KWARATA 51

Godiya ta mussaman gareku ma’abota mutunci da mutunwa , ngode ׳ ina godiya sosai wanda idan nace zanyi ta rubuta ngode ² sai cajin wayana ya ƙare ban gama rubuta godiyar ba ,
Hassan 80k
Hassana Masko
Hafsat Sa’idu Galadima
Muhammad Musa Muhammad { Na Allah… }
Halimatu Musa { Uwa }
Gaba ɗayan shafin nan na yau sadaukar wane ga masoyana a duk inda kuke a faɗin duniyar nan ina sanku ina ƙaunarku kuma ina alfahari daku , fatan alkairi a gareku
Kuma na gaishe ku…
Abdulrahman & Ja’afar , Allah ya tabbatar da farin ciki da kwanciyar hankali a gareku ubangiji ya jiƙanku yasa ku gama da duniya lafiya , Am3n
Juyawa ɗakin yakeyi dani kamar anayin hajijiya dani , wayyo Allahna ina zan dosa ? Mi zanyi ? Ya Allah ka kawomin mafita ka tausayawa rayuwata kuma ka tabbatarmin da alkairin ka , banda zaɓi sai naka banda wurin gudu ko tsira sai yadda kayi dani ya ubangiji al’arshi taimakon ka nake nema bana san taimakon kowa sai naka , duk abinda ya faru da Babana dani haka yazo a rubuce kuma babu wanda ya isa ya goge,
Da gudu na fito daga cikin ɗaki ina cewa yaku taron “yan uwana kuzo kowa ya biyoni domin dai yau wata baƙuwar rayuwa tana tunkaro mu , ciwon ba nawa bane ni ɗaya , babu babba ba yaro ba matar Baba ba mace ba namiji yau tashin hankalin gaba ɗayan gidan ya tunkaro ku taho Baba yana buƙatar taimako !
Ina faɗin haka nayi gaba da gudu , namiji ɗaya ya biyoni shine babban yayanmu yana ke Sultana ina zaki ? Banda lokacin bashi ansa gudu nakeyi kamar taɓaɓɓiya shima da gudu ya biyoni ina fitowa bakin titi na samu napep nace muje , Yaya yana fitowa tuni mun tafi , shima dafe kai yayi tare da riƙe ƙugu , ganin hakan ba mafita bane yasa ya tari mai machine yace yabi mishi bayan napep inmu.
Muna isa tun kafin napep inmu ta tsaya na dire na tun kari inda nake hango mutanen da basu wuce su biyu ba , sunyi rami sun saka hannun takobi cikin ƙasa tsinin kuma yana sama , bayan sunyi wa Babana wani irin duka a kai ya tafi duniyar ɗimuwa jini sai bin jikinshi yakeyi , bana iya gane fuskar kowa a cikinsu saboda rufe take idanuwansu kaɗai ake gani ,
Mai napep yana ganin haka ya gudu babu shiri dan tsira da rayuwarshi yayin da ni kuma na tunkari wurin haiƙan ina cewa kai na rantse da Allah idan wani abu ya sameshi gaba ɗayanku sai tsinuwar Allah ta tabbata kanku , ku barshi me yayi muku ne ? Me rayuwar shi ta tsone muku ko kune kuka bashi aron lumfashi ne ? Ubangijin al’arshi shine ya bawa Babana aron numfashi kuma shine ya bashi lafiya ku ɗin nan banzaye da ku baku isa ku fitar da ransa ba sai Allah yaso ,
Dariya sukayi sosai tare da cewa tou Allahn ne yaso shi yasa ma ya kirashi kuma yanzu zai tafi domin ansa wannan kiran idan kina iyawa ki kamo ran ki dawo dashi cikin jikinshi , suka ƙarasa maganar tare da ɗauko Babana suka birkitashi saitin zuciyarshi suka ɗagashi sama suka dakoshi saman takobin da ƙarfi , sai kuma suka ɗagoshi suka juyashi yana kallon sama suka sake sokeshi…
Da gudu na isa wurin Babana na durƙusa saman guyawu na , nace Babana karka sake ka rufe idanuwanka babu abinda zai sameka kallarni gani nan nazo Mamanka Uwar masu gida jikina yana ƙyarma na fara ƙoƙarin ɗago Baba amma na ƙasa idan kuma nace zan juyoshi ina tunanin inda bai yanku ba ma zai yanku ,
Babu abinda ke ɗiga daga cikin idanuwan shi sai hawaye yana lunshe ido nace kar kayi bacci ka rufamin asiri karka rufe ido idan ka rufe ido tawa ta ƙare , waye ? Waye wai waye mutumin da kake gani a baccin ka ? Waye ya kiraka wurin nan ? Karfa ka rufe ido yi murmushi yimin murmushi Babana , dakel ya ɗago idonshi ya kalleni cike da soyayya sannan yayi murmushi da gefen bakinshi la’elaha illallah muhammadur rasulillah ya ƙarasa tare da rufe idanuwanshi , nice na ida da S. A. W ,
Kai…….. Na shiga 3 na bani na lalace wayyoni Allahna wayyo rayuwa ina zan sa kaina , nace kar kayi bacci shine kayi bacci me yasa ? Me yasa kayimin haka haba Babana , shine zaka tafi ka barni ? Bayan kamin alƙawari baza ka tafi ka barni ba , shine ka tafi ka barni ? Ya ubangiji ka farkar dani wannan mafarki ka tausayamin badan halina ba dan darajar manzan tsira kasa bacci nakeyi ,
Isowar Yayana shima da gudu ya iso wurin cikin tashin hankali yaga Babanmu soke a saman takobi dan suna soke Baba suka gudu , shima wani irin ihu ya kurma hakan ya jawo hankalin jama’a , kafin kace me ? Wuri ya cika sai kuka nakeyi ina ƙarawa tare da cewa wai Allahna , wai Allahna , Allahu Akbar ,
Sauko Baba akayi daga saman takobin har yanzu murmushin da yayimin yana nan akan fuskarshi bai goge ba , kamar kace taso ya taso sai kayi tunanini bacci yakeyi , duk wanda yazo saiya haskashi saboda duhu yayi sosai , ganin ana ta kallemin Babana yasa na cire hijabina na lulluɓeshi a lokacin har Yayana yayi waya an kawo mota ,
Allah mai girma da ƙafafuwan shi yazo wurin nan amma gashi yanzu baya iya tafiya sai an ɗaukeshi , bayan an saka Baba a mota Yayana ya kamoni nima ya shigar dani duk muna zaune a baya yayin dana kwanta saman gawar Baba inaci gaba da kuka ,
Zuwan Mamy gidanmu na tuna ranar data zo ta samu Baba zaune a saman dakali tana bi bi biyyyy , murmushin da Baba yayi mata na tuno da alamar da yayi mata da ido , yau gashi daga Baba har Mamy duk basa cikin wannan duniyar , kai…. Wani irin ihu na sake kurmawa daga nan ban sake sanin abinda ya faru dani ba saidai na farko na ganni a ɗakina Dikko durƙushe a gabana idanuwan shi sunyi jajir Ashiru da Umar suna tsaye a bayanshi .
Tashi nayi cikin kuka na rungume Dikko nace me yasa ka kashe wayarka ? Kiyi haƙuri har yanzu wayar a kashe take banda caji , kauda maganar nayi da cewa kaga Babana ko ? Ranar da nayi faɗa dakai na dawo gida shine Baba yayi kuka yace Mamana shine kika tafi kika barni ? Ni na goge mishi hawaye da wannan hannun nawa na nunama Dikko hannun naci ga da cewa nace masa ai na dawo ,
Nace Baba kana tunanin zan tafi na barka ne ? Bayan bana iya rayuwa saida kai ! Dare da rana safe da yamma yanayin farin ciki ko damuwa halin yunwa ko ƙoshi babu kowa a zuciyata sai kai , farin ciki ya dawo rayuwar ƙunci da damuwa zata kama gabanta , cikin kuka nace shine ya tafi ya barni , ni in rayuwar ƙunci da ɓakin ciki wayyo Allahna , wai Allahna…..?
Inajina kamar inayin rayuwar da bana cikin sahun mutane yayin da farin ciki yake tunkaro rayuwata sai mutuwa tazo ta shafe wannan farin ciki , duk wanda yazo da niyar ya taimakeni sai a shafe labarinshi a duniya , bana so ka rasa rayuwarka ka tafi daga rayuwata kada kaima su kashe ka….
Juyawa Dikko yayi yace ma Ashiru ku jirani waje , fita sukayi , Dikko ya ɓanɓareni daga jikinshi ya zauna kusa dani yace ina Mamanki ne ? Cikin kuka nace ta gudu tabar rayuwata banma san ita ko “yar gidan wane ahalin suka haifota ba , ni ɗaya nake rayuwata a wannan ɗakin babu ruwan kowa dani nima banda ruwa da kowa babu mai so na sai Allah banda wanda zai nunamin kyakkyawa ko mummuna duk rayuwar dana ɗauko ita nakeyin abuna gani yau na zama marainiya…..
Kallona Dikko yayi yace ke ba marainiya bace Allah yana tare dake kuma Dikko yana tare da rayuwarki , duk wanda kika ga ya mutu kwananshi ne ya ƙare ki daina mishi kuka kiyi mishi addu’a , nace to , Dikko yana gidanmu shi ya tayani zama a ɗakina yana min nasiha sai 1:39am yabar gidanmu ,
Bayan tafiyarshi ma na tuna banyi magib ba bare isha’e , fita nayi nai alwallah nazo nayi sallah nayi karatun al’qur ani mai girma tare da roƙawa Babana rahma a wurin ubangiji , har gari ya waye banyi bacci ba kuma banje ɗakin da aka kwantar da gawar Babana ba ,
Tunda safe gidanmu ya fara ɗaukar mutane su Amisty da suka zo ɗakina suka sauka , suna shigowa ni kuma na tattara wayoyina da tawa data Mamy na fita , ɗakin da aka kwantar da gawar Baba na nufa , har anyi masa wanka an shiryashi yana kwance a mankara , ina tsuguniya abinda ya tunomin shine ,
Ranar da muna zaune dashi a ƙofar gida nace Babana ina sanka ina kuma tausayawa rayuwata ranar da za’a wayi gari babu ɗaya a cikinmu , murmushi yazo ya tsayamin a rai da maganarshi da yace min ai bazai tafi ya barni ba , a bayyane nayi magana cikin kuka nace shine ka tafi ka barni…
Naci gaba da kuka mai tada hankali , ina Allah ya jiƙanka ubangiji yasa ka huta , Allah yasa can yafiye maka nan Allah ya sadaka da mala’ekun rahma ubangiji ya kauda kai akan duk laifukan da kayi masa ya yafe ma ya gafarta maka ya baka aljanna dan arziƙin annabi muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wasallam….
Zainab ce ta riƙeni duk gidanmu Zainab tafi kowa tausayi na tana so na , tace Sultana kiyi shiru don Allah , cikin kuka na rungumeta nace don girman Allah ki tasheni daga baccin nan haka nan wallahi zuciyata ta kusa ɓarewa ,
Haƙuri kawai take bani , ina nan zaune a ƙasa kusa mankarar Baba sai kuka nakeyi , bayan wani lokaci kuma maganar Baba ta faɗomin a rai da yace idan har na mutu karki sake kimin kuka addu’a zakimin shine kaɗai zai tabbatarmin da soyayyar da kike min , shiru nayi naci gaba da gumji ina addu’a wa Babana ,
Misalin 08:50am gidanmu ya gama cika duk ta inda baka tunani , 09:00am aka ɗauki mankarar da Babana yake sama kwance za’a fita dashi domin salla tar gawarshi shi , shikenan Baba zai tafi inda bazan sake ganinshi ba bazan sake jin muryarshi ba har abadan abada duk soyayyar da yakemin ya tafi da gaske ya barni…. Sake ɗaukewa nayi na ƙara somewa !
Har akayi ma Baba sallah aka kaishi gidanshi na gaskiya Sultana bata san inda kanta yake ba , zata dawo² shiru har la’asar babu Sultana babu labarinta , duk wani taimako daya kamata ayi mata anyi amma har 5 na yamma bata dawo ba ,
Dan haka yasa Dikko yace a fito da ita a kaita asibiti , Zainab ce akan Sultana sai firfita take mata dama itace ta kula da ita a asibiti lokacin da Dikko ya farke mata mutuntakarta , da taimakon wasu matan aka fitar da Sultana aka sakata a mota da Zainab kaɗai aka tafi sai Ashiru dake tuƙi saishi Dikkon.
Asibiti mai kyau aka kai Sultana likitoci suka rufa akanta dan ceto rayuwata , amma duk yadda akayi saida Sultana ta kwana huɗu bata cikin hayyacinta , ga dai ido tana kallon kowa amma ƙiri² bata iya magana , bata ci bata sha sai kuka , hankalin Dikko idan yayi dubu ya tashi ya lallashi Sultana har ƙarfinshi ya ƙare amma Sultana taƙi tayi magana da kowa , da tsiya² Dikko ke bawa Sultana ruwan tea shima idan tasha saita amayar dashi ,
Zainab itace ta bawa Dikko shawara ko a riƙa ba Sultana fura duk tsiya dai ko tayi amai wata zata tsaya , Dikko yasa Ashiru ya samo fura ake ba Sultana amma ko tasha sai ta dawo da ita ,
Dikko yace haba An mata wai me yasa kikeyin haka ? Gaskiya banajin daɗin abinda kike yi ko nima so kikeyi in mutu shikenan sai ki huta ? Kiji tsoron Allah ki tausayawa rayuwata haka nan mana , ke shikenan abu baya wucewa wurinki ? Kina nufin ke Allah bazai jarabce ki ba ? Ko akanki ne aka fara rashin iyaye ? Ba’a fara a kanki ba , ba kuma za’a gama akanki ba , mutuwa tana nan tana zagayawa tsakanin rayuwar kowa kuma babu bararre a duniya duk wanda yazo sai ya koma , ina ilimin naki da kike alfahari kina dashi ? Wannan shine sakamakon da zaki sakawa rayuwa dashi ? Shi kukan mutuwa da kika ganshi ba’a gamashi kuma baya ƙarewa har sai ranar da rai ya ƙare kiyi haƙuri don Allah .
Murmushi Sultana tayi mai ciwo dan gani takeyi Dikko baima da hankali , ya za’ayi ta daina kukan rashin Babanta ? Ubanda ya ɗauki soyayya duniya ya ɗora mata , cikin “ya “ya sattin da wani abu itace kaɗai ya ɗauki duk soyayyarshi ya bata , taya ma zata manta Baba ? Taya zata daina kukan rashin shi ? Duk ma wanda yace tayi haƙuri ta daina kukan rashin shi wallahi mahaukaci ta ɗaukeshi ,
Banyi magana ba na sauko daga saman gadon na fice daga ɗakin , Dikko ya biyo bayana yana ina kuma zaki ? Banza nayi dashi ban juya ba kuma bansan abinda ya sameni ba bana iya magana sai hawaye , da sauri ya iskoni yasha gabana ina zaki nace ? Kaucewa nayi daga inda ya tsaya na tun kari hanyar fita asibitin ,
Zainab ma tambayata takeyi ina zanje duk banza nayi dasu nayi wurin mota na tsaya dan gida nake so inje , murmushi Dikko yayi mai nuni da baya san abinda nakeyi amma bai sake magana ba ya buɗemin mota na shiga na zauna ya rufe itama Zainab shiga tayi Ashiru ma haka amma yanzu Dikko yaja motar rashin a matuƙar ɓace ,
Har muka iso ƙofar gida babu wanda yayi magana , bayan yayi parking Zainab ta fita nima na fita Dikko kuma bai mana magana ba yaja motarshi yabar anguwarmu ranshi a ɓace , jiki a mace na shiga gida Zainab tana bina baya har ɗakina dan “yan gidanmu sai sharholiya sukeyi yadda kukasan ba mutuwa akayi ba , wayoyina Zainab ta kawomin tare damin bankwana tace Allah ya ƙaddara saduwarmu ,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Murmushi nayi tare da jinjinawa Zainab kai , ansar wayoyi na nayi ta fice ɗakin , tashi nayi na dudduba , kayana masu kyau da tsada duk an sacemin su kaf har kuɗaɗene gaba ɗaya an dauke su , tsoki nayi na fita nayi wanka na wanko bakina nazo nayi sallah magrib na gamesu da isha’e , ƙarfe 10 na dare kuma Dikko baiyi zuciya ba yazo ,
A saman dakali muka zauna , ya ƙaramin gaisuwa tare damin nasiha yacemin kuma idan Allah ya kaimu zaije Abuja kwana biyu zaiyi ya dawo idan ya dawo zai tafi dani , cikin kuka nace to kuma kayi haƙuri ɗazu da nayi maka shiru , jawoni yayi jikinshi cikin sigar rarrashi yace ba komai An mata ai kinsan bana iya zuciya dake ,
Murmushin ƙarfin hali nayi cikin shashshekar kuka nace Allah yasa kaima kar a kashe ka , yace shima da suka kashe shi sai kuma ya kauda maganar da cewa tunda har An mata tayi rashin lafiya nima banajin daɗi ,
Bai dai wani daɗe ba mukayi sallama dashi har mota na rakashi ya bani kuɗi masu yawa yace in ajiye mishi nace ni sata akemin yanzu , yace idan an sace ba komai idan baki da kuɗi na arami ki , nace nidai bana ajiyewa haba yi haƙuri ki ajiyemin , nace kuɗin sunyi yawa bazan iya ajiyewa ba , kallona yayi yace tou ibi wanda zaki iya ajiyemin , nidai ko ɗaya bana iya ajiyewa ,
Tou ɗauka na baki duka , zaro ido nayi banma yi mishi magana ba na wuce da sauri gida , An mata zo , da Allah kizo kiji , ban dawo ba , murmushi Dikko yayi yaja motarshi ya tafi…
Jiya Dikko ya koma Abuja kuma munata waya dashi yana gayamin ya ƙagara gobe tayi ya dawo kuma yacemin yanzu idan zan koma makaranta Abuja zai tafi dani bazan sake makarantar kwana ba , yace shine zai riƙa kaini yana ɗaukoni wai sai muzo katsina juma’a da daddare mu riƙa komawa lahadi da daddare , bawan Allah shi kaɗai ke lissafin shi , haka dai ya ƙari surutunshi yamin saidai safe.
Muna gama waya da Dikko aka aiko kirana , dan haka na ajiye wayar na fita , Al ‘ Ameen na gani ƙofar gidanmu bayan mun gaisa yacemin mai gida yace nazo na ɗaukeki ki gano wani gida idan yayi miki yana so acan zaki koma da zama , murmushi nayi nace aiko yanzu muka gama waya dashi bai faɗamin zaka zo ba ,
Al ‘ Ameen yace nidai shine ya aiko ni , ni kuma nace tou bazanje ba na juya da niyar komawa gida , matan dake bayan mota suka fito kaca² muka fara kokowa har sukayi nasarar dannani a mota Al ‘ Ameen aja muka bar ƙofar gidanmu…