NOVELSUncategorized
NAJEEB 3

“koda ibtisam ta shiga cikin gida, a kitchen ta iske ummi tare da fad’in sannu da aiki ummi?
Ummi tace yauwa, har an dawo? Amma kun dad’e
Ibtisam tace ummi ai dole mu dad’e, tunda na tafi da granny, tana tafiya kaman batayi, damma da zamu dawo a mota muka dawo.
Shigowan Granny ne yasa ibtisam barin wajan cikin fushi.
Granny tace kanki akeji.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9704, ‘t’: ‘200 by 600’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Ummi tama Granny sannu da dawowa, sannan taci gaba da aikinta tare da duba abubuwan da suka siyo Mata
Granny d’aki ta nufa inda taga ibtisam a kwance tayi ruf da ciki, tace ke Wai fushin Mai kikeyi haka ne?
Ibtisam ta tashi ta Fara magana kaman haka, wai Mai kike nufi dani ne? Akan wani dalili zaki samu mu shiga motar mutumin da bamu Sani ba, sannan harda wani cewa a amsan miki number d’inshi?
Granny tace toh fah, daka Abun arziki, ah lallai ba shakka, naga kin tsaya Jan aji, shine na taimakeki amma shine zaki tsaya kina min tujara, kuma Nasan ya miki munafuka.
Ibtisam tace oh haka kike tunani, toh ai sai ki aureshi tunda ke kika bu’kaci number d’inshi,sannan ni bai mun ba, sarai kin San babu maganan aure a gabana, karatu zanyi, gwara Kibar wannan maganan.
Granny tace au yanzu na gane, kodai Kore samari kikeyi ne? Inba haka ba ai nidai nasan Indai farin jini ne Ina dashi, sanda nake yarinyar kar kiga yanda akemin layi, samari Kala Kala, amma ke sai kace anyi miki asiri babu Mai zuwa, inma anzo kwana biyu mutum bai sake le’kowa, k’asa tayi da murya tare da magana cikin sigar lallashi tace haba takwarata ki fad’amin gaskiya kodai kina koransu ne In sun zo?
Ibtisam dariya ta saki, danta gano wayau take son mata, itama cikin sanyin murya tace Granny bana koransu, sune basa zuwa ta k’arasa maganan cikin sigar tausayi
Granny tace ikon Allah, wannan bakin jinin na dangin uwarki ne wlh, nidai sanda nake yarinya Kinga yanda ake mun layi kuwa? Cikin masu sona harda d’an Mai anguwa, amma na dage na auri kakanki, lokacin auren soyayya mukayi
Ibtisam dariya ta saki Sosai, tare da fad’in toh Granny nima basai ki bari inyi auren soyayya d’inba, kin San aure lokaci ne, Idan lokaci yayi zanyi
Granny tace hakane, lokaci ne amma da niya, ke gaba d’aya keda miskili baku da niyan aure
Ibtisam tace haba Granny Mai yasa ni d’aya kika sama ido, ga zarah bakya maganan ta
Granny tace ai kin girmeta, nafi son in fara ganin d’anki keda miskili, tunda kune manyan jikoki na, kuma ke takwarata miskili kuma takwaran masoyina, Kai Allah yaji kan Habibu.
Ibtisam ta amsa da Ameen, tare da fad’in an tuna da soyayya kenan?
Granny tace Kedai bari, ai in lokacin aurenki yayi Zan nuna miki yanda ake siye zuciyar miji
Ibtisam dariya take Sosai, lokaci d’aya ta tashi tare da fad’in bari inje in taya ummi aiki
Granny tace Mai yakon ki kwanta ki huta, daka kasuwa muka dawo fah, ni kafafuna sai faman zugi suke, danma wannan d’an arzikin ya kawo mu, ni d’an kiramun shi inji yakai inda zashi
Ibtisam tace wa? Lallai ma Toh Wlh bada wayata ba, wai Mai kike nufi dani? Duk fah abunda za kiyi bazan soshi ba, daka had’uwa da mutum, sai kace wacce tayi kwantai haba da dudu guda nawa nake, da zaki dinga tusa ni.
Granny tace Dallah Rufamin baki, kina wani dudu du guda nawa kike, kina shekara Goma sha bakwai, ace har yanzu kina zaune gaban iyaye, wannan wani irin abun kunya ne, Keko kunya bakya ji, kin ri’ka kin ri’ke a gida
Ibtisam tace tunda akanki nake ai dole kice haka, wlh Granny kina takura min, wanda suke Kai shekara talatin babu aure fah, su kuma muce me?
Granny tace aniyarki ta biki, bazan ga wannan abun ba, Bari Umar ya dawo, bazan d’auki wannan iskancin karatun ba Wlh, bazaki sa aita nuna niba, mu Fulani an San muna auren wuri
Ibtisam tace fulanin da kenan, Nina rasa irin wannan jaraban taki Wlh, waini yaushe zaki mutu mu huta ne, haba Mata ta sani gaba
Granny ta tsuke baki a dole ranta ya baci, tace sai a kasheni ai, aure ne dai sai anyi ko anki ko anso.
Fita ibtisam tayi tana fad’in basai kisa dole inyi ba, ni naga jaraba sai kace dole, naga dai auran sunna ne ba farillah ba, da zaki bi ki damu mutum, har takai bakin kofa ta tsaya tare da fad’in ke kika sani koh Ina cikin matan da Allah yasa ba zasuyi aure ba K……
Dallah Rufamin baki, mara hankali, kina son jaza ma kanki fitina da mugun baki, kodai Kema aljanun ne suka aureki irin na miskili? Kuka ta saki wi wi wi tana fad’in na shiga uku
Ganin haka yasa ibtisam ta nufeta tana fad’in, dan Allah kiyi shuru, kai Wlh Granny kina son kasheni, badai aure kike so inyi ba?
Da sauri Granny tace eh
Ibtisam tace zanyi, idan na tafi makaranta hala a can in samo miki santalelen saurayi, kinyi sai ayi
Granny tace ga Kabiru nan, kalla har kud’i Yaban, duba kiga nawa nema.
Ibtisam kaita girgiza tare da amsan kud’in cikin takaici ta kirga, tace dubu goma ne
Granny Tana share kwalla Tana fad’in Allah sarki d’an arziki kenan
Ibtisam ajiye mata kud’in tayi ta fita, cikin takaici
Bayan sallah isha’i, mahaifin ibtisam ya shigo gida, kaman kullum yanda ya saba, gaba d’aya suna falo suna fira.
Ibtisam tayi ma mahaifin nata sannu da zuwa tare da amsan ledan hannunshi
Umar gaida mahaifiyar tashi yayi tare da fad’in Barka da hutawa.
Amsawa tayi da yauwa, Ummaru ya kasuwa? Da fatan an dawo lafiya?
Yace Alhmdlh, tare da shiga cikin d’aki, ummi ta tashi tabi bayanshi
Ibtisam kam tunda ta ajiye ma abbanta ledan daya shigo dashi ta nufi d’akinta, wanda ita da granny suke kwana tare, tana shiga wayarta taga tana wuta, da sauri ta nufi wayar taga number ne, kaman Karta d’auka harya kusa tsinkewa ta danna tare da sawa a kunne.
Sallama yayi mata tare da fad’in Barka da wannan lokacin
Ko bata tambaya ba, tasan Kabir ne, gashi ta d’auka babu daman kashewa, dan haka ta daure tace yauwa.
Yace Nasan baki gane mai magana ba, dan Nasan ba’ayi saving number d’ina ba, but anyway tunda na kira an d’auka babu damuwa, Kabir ne, so yakike?
Dan tsaki tayi mara sauti, wanda koda mutum yana kusa da ita bazai jiba, balle na Waya,tace lafiya, tare da fad’in mun gode da rage mana hanya, Bari in kaima Granny wayar.
Da sauri yace a’ah dake nake son inyi magana, Plz ina bukatar kiban lokacinki koda minti biyar ne In babu damuwa
A hankali tace babu damuwa, zaka iya fad’a inaji
Yace toh gashi ko sunanki ban sani ba?
Tace uhm sunana ibtisam
Yace wow nice name, sunan yamin dad’i
Nagode tace
Yace sunana Barrister Kabir, ina aiki a federal high court dake Abuja, ni dan asalin Kano ne, Ina zaune da iyayena a rijiyar zaki, mu biyar iyayena suka haifa, nine babba sai kanina namiji da kannena mata uku, iyayena sun matsamin inyi aure but sai dai ban samu irin matar da nake soba, sai yau, ibti tunda na ganki naji kin kwanta min a rai, irin shigarki da kamalanki, sabanin irin y’an matan yanzu, ibti nida aure nazo miki bada wasa ba, Allah ya sani yau na fara ganinki amma gaba d’aya kin tafi dani, sai dai ban sani ba, ko zan samu karbuwa.
Shuru tayi ba tare da tace komai ba.
Jin tayi shuru yasa yace ibti, ya naji kinyi shuru? Koda yake ya kamata in barki kiyi tunani zuwa gobe, amma plz ina son ki duba magana ta, gobe insha Allah Zanzo.
Tace Allah ya kaimu tare da kashe wayan, tana tunani, toh mai yake nufi? Gaskiya ya kamata in fad’a mishi k’udiri na, tun Kafin ya jaza min, dan Wlh Inna sake Mai wannan tsohuwar zata jazamin bala’i ku…..
Jin muryan Granny tayi tana fad’ama abbanta, kasan Mai sunana taci Janus kuwa?
Abba yace Janus? D’an shuru yayi yana nazari miye Janus kuma? Can ya tuna da ibtisam da safe Kafin ya fita tace jamb ya fito tun jiya, murmushi yayi tare da fad’in Kai Alhmdlh Ashe taci jamb
Granny tace eh taci Janus, dole kayi murna ai, burinku ya cika, zata karatu.
Abba yace mama kiyi hakuri ba haka bane, da taita zama a gida babu aure ai gwara tayi abunda zata ci gaba, in mijin ya samu koda Tana karatu sai Ayi auran.
Granny tace nidai wannan abun Anfi karfina, amma tunda kace koda ta Fara karatun inta samu miji zatai aure babu damuwa, kwanan nan kuwa zatayi auran.
Abba murmushi kawai yayi, domin shima yafi bukatar tayi auran Kafin ta Fara karatu, duba da irin yanda duniya ta lalace, musamman yanda ake kallon macen da taje jami’a a matsayin wacce idonta ya bud’e, ake mata kallon y’ar iska wacce ta Waye da yawa, har maza kanji tsoran auransu, sai yasa baiso ta saka har kaduna ba, yafi son tayi karatu kusa dashi, amma mum ta nuna mishi tare da zarah zasu karya damu, yayi musu addu’a kawai.
Granny tashi tayi tare da fad’in Bari inje in kwanta na gaji, sai da safe.
Koda Granny ta shigo d’aki ganin ibtisam tayi tana karanta wata takarda, Granny tabe baki tayi tana fad’in karyan banza, waike y’ar boko koh?
Ibtisam ajiye takardan tayi tana dariya tare da fad’in wai Granny Mai yasa kwana biyu kika samun ido ne? Dan Allah ki barni in huta, ni Mata tabi ta isheni, gashi kin tsufa amma kinki mutuwa
Granny tace dan uban mutum ai saiya kasheni, tunda akan mutum nake rayuwa
Ibtisam tace yauwa Nima haka na gani, Aiba a kan kowa nake rayuwa ba, dan haka kibar takura min, da wani maganan aure dan Allah, kaman yanda mutuwarki lokaci kike jira nima haka lokacin auren nake jira
Granny tace aike baki da burin aure ko kad’an, amma Wlh bazan bari kiyi shekara hud’u a gida ba, wannan abun kunyar har Ina, ace mun ajiyeki babu aure, ni sai naga duk kin Fara min tsufa Wlh
Ibtisam dariya take Sosai tare da fad’in nice na yanke ma k’asa cibi, karshen girma, wlh Granny ki fita harkata
Granny taja tsaki tare da fad’in aikin banza, zaki gani ai, aurene sai kinyi ko zaki mutu.
Ibtisam kwanciya tayi tare da juya mata baya tana fad’in ki kashe mana wutan d’akin in kin shirya kwanciya.
Granny tace Wlh da wuta zamu kwana, in zan shiga tailat wai zatace toilet shine tailat, dame zan haska?
Ibtisam tace ina wayarki, ki haska dashi mana
Granny tace Wlh bazan kashe wuta ba, ni yanzu bazan dinga kwana cikin duhu ba
Ibtisam da takaici ya kamata banza da ita tayi tare da fara bacci, harta Fara bacci taji gurus gurus farkawa tayi, ganin Granny tayi tana cin goro
Ibtisam tace na shiga uku, wai miye haka? Dan Allah granny kibar cin wannan goran ki barni inyi bacci mana, haba ni Wlh kin isheni
Granny tace Dallah Rufamin baki, na hanaki bacci ne ko me? Ina ruwana dake? Goro nedai sai naci
Ibtisam d’aukan filo tayi tana k’okarin barin d’akin, da sauri Granny tace haba takwarata zoki kwanta nabar cin goran, zoki kwanta abunki, tana maganan ne cikin sigar rarrashi
Ibtisam tsaki tayi, Granny tace kinma uwarki bani ba, bata ce komai ba ta dawo ta kwanta itama Granny kwanciyan tayi haka suka kwana da wuta a kunne saboda granny tace in zata tailat Hhhhh.
Washe gari da safe Bayan abban ibtisam zai fita, yace ma ibtisam gobe zata shirya taje Abuja, sunyi waya da d’an uwanshi, yana saudiya amma goben zai dawo shima, yace ibtisam tazo can zai amsa takardun ta ita da zarah.
Ibtisam taji dad’i Sosai, domin ta tabbatar burinta zai cika na son karatu, Mai wuyar shine kawai ta Fara karatun,tasan Indai ta Fara babu zancan cewa ta Bari.
Granny dake zaune a falon ta kalli ibtisam tace Wai yaushe Kabiru zai zo? Kiramun shi mana inji.
Ibtisam tsaki taja tabar falon
Granny tace zanyi maganinki ai, wannan karatun babu inda zaki, aure zakiyi.
Ummi dake zaune tana dariya, kai Granny ko rigima, yanzu ta nuna ta amince da karatun ibtisam anjima kuma ta nuna bata yarda ba, ita har yanzu taki yarda da auran lokaci ne, gani take kaman ibtisam ce bata da niya.
Kaman yanda Kabir yace, suna zaune a tsakar gida su duka, domin Granny koda akwai wuta sai tace tafi son tasha iskar Allah, tafi dad’i, yaro ne ya shigo yana fad’in Wai ana sallama da ibtisam inji Kabir, da sauri Granny tace Jeka ce ya shigo inji grandi, Yaron Ya amsa da Toh tare da fita
Granny kallon ibtisam tayi data d’aure fuska tace Dallah tashi kije ki kaishi falon ba’ki, kin wani zauna kin tamke fuska kaman ba’kar kumurci
Ibtisam tashi tayi rai bace ta d’auko hijab sannan ta fita, da murmushi a fuskanshi, ganin haka itama yasa ta saki murmushi sai taga ya Mata kwarjini Sosai, gaba d’aya maganan da tayi niyan fad’a mishi sai taga bazata iya ba, wanda da ta fito da niyan ta fad’a mishi magana akan karya k’ara zuwa, amma saita tsinta kanta da gaida Kabir din, tare da fad’in shigo muje
Har falon ba’ki ta kaishi sannan ta fita, dan Kawo mishi ruwa, abun gaba d’aya mamaki yake bata, yau kawai data ganshi Wanda shekaran jiya bata ko kalleshi ba, taga had’uwa da cikan kamala a tare da kabir din, lallai inda inada burin aure yanzu dana amince dashi, domin namiji ne dako wace mace zatai burin samu, miji ne na nunama tsara, kabir chocolate colour ne, yana da tsawo amma ba Sosai ba, yana da d’an jiki kad’an shima ba Sosai ba, gaba d’aya ibtisam tsayawa tayi a kitchen tana tunani…. Hmm muje zuwa muga burin ibtisam zai cika, kona grandi ne zai cika Hhhhh?
~MARYAM OBAM~