YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 11 to 20

*********

Dakyar ya Iya juyowa Yana Kallan mummy Sai kuma yasaki hannun nijlah ya tako Har zuwa gabanta ya durgusa Kan gwaiwoyinsa tare da Hade hannunsa biyu,,idanunsa na hawaye..

Dauke Kanta mummy tayi Dan bataso soyayyarsa ta tauye Mata nata haqqin Har Taji ta amince da tafiyansa Duk da yasani zuciyarta bazata taba Lamunta da Hakan ba…

Qara rarrafowa yayi cikin kaduwar zuciya da fargaba yafara magana”mummy Dan Allah kiyi Karki juyamin Baya,,mummy fishinki masifane a gareni,,mummy karkisa nafada cikin fishin mahaliccina,,mummy nijlah matatace Kuma amana,,Bata Dan gata balle Dangi a kusa,,mummy Koda Suna kusa Na tabbata Basu da abinyi,,Ke mahaifiyace..

Nijlah marainiyace shiyasa nakesan taimaka Mata,,Amma kiyi tunani Idan Har baki yaddaba nizan hakura da nawa farin cikin nayimiki biyayya a matsayinki na uwa..

Yana gama fada ya Tashi beko jira amsar mummy ba ya kama hannun nijlah dake rakube jikin Kofa tana hawaye,,sedai yakai jikin Kofa ya Dan risina yace..

Yaya,, aunty lateefah Saida safe,,Yana gama fada Yaja musu kofa..

Yana fita mummy tasa kuka tana cewa kungani ko,, mashkur ya tafi shikenan sun kangaranmin da yaro ya Shiga Wani Hali,,Ko rantsuwa nayi baza kaffaraba Akan surkullensu Na Fulani sukayiwa yarona..

Hakuri su lateefa suka riqaba mummy harta Dena kuka,,nan ta kwanta tana Nishi Sama Sama tare da tinanin abinyi..

Mummy Dan Allah kiyi hakuri Karki Bari hawan jini ya kama mana ke,,Idan Wani Abu ya sameki wallahi Saina tada hankalin kauyen kankan gaba dayansa cewar Yaya cikin tashin hankali…

Mummy abin yazo da sauqi tinda yabaki zabi,,mu Kuma zamuyi masa zami mafi dacewa dashi,hakane lateefah shiyasa nakeso mummy ta kwantar da hankalinta,,da dadan kalamai suka riqa bin mummy Har bacci ya dauketa Bata Sani ba..

Mota yasa nijlah Shima ya Bude ya Shiga,,tinda suka fara tafiya nijlah take kuka tana qara qanqame jikinta,,hannu biyu mashkur yasa ya janyota jikinta,,nan ya kwantar da Kanta bisa cinyanshi Yana shafa lallausan gashin kanta tare da tuqi da Dayan hannunsa,,Duk da yadda yamata Bata Dena kuka ba Saima qara sautin kukanta tayi tana Kiran kaka,, sosai yakejin kukanta Har cikin zuciyarsa Dan haka yayi qoqarin dakatar da ita,,

Kiyi hakuri kinji amaryar mashkur,,indai Ina tare dake Babu me qara tabamin Ke,,turo baki tayi tana kuka tace..

To to ba agabanka wannan mutumin yayi cilli Dani ba,,Kuma aka zageni hadda zagin Malam Duka bakayi Magana ba,,

Karyar da murya yayi kama Yana Magana da Babbar budurwa yace,,Kuma shine abin kuka,,Shiru tayi tana qoqarin janye Kanta yasa hannu ya riqe Kan Yana murmushi,, shikenan kiyi hakuri bazasu qaraba,,kema Daga yanzu Idan ana tambayan matata kidena cewa gani,,koke bakisan Kunya irin Na Fulani ba,,

Murmushi nijlah tayi Har tana boye fuskanta a cinyanshi tace,,Toba kai bane Idan ana tambaya Sai kayi Shiru bakasan Gaya,,Amma Idan ka Gaya Ai Dai Bazan ce gani Bako..

Dungurinta yayi yace oh bazaki Dena fadaba Kenan?

Daga masa kai tayi alamar eh,,zaro Ido mashkur yayi tare da kewa lalala Ashe Ko Zan hadaki da Karan gidana tinda bakijin magana..

Wayyo Allah kado nadena,,Bazan qaraba,,kin tabbata dasauri ta Daga masa kai idanta taf da hawaye..

Dungurinta yayi Yana cewa kedai kinji Kunya baki da aiki Saina kuka,haka suka riqa tafiya Yana tuqi Suna hira..

Karfe 5 Na yamma mashkur ya isa Saban gidan daddy Wanda ya sha gyara kama da mutane a ciki,,tinda suka fara Shiga nijlah Ke kukan yinwa Dan ita Bata kallan gidan takeba sabida yinwan dake damunta Dan ma Tasha ruwa a toilet din mashkur lokacin data Shiga yin fitsari..

Daya Daga cikin bedroom ya ajiyeta Yana kallanta,,amarya Zaki fara wanka kafin kici abinci..

Badan taso ba ta Daga masa kai,,nan ya fara Dube Dube abinda zata Shiga wanka dashi be gani ba,,dasauri ya fita ya Shiga Wani Dakin,, wardrobe ya Bude nan ya dauko Saban towel dinsa daya ajiye kwanakin Baya ya dawo Dakin da nijlah Ke zaune tana rarraba ido..

Tana ganinshi ta Tashi da gudu tazo bakin qofan tana cewa,,kado gaskiya ka Dade nan gaba tare zamuna fita Dan gaskiya tsoro nakeji..

To shikenan yanzu Dai amsa wannan ki daura muje ayi wanka..

Amsa tayi Sai kuma ta kasa cire kayan jikinta,,hannu yasa ya janyota jikinshi yafara rabata da kayan jikinta,, girgiza masa kai tayi tana cewa kado bafa kyau babba yaga jikin mutum..

Nasani kokin manta Ni mijinkine,,lah mantawa nayi Amma ka barshi nagode nizan cire dakaina,, murmushi yayi Yana cewa saikace ta Iya wankan Toni Bazan Bari kiyi jiqa jiqaba,,kizo kinamin doyi a Daki..

Dire diren qafa nijlah tafara tana kukan shagwaba,Ni Allah Bana doyi,,gwalo mashkur yayi Mata tare da kashe Mata Ido daya..

Binshi tayi da gudu tana San kamashi suka riqa zagaye katan falon..

Shi Yana dariya ita Kuma tana masa kukan shagwaba lolxx…

Yawan comments yasa na muku typing Akan lokaci,,fatan zakuyi wanda yafi Na jiya..

*Comments & share*

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*SHAFA’ATU UMAR*

2⃣5⃣&2⃣6⃣

Be Bari ta kamashi ba Saida yaga alaman gajiya a tare da ita,,ga yinwa dake faman zaliganta,,nan ya fada saman bed Yana Mata gwalo..

Kuka nijlah tasa hadda hawaye tabishi Har Kan gadonta tana Dukan qirshinshi tare da turo Dan karamin bakinta,,kallanta ya tsaya Yana Yi tare da aiyana irin soyayya da zasu gudanar a lokacin da komai ya daidaita,,jiyake ajikinsa nijlah ta gama Zama komai nasa,,Duk kuwa da kankantar shekarunta Hakan Baze hanashi hutawa da matarsa ba,,sedai Wani bangare na zuciyarsa na hanashi aikata hakan tare da tinamasa dasha Abar kaunarsa Yasmeen..

Ganin yayi shiru Yana tinani yasa nijlah ta hadiye kukanta sakamokon Jin cikinta Na murdawa,,kallan mashkur tayi Sai kuma ta dauke Kanta gefe tana cewa.

Dan birni Dama ba’a Cin abinci anan,,nifa yinwa nakeji,tafada cike da yarinta,,kafin mashkur yayi Magana nijlah ta kama hannunsa,,a hankali ta Daga rigarta ta Dora hannun a saitin cikinta tace..

Taba Kaji yadda cikina yake juyawa,, Allah ciroma yake Kira..

Mashkur be amsataba Sai dariya daya saki Yana Kallan ta,,shagwabe fuska tayi,,idonta taf da hawaye,,kinga Karki Bata hawayenki,,yanzu zakici abinci me Rai da lafiya irin wanda baki taba Ciba kinji amarya..

To ai Baka Bani ba,,Sai gafara sa kakemin banga qaho ba”

Ahhh,, inye amaryar tawa haka ta Iya magana,,rufe Ido nijlah tayi tana boyewa a bayanshi,,nan ya Tashi ya dauketa ya Shiga toilet da ita,,Saida ya ajiyeta kafin ya fito dauko towel..

Nijlah Na ganin ya fita tayi saurin cire kayanta tare da tinanin inda ruwa Ze fara zuwa,,Kalle kalle ta fara tana dube dube Aiko idanta ya safka Kan Dan qaramin bahon wanka dake cike da ruwan dumi..

Murmushi tayi tana cewa kai kaga ruwa saikace Na wankan mutum 10,,soso ta dauka ta Shiga neman sabulu,,ta jima tana nema Bata gani ba Sai can ta hanqi shaving cream,,Da sauri ta dauka tare da budeshi shi Bata” Bata lokaci ba gurin matsashi jikin Soso tafara gogawa a jikinta,,ganin Baya kumfa ta qara zuba Wani,me yawa Wanda yafi nada..

Tana cikin wanke jikinta dashi Taji mashkur ya saki salati,,bayanta ta juya masa tana turo baki..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button