YAR SADAKA Page 11 to 20

Bashida yadda zeyi Dan haka ya dauko nasa ya matsa maclean,,amsa tayi tana boye fuska tace nagode..
Idan kin gama ga ruwa nan Sai kiyi wanka ,,ni ah ah,bayan nayi wanka dazan kwanta,,nifa kaka har fada takemin idan taga ina wanka kullum
To suda ba wannan na tambayeki ba,,wanka nace kiyi ko harkin manta laifinki,,shiru nijlah tayi tana kauda fuska,,nan ya fita yana cewa kiyi sauri ina jiranki..
Bata Dade ba ta fito tana turo Baki,,kallanta yayi yaga babu alamun wanka a jikinta, idansa akanta yace,,Amma dai Baki wanka ba???
Daga masa Kai tayi ta kuma qi qarasowa inda yake.
Meya hanaki Yi?
Kai tsaye nijlah tace,,ban iyaba,,
Murmushi kawai yayi kafin ya nuna mata sallaya,, hijabi tasa tayi saurin tada sallah Dan zuwa yanzu tafara gajiya da kallan dayake mata..
Kafin ta idar harya hau kan bed yana bacci yafara daukanshi..
Nijlah kasa hawa gadon tayi Dan tsoro,,nan ta kwanta kan sallaya itama bacci ya dauketa..
**********
Nasir nifa tsoran fita nake Dan wallahi gani nake kama malam ze iya gane wani abu,,dafashi Nasir yayi yana magana a hankali..
Kaga Bello ka kwantar da hankalinka,,ninasan malam baze kawo komai a cikin ransa ba,,tinda dai yana ganina a gari..
To shikenan Nasir Amma fa saika rakani,
Tashi Nasir yayi yana kama hannun bello,,kaga tashi muce kafin lokaci ya qure..
A kofar gida suka Sami malam danya kasa zaman gida,,sabida kukan da kaka ta damesa dashi,,yayi rarrashin harya gaji Dan haka ya dawo kofar gida koze Samu sauqin wani abun..
Yana ganin su bello yafara murmushi yana cewa..
Ah ah Muhammad bello harka dawo,,daga masa Kai yayi suka qarasa kusa dashi suka zauna..
Bayan sun gaisa,,Nasir yayi qoqarin sanar da malam abinda ya faru na rashin zuwan bello birni..
Nisawa malam yayi kafin ya maida hankalinsa ga Nasir yace..
Nasir nifa banaji a jikina yarannan mashkur ze wulaqanta nijlah,,jinake kama ze riqeta Amana kamar yadda muma muka riqeta,,duk da cewar mu dole tane,,sedai ina masa zatan alkairi,,idan kuma yaci Amana shida Allah,,Dan ko bamuyi masa Allah ya isaba nasan zata bishi..
Hakane baba to Dama shiyasa mukaga ya dace muzo mu gayama,,
Godiya sosai malam yayi musu kafin ya tashi ya shiga gida,,shidin ma karya yayima kaka yace bello yadawo lafiya kuma yaga gidan da aka Kai nijlah Dan Shima anyimasa karba ta musammam.
Sosai yakumbo taji dadin labarin malam harta fara sakin ranta daga damuwar datake ciki,,haka ta kwana cikin farin ciki..
*******
Kwana Yasmeen tayi tana fama da kanta ga wani zazzafan zazzabi daya rufeta Banda karkarwa babu abinda take,,ahaka har garin Allah ya waye tana nan nade cikin bargo,,,mama bata iya leqataba sabida haushinta datakeji,,abbane ya fito cikin shirinsa na zuwa office kalllan mama yayi yana cewa..
Hajiya yana ganki ke daya kina karyawa,,ina ita ‘yar lelen take??
Tabe Baki mama tayi tana nuna masa dakinta,,Abba be qara magana ba ya shiga dakin,,nan ya ganta kwance cikin bargo dasauri ya qarasa yana janjan bargon tare da kwalawa mama Kira..
Hajiya hajiya,,Baki da hankali Zaki barmin yarinya cikin wannan hali,,da gudu mama ta qarasa shiga tana cewa alhaji lafiya..
Inafa lafiya duba kiga halinda ‘yar lele take ciki,,wallahi idan wani abu ya Samu yarinyata sainayi maganin wannan yaran me suffar munafukai..
Kayi hakuri ba laifin kowa bane bace laifinta,,shidin mijintane ko Dan ita kadai aka haliccesa dazatasa irin wannan damuwan,,to wallahi bari na gayamiki,,idan ma kashe kanki kikayi shidai baze fasa abinda yayi niyyaba,,shashasha mara wayo,,
Kuka Yasmeen tasa tana karkarwa ta rungume Abba tana nuna mama,,tsawa Abba ya daka mama yana nuna mata hanyar fita..
Fita nace ki fita anan kafin nayi maganinki,,sai yanzu nagane bakya kaunar yasmeen,,ki haifeta da cikinki amma kina nuna mata kiyayya,,kodan ke bakisan zafin kishi ba..
Eh bansani ba,,maganar so kuma sedai ka fadi San ranka Dan ance kaso naka duniya ta qishi,,kaqi naka duniya ta soshi,kuma ni ba qin Yasmeen nake ba..
Kifita nace ko bakiji ba,,fita mama tayi sabida jin ihun na Abba yayi yawa,,mama na fita Abba ya Samu dakyar Yasmeen ta tashi zaune,, nan ya dauka waya ya Kira kanwarsa,,
Hello mami,,daga daya bangaren mami tace na’am Yaya,,barka da safiya..
Abba be iya amsa gaisuwa taba kawai yace idan mubeena na gida ki turomin ita yanzu,,to mami tace tana mamakin yanayin dataji muryan Dan uwan nata..
Daga mummy har aunty lateefah babu Wanda ya iya baccin kirki sai kusan asuba bacci barawo ya dauke mummy,,nan aunty lateefah ta zuba mummy ido tana zancen zuci,,tinanin ta inda zasu bullowa lamarin mashkur take taji mummy ta tashi tana cewa ke lateefah yarannan ya dawo..
Mummy wanne yaro?
Mashkur Mana,,girgiza Kai Yasmeen tayi tana cewa ah ah be dawo ba,,mummy ta Yaya ze dawo yana tare da wancan yarinyar..
Nidai da Zaki yadda da shawarana,,Allah gwara su dawo ta zauna anan gidan kafin muyi maganinta ta fita da qafanta..
Mummy batayi magana ba tace,,bani wayana,,wayan lateefah ta miqa mummy tana kallan abinda zatayi..
Number mashkur mummy ta Kira tana jinjiga qafa..
Mashkur na bacci wayar tafara ringing,,dasauri nijlah ta bude ido tasa hannu ta dauka wayan,,garin tabe tabe ta amsa Kiran..
Nijlah bata San ta daukaba sai jin maganar mummy tayi tana cewa Kai dan ubanka… Mummy bata qarasa magana ba taji nijlah nacewa Wai waye to bacci me wayan yake….
Comment & share
Share this
[ad_2]