YAR SADAKA Page 11 to 20

Bayan ta gama ya kalleta Yana murmushi yace,, kinyi Sallah Dana fita,,eh tace tana Maida masa da murmushi,,yauwa Yar albarka haka nakeso ki riqa Sallah Akan lokaci,,sedai inaso kiyimin addu’a a Duk lokacin data kikayi Sallah,,
To mezan roqa ma,,Naga kai kasamu komai Baka da Wani matsala,, murmushi yayi Dan ganin yadda nijlah keda wayo komai nata Na masu hankali take indai ba shagwabanta ya Tashi ba,..
Kawo kunnanki Zan gayamiki abinda Zaki roqamin,,to tace tana Tura masa kunnan a saitin bakinsa,,magana ya gayamata tayi saurin qocewa tana yimasa gwalo..
Ta tafi Daki da gudu,,binta yayi suka kwanta,,nan ya janyota jikinsa Yana shinshinata ahaka barci ya daukesu..
Cikin dare yajishi kwance cikin ruwa,,ga Wani irin wari Na Tashi,,hannu yasa ya shafa gurin tare da kai hannunsa Kan hancinsa,,tsamin Kashi yaji yayi saurin Bude idansa Yana cewa badai kashi nijlah tayi ba…
Nijlah Ko baccinta take Hankali kwance,,a hankali yasa hannu ya kunna fitila,,Yana ……
Comments & share
*Momn sultan ce*✍✍✍
???????? *’YAR SADAKA..*????????
*STORY & WRITING BY…*
*BY*
*MOMN SULTAN*
*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*
*SPECIAL GIFT TO…*
*AMARYA SURY BABY.*
2⃣9⃣&3⃣0⃣
Haskene ya gauraye Dakin nan yafara Dube Dube Yana mamakin ta inda doyi yake fitowa,,idansa ya Maida Kan nijlah dake baccinta tana qara juyi cikin gudawan daya gama wanke Mata jiki..
Subhanallah badai yarinyarnan kashin kwance tayi ba,, mashkur yafada Yana Duba jikinsa,,gani yayi Duk Kashi ya gama batasa Hatta wuyansa Saida ya Bata ga Kuma hannunsa daya taba lokacin dayaji laima a jikinsa..
Rasa abinda zeyi yayi ya Kuma nijlah Sai qara matsowa jikinsa take sabida jinta cikin sanyi,,tureta yayi ya daka matsawa Yana Kiran sunanta.
Afirgice ta farka tana addu’a tare da qanqameshi,,take yaji tausayinta sedai be nuna Hakan ba ya sake daka Mata tsawa a Karo Na biyu yace..
Dama haryanzu kina kashin kwance,,to wallahi Bazan laminchi wannan iskancinba Dan haka diapers zanke Samiki..
Kashi Kuma nijlah ta fada tana qoqarin Tashi zaune” hararanta yayi Yana cewa ah ah Karya nayimiki..
Hannu tasa Taji danshi a jikinta Dan haka ta turo baki tana cewa,, Allah bansan nayi ba nidai Naji cikina ya Murda Daga nan naganni a gona Ina Kashi..
Cike da masifa yace,,Toba a gona kikeba Akan katuwar katifa kikayi,,kinga yanzu saikisan yadda zakiyi damu..
Marairacewa nijlah tayi tana Hada hannunta tace,,wallahi bansan yadda Zan gyaraba nidai ka temakeni ka wankemin kada cikina ya kumbura,,wallahi tsami yafara damuna, nijlah ta fada tana toshe hanci..
Sabida haushi mashkur besan lokacin daya cire hannunta Daga Kan hancintaba Yana zazzaga Mata masifa..
Shiru tayi tana sauraransa jikinta Na rawa ta Rasa yadda zatayi dashi,,Dan ita Bata Saba Jin irin wannan fadan ba..
Seda yayi shiru Dan kanshi kafin nijlah ta kalleshi tana murguda baki tace,,
Naga Dai Duk kaika jamin wannan kashin,,Saida Nace kabani tuwan dawa kaqi kabani kaza da irin wannan taliyan ta larabawa Sai yanzu da haka ta faru Zaka Sani gaba kana….doke bakinta yayi da hannu biyu tare da kama kunnanta Yaja sosai Yana Mata kashedi..
Kinsan Allah Daga Yau Kika qara yimin kashin kwance Saina Miki Duka,,yanzu da a gidan mummy kikayi Yaya zanyi da raina,,Ina kikeso nasa kaina nijlah,,Ke haryanzu baki da wayo???
Idanta taf da hawaye tace kayi hakuri Allah Bazan qaraba,,tureta yayi ya Tashi a hankali Yana Kallan jikinsa,,rintse idonsa yayi Yana me Jin takaicin abinda nijlah ta aikata masa..
Yanzu yaya zanyi?
Ta Ina zanfara gyara jikina Dana wannan yarinyar,,Babu shakka Na Hada kaina da aiki indai irin haka ta cigaba da faruwa..
Tinda nijlah taga ya Tashi itama tafara qoqarin Tashi tsaye tana toshe hanci,,kallanta yayi yayi kwafa Yana cewa,,Idan baki cire hannunki a hanci ba Saina wanke Miki fuska da wannan kashin koba Ke kikayi ba,,Zaki Wani rufe hanci kama kama wanine yayi Miki..
Badan tasoba ya cire hannun sedai takasa hadiye saliva,,Yana Shiga toilet tayi saurin binshi,,harya Shiga ya leqo Yana Mata Magana da Ido,,tini ta gane abinda yake nufi Dan haka ta tsaya tsaye Akan gadon tana kuka..
Air freshener ya dauko yafara feshe Dakin dashi Yana sakin tsaki Akai Akai,,Seda yaji tsamin ya ragu kafin ya dawo Kan gadon..
Daga tsaye yafara cire kayan jikinsa,, nijlah Na ganin Ze zare wandansa tayi saurin rufe Ido tana juya masa Baya..
Babban wandansa ya cire ya rage daga Shi Sai Dan qarami Yana kallanta..
Tana Daga tsaye yace,,kicire wannan wandan kafin nayi boll dake,,kazama kawai,,Ni wallahi tinda nake bantaba aiki cikin dare ba Sai akanki,,Yoko jaririya nadauko Sai haka..
Kukanta ta qara volume shiko yayi shiru Yana sauraranta.
Zuwa can dabata ta fado masa ganin Bata da niyyar cire kayan yace,, shikenan nizan wuci Dayan Dakin Kinga saiki kwana cikin doyi,,da anjima kare yazo ya cinyeki..
Wayyo Allah kaka dan birni ze,,kifa denamin ihu Ko bakisan da makoftaba,,salan suyi tunanin satoki nayi”‘ uhmn uhmn Toni ka ciremin kayan Allah Bazan Iya tabawa ba..
Mamakine ya kamashi ganin yadda ta zage tana kuka takuma Qi taba jikinta ita a dole kyankyami takeji..
Babu yadda ya Iya haka yasa hannu ya cire Mata wandan,nan ya ajiye Kan gadon yasa hannu yajanyota jikinshi nan yafara cire Mata riga,,Yana gamawa ya safketa kasa Shima ya safko,,Gana daya ya tattare bedsheet din da kayan jikinsu ya dauko katuwan Leda yasa ciki,,nan ya Cilla cikin Shara Yana kallan yadda tafara karkarwa sabida sanyi..
Toilet ya Shiga ya Hada ruwa me zafi ya dawo ya dauketa,,cikin ruwan yasata yayimata wanka sosai,,Bayan ya gama Mata ya Bata towel ta daura,,Zaki Iya jirana a waje Nima nayi wankan,, girgiza masa kai tayi tana turo baki..
Banace kidena turomin baki ba,,koso kike Na zuba Miki Ido kinayin abinda kikaga Dama,,a hankali nijlah tace ah ah kayi hakuri..
Bude Mata kofa yayi yace ki zauna anan yanzu Zan fito ba dadewa zanyi b,,Yana gama fada ya Koma ciki yabar anan tsaye tana jin tsoro..
Bayan ya fito ya dauketa suka Koma daya dakin,,shida kanshi ya shafeta da Mai Shima ya shafa,,turarensa ya shafa Mata Yana Kallan yadda tayi Shiru kama ba ita ba,,Kan bed ya Koma hannunsa riqe da nata..
Suna kwanciya bacci ya daukesu,,be Iya tashin asuba ba Sai farkawa yayi yaji Har an idar da sallah,,dasauri ya Tashi ya fada toilet yayi brushe,a gaggauce yayi wanka sabida gajiya dake damunsa Bayan ya gama ya dauro alwala ya fito Yana tsane jikinsa da towel,,kallan Nijlah yayi Yana murmushi tare da Kiran sunanta a hankali..
Wardrobe ya bude ya dauko jallabiya,,nan ya shinfida sallaya ya tada Sallah,,Bayan ya isar yayi addua sosai tare da Neman mafita a al’amuransa..
Nan ya dawo kan gadon Yana tashinta,,ke nijlah tashi mana lokacin Sallah na shigewa..
Uhmn uhmn nika bari bacci nakeji,,Sallah zakiyi Sai ki koma baccin,,kinga nima Shi nakeji..
Kasa Tashi nijlah tayi saima juya masa baya datayi tana turo Dan qaramin bakinta,duk a cikin bacci..
Ganin tana Bata Masa lokaci yasashi fara yamata chakulkuli,,tinda bazaki tashiba ninasan maganinki..
Dariya nijlah tariqayi tana ture hannunsa,,nan ya dauketa ya kai toilet,,harya juya baya da niyyan tafiya yaji takira sunanshi..
Nini ban iya kunna wannan ba,,ta fada tana nuna kan famfo,, murmushi yayi ya kunna mata,,tsayawa yayi Yana kallanta kafin yace to madam Sai Kuma me,, brushe ta nuna masa tana satar kallanshi.