NOVELSUncategorized

YARIMA FUDHAL 31-35

*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
31

*BAYAN SATI ‘DAYA*
Cikin satin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da kawo kud’in auren Aynu da Ya Sayyadi Umar yayi kimanin dubu talatin tare da sanya ranar biki wata guda mai zuwa domin Baban Aynu yace baya son wasu bidi’o’i, shima Ya Sayyadin a nasa b’angarensa abin haka yake, hakan yasa bak’aramin dad’i yaji ba da yaji hukuncin da Babannata ya yanke a kan batun auren.
A cikin wannan lokaci ba zaka iya tantance halin da Aynu ta ke ciki ba farin ciki ko bak’in ciki Allah ne ya baiwa kansa sani sai kuma Aynun kanta.
Yauma kamar kullum tsaye yake jikin bishiyar darbejiyar dake k’ofar gidansu, yana zaman jiran fitowarta mintuna kad’an sai gata ta fito tana sanye da doguwar riga ta atamfa purple mai ratsin pink da adon fari ajiki sai ta sanya hijab pink mai hannu bak’aramin kyau kayan sukayi mata ba duk da cewar ita bak’ace amma hakan bai hana baiyanuwar kyawunta a cikin kayan ba.
Cikin takunta kamar bazata taka k’asa ba ta tako zuwa gareshi fuskarta babu yabo babu fallasa ta tsaya d’annesa dashi kad’an tare da yin sallama.
Ya Sayyadi ya amsa yana fad’in.
“Barka da fitowa”.
“Yauwa barka kana lafiya yasu Umma?”.
“Duk suna lafiya sunce a gaishe dake”.
“Ina amsawa sosai kuwa”.
Tayi maganar tare da yak’e har fararen hak’oranta na baiyana a waje.
“Kinyi kyau sosai Amaryata”.
Aynu tad’an rufe idonta da tafukan hannunta tana fad’in.
“Nagode sosai”.
Ya Sayyadi Umar ya cigaba da fad’in.
“Yanzu hankalina ya kusa kwanciya Aynu kina daf da zama mata a gare ni dama shine babban fatana a kodayaushe, gashi kuma inaji araina Allah ya amsa addu’ata”.
Aynu tad’anyi murmushi kad’an ba tare da ta ce komai ba illa wasa data hauyi da yatsun hannunta tana sauraren kalaman da ke fita daga bakinsa wanda a nata b’angaren bazata iya tan-tance ya matsayin kalaman suke aranta ba.
***
“Wai lafiya kake kuwa Magaji, tun dawowarku ka kwanta anan ka kasa motsi?”.
“Wallahi Hajiya ina fama da fever ne kawai”.
“Ayya sannu !, Allah ya k’ara lafiya”.
“Amin Hajiyata”.
“Wai kuwa ya batun ciwon Jalilah?”.
Yarima Fudhal yad’anyi ajiyar zuciya kafin yace.
“Nidai narasa gane inda matsalarta ta dosa domin duk iya gwaje-gwajenmu bamu gano taka mai-mai abin da yake damunta ba result d’inmu kawai maleria yake bamu”.
Fulani Bingel tayi shiru tana kallon Yarima cike da kulawa, kafin ta bud’e baki ta fara magana.
“Anya kuwa Jalilah ba gamo tayi ba?, sati guda abu yak’i ci yak’i cinyewa, kasan mutanan b’oyannan sune ke rik’ewa mutum baki ko k’afa ko hannu ko su toshewa mutum kunne”.
“Gamo kuwa Hajiya?”.
“E kana mamaki ne?”.
“E to zai iya kasancewa, nima abin da nake tunani kenan, amma Hajiya yakike ganin za’ayi?”.
“Kuje wajen Mallam Kallah may be a samu addu’o’in da za’a dingayi mata ko Allah yasa a dace bakin ya bud’e”.
“Ok hakanma za’ayi bari zuwa gobe da safe idan Allah ya kaimu sai muje ni da Anwar”.
“To Allah ya nuna mana goben lafiya, kaje ka kwanta yanzu ka huta kaji ko”.
“To Hajiya sai da safe?”
Yarima Fudhal ya fad’a yana mai mik’ewa tsaye ya nufi b’angarensa domin lokacin k’arfe goma na dare ne, gidan shiru kowa yayi makwancinsa sai kukan tsuntsaye kawai da ke tashi.
***
Malam Kallah ne zaune bisa buzunsa yana rubuce-rubuce gefe guda kuma almajirai ne rukuni-rukuni suna tak’ara(karatu).
Yarima Fudhal da Anwar sukai parking motarsu dai-dai rumfar suka fito dukansu zuwa inda Mallam Kallah ke zaune, sallama sukayi suna masu cire takalmansu suka shiga cikin runfar tare da rissinawa suka gaishe da shi, Mallam Kallah ya amsa fuskarsa fal murmushi yana mai aje allon da yake rubutu ajiki ya mai da hankalinsa kacokan kansu Yarima, tare da tambayarsu mutanan gida da kowa, Anwar yace.
“Duk suna lafiya Mallam”.
“To masha Allahu, ya Mai Martaba kuma kwana biyu yajini shiru ko?”.
“Yana nan lafiya amma ba shine ya aiko mu ba, munzo ne kan batun Jalilah”.
Cewar Yarima Fudhal kenan yana mai gyara zamansa ya fuskanci Mallam Kallah, Mallam Kallah ya d’anyi shiru kafin ya bud’e baki ya fara magana.
“E nima ina da niyar ziyartar Mai Martaba domin sanar da shi batu a kan ciwonnata amma tun da kunzo Alhamdulillahi”.
“Jalilah zan iya cewa ta taka *SAWON B’ARAWO* ne (littafin Noorieyya), abin da yasa nace haka kuwa jifa aka binne domin wani ya tsallaka sai akayi rashin dace ta tsallaka a daren ita kuma “.
Anwar da Yarima suka dubi juna cike da mamaki, yayin sa Mallam Kallah ya katse mamakin nasu da fad’in.
“Zan baku rubutun AYATUSSHIFA ta d’inga sha tare da shafe jiki insha Allahu da yardar Allah (S.W.A) koma mene zai karye, sannan kai kuma abin da zan fad’a maka”.
Yayi nuni da Yarima.
“Kana da mak’iya da yawa a cikin gidanku da waje yawanci jifan da ake yi kai ake yiwa sai dai kuma da taimakon Allah da taimakon Ayatul-kursiyyun da ka rik’e da kuma al-azkar sune suka zamo makami daga gareka don haka kak’ara dagewa wajen al-azkar da tsayuwar dare, domin abin da mu mutane bama ganewa ayanzu wannan Ayatul-kursiyyun da muke rainawa gata dai aya d’aya ce amma maganin da zatayi maka yafi dubu domin ita babbar kariya ce ga duk wani muminin da yarik’eta yana karanta ta ko yaushe dare da rana, sannan abu na gaba azkar muna shagala da yawa tare da barin damarmu a kodayaushe al-azkar nada matuk’ar kariya da muhimmanci a tare damu, domin idan kayi shi da safe Allah Ubangiji (S.W.A) zai sanya mala’iku suyita gadinga tun daga safiyya har zuwa yammaci, idan kayi shi da yammaci za’a sanya mala’iku suyita gadinga daga yammaci har zuwa asuba kagani mutum na cikin kariyar Ubangiji taya tuggun wani bil’adama zai ci shi?, koma mene mutum ya nufoka da shi sai dai ya koma kansa amma ba dai yazo gareka ba, Allah yasa mu da ce yasa mufi k’arfin zuciyarmu ya karemu daga sharrin mak’iyanmu”.
“Amin “.
Su yarima suka amsa tare yayin da kowa acikin zuciyarsa yake tunani na daban akan batun da Mallam Kallah yayi musu yanzu.
Sun d’an tab’a hira kad’an, wanda dukkan hirar wa’azi ne gami da nasiha Mallam Kallah keta yi musu, basu bar wajensa ba sai da jikinsu yayi la’asar sosai nasiharsa ta shigesu, sukayi masa sallam tare da karb’an rubutun Jalilah suka nufi gida.
***. ***. ***
“Ina fatan kinsanar masa ayi aikin nan da gaggawa ko?”.
“Ehh ranki yadad’e, yace ma cikin satinnan komai zai kammala”.
“Yauwa haka nake son ji, domin bahaushe ya ce da zafi-zafi akan daki k’arfe, tashi kije sai kin jini”.
Larai ta mik’e da tsumar jiki tabar falon Fulani Sokoto, tana fita su Yarima na kawo kai, zama sukayi gefan Fulani sokoto tare da gaisheta sannan suka fara sanar da ita dukkan abin da Mallam Kallah ya fad’a musu dangane da ciwon nata.
Fulani sokoto najin cewa Jalilah ta taka asirin da akayiwa wani ne, haba wa sai tamik’e zaune ta fara sababi da masifa.
“Ai wallahi duk ma mai hannu a ciki narantse da Allah da kansa zai bayyana kasan, har ni za’anunawa asiri?, ai ko da guraye mutum yake yawo yayi kad’an yamin haka, karku damu nasan waye yayimin hakan kubar komai a hannuna”.
Yarima da Anwar suka saki baki kawai suna kallonta cike da jimamin jin batun da ke fita daga bakinta.
Anwar ya mik’a mata gorar rubutun yana fad’in.
“Gashi ta dinga sha inji Mallam Kallah ta shafe jikinta, Fulani sokoto takarb’a tare da binsu da wani irin kallo da suka kasa fassara kona menene?.
Mik’ewa sukayi tare da yimata sai anjima suka fito daga falon, suna fita Fulani sokoto taja tsaki tare da dariya tana fad’in.
“Aikin banza aikin wofi har ni za’a nunawa bariki?, ayo asirin sannan a biyo ni da wani munafikin rubutu wai inji Mallam kallah, kuji wani rainin wayo wato a biyo ta hanyarsa a k’arasa kashemin ‘yartawa to ba dani ba wallahi Fulani Bingel da ni kike zancen dan nasan wannan duk tuggun ki ne burinki kawai kiga bayana ni da yarana to kafin kiga nawa sai naga naki, wannan abin kuwa zubar da shi zanje inyi wallahi abin da kuka k’ulla sai dai ya koma kanku”.
Haka Fulani sokoto ta shafe tsayin lokuta tana ta faman sambatu kamar wata tab’ab’b’iya Jalilah na d’aki tana jinta.
***
“Wai ni kuwa Aynu k
ina ya labarin Yarima Fudhal kuwa?”.
“Oho ni ina zan sani?, idan nemansa kike kije gidansu mana”.
“A a kawai dai tambaya nayi bai kuma zuwa ba?”.
Aynu taja guntun tsaki gami da jefawa Zainab harara.
“Wai ke meye naki a ciki akan Yarima nifa nariga na fidda shi daga cikin rayuwata tun ba yau ba”.
“Ni kam bana tunanin Yarima zai manta dake Aynu”.
“To ni namance da shi sai me?”.
Tayi maganar cike da masifa, Zainab ta fiddo ido waje tana fad’in.
“A a mai da wuk’ar yi hak’uri kada ki rufe ni da duka”.
Dariya suka d’anyi a tare, kafin Zee ta sake fad’in.
“Nifa ina ganin abune mawuyaci Yarima ya hak’ura dake tun yanzu”.
“To sai kuma gashi ya baki mamaki ya hak’ura ko?”.
“Bana tunanin hakan”.
“Kinga Zee mubar maganar Yarima dan Allah kina b’atamin rai muyi abin da ya kawo ni kawai”.
“To inajinki meke tafe da ke?”.
“Au kinma mance abin da nace zanzo muyi magana akai?”.
“Ohh yi hak’uri, yanzu tare kuke da Ya Sayyadin?”.
“E mana”.
“To bari ind’auko hijab muje to, amma kinsan ni banson bidi’a wallahi abarmu mud’anyi partynmu ko yane, saura kimin buk’ulu”.
“A a ni babu ruwana ke da mai bada kud’in”.
“E naji dai tashi muje”.
Suka mik’e suka fito daga gidan zuwa inda Ya Sayyadi Umar ke tsaye shi da wani abokinsa suna zaman jiran fitowarsu.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namecy Phirdauceey Jeebour.
32
*Mutane da dama na tambayata wai shin Yarima Fudhal ya hak’ura da Aynu ne koya?, nima dai bani da wannan amsar sai mu jira abin da alk’alamina zai bayar, nagode sosai Masoya iya wuya ana mugun tare*
***
“Wai ina na sanya wannan abin da aka kawomin ne?, inje inzubar da shi yanzunnan domin bansan abin da aka k’ullo a ciki ba”.
Cewar Fulani Sokoto kenan tana ‘yan dube-dubenta, kafin ta sanya wata ‘yar k’aramar Yarinya da ke aiki a wajenta ta kirawo mata Larai.
Mintuna kad’an sai gasu sun dawo tare, Fulani Sokoto ta dubi Larai da fad’in.
“Da kukai gyaran falon nan baku ga wata gorar faro ba?”.
“E ranki yadad’e bamu ga komai ba nan falon”.
Fulani Sokoto ta cije yatsa tana fad’in.
“Ikon Allah abin da mamaki sosai wallahi, nan fa na tashi na barta jiya namanta shaf “.
Tayi maganar tana mai nuni da gabanta inda take zaune, Larai tace ita dai bata ga komai ba.
“Tashi kuje to”.
Suka mik’e suka bar d’akin cikin rawar jiki, Fulani ta dubi Jalilah da duk diramar da ake tana zaune gefe rik’e da waya tana game.
“Ke !, Jalilah”.
Fulani ta kira sunanta, Jalilah ta d’ago kai tana duban Fulani.
“Ba kiga gorar faron ba?”.
Jalilah ta gyad’a kai alamu E, tsaki Fulani Sokoto tayi cike da takaici.
Yarima Fudhal ne yayi sallama cikin falon ya shigo, Fulani ta nemo wani munafukin murmushi ta d’ora akan fuskarta domin danne b’acin ran da take ciki don ka da Fudhal ya fahimci b’acin komai, Jalilah kuwa ajiye wayar tayi tana mai binsa da kallon fuskarta d’auke da murmushi ta d’an matsa masa inda take zaune, tana yi masa alamun yazo ya zauna.
Yarima Fudhal ya zauna kusa da ita yana gaishe da Fulani tare da tambayar jikin na Jalilah yak’ara da fad’in.
“Da fatan dai tana shan rubutun nata?”.
Yak’e Fulani tayi tana fad’in.
“E tana sha mana, abin da babu d’aci bare barci”.
Jalilah kuwa kallon Fulanin kawai take yi, Fulani ta mik’e tana fad’in.
“Bari inbarka da k’anwartaka ind’anje Shamaki”.
“To a dawo lafiya, nima office zanje yanzu”.
Fulani ta fice ta barsu nan zaune, tana fita Jalilah ta d’auki waya tare da shiga wajen text message tayi rubutu kamar haka.
“Yaya Mama fa bata son insha maganin nan”.
Ta mik’a masa wayar tare da mik’ewa ta nufi d’aki, mintuna kad’an sai gata d’auke da gorar rubutun ta fito, tana murmushi Fudhal ya tsare ta da tambayar.
“Me yasa bata so kisha?”.
Shiru Jalilah tayi domin ta rasa amsar da zata bashi, tana ji a ranta ba zata iya tonawa mahaifiyarta asiri ba, domin tana gudun b’acin sunan mahaifiyarta a idon Fudhal.
Karb’ar wayar tayi ta sake rubuta masa.
“Wai bata yarda da maganin ba zubarwa za tayi, amma dan Allah kada ka nuna mata kasan haka, zan b’oye maganin indinga sha ko wanne magani zaka kawo ka dinga bani zanyi”.
Yarima Fudhal ya karanta tare da yin murmushi yana mai duba agogon dake d’aure bisa tsin-tsiyar hannunsa kafin ya dawo da dubansa kan Jalilah yace.
“Karki damu ki dinga sha ab’oyen rubutun nada matuk’ar muhimmanci a tare da ke, lokaci ya k’ure domin nayi late sai na dawo”.
Yakai maganar yana mai dafa kanta ya fice da sauri, ajiyar zuciya Jalilah tayi mai k’arfi kafin tayi maza ta koma d’aki ta b’oye gorar rubutun ta dawo dalon ta zauna inda Fulani ta barta.
Sosai Yarima Fudhal ya mai da hankali kacokan kan ciwon Jalilah kullum yana jigilar karb’o mata magani duk da cewa a b’oye yake bata Fulani Sokoto bata sani ba, wasu kuma wajen Fulani Bingel yake a jiyewa kullum idan lokacin sha yayi sai taje ta sha ta koma.
Sai dai tana cike da kokwanto da mamakin yanda a kayi Yarima Fudhal ya yarda da abin da ta fad’a masa ba tare da yayi tunani ko tambaya akan dalilin da yasa Fulani Sokoto ba ta so Jalilah tayi amfani da magungunan da yake karb’o mata ba.
Amma sai dai ta gaza tambayarsa domin gudun zargi da tsoron wani abu da zai iya zuwa ya dawo.
Cikin sati biyu da fara ciwon nata sosai sauk’i ya fara samuwa sai dai matsalar rashin maganar da tafi damun kowa, amma Fulani Bingel takance ya kwantar da hankalinsa ya cigaba da addu’a sauk’i yana daga Allah.
***
A b’angarensu Aynu kuwa shirye-shiryen biki ake gadan-gadan domin bikin ya rage saura sati biyu a shiga cikin hidimar bikin, su Aynu anraba anko tare da taimakon Zee domin ita Aynu da cewa tayi kowa yasa kayansa amma Zee ta ce ina bazai yiyu ba dole ayi anko kamar yanda ake yi a kowanne biki, INA RUWAN ZAINAB MANYA, K’IRJIN BIKI KENAN.
*(Ni FA BAN GANE BA, ZEE TA KOMA B’ANGAREN YA SAYYADI UMAR NE?, YA ABIN YAKE NE?).*
“Yadai lafiya kuwa kake ta faman kirana a waya?”.
Anwar ya fad’a yana mai zama a d’aya daga cikin kujerun da ke gaban table d’in Yarima Fudhal.
“Babu komai rakiya nake so kamin”.
“Zuwa ina kenan?”.
Yarima ya kafe Anwar da shanyayyun idanuwansa ba tare daya bashi amsar tambayarsa ba ya mik’e tsaye tare da fad’in.
“Kai dai tashi muje kawai”.
Anwar ya d’anyi jim kafin shima ya mik’e yad’an zunkud’a kafa yana fad’in.
“Muje to amma fa kamai da ni d’an rakiya wallahi, ko ina nake kome nake yi sai ka kira ni inraka ka wani waje, na kusa samawa kaina mafita nima dai”.
Yarima najinsa baitanka masa ba domin yasan duk surutun banza yake yi bazai iya aikata abin da yake ikirarin zai yi ba.
“Kana jina kayi shiru?”.
Anwar ya jefa masa tambaya dai-dai sanda suka isa jikin motar Anwar d’in.
“Au wai a motata za’aje ma?”.
Ya sake jefawa Yarima Fudhal tambaya.
“E da a motar wa za’aje?, idan ba taka ba”.
Ya bashi amsa yana mai shigewa cikin motar ya zauna, tsaye Anwar yayi yana binsa da kallo.
“Ka shiga muje mana”.
“Wai driven d’inma ni zanyi?”.
“Kaga malam kafiya k’orafi da surutu dan Allah ka shigo kaja mota muje”.
Anwar yayi murmushi a can k’asan ransa yana mamakin hali irin na Yarima, yau ka ganshi fari gobe ka ganshi bak’i kullum da salon halin da zai nuna maka.
“Matarka zatayi fama wallahi”.
Anwar yayi maganar yana mai sanyawa motar key, idan kujerar da yake kai tayi magana to shima ya tanka, kwanciyarsa yayi jikin kujerar motar tare da lumshe ido kawai yana sauraron abubuwan da zuciyarsa take raya masa.
Sai da Anwar ya hau babban titi sosai sannan ya juyo fuskarsa ya dubi Fudhal da har lokacin yana kwance ido a lumshe.
“Wai ina zamu ne?, ka barni sai faman tafiya nake”.
“Unguwar kwari”.
Ya bashi amsa ba tare da ya bud’e idonsa ba.
“Unguwar kwari kuma?, kana nufin gidansu Aynu zamu je?”.
Yarima Fudhal ya bud’e ido tare da gyara zamansa kafin ya bashi amsa da fad’in.
“E unguwar kwari zamu je, amma ba gidansu Aynu ba”.
“To wajenwa zamuje a unguwar kwarin?”.
“Kai dai muje kawai zaka ga wajen wanda zamu je”.
Anwar bai kuma cewa komai ba ya juya kan motarsa ya hau titin da zai sada shi da unguwar, a dai-dai bakin layin sukayi parking motarsu, Fudhal ya fito ya tsaya jikin motar yana mai k’arewa layin kallo har Anwar d’in ya fito shima ya kulle motar yana fad’in.
“Sai ina kuma?”.
“Ka fiye tambaya ka…!”.
Maganar ta mak’ale a dai-dai sanda ya hango Zainab na fitowa daga cikin layin, Fudhal ya fad’ad’a murmushinsa tare da fad’in.
“Yauwa ga Zainab d’innan ma”.
Zainab ba k’aramin mamaki tayi ba sanda idonta ya sauka kan Yarima Fudhal, k’arasawa tayi da fara’a tare da sallama.
Fudhal ya amsa yana fad’in.
“Ina Aynu?, wajenta muka zo”.
Zee ta d’anyi jim kafin ta bud’e baki ta fara magana.
“Ai nad’auka ka hak’ura da ita wallahi”.
“Kamarya kenan, mai yasa kika ce haka kuma?”.
“Naga tun randa kukayi rabuwar babu dad’i baka sake nemanta ba, ko layinan ka daina zuwa”.
“Aiki ne ya tsare ni”.
“Ayya amma ba kada labarin aurenta ko?”.
“What..! Aure kuma?, wa zata aura?”.
Fudhal ya jero tambayoyin cikin rud’u da tashin hankali.
“Ya sayyadi Umar zata aura, nan da sati biyu masu zuwa”.
Yarima Fudhal yayi sauri ya jingina a jikin mota bai sake furta ko kalma d’aya ba, sabida ji da yayi bugun zuciyarsa na k’ara tsananta da bugu fiye da kima.
Zainab bata lura da yanayin da yake ciki ba ta cigaba da fad’in.
“Gaskiya nima banji dad’i ba wallahi, naso a ce aurennan da kai za’ayishi amma babu yanda muka iya haka Allah ya tsara”.
“E hakane dama ai matar mutum k’abarinsa inji malam bahaushe, mungode sosai Zainab”.
Anwar yayi maganar yana mai dafa kafad’ar Yarima, Zainab tace.
“To ni zan koma gida dama sak’o na kaiwa Aynu sai anjimanku”.
“To sai anjima ki gaida Mamanku”.
Cewar Anwar kenan, yayin da Zee ta juya tabar wajen.
Anwar ya bud’e mota ya zaunar da Yarima yana fad’in.
“Please ka sanya ranka salama dan Allah kada ka jawa kanka matsala fa?”.
Yarima Fudhal ya dubi Anwar da jajayen idanuwansa da suka rine daga fari zuwa ja tsabar d’acin rai.
“Yanzu Aynu zata iya auran wani ba ni ba?, why Anwar mai na aikata haka a rayuwata da SO yake wahalar da ni haka?, wanne zunubi na aikata wa Ubangiji ya jarance ni da irin wannan SO?, har zuwa yaushe ne zan samu muradin raina?, har tsayin wanne lokaci ne zuciyata zata samu abincinta, har yaushe ne idaniya zata samu haskenta?, yaushe ne rai zai huta daga fuskantar barazanar yin bankwana da duniya?, Anwar ka taimake ni dan Allah ina son Aynu wallahi inasonta kamar raina ita ce dukkan burina na duni…! “.
Bai samu damar k’arasa maganarba sabida kukan daya sark’e masa murya, sosai Yarima Fudhal ya bawa Anwar tausayi, yasan zafin so amma bai san zafin yakan kai har wannan matakin ba, ya rasa kalmar da zai lallashi Fudhal da ita hakan yasa kawai ya sanyawa motar key suka bar layin gidan domin ya fuskanci Yarima Fudhal baya cikin haiyacinsa a wannan lokacin.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdausy Jeebour.
Kuyi hkr dan Allah nayi mistake d’in number ne mai makon insaka 33 sai na sake mai maita 32 a wancen page fatan zaku fahimce ni nagode sosai.
34
Zaune yake bisa d’aya daga cikin kujerun falon, gabansa centre table ne cike da kwalaban giya kusan guda biyar gefensa kuma Shisha ce sai karan sigarin dake rik’e bisa hannunsa yana zuk’a lokaci-lokaci.
Idan ya zuk’i sigarin sai ya kora da d’aya daga cikin kwalaban giyar kamar wani tab’ab’b’e.
Tsaki yaja yana mai kashe karan sigarin ya jawo Shisha yahau sha, kafin ya mik’e tsaye yana maiyin ball da shishar tare da d’aga centre table d’in baki d’aya kwalaban giyar suka rotse hatta table d’in ba’abarshi abaya.
Juyawa yayi gefansa ya d’au wata giyar dake gefansa itama ya had’ata da bangon d’akin take ta fashe ruwan giyar na bin bangon.
Komawa yayi ya zauna yana mai cusa hannunwansa biyu cikin sumar kansa yana sosawa tamkar wani mahaukaci sabon kamu, duk wanda ya ganshi a wannan lokacin cikin wannan yanayin dole ya tsorata da shi.
“SAFIYA….!”.
Abinda ya furta kenan cikin ihu da k’araji badan babu kowa a harabar ba da babu abin da zai hana mutane shigowa wajensa da gudu.
Mik’ewa yayi cike da layin giya ya nufi hanyar fita daga falon ko takalmi babu a k’afarsa, duk inda ya wuce sai anbishi da kallo sabida yanda yake layi da had’a hanya, bai tsaya ko inaba sai cikin falon Fulani Sokoto yana Shiga ya zube bakin k’ofa.
Fulani da muk’arrabanta dake zaune falon sukayo kansa suna fad’in.
“Subhanallahi….! lafiya Yarima Jaleel?”.
Kama bango yayi yamik’e ba tare da yace dasu komai ba, Fulani na ganin haka ta fahimci halin da yake ciki, umarni ta bawa kowa ya fice aka barta daga shi sai ita sai kuma Jalilah.
Kamo hannunsa tayi takaishi tsakiyar falon ta zaunar dashi tare da jinginashi da jikin kujera kafin ta koma ta zauna tana mai binsa da kallon takaici.
Kafin tamik’e tsaye tana faman safa da marwa Jalilah kuwa sai bin Fulani da Jaleel take da kallo.
Can Fulani ta koma ta zauna tare da sakin wata irin ajiyar zuciya kafin ta bud’e baki ta fara magana.
“Haba Jaleel har yaushe ne zakayi hankali?, yaushe ne zaka nutsu kasan ka girma?, mai yasa kake k’ok’arin ganin ka b’ata gobenka ne?”.
“Kullum fad’i tashin da nake akanka ne, ina tufka kana warwara haba Jaleel ka nutsu mana ko ka samu ka cikamin burina Jaleel”.
Duk surutun da Fulani take Jaleel kawai binta yake da kallo amma a zahirin gaskiya ko kad’an maganganun basa tasiri a kwakwalwarsa.
A hankali ya bud’e baki yana fad’in.
“Naji Momy zan daina amma ki taimaka ki auramin wacce nake so nima dan Allah”.
Dogon tsaki Fulani taja tana fad’in.
“Au dama akan mace kake son ruguzamin burina Jaleel?, akan mace kake neman b’atawa gobenka”, wace ita? fad’amin ko wacece ni kuwa duk yanda zanyi sai na aura maka ita indai har zansamu cikar burina Jaleel”.
“Safiya ce ! Momy ita nake so”.
“Safiyya kuma ! wacce kenan?”.
“Gimbiya Safiyya Momy”.
A razane Fulani take bin Jaleel da kallo cike da rud’u da tashin hankali, ba Fulani ba har Jalilah dake zaune gefe tana jinsu ta girgiza dajin batun da Jaleel yazo da shi.
“Jaleel kana cikin hankalinka kuwa?”.
“E Momy nidai ita nake so, idan na rasata zan iya rasa rayuwata Momy”.
“Amma dai ina kasan angama magana Fudhal zata aura”.
“Nasani Momy amma tun farko nine nake sont…..!”.
Bai kai ga k’arasa maganarsa ba sai jin k’arar saukar maruka yayi a duka kuncinsa guda biyu, cikin firgici ya dafe fuskarsa yana bin Fulani da kallo bai kuma magana ba yami’e cikin layi ya fice daga falon.
Fulani ta koma kan kujera tazub’e dab’as zuciyarta na suya da k’una akan maganar da Jaleel yazo mata da ita yanzu har ace yau Jaleel ne take fad’a yana fad’a.
“Meke faruwa ne?”.
Abin da ta furta kenan cikin ranta da sauri ta mik’e tsaye kamar antsikareta duban Jalilah tayi tana fad’in.
“Maza jeki saka a kirawon Larai…au namanta kefa baki da baki yanzu”.
Takai maganar tare da jan tsaki, mik’ewa tayi ta fice daga falon tabar Jalilah zaune.
Kwance yake kan carpet ya d’ora kansa bisa kusun idonsa a lumshe kamar mai bacci amma a zahiri ba baccin yake ba, domin daka kalli gefan idonsa ruwan hawaye zakaga yana fita lokaci-lokaci, can ya mik’e zumbur kamar antsikareshi yana mai dafe kansa da yake sara masa d’aga kai yayi ya dubi agogo lokacin k’arfe tara na dare 9pm.
Toilet ya nufa ya wanke fuskarsa yana fitowa yayi waje zuwa harabar gidan, yana tafe zuciyarsa na cigaba da tsananta bugu amma duk da haka ya d’aure harya k’arasa bakin k’ofar falon da sallamarsa yasa kai cikin falon ba tare daya nemi iso ba.
Mai Martaba na kishingid’e a falo yaji sallamar Fudhal d’in tare da shigowarsa, murmushi ya fad’ad’a a fuskarsa Mai Martaba yamik’e zaune yana fad’in .
“Zonan zauna Magaji, kamar kasan yanzu nake zancen insaka a kirawomin kai”.
Yarima Fudhal yayi k’ok’arin nemo murmushi ya d’ora a kan damuwar dake kan fuskarsa, ya durk’usa ya gaishe da Mai Martaba tare da gyara zama danjin mai zai ce.
Gyaran murya Mai Martaba yayi yana fad’in.
“Munyi magana da Iyayen Saima sunce sun janye maganar aurenka da ‘yarsu, sannan kuma muntsai da bikinka kai da Safiyya nan da sati biyu masu zuwa hakan yayi maka ko a k’ara?”.
“Duk yanda kukayi dai-dai ne Abba, amma ina da ‘yar magana akan batun auren”.
“Babu damuwa ina jinka fad’i”.
“Abba ka taimaka dan Allah bawai zanyi jayayya da kai bane na yarda zan auri Safiyya amma ka yarjemin in auri Aynu dan Allah Abba”.
Mai Martaba bin Fudhal yayi da kallo kawai yana gyad’a kai kafin yayi murmushi yana mai fad’in.
“Nima a matsayina na Mahaifinka zan umarceka da abu guda d’aya a yau koda bayan raina kada d’ayanku yayi gangancin had’amin zuri’a da talaka !”.
Cike da mamaki Fudhal yake bin Mai Martaba da kallo yarasa wacce irin k’iyayyace Abban nasu keyiwa talaka haka?, ya bud’e baki zaiyi magana kenan sai ganin fad’owar mutum sukayi cikin falon.
Jaleel ya tako da Sauri ya zube gaban Mai Martaba tare da kama k’afarsa yana fad’in.
“Dan Allah Abba kada ayi auren nan wallahi Abba nine nake sonta Momy ce tace kada nafad’a inbari a aurawa Broda”.
“Kai lafiyarka kuwa?, akan wa kake magana ne?”.
“Gimbiya Safiyya Abba itace wadda nake so dan Allah Abba a auramin ita ni nafi dacewa da ita ba Fudhal ba”.
Mai Martaba mik’ewa yayi tsaye yana mai bin ‘ya’yan nasa da kallo kafin ya koma ya zauna yana fad’in.
“Wato kuna so kumai da ni k’aramin mutum ko?, mai yake damun kune?, kai da nake ganinka mai hankali Magaji ashe kallon kitse nakewa mai?”.
“To kutsaya kuji ni da kyau ko bayan raina babu kai babu auren ‘yar matsiyatarnan Magaji aurenka da Safiyya kuma babu fashi, kai kuma Jaleel ko zaka mutu bazan tab’a canja maganata ba akan ka dai, yaushema kake da hankalin da zanyi maka aure yanzu kana tunanin duk abin da kake aikatawa bani da masaniya a kai?, Ku tashin kuficemin daga nan kada insake jin Wanda yazomin da makamanciyar irin wannnan maganar”.
“Ku b’acemin daga nan nace…!”.
Yayi maganar cikin tsawa ba shiri suka mik’e suka fice kowannansu zuciyarsa cike k’una da b’acin rai.
Babu wanda ya tankawa wani har suka isa part d’insu kowa ya nufi d’akinsa.
Yarima Jaleel dai yana shiga d’aki fridge ya nufa ya d’auko kwalaban giyarsa yahau sha babu ko k’ak’k’autawa bare yayi tunanin zata iya illata shi.
Fudhal kuwa yana shiga d’akinsa kwanciya yayi bisa katifarsa yana juyi yayin da zuciyarsa ke cigaba da tsananta bugu tare da zafi.
Har kusan k’arfe biyun dare amma al’amarin nasa babu sauk’i sai da takai takawoma juyinma da k’yar yakeyinsa.
Jiyayi amai na taso masa da rarrafe ya shige toilet amma sai aman ya koma, nan yayi k’arfin halin mik’ewa yana dafa bango har ya fito daga toilet zuwa tsakar d’aki anan ya yanke jiki ya fad’i numfashinsa na fita sama-sama.
Hello
My luvly fans
Har yau dai bazan gajiya da baku hak’uri ba, abubuwane suka rik’eni amma yanzu alhmdlh insha Allahu indai ba wani uzuri mai k’arfi ba kullum zaku dinga samun post nawa da yardar Allah har Allah ya nunamin inkammala muku ngd sosai masu call & message kuma raina iya wuya ana tare.
Bissalam
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdausi Jeebour.
35
5:00AM
Har aka kira sallar asuba Yarima Fudhal yana ji amma ya gagara tashi wayarsa dake can kan katifa sai faman ringing take yi har tagaji ta katse.
Fulani Bingel na shirin shiga toilet domin ɗauro alwala wayarta tahau ringing hakan yasa tayi saurin ɗagawa domin ba k’alamin faɗuwar gaba taji ba alokacin aranta ta furta.
“Ko waye ke kirana da asubar nan Allah yasa dai lafiya?”.
Tayi maganar tana mai ɗaga wayar tare da karawa bisa kunnanta.
Daga can ɓangaren aka amsa da faɗin.
“Hello Hajiya lafiya kuke kuwa?”.
“Lafiya ƙalau Sadiya wani abune ya farune naga kiranki da asubar nan?”.
“Wallahi Hajiya hankalina ya kasa kwanciya ne tun jiya da dare nake kiran wayar Fudhal baiyi picking ba, yanzuma sai da na kira amma bai ɗaga ba”.
Fulani take taji gabanta ya tsananta faɗuwa amma ta daure ta bata amsa da faɗin.
“May be yana bacci ne, idan ya farka nasan zai nemeki”.
“To amma dai Hajiya kisa adubo shi”.
“Insha Allah bari inyi sallah”.
Fulani ta katse wayar tare da shigewa toilet a can kasan zuciyarta kuwa addu’a kawai take ta faman zubawa domin tasan cikin kwanakin nan kaf baya cikin nutsuwarsa ita al’amari nasama bakaramin tsoro yake bata ba.
A gaggauce ta ɗauro alwalar ta fito ta shimfida abin sallah ta tayar da sallah.
Ta nayin sallama ta fito daga ɗakin domin zuwa dubo Fudhal sabida zuciyarta ta kasa jurewa.
Gidan shiru babu kowa har ta isa part ɗin nasu, kofar ɗakinsa buɗe dan haka kai tsaye ta sanya kai cikin falon ta nufi bedroom ɗinsa tana sa kai ta hangoshi kwance tsakar ɗakin sai nunfarfashi yake sama-sama da gudu ta karasa wajen tana faɗin.
“Subhanallahi…! Baka da lafiya Magaji?”.
Ta karasa Kansa kenan ta ɗago shi sai ga Anwar ya faɗo ɗakin shima shine ya taimaka mata ya miƙar dashi tsaye sai lokacin suka lura a she aman jini yake yi da basu lura ba da yake dumm light ne a ɗakin da sauri sukayi waje da shi Anwar ya sanyashi a mota sannan ya juyo ya kalli Fulani yana faɗin.
“Bari in wuce da shi asibitin kafin ki sanar da Mai Martaba domin yana bukatar taimakon gaggawa”.
Bai jira jin amsartaba ya shige mota yaja da gudu yabar harabar gidan, Hajiya ta koma ciki da sauri kai tsaye shashin Mai Martaba ta nufa ta Sanar dashi halin da ake ciki.
Nan da nan aka tashi driver suka bi bayan Anwar.
Anwar bai tsaya a ko inaba sai a NANAH KHADIJAH PRIVATE HOSPITAL kai tsaye Emergency aka nufa dashi.
Anwar ya kasa zaune ya kasa tsaye sai safa da marwa yake, a haka su Mai Martaba suka taddashi abinka da masu gari office ɗin Babban Doctor aka kai Mai Martaba ya zauna tare da Hajiya idan banda addu’a babu abin da ko wanne daga cikinsu yake yi cikin ransa.
Likitoci sun shafe tsayin a wanni biyar akan Yarima Fudhal kafinsu samu nasarar dai-daita numfashinsa dake barazanar yin bankwana da duniya.
Babban likitan ya fito yana share gumi ya nufi cikin office ɗinsa inda ya barsu Mai Martaba na zaman jiransa.
Ya bude wani file yayi ƴan rubuce-rubucensa kafin ya ɗago kai yana binsu da kallo ya bude baki a hankali yana faɗin.
“Ya akayi kuka bari yana wasa da bin ƙa’idojin shan magani?, nasan kunsan illar dake tattare da ciwonsa, ga kuma damuwa daya sanyawa ransa da yawa Wanda yin hakan na daf da Ku iya rasashi baki ɗaya”.
Mai Martaba da Hajiya bin Doctor kawai sukeyi da kallo domin basu fahimci maganarsa ba.
“Amma Doctor mene kake magana akai haka?”.
Cewar Mai Martaba kenan yana mai bin fuskan Doctor ɗin da kallo.
“Kamar ya?, kuna nufin kuce bakusan ciwon dake damun ɗanku ba?”.
Doctor yayi maganar yana mai jingina a jikin kujerar da yake kai, tare da ƙare masu kallo ɗaya bayan ɗaya.
“E gaskiya bamu sani ba, amma kada kaga laifinmu abisa hakan domin ba anan ya girma ba”.
“OK a takaice dai ɗanku na ɗauke da ciwon zuciya ne wanda ya kai matakin ƙarshe da zai iya rasa ransa”.
A tare Mai Martaba da Fulani Bingel suka mike, Fulani inbanda innalillahi wa’inna ilaihi razi’un babu abin da yake fita daga bakinta.
Anwar dai na gefe ya rasa abin da zai ce sosai yake jin tausayin Yarima Fudhal cikin ransa.
Doctor ya buɗe baki ya cigaba da faɗin.
“Ku zauna insha Allahu babu wata matsala munsamu dai mun dai-dai ta tsayuwar nunfashinsa, amma munaso musan dalilin daya haddasa masa wannan ciwon, sannan kuma munaso musan WACECE AYNUL-HAYAT?, da dukkan alamu soyayyartace ta jefashi cikin wannan yanayin? sabida bakinsa babu abin da yake furtawa sai ita”.
Anwar dake tsaye gefe neman guri yayi ya zauna yana mai lumshe idanuwansa da sukeyi masa zafi sosai, yanason yin magana amma ya gagara furta ko kalma ɗaya.
“Doctor ciwon ya jimane a jikinsa ?”.
Cewar Fulani kenan tana mai goge kwallar dake kokarin zubo mata.
“E to a bincikenmu ciwon ya kai tsayin shekaru goma zuwa goma sha uku”.
Shiru office din ya ɗauka naɗan wani lokaci kafin Anwar ya katse shirun da faɗin.
“Nasan dalilin ciwon nasa !”.
Nan Anwar ya bawa Doctor labarin dalilin samun ciwon zuciyarsa ya kara da faɗin.
“Aynul-hayat da kaji yana faɗi itace yarinyar da yake so, kuma sonta ne dalilin tsanantar ciwon nasa”.
Doctor yayi shiru tsayin wani lokaci suna kallonsa kafin ya fara rubuce-rubuce cikin file ya ɗago yana kallon Mai Martaba.
“Duk yanda za’ayi indai kuna son ɗanku to dole ne idan ya farka ya fara tozali da abin da ya sakashi a cikin wannan halin idan kuwa ba haka ba zan iya cewa sai dai kuyi hakuri da shi !”.
Cikin fushi Mai Martaba ya mike yana faɗin.
“Kana nufin inje innemawa Magaji auren ɗiyar mutsiyata?, ina bazai yiyuba duk yanda zakuyi kuyi amma auren Magaji da wannan yarinyar bazan taɓa lamunta ba”.
“Kayi hakuri Mai Martaba halin da yake ciki zamu duba..!”.
“Dakata Doctor…! Ni bana magana biyu, ina roka masa Allah ya bashi lafiya amma aure babu shi da waccan yarinyar ko bayan raina”.
Yana faɗin haka ya saka kai ya fice daga office ɗin, Anwar da Doctor suka bi bayansa da kallo, Fulani kuwa nan tayi zaune tana sharar kwalla.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button