NOVELSUncategorized
RAINA KAMA (BOOK 2) 24&25

~Book 2~ ????????2⃣4⃣
………….Kallonsa Nuren yayi da y’ar dariya, “angon jego ai dole kake sauke numfashi, irin wannan aiki dakayi haka? Y’ay’a uku fa a lokaci d’aya, a fuska dai kamar bazaka iya komaib…..”
Nuren bai samu k’arasawa ba saboda filon kujera d’aya daki bakinsa, wanda Galadima ya jefa masa.
Dafe baki Nuren yayi yana kallonsa cikin 6ata fuska.
Galadima ya cije lips yana fad’in “cigaba mana parrot ”.
Nuren ya cire hannun yana kwafa da jinjina kai, alamar zan kamaka ne.
Galadima ya ta6e baki yana hararsa, “yaro aini yanzu na daina halin yara, sai dai kayi da wani kuma”.
Dariya Nuren ya kwashe da shi, “o manya o manya, ai yakamata ma mai martaba yay murabus yabaka kujera kawai, kainefa Wanda kafara kafa tarihi a masarautar nan, Sarki Salisu barde shi yak’in filin daga yaje ya samo sunan gagara badau, kaikuwa yak’in kashe arna kaje kasamo sarakunan gagara badau”.
Girgiza kai kawai Galadima yayi yana fad’in “kai dai d’an iskane wlhy, yakamata papi sumaka aure kodan y’ay’an mutane su samu lafiya ma”.
“ni wlhy dama zakaje kace amin auren daka taimakeni”. Nuren ya fad’a cikin ta6e baki da d’aga kafad’a.
Murmushi Galadima yayi yana gyara zama, “ALLAH ya shiryeka to, mike tafiya akan al’amura?”.
Zama Nuren ya gyara yana komawa serious, “wlhy d’an uwa abubuwannan sun cika tsauri da yawa, a duka mutanen nan uku da yarinyarnan ta fad’a da gaske fa babu SD, amma ga pictures d’in wajen mutum 30 ka nunama Mumcyn Triple’s ko zata ganeshi a cikinsu. dukansu yaransu tanderu ne, Sannan nifa inaga lokaci yayi da zaka binciki Muftahu face to face, dan lamarinsa yafara birkitan tunani gaskiya”.
“kafad’i gaskiya Nuren, nima kuma ina tunanin hakan shine mafita, dan ni kaina lamarin nasa yafara kaini ga dogon nazari”.
“To ALLAH yasa muji alkairi”.
“amin dai”. Galadima yafad’a yana mik’ewa, “nifa na shige zan kwanta, ka kwana lafiya”.
“ok ALLAH ya tashemu lafiya gwauro”.
Galadima yay dariya, batareda ya juyoba yace, “duk lalacewar goma dai tafi biyar albarka tuzuru”.
Nuren ya kwashe da dariya, yana fad’in, “oho dai, muma mun kusa zama gomar”.
★★★★★★★★★★★★
Zumid’i ya hana Momma komai, ta k’agara Abie yafarka yasha kanu, hakama su Samha su dawo school suji babban labari.
Ana cikin haka saiga Sauban tamkar an jehoshi, babu kunya ya rungume Momma yana fad’in “wayyo dad’i Momma y’ay’a uku fa wlhy, kuma dai-dai da ranar haihuwar Yaa Sam, dan yau birthday d’insa wlhy, ciwon aunty gimbiya ya mantar dashi”.
Itama rungumeshi tayi cikeda farin ciki, “hakane wlhy my love, yau ina cikin farinci mai tarin yawa, tarihi ya maimaita kansa da wani sabon salo mai banmamaki”.
“Wlhy nima haka Momma, kallafa pictures d’in babies d’inmu”.
Dukda tagani itama bata katse masa hanzariba ta kar6a wayarsa tana kuma kallo, harda na Munubiya.
Momma tace, “kai yau innarsu yazataji, jikoki 5 a lokaci d’aya, baiwar ALLAH, dama mahak’urci mawadacine, tayi kukan shekaru masu yawa ga lokacin dariya kuma yayi”.
“wlhy kuwa momma, nakira Yaa Sam batajeba”.
“Ai yama manta wayoyinsa a nan, kasan sun tafi hankalinsa ba kwance ba, nima da wayar Muftahu mukayi wayar”.
“wayyo Momma dan ALLAH kicema Yaa Sam mutafi gobe, wlhy kamar nayi tsuntsuwa na ganni a 9ja nakeji”.
Dariya Momma tayi, tarasa inda zata saka kanta dan dad’i.
Motsin da Abie ya farane yasakasu maida hankali garesa, idonsa ya bud’e ahankali a kansu. ganinsu tsaye kansa sunata murmushi saiya ma Momma alama da ido wai miya faru?.
Da sauri Sauban ya rungumesa yana fad’in “Albishirinka Abie d’inmu, matar Yaa Sam y’ay’a uku ta haifa”.
Ba k’aramin shock bane ya kama Abie, ya kalli momma alamar da gaske?.
Kanta ta jinjina masa tana murmushi.
Wasu hawayen dad’ine suka gangaro a kumatunsa, fuskarsa d’auke da k’ayataccen murmushi, A hankali yaketa jero Alhmdllh. Yace, “Mafarkina na shekaru da yawa yazama gaskiya Zeenah, tabbas ubangiji shine masanin gaibu, ya ALLAH na gode maka, godiya marar yankewa balle gajiyawa”.
A hankali yake maganar Amma su Momma naji saboda sun matsar da kunuwansu.
Dad’i duk yakuma lullu6esu, Abie yakuma fad’in “Zeenah wannan yarinya ta zama alkairi ga Ahalinmu, ALLAH ya albarkaci rayuwarta da abinda ta Haifa daku ma gaba d’aya”.
Sauban da Momma suka amsa da amin.
Yace a kira masa Galadima.
A time d’in sunta neman Number Mom amma bata wuceba saboda Network, hakama ta Nuren da Muftahu, daga k’arshe dai sun hak’ura ne sai wani lokacin a sake gwadawa.
Yau dai kam har doctor’s d’in Abie sun shaida yana cikin farinciki, dan jikinsa ma ya nuna haka, k’arfin muryarsa ya k’aru, hakama bugun zuciyarsa dawasu yankunan halittun jiki dake bama d’an adam garkuwa, sun tabbatar a kowanne lokaci ALLAH zai iya gwada ikonsa ga wannan bawa, bayan tsawon shekaru daya d’auka a kwance sai an juyashi.
Wannan albishir ya k’ara yalwata farin cikin wannan ahali, saima dasu Samha suka iso, duk sun rikice da ihun murna, yau d’in ta dabance a ransu.
Isowarsu ce ta tunama Galadima da ranar haihuwarsa dai-dai da haihuwar yaransa, kuma dai-dai da haihuwar su Munaya ma????????.
Wannan abin al’ajab da yawa yake, ita kanta munaya sai lokacin ta tuna, wayar Ayusher ta kar6a ta kira Munubiya tana mata tuni da ranar haihuwarsu. dad’i ya kama Munubiya ma, dan itama ta shafa’a, sai murna kan murna ta k’aru????????♀.
**************************
Uban gayya dai Galadima da k’yar barci 6arawo yake sace sa a kowace rana, daya rimtse ido ‘y’ay’an sa kawai yake hangowa, badan kar aga rashin hak’urinsa ba shikam da dasu zai ringa kwana.
O baban zumud’i????????????.
A 6angaren yalla6iya ma hakane takan kasance, da taga laraba tayi barci dash Ayusher da Samha, (dayake itace take kwana dasu) saita tashi ta dinga d’aukarsu d’ai-d’ai tana runguma da musu addu’oi, jitake kamar ta had’iye kayanta ta huta kawai, takan dad’e tana Abu d’aya kafin barci yaci k’arfinta take kwantawa.
Tosu yalla6iya anaso ana kaiwa kasuwa????????.
*************************
Fad’a muku yanda abubuwa suka cigaba da kasance ga y’an barka ai 6ata lokacine ma, dangin Munaya ma sun taka rawar gani, Ayusher ma dai ta dawo nan zata zauna har ayi suna, hakama madam Innaro Galadima da kansa yaje ya kwasota????????, aiko baki har kunne.
Gaskiya fans sannunku da k’ok’ari, irin wannan tururwa haka, lallai kunma Galadima halacci shida yalla6iya, ALLAH ya saka muku da alkairi dai my sweetness????????????????????????????❤????????.
Dole Galadima ya nemi waya da sim card ya lalubo su Abie da Momma d’insa da jakadiya dabasu samu zuwaba, suna shan hira a kullum shida su Abie ta video call, ga jarirai aita jera musu sunata shan kallo abin birgewa, Abie jiyake kamar yay tsuntsuwa ya gansa a 9ja, tsakanin nan yana cike da kewar k’asarsa ta haihuwa, yana fatan yakuma takata ko sau d’ayane kafin yabar duniya.
“Insha ALLAH zaka taka da yawa Abie????”.
Mu tafi ran suna kawai????⛹????♀⛹????♀.
Abubuwa da yawa sun faru a kwanakin bakwai d’innan, sai dai Alhmdllh bamasu tayar da hankali bane, dan jinjirai suna cikin k’oshin lafiya da kariyar ubangiji.
Samha dai konan dacan bata matsawa, duk wani motsinta nakan yaranan, tazama bodyguard d’insu itada Ayusher da hajiya innaro, dan itamafa ta kafa ta tsare????.
Mama Fulani dai ta danne zuciyarta tazo har sashen Galadima taga babies, harma suka samu k’yauta mai tsoka daga gareta.
Ana gobe suna masarautar gagara badaufa tayi dank’am da jama’a, dan bikin suna na ban mamaki Sarki ya shirya, abin ba’a cewa komai. Inno ma dai wannan karon ba’a barta a baya ba, tazo masarautar su sunan tatta6a kunnenta, kuma 6angaren mama Fulani ta sauka????????.
Koba komai zata kafa zata tsare, takuma raka ta jira????????♀???? mana ga Mama Fulani.
Harun da baya k’asar yayi tafiya a fannin aikinsa yau ya diro a Daren suna cikin masarautar, dama tun yana can labari yagama Isar masa Galadima ya samu y’an uku, Muftahu da kansa ya kirashi ya Sanar masa haihuwar, Yakuma tura masa hoton babies????????
*****************
Wajen 8pm Galadima suka dawo daga masallaci sallar isha’i, shikad’ai ya shige falonsa, dan yana son magana da Munaya, gaba d’aya yinin yau tun safe daya Shiga bai samu komawa wajensu ba saboda hidimomi sun masa yawa.
Ayusher ya kira, dan itama Munaya batazo da waya ba, lokacin da su Sauban zasu taho kuma basusan inda ta saka layinta Na Nigeria ba, sai sukaga babu amfanin d’akko wayarma.
d’agawa Ayusher tayi, Galadima yace ta bama Munaya.
Murya k’asa-k’asa tace bata da lafiya.
Tashi yay daga kwanciyar da yayi, yace, “ciwon cikin ne dai?”.
“eh shine wlhy Yaa Galadima ”.
Dukda kunyar shiga mutanen yake dole ya mik’e ya fita, sashen nasu kam Alhmdllh da yawan jama’a babu laifi, ga yawan bayi da suka k’aru saboda inno da tawagarta, dukda ba’anan ta sauka ba.
Tunda ya fito suketa gaisuwa da jama’a, wad’anda ma basu sanshiba yau sun gansa, musamman wasu a y’an uwan Munaya. cirko-cirko ya iskesu tsaye, Munaya Na kwance a gado ta cure waje d’aya da alama tanajin ciwon sosai, Aunty Mimi nata faman jijjiga yaron d’aya dake kuka.
Duk kallonsa sukayi, cikin damuwa yace, “ciwon cikinne?”.
Da eh suka amsa masa, ya taka zuwa gaban gadon ya zauna kusada ita, har zai ta6ata Mom tamasa nuni da a’a ya barta. dakatawa yayi shima ya zuba mata ido cikin tausayawa, gaba d’aya fita hayyacinta take idan cikinnan yana ciwo, kuma saida ta kwana biyu da haihuwa sanann yafara. ya tsira mata idanu ganin yanda take zufa, dukda garin akwai sanyin ruwan da akayi da yammaci.
Yakai tsawon mintuna 30 a zaune kafin ya lafa mata, ahankali tafara gyara kwanciyarta tana mik’ewa sosai, da Galadima suka fara had’a ido, yace, “sannu”.
Kanta ta d’aga masa cikin murmushin k’arfin hali, suma duk sukai mata sannu sauran.
Nanma ta amsa cikin d’aga kai. Maganin da laraba ta tace a Kofi ta mik’o mata, Na gargajiyane, kar6a tayi ta shanye tana yamushe fuska, ta mik’a mata kofin sannan ta zauna sosai.
Tausayinta ya kama Galadima, iyaye mata nashan wahala akan y’ay’a, ALLAH ne kawai zai biyasu.
Ganin ta dawo dai-dai duk sai suka fita suka basu waje, bayan Aunty Mimi ta d’ora masa babyn a cinyarsa.
Sannu ya kuma mata yana gyarama yaron kwanciya, murya a hankali tace, “ya daina ai, amma wlhy ciwon cikinnan yamafi haihuwar zafi”. ‘ta k’are maganar idonta cike da kwalla’.
Tausayi ta kuma bashi, ya matso kusada ita sosai yana ruk’o hannunta, yace, “insha ALLAH Akash zai zo miki da Magani zuwa gobe, zai daina gaba d’aya ”.
Kanta kawai ta d’aga masa amma batace komaiba.
Kukan da macen tayi yasakasu kallonta su duka, nuni yamata ta d’auketa.
Batayi musuba ta d’auketa ta saka a acinya, kamar jira suma sauran suka farka harna hannunsa, kai Munaya ta dafe tana fad’in “ni jikar fharuk ku shikenan da d’aya ya tashi kowa saiya tashi”.
Murmushi yayi, “to basu birgeki ba ma, sunyo gadonku ne keda Munubiya, Ku ba haka kukayiba?”..
“a’a mukam ba irin wannan mukayiba yalla6ai”.
“humm, ai inna ta sanarmin komai yarinya”.
Da mamaki Munaya ta waro masa ido, ya d’aga mata gira yana kashe ido d’aya.
‘Dauke idonta tayi cikeda basarwa.
Shima saiya mik’e tsaye d’auke da yaron d’aya, ya kalli agogon dake a hannunsa sannan ya kalleta “inason ganinki”. daga haka ya sunkuya ya d’auki macen ya juya zai fita.
“wai ina?”. ta fad’a da saurin dan karya fice.
Juyowa yayi ya d’an kalleta, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace, “sashena”. bai jira cewarta ba yay ficewarsa.
Kanta ta dafe tana sauke ajiyar zuciya, shi bama ya ganin gida cike da mutane, fitinar yalla6ai yawane da ita wlhy. batayi yunk’urin binsa ba, saima zaman shayar da Wanda ya bari tayi, harsu Samha suka dawo ganin ya fita.
Shikam yanacan kwance a gado ya d’ora yaran saman cikinsa yana shafa bayansu, yayinda zuciyarsa ta tafi wata nahiyar tunani, ganin lokaci yaja bata zoba ya kalli a gogon hannunsa, shidai bazai kuma kiranta akan tazo ba, idan ta gadama kartazo.
Mom data lura babu sauran yaran ta tambaya, cikin kunya Munaya tace, “suna wajensa”.
Banbancin babba da yaro saurin fahimta, mom ta fahimci d’an nata yana buk’atar ke6ewa da matarsa, shiyyasa ya d’auki abinda dole tabishi inda yake ta kar6o..
Tace, “to aiko jeki ki kar6osu, dan shirin barci zan musu nima Na kwanta, gobe ba zama za’a samuba hidimomi zasuyi yawa”.
Kamar Munaya tai ihu haka taji, to a aiki Ayusher da Samha su kar6osu mana, ai ba dole sai itaba, amma babu yan da ta iya, dan bazata iya sa6a umarnin Mom ba dai.
Dogon hijjab ta d’auka ta zumbula, Mom kamar tayi dariya, a ranta tace, Munaya shi namiji ai ba’a hanashi yanda yaso, balle naku na yanzu da suke a fetsare ma.
Harzata fice mom tace, “shima zoki d’aukesa”.. Ta kalli mom d’in tana fad’in “mom aikuma zasuyi yawa wajen d’akkowa”.
“eh d’auka, basai ya tayaki ku d’akko ba”.
Babu yanda Munaya ta iya dole shima ta dawo ta d’aukeshi, sai wani k’yallo idanu yakeyi Lamar yasan mi akeyi.
Babu kowa a afalon, harma television an kashe, babu yanda ta iya dole ta nufi bedroom d’in, saida tayi sallama yabata izinin shiga sannan ta shiga.
Harta zauna idonsa a kanta itada babyn hannunta, saiyaga ta k’ara masa k’yau ma da girma.
Yace, “kin gama jan ajin? ai saki bari sai randa nazo tad’i ki jamin bawai yanzu ba”.
Munaya ta ciza lips d’inta kawai batare da ta tanka masaba,
Yaran ya kwantar gaba d’aya, sannan yatashi zaune yana fad’in “taso”.
“intaso kuma, ba magana kace zamuyi ba? please ka fad’a a haka”. ta fad’a kamar zatayi kuka, (Dan hirar innaro da laraba ta tuna da sukace jiya wata yarinya sati biyu da haihuwa ta yarda da mijin saiga ciki ya fito yaro Na wata uku, ciki wata biyu da sati biyu????, itama fa yanzu kaffa-kaffa zatakeyi da Galadima, inma baka badaba sai’a saka maka k’arfi????????).
Tsaf Galadima ya fahimceta, dan haka yay wani miskilin murmushi yana fad’in “oh kina min bak’in cikin sake ajiye abin cikin kwan ne?”.
Sosai Munaya ta waro idanu, a firgice tace, “ban ganeba?”.
“Zaki gane lokacin da kika zo hannuna”.
Ta yunk’ura da sauri ta mik’e, ita tama manta da yaro ajikinta, ALLAH dai ya kiyaye tai saurin tarboshi, Galadima ma dirgowa yay daga gadon, saidai kawai ta gansa kusada ita.
Rungume yaron tayi tana sauke ajiyar zuciya, gashi mai kamar mara lafiyarne.
Shima Galadima had’ata yay itada yaron ya rungume, ganin haka saita mik’a masa shi ita ta janye jikinta. hannunta ya rik’o ya maidota, daga k’arshema janta yay zuwa gado, ya zaunar da ita shima ya zauna, fuskarsa babu walwala yace “Munaya badai haka kikemin ganganci da yaraba?”.
A tsorace ta girgiza masa kai idonta Na cika da kwalla, “wlhy yalla6ai a’a, yanzu ma Na shafa’ane”.
Taune lips d’insa yay tayi yana kallonta, haushima ya hanashi samo amsar bata, jima yake kamar ya maketa, anya zaibar yarinyarnan zuwa wani wankan banza can, taje tamasa wasarere da yara?.
Yanda ya koma duk saitaji babu dad’i, shi yaronma bafa kuka yakeba, yad’an dai firgita ne kawai yay kamar zai shid’e.
Saida ya gama cikarsa da batsewa sannan yay kwafa, ita shima abin yabata mamaki, shikenan yanzu y’ay’ansa kawai ya Sani, mutum bazai ta6a iya kuskure ba a Kansu saiya hauma mutane bala’i, shin ya fita sonsune itada tasha wahalar d’aukar ciki da haihuwa?.
Kwantar da yaron yay yanata wani had’e fuska, itama tasha kunu ta shareshi.
K’aton akwatin dake gefensu ya matso dashi, kayane Na jinjirai masu k’yau da birgewa, Wanda kallo d’aya zaka musu Kasan Na musamman ne, kala-kala ne amma kowanne set uku ne, abinda ya banbanta su wannan Na macene wannan Na mazanne. kowanne da takalma abindai masha ALLAH.
tsaf Munaya ta gama gani, ta kallesa tana fad’in “Sunyi k’yau”.
Yana basarwan nan tasa yace, “wanda zakuyi amfani dashi gobe ne, idan akwai abinda bai yiba saiki fad’a da safe a nemoshi, ga naki nan kema”. ‘yay maganar yana nuna mata d’ayan akwatin’.
Jawowa tayi ta bud’e, duk an d’inka kayan, kayane masu tsadar gaske Na mace y’ar gata, bama tasan ta rungumeshi ba Dan dad’i, sai jero masa godiya da addu’oin fatan alkairi takeyi.
Shima tuni ya manta da fushin ya rungume kayarsa yana murmushi. cikin kunnenta yace, “kinfi k’arfin komai a wajena friend dan kin gamawa Muhammad Sameer komai”.
Munaya ta murmusa tana d’an dukan k’irjinsa, tace, “kana shamin k’amshin ne nagama maka komai?”.
Hannunta ya rik’e yana murmushi, yamatso da fuskarsa gab da tata, murya k’asa-k’asa yace, “ke d’ince Zuma ce…… ”
Harar data dalla masa ta sakashi fasa k’arasawa ya wani basar yana kashe mata ido d’aya, “dad’ina dake akwai mazurai, gaki babu k’arfi ga tsoron tsiya”.
Munaya tayi dariya, “aka gaya maka banida k’arfi? kabari nakuma samun lafiya sai a gwada kwanji”.
Wata dariyar mugunta Galadima yayi yace really?”.
“yes” ta fad’a cikeda karsashinta.
Ya mik’a mata d’an yatsansa alamar su k’ula.
Babu musu tabada nata itama suka k’ula. Murmushi yaytayi saboda muguntar dayasan yana shiryawa, wadda ita Munaya bata fahimci komaiba a ciki saboda wauta.????
*_Washe gari_*
Ta kasance safiyar suna, inda aka rad’a sunan yara bayan sallar Asubahi, *_Abdurrahman, Abdurraheem, and Amaturrahman_* masha ALLAH Babies ALLAH ya raya Ku akan sunnah da tafarkin addinin Islam.
Yara sunsha Addu’oin fatan alkairi sosai, tun kuma a safiyar shagalin suna ya fara, dan kowa yana cikin walwala da farinciki, mai jego munaya ansha k’yau itada babies har an gaji, kamar ka sacesu ka gudu, hotuna dai suna shansu kala-kala a yau d’inan, Su Momma ma da basa kusa anata sambad’a musu, dan duk wani motsin da za’ayi Sauban da Samha basa gajiya da tura musu, sai sukaji tamkarma suna nan suma, saboda kallon komai suke tamkar live, farin ciki da walwala sun yalwatu a zuciyar Abie, bakinsa yakasa rufuwa dan tsabar nishad’i daya tsinci Kansa yau aciki.
Hummm babbar magana, kayan barka dai sun iso, fans yaufa nasha kallo, kaga Inda akeyi don ALLAH, ta bakin Munaya tace INA zasu da wad’annan kaya haka, lamarin tamkar fariyya, gashi kowanne sashe sai kawo nasu sukeyi, gidan sarauta manya, babu Wanda zaiso aga kasawarsa, ballema wannan kana k’inyi za’a CE bak’inciki kakeyi, shiyasa mama Fulani aka ware aka zuba kayan barka Na gani Na fad’a, daga gidansu Munaya ma su inna sun taka rawar gani dai-dai k’arfinsu, daga ita har Munubiya komai iri d’aya aka musu, kayan babies ne kawai Na munaya yafi Na munu saboda su su uku ne ita kuma Nata biyu.
Nanfa y’an gidan suka Shiga k’us-k’us d’in gulmar Ina inna ta samu kud’in yin wannan hidima haka? dansu basuyi zaton hakanba, musamman da abin yazo da yawa ma, itadai inna ma ko kallo basu isheta ba, hidimar gabanta da farincikin datake cikine a gabanta, bakinta yakasa rufuwa saboda farinciki da godiyar ALLAH mai sassauya al’amura a yanda yaso a kuma lokacin da yaso, idan ALLAH ya jarabceka karkayi bak’in ciki, hak’urinka zai iya zama sauyin alkairi a gareka, inama iyayensu Nada rai suga wannan k’yak’yk’yawar rana, ta share hawayenta tana murmushin farin ciki, sannan ta kira y’ar uwarta a waya suka cigaba da tattaunawa.
*****
K’arfe uku da rabi kuma za’a gudanar da gagarumar walima da aka kama babban hall Na musamman.
A wannan rana yara dai har fada aka kaisu sukayo gaisuwa da hotuna da mai martaba da gayyar y’an uwa da abokan arzik’i, su Harun dai sune gaba-gaba, uban gayya kuwa Muhammad Sameer Saifudden Galadima Baban y’an uku???? ai ba’a cewa komai, koma ganinsa ba’ayi saboda tsabar shiga hidima, wannan suna ko bikidai iyaka kenan.
Nasan kuma fans duk kunyi shirin wannan walimar baje dad’i????????. Nifa buhu Na tanada walle????, saura kuce Bily tacika zari da son banza kuma????, har y’an anguwarmu saina kar6oma gifts d’insu????????????????♀.
****************
Alhmdllh yaran Mununbiya ma an rad’a musu suna bayan sallar Asubahi, Namijin *_Aminudeen macen Ameenatu_* ALLAH ya raya wad’annan yara masu albarka????????????.
Yau daikam farin cikin da Abba da innarsu suke ciki 6ata lokacine ma, kai da dukkan masoyansu irinmu, masu bak’inciki kam Ku k’ara himma, hassada ga mai rabo takice????????????♀.
Kowa nabashi dama ya k’iyastama zuciyarsa yanda bidirin suna yake guna, dan Alk’alamin Bily yau yayi k’ank’anta wajen wallafowa, sai mugama Na wannan satin bikin sunan bai k’areba????……………..✍????
Kuyi manage da wannan yau inada uzuri????????♀.
☺my Guy’s a kafta kawai danjin yanda bikin suna zai gudana gobe idan ALLAH ya kaimu, kowa dai ya k’ure adaka dan karfa a kawo mana raini????, kunsan dai halin mama Fulani, tana iya hanawa abarmu shiga????????.
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????
*_typing????_*
???? *_HASKE WRITERS ASSO….._*
*_♦RAINA KAMA…..!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
~Book 2~ ????????2⃣5⃣
…………….Aunty Salamah da kanta tazo yima Munaya kwalliyar zuwa wajen walima, saida tafara biyawa tama Munubiya sannan ta wuto nan, ta iske su duk a damuwar kukan da Abdurrahman ketayi, sai faman jijjigarsa akeyi amma yaro yak’i yin shiru, an basa nono yak’i kar6a, innro ta kar6esa ta hura masa kunne, ya kuma k’yak’yacewa da sabon kuka yana dunk’ulewa waje d’aya, tace “inaga kunnensa ke ciwo yaronnan”.
Munaya Na gefe zaune ta zuba tagumi kawai tana kallonsu, ita kad’ai tasan suyar da ranta ke mata, gashi Galadima baisan wainar da ake toyawa ba, yanacan tareda su Akash da suka iso yanzu.
Innaro ta dungureta, d’ago idanu tayi ta kalleta, ta mik’a mata Abdurrahman daketa sauke ajiyar zuciya, “d’iga masa ruwan nono kad’an acikin kunnen insha ALLAH idan aka dace zai daina”.
Kar6arsa tayi, ta d’ora kan cinyarta, dukma ta rikice ta rasa yanda zatayi, saboda sai mimmik’ewa yakeyi azaba na cinsa, ga Amaturrahman itada Abdurraheem suma sun d’akko nasu kukan, laraba ta rik’e matashi ta samu ta d’iga masa, ruwan nonon Na shiga yakuma mimmik’ewa yana kwalla ihun sabon kuka.
Saiga hawaye a na zuba a idon Munaya, tasaka hannu ta toshe kunen ta kozataji sassaucin jin kukan nasu dake d’aga hankalinta.
Tausayinta saiya kama laraba, tasan indai wannan ne yanzu ma aka fara, yaro d’aya ma ya kake k’arewa balle yara uku.
Cikin amincin ubangiji kuma duk sai sukayi shiru, innaro da laraba sunata faman jijjiga, itama Aunty salamah ta kar6i Na hannun munaya, tun suna ajiyar zuciya har barci ya kwashesu. Munaya ta shige bayi tana share ragowar hawayenta.
Baki innaro ta ta6e tana fad’in “lallai aiki yasamu mata, yo indai kukane yanzu ma kika fara”.
Daga Aunty salamah har laraba dai babu Wanda ya tanka.
Munaya kuwa data jiyota daga bayi tace “aniyarki ta biki, mai mugun fata kawai”.
Wanka tayo ta fito, Aunty salama kawai ta tarar a d’akin sai bayi biyu dake morping, suka durk’ushe k’asa suna gaida Munaya.
Hannu ta d’aga musu kawai dan batasonyin magana, har yanzu raunin tausayin Abdurrahman baibarta ba. ta kallesu duk suna kwance kan gado barci ya d’aukesu, yayinda Aunty Salamah ke zaune kan sofa tana warema yaran kayan da za’a saka musu.
Ta d’ago ido tana kallon Munaya, “haba auta kuka kikayi da gaske? Please kidaina musu kuka, ba’ason uwa Na zubarma d’a hawaye dukda wannan Na tausayine kinji”.
Munaya ta had’iye abinda yamata tsaye a mak’oshi tana gyad’ama Aunty salamah kai.
Saida Aunty salamah ta gama ware kayane sannan ta taso suka fara kwalliyar, anutse sukeyin komai, dan da sauran time, hakama Munubiya a nutse aka mata tata, anama Munaya tana kallon hotunan Munubiya, taji dad’in yanda y’ar uwarta tasha k’yau, dukda ma batakai ga saka kayaba.
★★★★★★★★★★★
Muftahu nata kai kawo a tsakar d’akinsa, tunanin tawace hanya zai fargar da Galadima kawai yakeyi, dan dolene saida hannunsa zaiyi wannan aikin, saboda had’arinsa, gudun kar reshe ya juye da mujiya, sannan aikin yana buk’atar takune da sirri.
Fitowa yay yanufi can cikin k’aton lambun masarautar indasu Galadima suke tareda mafi yawan y’ammata da samarin masarautar.
Wasu sunata hirarsu in group, wasuko hirar tasu ta masoya ce, Muftahu ya k’araso inda su Galadima suke, sun baza babbar darduma anata hira, Bama zaka ta6a Sanin suna lambun ba saboda sunacan ciki nesa da sauran yaran.
Galadima na zaune a gefe cikin kujera, ya d’ora k’afafunsa a wata kujerar, sanye yake da farar shadda d’inkin boda, fuskarnan babu walwala ko kad’an, gaba d’ayan hankalinsa yanaga system d’in daya d’ora bisa cinya yana latsawa.
Muftahu ya mimmik’a musu hannu sukayi musaba cikin fara’a. Amma tsakaninsa da Harun ba hakan baneba, kowa murmushi mai cikeda ma’anoni yay ma d’an uwansa, kafin su saki hannun juna. Muftahu ya matso kusada galadima shima ya bashi hannu sukayi musabaha, k’aramar takardar dake mak’ale a hannunsa ya sakarma galadima a hannu.
Kallonsa galadima yayi, sai yay masa murmushi yana signal da ido alamar ya duba.
Galadima bai ce komaiba ya cigaba da abinda yake ya basar da takardar. Muftahu kuma ya koma cikin su Harun aka d’ora hira, tamkar babu abinda ke damunsa.
Galadima baibi takan takardar da Muftahu ya basaba har tsawon wasu adadin mintuna, sannan ya bud’e ya duba.
_Ranka ya dad’e ina buk’atar muyi magana kafin a zauna wajen walima, magana mai muhimmanci please._
Iya abinda ke jikin takardar kenan.
Galadima ya d’an ja eyeglasses d’insa k’asan ido ya kalli Muftahu, cije lips nashi yayi yana janye idonsa.
Ya sauke k’afafunsa yana d’ora laptop d’in saman kujerar, ya d’auki ruwan gabansa yana sha da maida hankali garesu. jin hirar tasu ta y’ammata ce sai ya zuba musu ido kawai bai saka bakiba, dan shi dama ba’a wannan hirar dashi tun can da, suma duk sunsan haka, shiyyasa ko suna shirmensu basa sakoshi.
Ganin zasu saka masa cinwon kai saboda hayaniyarsu Na Neman yin yawa saiya mik’e d’auke da Laptop d’insa.
Duk kallonsa sukayi, Zayyan yace, “ina zuwa daddyn Triple’s?”.
K’aramin tsaki yaja, da k’yar ya bud’e baki yace, “zaku samin ciwon kaine, zanje nad’an huta kafin time yayi”. ya k’are maganar da kallon agogon hannunsa.
Matawalle yay murmushi yana salute nashi, shima murmushin ya masa yana kaimasa rankwashi, ya kauce gefe yana murmushi, (dayake shima bai cika hayaniya ba).
Wuce warsa yay cikin takun nan nasa Na izza da k’asaita, da sauri wasu yaran masarautar dasuka had’a tasu dabar agefe biyu aciki suka taso suka k’ar6i laptop d’in hannunsa saboda girmamawa, ya mik’a musu yana murmushi, yana gaba suna binsa a baya, sai zuba masa surutu suke akan shagalin daza’a sha yau, shidai murmushi kawai yake musu babu magana, basu damuba, dan kowa yasan halin galadima a masarautar nan, haihuwar nan ma wasu da yawa zasu iya cewa sunga hak’oransa a waje. duk inda suka gitta ana kwasar gaisuwa, bayi kam zubewa suke domin girmamawa a garesa.
Har sashensa suka masa rakkiya, sarkin mota ya kar6a laptop d’in ya k’arasa masa da ita zuwa ciki..
Baibi ta ainahin k’ofar da zata kaishi babban falonsu ba, saiyabi wata k’aramar k’ofa da kai tsaye nasa sashen zai shige basai mata y’an suna sun gansa ba.
A falo ya iske Sauban kwance yana barci, da alama yagama yawonsa ne gajiya ta makesa, da kallo Galadima ya bisa, amma dan ya tabbatar da lafiyarsa saiya d’ora yatsunsa biyu a wuyan Sauban d’in, babu zafi, ya maida goshinsa saiyaji zafi sosai, Galadima ya girgiza kai, yasan dama ba lafiyace zata saka Sauban barci a irin wannan lokacin ba ana wannan hidimar.
Bai tasheshi ba ya shige cikin bedroom, zama yay a bakin gadon yana cire bottom d’in rigar guda uku, ya huro isaka daga bakinsa yana zamewa ya kwanta batareda ya cire rigarba, zuciyarsa tana ta jujjuya mi Muftahu yake nufi ne? wace magana zasu tattauna?. waya ya jawo da nufin kiransa, sai kuma ya fasa, jefar da wayar yayi yamik’e yana ida cire kayan gaba d’aya. ya shige wanka.
ya ja adadin wasu mintuna masu tsayi kafin ya fito sanye da bathrobe fara sol, sai k’aramin towel a hannunsa yana goge fuskarsa zuwa wuyansa.
Yana tsaye gaban mirror zai fara shafa mai ya jiyo ana knocking d’in k’ofar falonsa, Computer d’in daya ajiye wadda yake kallon kowane 6angare na sashen daga cctvs cameras d’in daya zagaye ko ina, tun zuwan dayayi Na k’arshe ya saka akayi masa wannan aikin, sannan ya d’auki mataki akan waccan cctv d’in da Munaya tamasa hannunka mai sanda da ita.
Sarkin k’ofa ya gani, sai kuma Muftahu daga can waje alamar yana jiran iso ne.
Guntun tsaki Galadima yayi, ya fito zuwa falo, Sauban dake barci ko motsi baiyiba balle yasan ana knocking d’in. yana daga tsaye yabama sarkin k’ofa izinin shigowa.
Cikin girmamawa yace, “ranka yadad’e yalla6ai Muftahu ne ke Neman iso”.
Da hannu Galadima ya masa nuni da ya shigo.
Sarkin k’ofa ya amsa da to sannan ya fice.
Komawa Galadima yay ciki yacigaba da shafa mansa, saida ya gama tsaf sannan ya zira jallabiya Brown ya fito.
A falo ya iske Muftahu zaune yana control d’in television da remote.
Galadima ya zauna a kujera mai zaman mutum d’aya, sai wani d’aure fuska yake.
Muftahu bai wani damuba, dan yariga ya saba da wannan ai.
Kallonsa Galadima yayi cikin lumshe ido yana fad’in “Mike faruwane?”.
Ajiye remote d’in Muftahu yayi, ya kalli Sauban dake barci.
d’an ta6e baki Galadima yayi, yace, “karka damu, kayi maganarka kai tsaye kawai”.
Cikin jinjina kai Muftahu yace, “Ok, babu abinda ke faruwa saidai shirin faruwar kam, Ranka ya dad’e bamuda isashen lokacin wata magana mai tsawo yanzu, saidai ga wannan takardar ka duba, so yanzu wannan ne akan ga6a, shine yakamata mu d’au mataki akansa, daga baya komi kenan namaka alk’awarin warware makashi, fatana dai ka fahimci wannan d’in saboda had’arinsa”.
Kar6ar takardar Galadima yayi, ya d’auki medical glasses d’insa daya ajiye a teble glass d’in dake gefen haggunsa ya saka, duba takardar yay a tsanake, cikin wani yanayi dake nuna tsantsar tashin hanki yace, “Muftahu wannan maganar gaskiya ce kokuwa? karkamin wasa da hankali a wannan karon dan bazan d’aga maka k’afa ba a wannan ga6ar alwashi nane”.
Murmushi Muftahu yayi, ya sauke ajiyar zuciya yana fad’in “Nabaka wannan damar, inhar kayi gamo da sa6anin hakan karka barni da numfashi ranka ya dad’e”.
Wani shegen Murmushi Galadima yayi, yamik’e d’auke da takardar ya koma bedroom batare da kuma kallon Muftahu ba.
Tausayin Galadima ya kama Muftahu, mik’ewa yay shima ya fice.
Jefar da takardar Galadima yayi akan gado yana taune lips nashi tamkar zai huhhudashi, wata irin suya zuciyarsa ke masa, lallai dolene ya jinjinama Munaya, dan ta taka rawa wajen shagaltar dashi wanene shi? minene burinsa?, ganin tunani bazai masaba yatashi jikinsa Na rawa yafara wasu had’e-had’en abubuwa, waya ya d’auka ya kira Ayusher, ta d’aga cikin hanzari tana mik’ama Munaya dake shayar da Amaturrahman data tashi daga barci tana kuka.
Kallonta tayi da mamaki tace, “wace Ayusher?…….”.
Galadima ya katseta da fad’in “ki kawomin kayanda su Abdurraheem zasu saka”. iyakar maganar da yay kenan ya yanke wayar yana cigaba da latse-latse, zuwa can kuma ya ajiye ya mik’e yana cire jallabiyar jikinsa.
Baki sake Munaya tabi wayar da kallo, mike damun galadima haka? Muryarshi irin wadda tasan asalin galadima ce, hakan na nufin akwai matsala kenan? to mine zaiyi da kayan da yara zasu saka?. batada mai bata wad’an nan amsoshin dan haka ta mike tana ajiye Amaturrahman d’in, aiko ta fashe da kuka an cireta bata k’oshiba, tsaki Munaya tayi tana fad’in “ai saikiyi tayi, ku matsala ubanku matsala mutum yarasa wazai kama.
Ayusher da Aunty Salamah suka kalli juna suna gumtse dariya.
Gyale taja ta lullu6a, dama tasaka doguwar rigar matirial kafin dai time ya k’arasa. ganin zata wuce yarinya na kuka Auntu Salamah tace, “dawo ki d’auketa mana, idan kinje can saiki bata nonon”.
Tamkar Munaya zata saka kuka haka ta dawo ta kwashi Amaturrahman ta fice tana k’unk’uni.
A falo ta iske Sauban Na barci, wucewa tayi cikin bedroom d’in kanta tsaye, amma saida tayi sallama ya bata izinin shiga.
Tun da ta shigo taga yanayin da yake sai gabanta ya dad’i, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki ta mik’a masa ledar data zubo kayan sannan ta zauna a kunyace saboda yanayin da yake babu kaya.
Ba tare da ya kalleta ba ya hau Fiddo kayan, ya zubesu saman gado yana d’aukar hotonsu a waya, yay latse-latse nawasu mintuna kafin yasaka wayar a kunne.
“Saleem ka dubamin kalar kayannan, koda basu kaisu tsadaba, yanzunan kataho ka kawominsu”.
Bataji mi Saleem yafad’a daga canba.
Muryarta a raunane tace, “yalla6ai mike faruwa wai?”.
Jajayen idanunsa ya d’ago ya kalleta, k’ala baice mataba ya mik’e ya d’akko wani k’aramin box ya dawo ya zauna, ita duk saima kunya takuma kamata, saboda dagashi sai boxer, amma taga ko a kwalar rigarsa bai damuba, hidimar gabansa kawai yakeyi.
Kwantar da Amaturrahman tayi kusa dashi ta tashi zuwa wardrobe d’insa, k’aramar t-shirt ta d’akko, tazo ta mik’a masa.
Ya d’ago ido yana zuba mata harara, dukda ta tsorata saita daure tace, “please mana yalla6ai”. tayi maganar muryarta a raunane.
Saida yayi k’aramin tsaki kafin ya amsa ya saka, wani abu da batasan minene ba taga yana mak’alawa jikin kayan yaran, saida yagama tsaf sannan ya maidasu a ledar, kallon Amaturrahman dake k’yalla y’an idanu zata fara k’aramin kuka yayi, ya shafa kumatunta batare da ya d’auketa ba.
Laptop d’in sa ya jawo ya saka eye glasses d’insa, ya kalli Munaya yamata alama da ido akan tazo.
Babu musu ta taso zuwa kusa dashi ta zauna.
Laptop d’in ya d’ora mata akan cinya yace, “wanene SD a cikin su?”.
Nutsuwa Munaya tayi tana kallon hotunan, cikin waro ido tace, “kai ga Fu’ad ai”.
Da mamaki Galadima yace, “Fu’ad!?”.
“eh wlhy yalla6ai, Wanda ya kaimu birnin gayu plaza ranar da abunnan ya faru”.
Kar6a laptop d’in Galadima yayi yakuma kallon hoton da k’yau yana taunar lips, kuma mik’a mata yayi batare da yace komaiba. itama batace dashiba tacigaba da bin hotunan da kallo sannu a hankali. Harta kai k’arshensu babu SD. ta kalleshi cikin damuwa, “yalla6ai babushi fa anan gaskiya”.
Kansa ya jinjina mata yana kar6ar laptop d’in, cigaba yay da danne danne, itadai Munaya tana kallonsa.
Kuma d’agowa yay ya kalli Munaya, “duba annan kuma fa”.
Kallon hotunan ta shigayi, canko saiga hoton SD, tace, “Alhmdllh gashi anan”.
Kallon hoton Galadima yayi, da mamaki yace, “kinsan wanene wannan kuwa?”.
“Ah! yalla6ai SD ne mana”.
“Munaya kin tabbata wannan ne kika gani a wajen Abba?”.
“Wlhy shine yalla6ai, bazan ta6a manta fuskarsa ba ai komai dad’ewa. balle acikin abinda bai rufa 2years ba, amma kasanshi ne?”.
Bai iya cemata komaiba, sai zuciyarsa dake wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata fad’o, mamaki ya hanashi motsin kirkirma, Alhaji Shehu Darma shine SD kenan, babban Amini kuma d’an uwa ga Mahaifin su Samha, innalillahi, ya abubuwa keneman koma masa rikid’ar hawainiya haka?, wannan fa Fu’ad d’in d’ane ga yayar Uwargidan Sarki mahaifiyarsu Matawalle, cikin cije lips ya buga hannunsa akan gadon yana fad’in “Kai!!!! miyasa hakane? miyasa duk Wanda Na yarda dashi shike fara bayyana a maicin dunduniyata?!! miyasa rayuwa tazomin da irin wannan rikicin ne?, oh God!!”. ‘ya k’are maganar cikin matsanancin k’araji, tareda runtse hannayensa waje d’aya.
Tsoro ya kama Munaya, ganin yanda duk ya rikice kamanninsa suka canja, idonsa yayi matuk’a jajur, jijiyoyinsa da gashin jikinsa duk sun mimmmik’e, ga Amaturrahman data tsorata lokacin daya buga gadon, d’aukarta tayi tahau jijjigawa.
Sauban ma a firgice ya tashi, ya hau waige-waige, ganin babu kowa a falon saiya nufo hanyar bedroom d’in Galadima, tabbas muryarsa yaji a yanayin da ba’aso. harzai murd’a k’ofar saiya fasa saboda jin kamar muryar Munaya tana magana.
Tunda tasamu Amaturrahman tayi shiru sai ta d’auki towel d’insa ta goyata, ta matsa kusadashi a tsorace, hannunta ta d’ora akan nasa daya dafe mirror, ko motsi baiyiba balle ya kalleta.
Murya a d’arare kuma a sanyaye tace, “please yalla6ai, fushi baisa a samu sauk’i saidai ya k’ara zafi, kaine kasha gayamin wani karatun baya buk’atar fassara ko dogon nazari, akan barsane kawai a yanda yazo, dukda bansan tushen matsalarba zan iya bada gudunmawa wajen kama bakin zarenta, kayi hak’uri ka kwantar da hankalinka, ita fahimta fuskace, ba fushinka ko tsantsar damuwa ne abin buk’atarba yanzu, d’ana tarkon dazai fara kamo maka hannun mak’iya shine jarumta, ka danne kuma ka daure, ni dama Dan banida ikon hana walimar nanne kawai, amma inaji a jikina akwai lauje cikin nad’i, saidai wad’anda suka nad’a d’inne bamuda ilimin saninsu sai ALLAH yaso Samar damu, amma ai duniya makarantace, idan su a can suka yini kaikuma saika nuna musu kwana kayi, lokuta da dama fushinka ke lalata maka aiki, dan inhar kana cikin fushi dukkan aikinka tafiyar hawainiya yake, wannan lagon naka suka samu suke wasa da hankalinka, koda ace wani ya salwanta cikin yarannan karka d’aga hankalinka, ALLAH n daya baka yafika sanin hikimar k’addara hakan, duk lokacinda kaga Matsaloli sun raunana, buk’atu kan kuma kan yalwata ne, kasa a ranka wannan wata damace tazo gareka, ai duk lokacin da aka rasa kwallo a cikin wasa, ba wasan ake dainawa ba, wata kwallon ake jehowa a cikin fili”.
Duk maganar da takeyi ko motsawa baiyiba, baikuma juyo ya kalleta ba, saidai alamu sun nuna yana saurarenta, ta janye hannunta ta juya zata fita tana hawaye.
Cak ta tsaya saboda rik’o hannunta da yayi, kusan minti 1 suna a haka, ta waigo ta kallesa, har yanzu yana a yanda yake, kallon hannunsa daya ruk’o nata tayi.
Bai kalletan ba kuma bai saki hannunba yace, “Lallai ina shaidama dukkan Wanda ya maida rayuwata data ahalina magijin kallonsa, zan tsiyayar masa da idanun, sannan zan kacaccala rayuwarsa Na binnesa da ransa”. ya mik’e tsaye sosai tareda juyowa ya jawo hannunta ta fad’o jikinsa, saurin dafe Amaturrahman dake bayanta tayi da d’ayan hannun. Ya saka idonsa dasuka firgitata cikin nata, fuskarsa dab da tata yace, “kedai kibama yaranki kariya kawai, dan sune fitilar zuciyar mijinki”.. sakin hannunta yay ya zagayeta yabar wajen.
Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo, yayinda zuciyarta keta kuma maimaita maganar tasa, _yaranta, kuma mijinta?_ mi yake nufi to?, amsar itace bata saniba.
Jitai kawai ya saka mata ledar kayansu Abdurraheem a cikin hannu, baice k’alaba yabar wajen zuwa gaban wardrobe d’insa yafara fiddo had’add’iyar Shadda gizna ash colour, sai maik’o take da d’aukar idonu.
Ganin ya shareta yana cigaba da hidimarsa itama saita juya ta fice.
Tunda Sauban yaji motsin kama handle d’in k’ofar yabar wajen da sauri.
Fitarta babu dad’ewa Saleem ya kawo kayanda Galadima ya umarcesa.
__________________________
Munaya Na komawa Aunty Salamah tahau shiryata, dukda taga a yanayin data dawo bata tambayeta daliliba, saida tagama gyara mata fuska tana gyara mata gashi Munaya tafara fad’a mata iya abinda taga ya dace kawai Aunty Salamahr ta iya Sani, sauran kuma sirrinta ne ita da mijinta.
Murmushi Aunty Salamah tayi, tace, “dukda banida tabbacin faruwar wani Abu dagani har Munubiya dama mun shirya hanyoyin d’aukar matakai saboda tsaro, kowa baisan dalilin Munubiya na dagewa akan ki dawo gida ki haihuba, amma ita tasan dalilinta, ba son zuciya ya sakata yin hakanba, Ubangiji Na kallon kowa kuma zaiyi maganin komai, tun a shekaran jiya Saleem yazo mungama tsara komai dama, kuma ya tabbatar min Muftahu yasan komai dan yaga alamar shima tsaye yake da k’afafunsa, inaga yau dai shine yabama Galadima satar amsa, kuma hakan da yayi shine dai-dai, saboda duk abinda zai faru a yau d’innan shi Galadima zai fara zargi”.
Munaya tace, “hakane Aunty Salamah, shiyyasa wlhy Muftahu yafara bani tausayi, ALLAH ya kawo ranarda zai wankesa ayi walk’iya aga kowa dai”.
Amin ya rabbi gimbiyar Galadima Sameer, ku kwantar da hankalinku, komai kam ya taho gangarar zuwa k’arshe, dan alamomi suna nuna haka”.
“nima inajin haka a jikina Aunty Salamah”.
Da wannan hirar aka gama gyaran kan tahau shiri cikin less d’inta Ash colour irin kamar kayan da Galadima zai saka kenan.
Hummm masha ALLAH, maganar k’yawun da Munaya tayima 6ata lokacine, amma tayi k’yau.
Yaranma tsaf aka gama shiryasu, abin kamar ka sacesu ka gudu, sunyi fes.
Kowa yagama hada-hadar shiri, ana fitowa daga sallar La’asar za’a fara kwasar mutane zuwa hall d’in da aka tanada.
*_4:00pm_*
Dukkan mai ruwa da tsaki akan wannan taro ya hallara a gaban motocin da za’a kwashi jama’a, ana fitowa daga salla kuwa aka fara tafiya.
Munaya dai tana d’aki bata fitoba, hakama Galadima saida ya dawo salla sannan yafara shiri ma shi.
Saida kusan kowa ya tafi sannan iyayen gayya suka fito.
Munaya ce tafara fitowa, kuyangi Uku Na d’auke da yaran a bayanta, yayinda wasu kuma ke take mata baya, a babban falon sashensu suka tsaya jiran fitowar Galadima.
Tunkan ya fito daddad’an k’amshinsa ya fara isowa, saikuma sautin takun takalminsa wanda tarihi yaso maimaita kansa ga munaya, dan takun nasa Na daidaituwa ne da bugun zuciyarta.
Yana gaba Sauban na binsa a baya, Tunda ya fito Kuyangin duk sukai k’asa da Kansu, yayinda ya k’araso sai suka zube k’asa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai ya d’aga musu, idonsa akan Munaya wadda itama ta risinar da idonta tana masa kallon k’asan ido.
Ba k’arya yayi matuk’ar k’yau, komai nasa Ash colour ne, kuma kayan sarauta y’an asali, harda rawanin daya kuma fiddi ainahinsa Na jinin sarauta, rawanin ya sakaya sajensa hancinsa zuwa bakinsa kawai ake iya gani, idanunsa na cikin eyeglasses dabaka isa kaga kwayarsu ba, dan ya toshe su 6am.
Juyawa yay ya kalli Sauban dake gefensa, Sauban ya fiddo Alk’yabbar dake cikin bag d’in hannunsa ya mik’a masa, kar6a galadima yayi yana mik’ama Sauban had’ad’d’iyar sandar hannunsa da zaka iya d’auka ta gold ce, ya warware alkyabbar ya matsa gaban Munaya dake tsaye har yanzu, yayinda kuyanginta ke a dur kushe har yanzu suma.
Matsawa yay jikinta tamkar zai rungumeta, k’amshin turarensa ya cika hancinta ta lumshe idanu, ya sako alk’yabbar ta bayanta, Sauban na gefe yanata zuba murmushi da d’aukarsu hoto.
Tamkar sokuwa haka Munaya ta tsaya har Galadima ya gama saka mata alk’yabbar a jiki, ya juya Sauban yakuma bashi turaren dake cikin jakkar, feshi ya shiga yimata da turaren, zuciyarta sai kaikawo take yi na d’umbin mamaki da al’ajabin wannan salo,
Bayan ya gama ya maidawa Sauban turaren yanama Munaya nuni da suje da hannu.
Haka suka fito a jere Kuyangi na take musu baya, yayinda Sauban yake gefe yanata zuba musu hotuna a Camera.
Motar da Sarki ya bada ita aka bud’e musu suka shiga, Sauban ya kar6i yaran d’ai-d’ai ya mik’a musu, sannan ya shiga gaba kusada sarkin mota da Amaturrahman shima.
Motar ta d’auki shiru tamkar babu wani mahaluki mai numfashi, Galadima ya zubama Abdurahman dake hannunsa ido kawai yana kallo, yayinda ya sak’ala hannunsa d’aya cikin Na Munaya yana murzayatsuna a hankali.
Itama dai tayi shiru sassan jikinta Na kar6ar sak’on ninsa.
A haka suka Isa har cikin harabar hotel d’in, Wanda ya cika dank’am da motoci, duk Wanda yagani yasan yau taron Na manyane, kodan tsaro Na musamman da wajen ya samu tundaga farkon Layin da hotel d’in yake.
Sauban da Sarkin mota suka fito, ba’a bud’e su Munaya ba, kalonta Galadima yayi fuskarnan dai babu walwala har yanzu, batareda yayi maganar ba ya kamo kwalliyar zaren gaban alk’yabbarta ya matso da fuskarta kusa da tashi, ta bud’e baki zatai magana ya d’ora nashi.
Saida ya shanye jambakin lips d’inta tas sannan ya saketa yana zuba mata harara.
Idonta harsun tara kwalla, cikin lumshe idanu da k’asaitacciyar muryarnan tasa mai had’e da izza yace, “Sau d’aya nake gargad’i, karki bari nasake miki na uku akan fita da lipstick a baki”. ya k’are maganar da kad’a mata yatsansa.
Wani yawu Munaya ta had’iye kawai tana jinjina masa kai, wannan ikon ikoko yana bata mamaki, shiyyasa fa tace Aunty salamah ta saka mata janbakin kad’an, gashi yamata k’yau amma tsabar mugunta ya shanye, lips d’insa sai zafi yakeyi, ta harari Abdurraheem dake cinyarta, saikace shine yayi laifin????????.
Bud’e musu akayi suka fita, Samha da Ayusher suka kar6i yaran.
Munaya taji matuk’ar dad’i da ganin ashe harda y’ar uwarta a walimar, itama sunsha k’yau cikin Brown d’in kaya itada yaa Marwan, tana cikin less irinna Munaya, kalarce kawai ta banbanta, shikuma Yaa Marwan harda babar riga, maganar k’yawun dasukaima 6ata lokacine, suma Yaa Fadeel da Feena suna d’auke da yaransu.
Sun shiga cikin hall d’in da tawagar rakkiyar Kuyangi da dogarai, masha ALLAH Munaya tafad’a dan ganin d’unbin jama’a da aka Tara a wannan k’aton hall, manyan mutane da iyalansu sun halarci wannan waje, hakama ahalinsu Munaya kwai da kwarkwata sunzo, harda y’an anguwarsu, duk yawan mutanen nan bai hana a saka mata kan tsaro masu tauriba a wajen.
Kowa saida su Galadima suka birgesa, abin akwai tsantsar birgewa da sha’a a cikinsa,
A cikin fans harda masu k’yasa Galadima????????.
barama namuku gulma, can Na hango muku tawan Miss xoxo fa idonta kamar zai fad’o, hakama zee bawa da Aysha dansabo da kdeey????, dukda harar da Maman Khady da takwara billy galadanci ke musu sunk’i rusunar da idanu, lamari ya girmama Slimzy harda k’ok’arin mik’ewa fa wai zata iya barin sadeeq d’inta, da sauri saffiya Huguma ta maidata mazaunin tana hararta, Ummi Ai’sha tace, “kai dan ALLAH Ku nutsu kar’ace ‘yan Haske muncika ruwan ido”, Faxy Fation da party zarah da Feedohm sukace ai Galadima d’inne fa yaji gishiri da magi, Hafsat Rano ta toshe baki tana dariya, hajja kam yitai kamar bata wajen, sai loda nama take a baki, Ayusher da khaleesat dake kallonta sukace wai hajja bazaki rage filiba a cikinki?, Mamu gee tace, “kukuma ga sa ido” “kema k’ya fad’a dai” cewar zee yabour, Asmy b Aliyu datun d’an tai shiru itada Ummu Basheer suka yamutsa fuska suna fad’in “please kuja aji mana ‘yan haske, kunafa ganin yanda aka karrama mu fiye da kowa, karku jafa a maidamu kujerar baya wlhy”. Ni bilyn Abdull da lamarinsu ya girmeni nace, “kubarsu kudai kawai, sosuke susa a hanamu ganin sarakuna, kokuma mama Fulani ta rainamu, kuna dai ganin innaro ma kanta yanda taja aji ta kwamushe a gefe tana mazurai.
Miss xoxo dake gefena tayi k’asa da murya tana dai-daita kanta, tace, “gaskiya kika fad’a tawan, nidai kinsan dama dai Galadima ya dad’e a k’ok’on raina, ko sau d’ayane kisan yanda kikayi aka mana hoto tare”. Nace, “karki damu tawan, Salfe ma zakuyi, amma fa ki kula, dan Munaya babu sauk’i”. “gulmar mi kukeyi?” cewar Ayusher tana jeho mana handkerchief d’in hannunta. zamanmu muka gyara nuna wani basarwa????, kunsan fa muma mun fara koya a wajen Galadima????.
Lallai, fans sannunkufa, lallai kunma munubiya da Munaya kara, ko Galadima nasan kun gama birgesa aradu, irin wannan anko da kukasha, ko a UK albarka y’ay’an baba buhari????.
____________________
Isowar Sarki Jalaluddeen da Sarki Abdul-fatah da tawagar wasu amintattun sarakunan abokan Abie ya saka kowa ya mik’e cikin girmamawa, saida suka zauna sannan kowa ya koma ya zauna, an fara bud’e taro da addu’oi ga jarirai da kuma kakansu sannan aka fara gudanar da abinda ya Tara jama’a cikin nutsuwa.
Kusan dai lamari Na manya, mudai Fans d’in raina kama sai zuba salfe muke, karkaje kabada labari ace k’arya ka zula bakajeba????, shiyyasa muka kafa hujja koya kukace my sweet fans????????♀?????.
Masu 6oyayyen shiri a zuciyaa fa sunata k’iyasata yanda abubuwan da suka shirya zasu gudana, saidai kuma idan sunsan wata basusan wataba, dan eyeglasses d’in idon Galadima Google ne????, (wato camera ne) tundaga Inda yake yanayo zooming d’in wad’anda suka k’arshen hall d’in ma, duk Wanda zuciyarsa ta saka masa alamar tambaya akansa yana tantancesu ne d’aya bayan d’aya.
Nidai Galadima ka kula banda fans d’in raina kama????????????.
Anyi nisa da taro harma Anfara zubama cikin maik’o da mask’i, ga mai zak’i da sanyi muna korawa, Galadima ya kalli agogon azurfa dake hannunsa sannan ya d’ago ya kalli Muftahu suka had’a ido, lips ya ciza, Muftahu daya fahimci yaren ya gyad’a masa kai, ya kuma kallon Saleem da Nuren da Aunty mimi Mom and Sauban Samha Ayusher, kowannensu Kansa ya gyad’a alamar fahimta……………..✍????
Turk’ashi, tofa masu karatu, shin mike shirin faruwane haka? Wannan amsa tana page 26 da zaizo ranar Monday insha ALLAH. musha weekend lafiya sisters and brothers.????????????????????????
Barkanku da juma’at????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????