Labarai

A Karshe dai Kotu ta tisa Keyar Aminu Zuwa gidan Yari

A Karshe dai Kotu ta tisa Keyar Aminu Zuwa gidan Yari

Kamar dai yadda kuka sani an kama Aminu Adamu Yau kusan kwana goma sha biyu kenan Sakamakon Zagin matar shugaban kasa Aisha buhari da yayi.

Jaridar BBC hausa ta ruwaito cewa an gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin matar Shugaban Najeriya, Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

An tabbatar cewa an gurfanar da Aminu a gaban wata kotu dake Abuja babban birnin kasar, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Kuma akan hakan muka bukaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba. Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe.

Yan Nigeria da dama nata tofa albarkacin bakinsu akan wannan magana inda da dama suke bayyana cewa kwatakwata ba’ayiwa Aminu Adalci ba wasu kuma na fadin abinda yayi shiya jawa kansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button