Labaran Kannywood

Bidiyo: Ana zaton jaruma Mommy Gombe ta fara daukar fim a kasar Dubai

Fitacciyar jarumar Kannywood Maimuna wadda akafi sani da Mommy Gombe ta wallafa wani fefen bidiyo a shafinta na Tiktok,a cikin bidiyon wakilin mu ya gano mana a kasar Dubai aka dauke shi,sannan an nuna yadda Larabawan sukewa jarumar kwalliya gami da daukar ta bidiyo har tana rawa.

Lamarin yayi matukar bada mamaki,wasu suna ganin ba lallai fim ta fara ba duba da yanayin banbancin kabilar su,ita Bahaushiya su kuma Larabawa,sannan kuma ko a kwanakin baya anyiwa Jarumar ca akan rashin iyawa ko kuma muce kwarewa a Yaren na Nasara.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa, kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button