YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Ad

_____

Mummy na ganin shigowar mashkur hannunsa riqe Dana nijlah ta Mike tsaye”jikinta Har kyarma yake gurin finciko nijlah ta cillata Baya tana nuna mashkur da dan yatsa’wallahi Karya kake mashkur nadena zubamaka Ido kana yadda kaso” kwana fa kayi tare da wannan shegiyar yarinyar,mummy ta fada tana nuna nijlah dake rabe jikin bed tana hawaye’Nan take zuciyar mashkur tafara bugawa da qarfin gaske Babu abinda yake kallo Sai nijlah data daskare tsaye tana mamakin halin mutanan da Allah ya hadata Zama dasu” 

Yanzu shikenan ahaka zanyi rayuwa? Adakeni lokacin da akaso,,a zageni Duka Ni daya?

Nijlah ta tambaya Kanta tana sakin kuka meban tausai..

Girgiza Mata kai mashkur ya shigayi yanasan hanata kukan,,da yanada Iko jikinsa ze janyota ya rarrasheta koya rage Jin abinda yakeji a cikin zuciyarsa..

Dan gidanku auta Bada kai nake Magana ba,,kodai kurma ka Zama?

Fuskar mashkur sake yake kallan mummy Amma a can cikin zuciyarsa bacin raine chinkuye a ciki sedai bashida damar nunawa mummy Hakan..

Ka tsareni da ido Ko bakaji tambayan danayi Maka ba?

Murmushi yayi Wanda yafi kuka ciwo ya Bude baki ahankali zuciyarsa na bugawa yace’mummy bafa a gurinta Na kwana ba,,inacan muna tsara yadda za’a gudanar da bikinmu da Yasmeen to shine dare yayi,Saina zauna Na kwana acan..

Yanzu dazan dawo shine Na biya Na taho da ita Ko nijlah mashkur ya qare maganar cikin bugawar zuciya da zillimin Baran baramar da nijlah zata Iya yimasa..

Dasauri nijlah tashiga Daga kai tana cewa eh.

Ad

Kaga auta banisan qarya?

Cike da shagwaba Mashkur ya fada jikin mummy Yana cewa’ Toba ga yarinyar nan tsayeba Ai saiki tamabayeta” to to shikenan yanzu a Ina kuka tsaya Kan batin shagalin bikin?

Dariya mashkur yayi Yana Kallan nijlah da tinda ya ambaci aurensa ta hadiye kukan tana kallansa” nan ya kashe Mata Ido Yana cewa’ Ai mummy ki kwantar da Hankalinki Dan munriga mungama Hada komai kedai kawai ki jira lokaci..

Dariyar farin ciki mummy tayi tana shafa Kan mashkur tace’ Yau Dan albarka kaga shikenan Nima zanga auren auta Na” sosaima yafada Yana janye jikinsa.

Mummy nizan Shiga daki inasan watsa ruwa a jikina’ Yana dakyau Ai,,Amma Dai Idan ka shirya gurin mutuniyar zakaje?

Sosa kai mashkur yayi Yana cewa’ eh Mummy 

Shiru nijlah tayi tare tare da yin tsuru tsuru da Ido tana kallansu daya Bayan daya yayinda hawaye suka riqa zirya a idonta,, ganin yadda gaba daya mashkur ya manta da ita tsaye Saima maganar aurensa yake,,

To waima yaushe aka bashi aurena dahar yafara maganar Wani auren?

Nijlah ta tambaya Kanta..

Sedai abinda Bata Sani ba shine” Duk abinda mashkur yake Yana kallanta tare dajin matsanancin tausanta bashida yadda zeyi shiyasa ya zuba ido akemata yadda akaso..

Mashkur Na satar kallan nijlah ya fita a Dakin Yana addu’a Allah yasa nijlah ta biyo bayansa,, harya fita Beji alaman tahowantana Dan haka ya tsaya Daga kofa Yana leqenta…

Nijlah Na ganin tafiyan mashkur ta Daga qafa a hankali tanasan binshi Taji mummy tace”dawo Nace,,

Dan ubanki Ina Zaki bishi?

Muryar nijlah Na rawa tace” uhmn Zan”

Uhmn uhmn me” wato Kan ansaba bin Maza a gindi a gandi kuna yawo da shanu shine Zaki bishi kuyi wankan tare Ko?

Shiru nijlah tayi tana wasa da hannunta..

Kibani amsa” nasan Dai babu abinda Zaki Iya a bed dadai yawan jejeni nasan anan kikafi kauri..

Tsuru tsuru nijlah tayi tana tsoran kada mummy ta doketa,,bakinta Na rawa tace” 

Dan Allah baba kiyi hakuri Bazan qaraba” 

Ah ah Wallahi Zaki qara,,indai shawan jejine Dan baki Samu gurin Zama anan ba..

Ita Dai nijlah Bata qara Magana ba Banda rawa Babu abinda jikinta yake” akankali Takai kallanta ga kofa Aiko taci sa’a idanta ya safka Kanna mashkur” hannu yasa ya yaficeta dashi tare da yimata alamar Kira..

Aida sauri nijlah tayi hanyar fita tana tafiya tana Hada hanya.

Ke dawo Dan ubanki Ina zakije” hannu yasa ya rufe bakinsa Yana Mata alama da kada tayi magana nan itama tasa hannu ta rufe bakinta tana kuka a hankali”

Duk abinda mashkur yake daddy Na tsaye a bayansa sedai yarasa abinda yakewa hakan danshi ba cikin Dakin yake kallo ba” hakanan jikin mashkur ya dauki rawa nan daddy yasa hannu ya janyeshi Daga jikin qofar ya Kuma sa kai ciki..

Mummy bataji zuwan daddy ba ta shigaba da zazzaga Mata masifa” sabida Ke mayyace kinkasa gane cewa ba’a sanki,,Sai liqewa yaro kike Yana guduwa,,Ni wallahi naso ace mutuwa kikayi da tinin Na huta da damuwa..

Tana leqewa yaranki Koshi Yana liqe Mata” kinga hajiya ki kiyayi kanki” Idan baso kike rabo ya kasheki ba daddy ya fada cikin daure fuska,,

Kina nan kinsa masa Mata gaba kinacin zarafi Shi Kuma ya labe Yana Kiran matarsa Amma sabida tsabar San zuciya kinkasa ganewa..

Tabe baki mummy tayi tana cewa’ to Wai Alhaji me nayi kawai sabida Na hanata zuwa dakinsa saika hauni da fada,,Ko Dai sokake gaba daya yarinyarnan ta tare masa a Daki Sai Abu mara Dadi yafaru azo ana zance da karkata kai?

Nauyayyen ajiyar zuciya daddy ya safke Yana cewa’wanne irin Abu mara Dadi?Naga Dai matarsace ta Sunna Dan haka kibarsu suyi rayuwarsu yadda sukeso..

Hhhhhh wacce irin rayuwace za’ayi da wannan jaririyar yarinyar Ko bakaga yadda take ba” Ni wallahi bansan meyasa auta ya kwaso wannan ba,, ka dubetafa kama an daura muciya zani.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button