Al-Ajab

Yadda mata 4 suka sace ni, suka sanya ni a ɗaki tare da yi min fyade babu adadi, Magidanci

Wani mutum ya bayyana yadda wasu ‘yan mata suka dirka mishi kayan maye, suka yi garkuwa da shi tare da yi masa fyade, LIB ta ruwaito.

 

Ma’aikacin ma’aikatar hada leda wanda zai kai shekaru 20 da doriya ya bayyana yadda wasu ‘yan mata suka damke shi yayin da yake cikin abin hawa a garin Jalandhar da ke Punjab a Indiya, ranar Litinin, 5 ga watan Disamba.

 

Ya be sun dinga lalata da shi na tsawon sa’o’i da dama kafin suka yar da shi a wani wuri cike da itace da dare.

 

Mutumin ya bayyana yadda lamarin ya faru inda yace ba ya don bayani dalla-dalla bisa bukatar matarsa.

 

An samu rahoto kan yadda ta bukaci kada ya yi korafi saboda yanzu haka suna kokarin ganin ya dawo daidai.

 

Mutumin ya shaida yadda matan guda hudu suka fito daga cikin wata farar mota inda suka fincike shi suka jefa motar.

 

Ya ce turanci suka dinga yi kasancewa ba ya jin yaren, Punjabi kadai yake fahimta.

 

Kuma lamarin ya faru ne da misalin karfe 3am na dare yayin da suka daure masa idanu da hannaye kafin suka dawo da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button