YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 21 to 30

Ad

_____

Bacci mummy ta maimaita tare da janye wayan daga kunnanta tana duba number data Kira”Number mashkur ta gani nan ta qara mutsika idanta tanasan tabbatarwa,,shidinne ba wani ba..

Ranta a mugun bace tace,wacce shegiya ke magana?

Murmushi nijlah tayi tana qara bude Zara Zaran idanta tace,,Kai amma dai wannan anyi babbar banza,,da girmanki kina zagi sai kace wadda ta Kira wayar danta ko mijinta..

Kasa magana mummy tayi,,Banda kallan number mashkur babu abinda take tana jinjiga Kai,,mamakinta be qareba sai da taji muryan nijlah na cewa,,,

Nidai na gayamiki wannan number mijina ne,,karki qara Kira tinda ke…..

Wani uban zaki mummy ta saki tana tashi tsaye,,bakinta na rawa tace,, nijlah Dama kece???

Murmushi nijlah tayi jin me maganan ta santa,,Dan haka takasa qasara abinda takesan gaya…

Nijlah ni kike zagi,,Dan ubanki,,hannu nijlah ta dora a kasa tana cewa,, Allah ba zaginki nayi ba,,dan Allah Baba kiyi hakuri kwaran kwatsa dubu bansan kece ba…

Kuka mummy tasa tana cewa shikenan auta Ka daukomin masifa,,wallahi karatunka be amfanamin komai ba sai tashin hankali,kukane yaci karfinta Dan haka ta katse kiran..

Daddy ne ya shigo dakin Jin kukan mummy ya tsaya a kanta Yana sauraranta”

Ad

Beyi magana ba Saida yaji ta tsaya da kukanta kafin yasamu guri kusa da ita ya zauna Yana fuskantarta,,cikin kuka mummy tace..

Kagani ko alhaji,,zuba Mata Ido yayi yanasan Jin abinda ke faruwa..

Kuka mummy ta qara saki tana cewa,,yanzu wannan yarinyar me sunan aljanu ta dauka wayana tagama zagina ta uwa ta uba,,har tana cewa wai nayi girman banza..

Bakin daddy na rawa yake tambaya,,wacce yarinyace wannan kuma meya hadaki da ita???

Kaima kasani ba Wanda ze iya cimin mutumchi irin wannan yarinyace da mashkur ya dauko..

Ran daddy bace yace,,Dama ita nijlah har waya gareta” 

Mashkur fa nakira yanzu shine ta dauka take zagina..

Shikenan kiyi hakuri ninasan batasan Wanda ta Kira ba,,Amma zanyi Mata magana,,wallahi baze zauna da ita ba Kaji harna rantse,,sedai ya zaba koni Ko ita,mummy ta qare maganan tana huci..

Gyara Zama daddy yayi Yana Kallan mummy kafin ya Bude baki a hankali yafara magana”

Se yaushe Zan gayamiki ba saki tsakanin mashkur da nijlah,,kokin manta Akan wannan Yar maganar kusan kwana mukayi dake muyinta..

Koma Dai menene Nina haifi yarona Dan haka Dole yabi umarnina eheeee..

Fuskar daddy dauke da murmushi yace,,Nima bance Wani ya Haifa Miki Shiba,,sedai Kamar yadda Allah ya Dora Miki haqqi akansa haka yanzu ya Dora haqqi matarsa akansa,,

Cike da masifa mummy tayi Kan daddy,,karka qara cewa nijlah matarsace Dan ni banyiwa yarona aure ba..

Haba hajiya karki nemi ki maida kanki jahila,,nasan kinsan auren mashkur da nijlah ya dauru sabida a gabanki Na Kira Nasir mukayi Magana Se yanzu Zaki tsiro da wannan maganar.

Eh Koma Dai menene sakinta zeyi..

Shiya gayamiki Baya santa?

Oho Dai nidai Na gayama,,yarinyar da ta gama zageni kana nufin da ita Dana Ze zauna..

Kinga hajiya ki dawo cikin Hankalinki,,ninasan nijlah bazata Iya kallanki ta zagaba,,nasani koba komai tana da tarbiyya da sanin darajar Dan adam duba da ganin inda ta fito…

Dan haka nake Han hankalinki daki zubda makaman yaqinki indai kinaso girmanki ya dore a idan wannan yarinya…

Tabe Baki mummy tayi Dan ita batasan abinda Zata fada ba sai dai zuwa yanzu jikinta yagama yin sanyi ganin Yadda daddy da mashkur suka dauka yarinyar..

Har daddy yakai kofa yaji muryar mummy na cewa,,toya maganar ita yasmeen,,ko shikenan tinda yasamu yar fulani,,koba komai kema Dan Fulani kike aure kinga Ko ba laifi bane Dan danki ya auri ‘yar Fulani..

Maganar Yasmeen,,naje munyi Magana da mahaifinta Na Kuma gayamasa abinda Ke faruwa,,yanzu shawara ta rage naso Idan zata aureshi to,,Idan Kuma sun fasa shikenan Sai muyi fata Allah yabata Wani..

Daddy Na gama fada ya fita ya bar mummy tana zazzaga masifa,,a falo ya hadu da aunty lateefah nan ya nuna ta da yatsa..

Ke Kuma inaso gobe goben nan ki tattara ki Koma gurin mijinki,,Idan ba haka ba Saina Saba Miki,, shashancin banza kawai,,Daga ku Har uwar Taku an Rasa me hankali…

Kan aunty lateefah Na qasa Har fa daddy yagama fada ya fita,,Yana fita ta shiga Dakin mummy da gudu..

Kusa da mummy ta zauna tana rarrashinta,,mummy kiyi hakuri Ni inaga kawai kice su dawo gidannan da Zama,,inyaso saiki kwace nijlah,,shikuma ya tafi da yasmeen..

Lateefah nifa banasan yarinyar nan,,wallahi Na tsani fulani,,daddynkuma Danya zamamin Dole shiyasa nake zaune dashi..

Mummy Duk da haka Ke Zaki sauko Danni banga alamun zasu rabu da wannan mayyar ba,,Aiko Dole ya rabu da ita indai Nina tsugunna Na haifeshi..

Hakane mummy Amma Baki ganin yadda daddy yayi ruwa yayi tsaki a cikin lamarin nan,,nidai ina tsoran abinda zeje ya dawo,,yanzu ma bakiga yadda yayimin ba,yace gobe na tattara kayana na koma gidana..

Mummy na huci tace au haka yace,,to wallahi babu inda zakije sai an gama da matsalana.

Mummy nidai gaskiya tsoran daddy nakeji,,kibari kawai mayi a waya..

Ba haka mummy taso ba sedan batasan laifin yaranta Dan haka tace to shikenan yanzu ki Kira auta yazo ayi magana kawai..

Mummy keya kamata ki kirashi ko bakiga yadda yakemin magana kamar wata sa’arshiba,,kodan yana ganin Shima yanzu ya girma harda aure..

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button