MADADI 1-END

MADADI Page 51 to 60

Sai da ta ganta a cikin tasha tukkuna hankalinta ya kwanta ta samu wani ke’bantaccen guri ta zauna tana mayar da numfashin wahala, gabadaya jikinta a rikice yake sam ba tajin dadinsa daurewa kawai takeyi, a hankali ta zuge zif din jakarta ta dauko wayarta ta bude numbar Salim ta nemo ta shiga kiransa.Salim na kasuwa a lokacin cike da zumudi ya daga wayar tare da ambatar sunanta…..Kuka tasa mai shashsheka tace”Salim ina cikin tashin hankali mai girma dan Allah kayi hakuri da abinda zakaji daga bakina wallahi duk abinda ya faru tsautsayi da kaddara ne amma nayi al’kawarin sai na salwantar da cikin da yake kokarin ruguza mana farin cikinmu.” Cike da so yasan abinda ke faruwa yace.”Naja’atu wai meke faruwa ne? naji kina wata magana wacce na kasa fahintarta.” Hawaye tagoge tace”Salim ciki ne dani.”? Yaji gabansa ya fad’i! sai yayi d’if takaicin kamar ya kashe shi…Ta cigaba da cewa”Dan Allah kayi hakuri salim kada kace na yaudareka ba laifina bane wallahi karfi ya gwada min har hakan ta faru gashi yayi min ciki ba tare dana fargaba wannan dalilin yasa na yanke shawarar zubar dashi dan wallahi ni bazan haihu dashi ba tunda bana sonsa.” Salim yayi murmushin mugunta da fadin”Yanzu kina ina.”? kai tsaye tace”Gani a cikin tasha zan bar garin gabad’aya dan nagaji da zama cikin wannan masifa.

Yace.”Kiyi hakuri kada ki tafi ki dawo gida sai mu san yanda za’ayi.” Tace”Salim nifa wallahi sai na zubar da cikin nan hankalina zai kwanta.” Yace.”To yanzu wane gari kika nufa haba Naja’atu kiyi hakuri ki kar’bi qaddara mana.” a fusace tace”au abinda zakace kenan Salim? ashe dama ni kadai nake wahalar da kaina a kanka ko.” Yace.”Ai dama na fada miki tuntuni kinfi karfina ni yanzu ke auntyna ce dan haka hakuri shi yafi alkairi a tsakaninmu.” Cike da bacin rai tace”Shikkenan salim nagode da butulci dama ai idan ba kayi min haka ba to baka cika namiji ba idan baka aureni ba akwai maza a duniya wanda suka fika komai da komai kuma ba zan fasa abinda na kudurta ba.” Tana gama maganarta ta kashe wayarta….Salim yayi sauri yayi serving din rocouding din da yasa ya sake kiran wayartata, kin dauka tayi ta hada kanta da gwiwa sai kuka take…Salim ganin taki daga wayar sai yayi murmushi a fili yace.”Alhmdullhi bukatata ta biya. numbar Kawun nasa ya shiga kira…Abbah Abbs ya daga wayar kafin ma yayi magana yaji muryar Salim din cikin tashin hankali yana fad’in “Kawu gida babu lafiya Naja’atu ta gudu ka bude whasap na turo maka muryarta yanzu muka gama waya da ita tana sheda min hukuncin data yankewa kanta.

Abba Abbas kasa gane maganar yayi yace.” Kai ka nutsu kayi min bayani ina zata nufa bayan yanzu mukayi waya da abokina magaji yace tana gida lafiya lau…Salim yace.”Wallahi kawu babu wasa a cikin maganata idan kana so ka gazgata ka bude audion dana turo maka ta whasap..Abbah Abbs hannunsa na rawa ya kashe wayar ya shiga whasap kawai sai yaga yayi exipire tsaki yaja yayi saurin shiga playstore domin dauko wani.

Can gida kuwa Baba Larai ta gama aikace-akaicen ta ta shiga dakin da naja’atun take domin ta dubata, taga bata dakin sai tayi tunanin kota tana toilet sai ta zauna gefan gadon Mufida tana jiran fitowarta…..Zaman minti ashirin tayi a dakin ba taji motsinta ba, sai ta mike da sauri ta isa bakin bandakin tana kiran sunanta. shurun da taji ne yasa da sauri ta tura kofar bandakin, tana rarraba idonta a ciki babu naja’atu babu dalilinta…Cikin faduwar gaba ta fito palon tana dubata hade da kiran sunanta. shuru taji babu alamunta a gidan, sai ta bude kofar palon ta fita da sauri ta nufi bakin gate.

Malam Ayuba maigadi na zaune shida Yunusa suna hira Larai ta karasa tace”Malam Ayuba kana zaune anan ko kaga fitowar Naja’atu.” Malam Ayuba yace.”Eh kwarai kuwa kimanin awa d’aya data wuce ta fito da akwati a hannunta nine ma na bude mata karamar kofa ta fita.

Baba Larai jin maganar akwati sai taji wani irin fargaba ya rufe ta, da sauri ta juya ta koma cikin gidan ta dauko mayafinta kai tsaye gidan aunty maryam ta nufa tana adduar Allah yasa kada yarinyar nan tace zataje wani gurin

Aunty maryam ta shiga rud’ani mutuka jin maganar da Larai ke tafe da ita, Gaskiya naja’atu bata da hankali kuma taurin kanta ne zai kaita ya baro.

Waya ta dauka ta kira mijinta a sanyaye ta fada masa halin da ake ciki…Abbah magaji bai nuna alhini ba dan shi a tunaninsa ina naja’atu ta sani da xata je? Yace.”Kada ku damu naja’atu babu inda za taje watakila tana can kofar na’isa gidan malam ko gidan alhaji dan haka dukkaninku ku kwantar da hankali.” 

Aunty maryam jiki a sanyaye tace to shikkenan Allah yasa tana can din.” Kashe wayar tayi tana wasiwasi a cikin ranta itafa ranta bai amince da cewar yarinyar na kofar na’isa ba, tafi zargin ta gudu ne kamar yanda kullum take cin alwashi sai ta bar gari gabadaya yanzu ta dawo daga rakiyar yarinyar,

Abbah Magaji na kashe wayar kira ya sake shigowa yana dubawa yaga abokinsa ne da sauri ya daga wayar da sallama a bakinsa….Abbah Abbas cikin tashin hankali da damuwa yace.”Alhaji magaji ya akayi haka ta faru ? ya akayi kukayi sake irin haka har yarinyar nan ta samu nasarar fita daga gida da sunan guduwa inata nufa cikin halin lalura.”? Abbah magaji yace.”Subahanallahi! kada dai maganar da maryam take fada min gaskiya ne Alhaji.”?

Abbah Abbas yace.”Gaskiya ne naja’atu ta had’a kayanta ta gudu! Yanzu na saurari recoding wayarsu da Salim ta kirashi ta sheda masa hukuncin da ta yanke akan cikina dake jikinta zata zubar dashi kuma komai rintse sai ta rabu da aurena shin me yayi zafi har yarinyar nan ta yanke mana wannan mummunan hukuncin.” Halisa dake gefansa a zaune wani murmushi ta saki ta sake gyara zamanta tana sake kasa kunneta a kan wayar da yake.

Abbah Magaji ya mike tsaye hankalinsa a tashe sai kiran kalmar innalilihi wa’ina ilaihi raji’un yake! gabadaya kansa ya kulle ya rasa abinda zaice..Da kyar yace.”Wallahi Alhaji Abbas ban ta’ba tsammanin yarinyar nan zata aikata wannan mummunan aikin ba tabbas dana san haka zata faru zan dauko ta dawo gabana ta zauna har ka dawo! to rashin sani yafi dare duhu! babban tashin hankali anan shine ina ta nufa cikin wannan halin da take ciki.

Abbah Abbas kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a Nejeria yace.”Nima shine babban damuwata amma babu komai dukkanin tsanani yana tare da sauki Allah zai tsareta ita da abinda ke cikinta idan Allah yasa dan dake cikinta zai taka duniya ina rokon Allah ya tsare min shi a duk inda zata shiga idan kuma bukatarta ta biya akansa sai na roki Allah ya maye min gurbi da wani.”Wannan kalaman na abokin nasa sunsa jikinsa yayi sanyi yace.”Alhaji kayi hakuri dan Allah insha Allah yarinyar nan ba tayi nisa ba tana kusa yanzu zan koma gida zansa aje a duba gidajen dangi ko can ta nufa dan Naja’atu bata san kowa a wani gari ba ballantana taje.”

Murmushi takaici yayi yana jin wani irin d’aci a bakinsa yace.”Allah ya jishshemu alkairi.” kashe wayarsa yayi yana jin wata masifaffiyar tsanar yarinyar a cikin zuciyarsa babu shakka ta salwantar masa da gudan jininsa sai ya nuna mata shi d’an halak ne….

Abbah magaji ya jima ri’ke da wayar a hannunsa ya shiga tunani da nazari akan abinda yarinyar ta aikata gaskiya bai ta’ba tsammanin faruwar haka daga gurinta ba sosai yarinyar tayi masa bazata….Kafin ya nufi gida sai da ya kar’bi wayar Salim ya saurari muryar Naja’atun nan ya sake gazgata maganar abokin nasa…kai tsaye motarsa ya shiga ya nufi kofar na’isa domin shedawa iyayensu halin da ake ciki.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button