YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 41 to 50 (The End)

Ad

_____

Kuka yake kama qaramin yaro,,Banda Kiran sunanta Babu abinda yake.Ido daddy ya zuba masa Yana hawaye yayinda bakinsa be bar tofa masa dukkan addu’oin da suka zomasa ba’Amma duk da haka mashkur Bai Dena bige bige ba Yana Kiran nijlah.

Ganin yadda daddy ya zuba masa ido hawayen tausan Dan nasa na zuba cikin kurmin idonsa Batare daya qara cemasa komai ba yasa mashkur yin wani irin kukan kura ya fizge qarin ruwan dake daure a hannunsa ya diro daga kan gadon Yana cewa’

Nina tafi Na nemo ta,,bazan iya rayuwa Babu itaba wallahi daddy nasaba da ita.

Sai yanzu hankalin daddy ya dawo jikinsa yayi saurin tare mashkur Dan Shi bemasan ya fado ba.

Dakyar yake janshi yanasan maidashi kan gadon sedai Sam mashkur yaqi basa damar Hakan Kuka Kawai yake Yana ihu tare da Kiran sunan Nijlah.

Lokaci guda ya hada zufa Suna Shiga kokuwa shida daddy,,Shi yanasan kwacewa ya tafi neman nijlah Shi Kuma daddy Yana qoqarin kwantar dashi kan gadon sedai mashkur yaqi bashi damar hakan gashi Babu kowa cikin dakin,,likitoci duk sun fita sabida an kawo wani mara lafiya.

Cikin bacin Rai da takaici daddy ya daka mashkur tsawa Yana’ kai auta ka nutsu mana,,so kake ka fita muma mu Shiga uku,,idan ka fita ina zaka je?koso kake ka Shiga Duniya sabida rashin mace?

Ba qaramin takaici da rashin Jin Dadi maganganun daddy sukayi masa,,jiyayi maganansa kama Yana yankan naman jikinsa Dan haka ya fizge jikinsa da karfi yayi bakin kofa Yana cewa’

Tafiya zanyi daddy’ nijlah ba wata bace matatace ta Sunna Wanda take Amana a gareni’ daddy nijlah amanace Dan haka nima Sai Dai ku rasani Kamar yadda itama iyayenta suka rasata’ Wallahi bazan bazan dawo ba saina ganta idan Kuma Na rasata nima acan Zan qare rayuwa sabida rayuwana bashida wani amfani idan Bata..

Tassss tassss tassss daddy ya saukewa mashkur lafiyayyun marika har guda shida Yana cewa’

Ad

Baka da hankaline to idan Baka dashi maza maza ka dawo cikin nutsuwarka’ 

Da kasan kanasanta Na dauki gida Na Baka Amma kayi watsi dashi kake kawowa mahaifiyarka ita alhali kasan ba kaunar fulani take ba,, mashkur mahaifiyarka tana da tabo Wanda wani fulani sukayimata sedai ta kasa ganewa ba duka’ jama’a suka zama daya ba,,nayi iyakar qoqarina ta dena taqi kai Kuma kaje ka dauko yar fulani fulaninma matsiyata,, tayaya kake tinanin zata hakura ta zauna da ita..

Shine yanzu inama Magana kanaji kake Abu kama mara hankali,,hauka kake kome? 

Daddy ya tambaya a zafafe ganin inba haka yayimasa ba bazasu wanye lafiya ba..

Tinda mashkur ya dafe kunci be qara yin gurin dagowa ba har saida daddy yakai aya,kafin mashkur ya Dago jajayen idanunsa Yana kallan daddy dasu sedai har zuwa yanzu bashi da Magana daze iya fada.

Ka wuce ka kwanta nace’

Daddy Na samu lafiya gida Zan wuce’

Amma Dai duk da haka ka kwanta likita ya bamu sallama ko?

Ah ah daddy ni tafiya zan, Dr bashida maganin ciwo Na gwara Na koma gida kona mutu a dakin mahaifiyata mashkur yayi maganar cikin tashin hankali da damuwa.

Sosai Yaba daddy tausai har besan lokacin dayasa hannu ya janyosa jikinsa ba Yana shafa bayansa.

Kan gadon daddy ya zauna mashkur Na kwance a qirjinsa,, mashkur beyi qoqarin kwace waba sabida neman me rarrashinsa yake a wannan lokaci Dan haka ya qara lafewa a jikin daddy Yana fidda numfashi da sauri da sauri..

Nauyayyar ajiyar zuciya daddy ya safke Yana kallan mashkur kafin ya bude baki a hankali yace’

Auta ba qinka nake ba kada ka dauka haka,sedai ina tsoran kada kaima mu rasaka tinda naji furucin bakinka Na cewa bazaka dawo ba har Sai kaga nijlah.

To a ina zaka ganta?kasan inda take.

Shiru mashkur yayi Yana fidda sautin Kuka a hankali a hankali.

Auta kayi shiru daddy ya tamabay cikin lallashi da da dabara?

Uhmn daddy bansani ba,,sedai a duk inda take jikina Yana gayamin Babu kwamciyar hankali’ni tsorona kada ‘yan iska su dauketa suje suyimin asaran Dana Dade ina tattali,,daddy ka taimakeni aga nijlah wallahi zuciyana yana Shirin tarwatsewa.

To to ya isa haka,,banaso kana tada hankalinka insha Allah za’a ganta Kaji ko,, yanzu ka zauna kafin dr yazo..

Badan ashkur yaso ba ya zauna Yana ta jinjiga kai da ido daddy ya bishi Yana mamakin irin sanda ya jefa kanshi gurin yiwa qaramar yarinya kama nijlah..

Da kuka aka fara kwankwasa dakin daddy dame zaune ya janye mashkur a jikinsa ya je ya bude kofan’

Yasmeen ce tsaye ita da mubeena suka shigo’ gaba day idon Yasmeen ya rufe Babu abinda takesan gani sama da angon nata shiyasa ko daddy Bata kula dashi ba ta tafi jikin gadon tana ihun kuka..

Ganin haka yasa daddy fita a dakin Yana girgiza kai domin kallo daya yayima Yasmeen ya gane itace budurwan mashkur.

Yasmeen batayi wani tunani Na ta fada jikin mashkur tana kuka tana cewa’

Baby meya sameka yanzu muna restaurant aunty lateefah ta bugo take gayamin Baka da lafiya,, baby ina ke ma ciwo?

Murmushi mashkur yayi a karo Na farko dayasa hannu ya rungume Yasmeen Yana shafa bayanta’ 

Dakyar yasamu nutsuwar janyeta a jikinsa Yana cewa’ zauna anan Yasmeen.

Kiyi hakuri kidena Kuka kinsan banasan wannan damuwan naki.

Dariya mubeeena tayi tana cewa’ ah inye wato kaida za’a rarrasa Kaine ka dawo rarrashin wani?

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button