Al-Ajab

Yadda wani mutum ya arce daga Otel bayan budurwarsa da suke tare ta mutu a daki

Manajan wani Otel dake Igbogbo a Ikorodu jihar Legas ya kai kara ofishin ‘yan sandan dake Ikorodu bayan ya tsinci gawar wata mata a daya daga cikin dakunan otel din.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benjamin Hundeyin ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Legas.

 

Hundeyin ya ce bisa ga bayanan da manajan Otel din ya bada ya ce matar wacce shekarunta basu wuce 46 ba ta zo otel din r tare da saurayinta Alfa Sule a babur.

 

Ya ce Alfa da budurwarsa wace aka gano sunan ta Muinat sun kama daki tare a otel din a ranar Juma’a.

 

Hundeyin ya ce sai dai a ranar Asabar da misalin karfe Shida na safe manajan ya tsinci gawar Muinat yayin da yake duba dakunan dake otel din sannan Alfa ya gudu ya bar babur dinsa.

 

“Babu alamun cewa Muinat ta yi fada ko alamun an shake ta kafin ta mutu sannan shi saurayinta Alfa ya gudu.

 

“Rundunar ‘yan sanda sun zo dakin sun iske gawar matan kunfa na fitowa daga hancinta.

 

Hundeyin ya ce rundunar ta kai gawar zuwa asibiti domin ci gaba da bincike sannan a fara farautar Alfa.

 

Ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifi iron haka ta rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button