Yadda lakcara da ƴaƴansa su ka yi wa budurwa tsirara tare da lakaɗa mata baƙin duka

Wani lakcara da yaransa sun kai wa wata budurwa farmaki inda su ka yi mata tsirara tare da lakada mata dukan tsiya bayan ta samu hatsaniya da diyarsa, LIB ta ruwaito.
An dauki bidiyon Dr Fred Ekpe Ayokhai, lakcara a jami’ar tarayya ta Lafia da yaransa yayin da su ke mai wa budurwar mai suna Blessing Mathias hari a Jihar Nasarawa.
A daya daga cikin bidiyoyin, an ga Dr Fred rike da almakashi yayin da yake yankar rigar Blessing yayin da take rokonshi gafara.
Blessing ta rika rigarta da karfi da hannayenta don ta adana tsiraicinta amma yaran Dr Fred sun tilastata cire hannayenta don mahaifinsu ya yaga rigar ba tare da taba kirjinta ba.
Sannan sun nemi ta bai wa ‘yar uwarsu Emmanuella hakuri akan abinda ta yi mata a baya. Cikin biyayya Blessing ta durkusa tana ba ta hakuri, amma Emmanuella ta ki amincewa ta hakura.
Wannan yasa Fred ya ci gaba da yankar rigarta. Bayan yanke rigar har zuwa kwankwasonta, Blessing ta kwanta kasa don tsirara yayin da iyalan Dr Fred ke dukanta.
Wannan bidiyon ya dauki hankalin mutane da dama inda kowa ke kira ga hukuma akan daukar mummunan mataki akan Fred da yaransa.
Dama asali Blessing ce ta fara cin zarafin Emmanuella saboda namiji, an wallafa bidiyon Blessing yayin da take cin zarafinta. Duk da haka, mutane na ganin bai dace ba harin da ‘yan uwan Emmanuella su ka kai wa Blessing.