Uncategorized

TAKUN SAKA 29

 

*_Typing????_*Albishirinku mata????.*

shin Ina ma’abota ado da kwalliya????️? Ina team no makeup????️? Mata gareku ina mai tabbatar muku dacewa duk wanda takeneman kayan gyaranjiki walau matsalan fata kike fama dashi kamarsu pimples, tabo, sunburn,nankarwa, knuckle ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki Dama sauransu walau Kuma kawai kinasan kigyara fatarki kizamto tauraruwa abarso abar marari agurin kowa????Mata inamai tabbatar muku

dacewa kujaraba kayan mg’s skincare Koda gudane dg cikin kayansu kuga abun mamaki????????‍♀️ domin kayansu kankat ne Koda iya sabulunsu Kika Dana saikinfita zarra cikin Mata domin ynd fatarki zaikoma Shar kamar Madara kidinga kyalli kina haskakawa duk inda kikayi se ankalleki????Kuma wani abun jindadin ma shine duka kayansu organic ne  Babu na bleaching kawai zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural beauty dinki inma NASA haske kikasiya natural ne kawai bn bleaching b????‍♀️mekike jira hjy maza garzayo kinemi naki acikin farashi merahusa kigyara jiki kiyi fes abinki baruwanki da sekinyi kwalliya inzaki fita????kifita aganki da zallar kyawunki hjy????kanawa mutanenmu ina godiya Kuna nunama mg’s one luv tnx for ur patronage dama Yan sauran state mg’s na godiya may your pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu????Yar shawarmannan karta gagareni????????Henajiku lvs????

Meso should chat

08062991549

07046881166

Call 08064532391

Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k

Instagram:glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

Team glow✅

 munayin makeup Yan kaduna gamai bukata ze iyazuwa nd munazuwa gida shima in anaso

08062991549

_________________________

*_Chapter Twenty Nine_*

…………..“Ina da son yara matuka, duk da ban son yawan hayaniya da yawan magana. Sannan kuwa nima yaro ne, hakan yasa a koda yaushe zaka ga yara zagaye da ni musamman saboda Habib da wasu jariran biyu da mama mai kula damu take raino tare da Habib. Wannan dalilin yasa suka taso tamkar ƙannena a gidan marayun, idan sukai laifi nike hukuntasu na musu faɗa, sannan nine ke kula da karatunsu dan mun cigaba da zuwa makaranta musamman ma ni dana fara secondary a wajen gidan marayun da baba ke kaini da kansa kullum bayan na ƙarasa shekara ɗaya a primary ɗin gidan marayun. Mama mai kula damu ce ta sakamin suna Master duk da bana so banƙin amsa mata. A hankali sai sunan ya bini a gidan kowa ya koma kirana da Master har su Habib”

          “Ina girma sunan Master daya kashe Abbana na ƙara zama a ƙwaƙwalwa ta fiye da karatu, a gefe kuma da an tashi a makaranta nake tafiya talla batare da sanin baba ba da hukumar gidan marayu. Kai wani lokacin ma bana zuwa makarantar gaba ɗaya. Da kuɗin sana’ar nake sayoma su Habib sweets, biscuits da kayan kwaɗayi na yara. Tun kowa bai farga ba har suka farga dani. Baba ya dinga min faɗa, sai dai da ga ƙarshe kuma da kansa ya bani kuɗaɗe da bawani yawane da su ba na cigaba da sana’ar dan ya fahimci inaso. Saboda tunda aka hanani saina ɗauka ƙunci da fushi na sakama kaina.”

      A lokacin dana kammala secondary su Habib suka shiga na fara tunanin kutsa kaina cikin ƴan jagaliya, dan na gama nazarina kaf ta wannan hanyarne kawai zan iya nemo Master daya kashe mahaifina. Anan ɗin ma batare da sanin Baba ba na faɗa cikin ƴan daba tare da zama da kaina naima facemask ɗina wasu gyare-gyare saboda ni mutum ne mai fasaha matuƙa tun ina da ƙarancin shekaru, sai dai ALLAH ya tsareni bana shan komai na maye, duk sanda kuma zasu aikata tsiyatakunsu nasan ta yanda zan zille musu. Dan na shiga cikinsu ne kawai dan neman ilimi da kuma neman Master. A gefe kuma na takura baba akan mubar gidan marayu, dan na tabbatar zan iya rikemu mu duka da sana’ata da zuwa lokacin tayi ƙwari na daidai talaka mai neman cin yau da gobe. Da ƙyar baba ya yarda muka dawo cikin mutane da zama a gidansa ɗin nan da muka bari shekarun baya. Ni na cigaba da buga-bugar karatu akan su Habib duk da lokacin dai da ɗan saukin wahalhalu akan mai karatun secondary. Yayinda niko a dalilin ƙoƙarin da ALLAH ya bani wani bawan ALLAH ya ɗauki nauyin karatuna na jami’a a ranar taron tshoffin ɗalibai da akai na makarantarmu.”

        “Na cigaba da kutsa kai cikin ƴan daba ina neman Master a sirrance har ALLAH yasa na dace na kasance ɗaya da ga cikin yaransa, dan zuwa yanzu ya matuƙar gawurta. Cikin ƙanƙanin lokaci na zama amintacce a wajensa, dan ina bala’i-bala’in kwantar masa da kai har sauran yaransa najin haushi da takaici na. Ban damu ba, dan tunaninsu da nawa dabanne suke haukarsu. A zahiri ina cigaba da karatun jami’a. Baɗini ina karantar kowanne motsi na rayuwar Master, gefe kuma ina kasuwancina da ALLAH ya sakama albarka mukeci muke sha ni da waɗan da nakema kallon ƙanne kuma ahalina bayan Habib. Bayan kammala jami’ata na shirya takanas na kaima wanda ya ɗauki nauyin karatuna result ɗina dan ya gani, tare da sake masa godiya. Yaji daɗi, ya kumayi farin ciki a take anan ya bani jari mai kauri da zan iya riƙe kaina harma da ƙannena.”

          “Koda na dawo na nunama baba ya sanyamin albarka, ya kuma bani shawarar maida hankali akan kasuwa basai na jira aiki ba, na amince da shawararsa dan haka na ƙara jari akan kasuwancina, UBANGIJI mai rahama dan-danan harkoki suka buɗe na canja mana gidan zama, na kuma koma makaranta nima. Domin cigaba da karatuna akan computer a wajen ƙasarnan. Tunda na tafi ban dawo ƙasata ba sai da na kammala karatuna. Amma koda yushe ina sanin motsin su Habib. Tun kafin na dawo na gama tsara yanda an tunkari master, dan kuwa na samo horo na musmman akan abubuwa masuyawan gaske.”

             “Yarana sunyi farin ciki da dawowata nima kuma nayi farin ciki da ganin sun zama manya sun kuma sake hankali. Sai dai kuma na iske baba babu lafiya. Hankalina ya tashi matuƙa dan ina sonsa hakama su Habib, duk muna masa kallo ne na uba. Kwanana biyar ALLAH yay ma baba rasuwa. Tabbas munji wannan mutuwa dan su Habib kuka rurus suka dinga yi suna sake ɗaga hankalina. Sai da na dage matuƙa suka dawo hankalinsu. Da ga lokacinne na fara basu horaswa ta musamman da basu san manufarta ba. Na kuma sake komawa cikin su Master da zuwa yanzun dukkan sirrinsa a tafin hannuna yake, dan dukkan abokan mu’amularsa a cikin manya da ƴan ta’adda irinsa na sansu nasan inda suke, nasan makamar harkokinsu. Na iya maganarsa. Na iya salon tafiyarsa na iya abubuwa da dama irin nasa wanda inhar na juye maka shi baka isa cewa bashi ɗin bane, musamman idan na saka mask na fuskarsa. Indai taƙaice muku zance a wani dare batare da sanin kowaba a cikin yaran Master na ɗaukesa, zuwa safiya na maye gurbinsa, yaransa kuma duk nabi hanyoyi daban-daban aka kamasu ɗaya bayan ɗaya ta yanda babu yanda ubannin gidan Master zasu iyama ganosu balle cetonsu………”

       “Kenan yanzu duk kuɗin da ake sata a banki da sunan Master wancan ne ba kaiba Yaya Isma’il”.

    Ammar ya faɗa cikin katsesa da zaƙuwar son jin yaya take ne.

        Wani ƙasaitaccen murmushi Master ya saki. tare da kai hannu ya shafa kan Ammar. “Da ga shekara biyu zuwa yau duk nine”.

     Kai Ammar ya jinjina cike da gamsuwa. Sai faman murmushi yake dan shikam jin wata sabuwar ƙaunar shi yake har cikin jini da ɓargo duk da har yanzu bai faɗi dalilinsa na wawasar kuɗaɗen ba bayan dalilin kama Master daya kasance mai laifi a garesa.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button