƙaci ganin basiru wanda aka turo ciki wheelchair???????????? ƙafarsa ɗaya a yanke saboda riɓewar datayi yana prison, dan dukan da ƴan sanda sukai masa a wancan lokacin yata cinsa, rashin gata kuma ya hana ya samu kulawa harta zama ciwo wadda ke fidda ruwa mai wari, wannan dalilinne yasa aka tsanesa a cikin jail, kowa ke ƙyankyaminsa da hantararsa, to fiddosan nan da akai likitoci sukace dole a yanketa saboda cutar ciwon suga dake a jikinsa ba’a saniba, gashi hartaci ƙarfinsa sosai.
Amaan ne ya biya kuɗin aikin, aka kuma gudanar cikin nasara.
Tunda Aka shigo da basiru cikin kotun akan Ummukulsoom ya fara sauke idanunsa, koyaya Ummukulsoom ta koma fuskarta bazata taɓa ɓoye masaba, dan tunda ya barta tunaninta bai taɓa barinsaba, yana turetane kawai da ƙarfin tsiya saboda huɗubar shaiɗan limamin zuciyarsa da yayta jagorancin munanan ayyukan daya tafka.
Yanda ya kafeta da idanu yana sharar hawaye ya saka Ummukulsoom sake haɗe fuska ta manna eyeglasess ɗinta saman ido sosai, saɓanin da data ɗan jawosa ƙarshen hanci.
Hakan na nufin babu wasa a tattare da ita, dan haka shima saiya kama kansa ya koma kukan zuci, tunda take zuwa asibiti dubashi bata taɓa zuwa idonsa biyuba, sai bayan ya tashi a barcine talatuwa ko inna ke sanar masa Ummukulsoom tazo dubashi ta wuce, a duk sanda aka faɗa masa hakan sai yayi kuka, sai gashi a yau ya ganta a inda baiyi tunaniba, tana a matsayin mai kuɓutar dashi itada ya wulaƙanta, itace ta ceto iyayensa daga wahalar ciwo da suke ɗanɗana ta hanyar kaisu ga maganin da ubangiji ya basu waraka, Ummukulsoom da yake ganin yafi ƙarfinta saboda ɗan karatun digiri da yayi yau itace a gabansa matsayin lauya mai zamani, ta zame masa RAINA KAMA, dama masu iya magana kance CIKI DA GASKIYA wuƙa bata hudashi, shi gashi rashin gaskiyar yasa yaja wukar tai fata-fata da nashi cikin, da yanzu suna tare da ƴan yaransu abin sha’awa, jiba yanda ɗan matashin cikinta yay mata ɗas, Ummukulsoom ta zame masa *WUTSIYAR RAƘUMI* a lokacin da komai yafi ƙarfinsa hatta da ƙafafu da ƙyawun da yake takama da tinƙahon dasu………….
A ɗan tsawace Ummukulsoom taima basiru data ga baya tare da duniyarsa magana, ya kawo numfashi a zabure yana kallonta jiki na ɓari, sassauta ɗaurewarta tayi gudun karta ruɗar dashi ta sake jeho masa tambaya da faɗin “Kasan wannan ai malam basiru?” ta ƙare maganar da nuna Suhailat…………✍????