NOVELSUncategorized
YARIMA FUDHAL 36-40

*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdausi Jeebour.
36
Doctor ya dawo da dubansa kansu Anwar tare da ajiyar zuciyar yana faɗin.
“Gaskiya Hajiya kusan yanda zakuyi Ku nemawa Yarima Fudhal abin da yake so, domin yin hakanne kaɗai zai iya taimakawa wajen cetonsa daga halin da yake ciki sai kuma addu’a wadda ita yafi buƙata a halin yanzu”.
Anwar ne yayi ƙarfin halin faɗin.
“Zamuyi ƙoƙarin ganin munshawo kan Mai Martaba insha Allahu, yanzu zamu iya zuwa mu ganshi?”.
“A a sai dai ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu munga yanda yanayin jikin nasa zai kasance, yanzu zaku iya tafiya gida”.
Ya kai maganar yana mai miƙewa domin fita daga office ɗin, Anwar da Hajiya suka take masa baya.
Sai da ya kai Hajiya gida sannan ya wuce gidansu.
Tun kafin Hajiyarsu Fudhal ta dawo labarin ciwon Fudhal ya baza cikin gidan, tana Shiga falonta aka fara zuwa gaisuwa tare da gamba tambayar jikin Fudhal.
Ɓangaren Fulani Sokoto kuwa bazaka iya tantance halin da take ciki ba farin ciki ko baƙin ciki ?, amma anawa hashashen zan iya cewa Fulani Sokoto farin ciki ne fal cikin ranta akan ciwon Fudhal domin tana ganin kamar mutuwa zaiyi idan kuwa babu fudhal magajin sarauta dole Yarima Jaleel ne , sai dai tsananin damuwar da Yarima Jaleel ya jefata shike danne farin cikin da take ciki.
Mai Martaba kuwa ranar ko fada bai zauna ba idan banda safa da marwa babu abin da yake a falonsa, a wannan halin ne Fulani Bingel ta taddashi ta nemi guri ta zauna shima ya zauna ba tare da kowanne daga cikinsu ya furta ko kallama ɗaya ba.
Daga can Fulani Bingel ta katse shirun tana faɗin.
“Amma ina ganin kamar hukuncin daka yanke akan ɗanka yayi tsauri, kada ka zamo ɗaya daga cikin iyaye masu tauye haƙƙin ƴaƴansu daya rataya a wuyansu, kasan dai Magaji yaro ne mai ladabi da biyayya Wanda baya tsallake dukkan dokar da muka kafa masa, amma ya kamata sau ɗaya dai shima ka bashi dama ya samu farin cikinsa, kamar yanda ya kasance yana faranta mana tsayin shekarun, kayi hakuri idan na faɗi kalma ɗaya data ɓata maka rai ka gafarce ni na barka lafiya”.
Fulani ta miƙe tana mai ficewa daga ɗakin, tabar Mai Martaba nan zaune kamar ta jona masa wutar lantarki, a can kasan zuciyarsa yasan gaskiya ta faɗa sai dai shi bayajin a ransa zai iya jure haɗa zuri’a da jinin talaka”.
Al’amarin Yarima Jaleel kuwa ranar wuni yayi a ɗaki baiko leƙo waje ba inbanda bankawa Kansa kayan maye babu abin da yake yi ya zama tamkar wani mahaukaci hakan yasaka bai San wainar da ake toyawa ba a cikin gidan.
” Wai Hajiya mai yasa Magaji ba zai iya haƙura da yarinyar nan bane?, tunda Abba ma baya so sai kace dole?”.
Cewar Sa’ida kenan, Aunty Sadiya dake zaune gefe tana shirya ‘yan biyunta tayi murmushi kafin ta bata amsa.
“Kema dai Sa’ida kamar baki san al’amarin so ba?, ko kaɗan bana ganin laifin Magaji ina tausayawa rayuwarsa sosai wallahi, Abba mahaifine agaremu amma shine da laifi daya hakura anyi auren nan da duk hakan bata kay ba da nasan babu wanda zai san Magaji nada ciwon Zuciya”.
“Ni kuwa kinsan abin da yake bani mamaki Aunty Sadiya?”.
“Aa”.
“Cewa da akai sanadin ciwon akan matsalarsa da iyayenta ne, abin da yafaru tsayin shekaru dasu ka wuce sai kuma gashi ya mace akan son ɗiyarsu”.
“Babu wani abin mamaki da ikon Allah Sa’ida, domin Allah baya yafe laifin wani akan wani, mahaifinku yayi kuskure Sosai awancen lokacin sakayyace kawai take bibiyarmu amma har yanzu ya gaza fahimtar hakan, “.
Fulani Bingel ta bata amsa tana mai share kwallar dake kokarin zubowa daga befan idonta, Jalilah dake zaune gefe tana jinsu tana son cewa wani abu amma babu dama, hakanne ya sanyata fashewa da kuka musamman idan ta tuna irin ƙiyayyar da suke masa su da mahaifiyarsu sai gashi shine yafi kowa damuwa da ciwonta.
Mikewa tayi da gudu ta fice daga falon ta nufi part ɗinsu tana Shiga kai tsaye ɗakinta ta wuce ta faɗa kan gado tana mai cigaba da rera kukanta sai da tayi kuka mai isarta kafin ta mike ta shige toilet ta wanko fuska ta dawo tana mai zama gefan katifarta tayi ta gumi tana aikin tuananin neman mafita akan wannan al’amarin.
A can ƙasan zuciyarta tana son warwarewa Abban nasu wata sarkakiya sai dai tana gudun jawa mahaifiyarsu tsana a gun Mai Martaba da kuma yan’uwansu tare da tsoron yanda Mai Martaba zai ɗauki batun.
Tun da aka kwantar da Yarima Fudhal ko dan yatsansa baya iya motsawa domin baima San a duniyar da yake ba, yana rayene amma kamar matacce ban-bancinsa da matacce ɗaya ne shine numfashi ko numfashinma ta computer dake gefansa ne kawai zaka kalla kasan yana da rai.
Ranar dasu Aunty Sadiya sukaje babu wanda baiyi kuka ba cikinsu musamman Jalilah rungumeshi tayi tana aikin kuka har sai da aka janyeta.
Ranar suna dawowa basu wuce ko inaba sai part din Abbansu domin su roƙeshi ya sauko daga dokin naƙin da ya hau, amma fafur yaƙi daga ƙarshema korarsu yayi dukansu suna kuka suka baro falon nasa, sai bayan fitarsu kuma jikinsa yayi sanyi sosai hardai daya tuna maganar Aunty Sadiya ta ƙarshe kafin ya koresu.
“Abba kayi hakuri dan Allah bawai munzo ne akan dole ka yarda Magaji ya auri wacce baka so ba, munzone akan ka taimaka kaje ka ganshi koda sauɗayane domin yana bukatar addu’arku sosai, ya kamata ka janye daga fushin da kake da shi ko yasamu wani sassaucin na ciwon nasa, sabida fushin iyaye babbar masifa ce ga ɗansu”.
“Bayan haka Abba ka gafarce ni abisa abin da zan fada yanzu duk da nasan dole maganar zata ɓata maka rai”.
Shiru tayi naɗan wani lokaci kanta a ƙasa kafin ta cigaba da faɗin.
“Abba mene dalilinka naƙin talaka haka?, talaka baya da gata aduniya ne?, shin talaka ba mutum bane kamar kowa?, Shifa Ubangiji babu ruwansa da talaka ko mai kuɗi, sarki ko malami shugaban kasa ko gwamna yaro ko babba duk ɗaya suke a wajen Allah ban bancinsu kawai shine Wanda yafi tsoransa, Abba kasani shifa arziki da mulki ba madogara bane domin ko babu mutuwa akwai tsufa Abba, a matsayinka na shugaba idan baka kyautatawa al’ummar da kake mulkaba taya kai ma zakayi tunani Allah zai kyautata maka, Abba……”.
“Ke…! Dakata kinfi ni sanin haka ne?, ko kuwa kinaso ki nunamin kinfini sanin ya kamata, Fudhal ɗa nane nike da iko inyanke dukkan hukuncin da naga dama akansa, Ku tashi Ku ɓacemin da gani sha-shan yara kawai…”.
Yana zuwa nan ya runtse ido sosai yaji ransa na suya da ɗaci akan abin da ya aikatawa ƴaƴan nasa, sai dai shima baya da masaniya akan dalilin da yasa yake musu hakan, amma har ga Allah yasan gaskiya ta faɗa.
“Mene dalilina akan tauyewa ƴaƴana haƙƙin abin da suke so?”.
“Son zuciya…!”.
Ya bawa kansa amsa, girgiza kai yayi cike da takaici, yana daga idonsa kasan carpet yayi to zali da wata takadda yasa hannu ya ɗauka ya buɗe a hankali rubutu ya gani ciki da bayan takaddar, haka kawai yaji aransa ya kamata ya karanta domin ya ji abin da ta kusa.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S. A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S. A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY PHIRDAUSY JEEBOUR.
37
Ga abin da wasiƙar ta ƙunsa.
“Assalamu alaikum.
Abba ina mai baka haƙuri akan abin da zan faɗa bana fatan ko kalma ɗaya tasanyaka fushi sai dai fatan ka fahimce ni, kayi hakuri Abba ka yafewa Fudhal kasa ni shi dan Adam ajizine baya da masaniya akan abin da zai aikata domin komai ya faru ga bawa dama can rubutacce ne, Abba ni na sani dukkan abin da yake faruwa tsakanin Fudhal da Jaleel akan Gimbiya Safiya wallahi Abba sa hannun maƙiya ne kayi haƙuri ka fahimci ko wanne daga cikin su ka daure kaje ka dubo Fudhal kaga halin da yake ciki bawai ina faɗin ka amince masa da auren wacce baka so ba a’a fatana kaje kaga halin da yake ciki may be zaka iya sanin hukuncin da zaka yanke akan haka.
BISSALAM”.
BISSALAM”.
Sarki Ubaiyd ya karanta wasiƙar kusan sau biyar tare da shafe tsayin lokuta yana jujjuya wasiƙar sosai jikinsa yayi la’asar, yayin da ƙasan zuciyarsa ke azalzalarsa da ƙin yarda da batun sai dai yayi nasarar yaƙar kasan zuciyartasa ɗari bisa ɗari.
WASHE GARI
Washe gari tun misalin ƙarfe bakwai Fulani Bingel da Fulani sokoto suka shirya domin zuwa dubo halin da Yarima Fudhal yake ciki.
Jalilah ma ba’abarta a baya ba, domin da kanta ta Shiga kitchent ta ɗanyi masa girki mai ruwa-ruwa yanda mara lafiya zai iya ci.
Fulani Bingel ta dubeta sai faman tiri tiri take da kwandon kayan abinci guntun murmushi tayi kafin ta dafa ka faɗarta.
“Jalilah girki ki kayi masa ne?”.
” E Hajiya “.
“Ayya baki San haryanzu bai dawo haiyacinsa ba?, baya cin komai Jalilah mai da abincin kizo mutafi”.
Takai maganar dai-dai sanda driver yayi parking a gabansu suka shiga Jalilah kuma ta bawa ɗaya daga cikin dogarawan dake yawo a farfajiyar gidan kwandon kayan abincin ta shige mota itama suka tafi.
Ko da suka isa asibitin can suka tadda Aunty Sadiya tuni ta jima da zuwa ma, Aunty Sa’ida ce sai bayan da sukaje sannan ta je ita ma.
‘Yan dubiya ne suka fara sallama daga wannan ya fita sai kaga wasu sun shigo duk da cewa ba’a aganinsa sai dai ka leka ta glass ɗin windown ɗakin da yake kwance kamar gawa ansanya masa oxygen babu wani abu dake motsi a jikinsa sai saitin zuciyarsa da ake iya ganin bugawarta ya rame sosai kai kace yayi shekaru irin biyun nan a kwance.
Mai Martaba na kishingiɗe bisa kusun Jakadiyya tayi sallama a ruɗe ta shiga tana mai zubewa kasa tare da faɗin.
“Mai Martaba Yarima Jaleel fa na daf da rasa hankalinsa yayi Marisa sosai Yallaɓai…!”.
Mai Martaba miƙewa yayi bai jira karashan maganarba kai tsaye ya fice daga ɗakin Jakadiyya ta biyo bayansa da sauri.
Tunda yasa kafa falonsa yake cin karo da kwalaban giya da karan sigari dakin inbanda wari babu abin da yake yi, Yarima Jaleel na kwance sharkaf tsakar ɗakin sai amai ne ke fita daga bakinsa mai warin tsiya.
Juyowa yayi yana duban Jakadiyya yace.
“Asamu a gyarashi akaishi a sibiti”.
Yana faɗin hakan ya fice daga ɗakin ya koma part ɗinsa.
“Wacce irin ƙaddara ce wannan?, mene ya jamin hakan?”.
Mai Martaba ya faɗa cikin ransa tare da cigaba da zaga falon, kafin ya shige bedroom ɗinsa domin shiryawa.
Ana isa da Yarima Jaleel asibiti shima kai tsaye emergency aka nufa dashi.
Suna zaune sai ganin faɗowarsa cikin ɗakin kawai sukayi, binsu yayi da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ya sauke idonsa kan Yarima Fudhal dake can kwance, karasawa yayi jikin win windown yana kare masa kallo sosai tausayin ɗan nasa ya kamashi take yaji zuciyarsa ta karye jiyayi ba zai iya jurar rasa ƴayansa maza har biyu ba waɗanɗa sune magada a bayansa.
Duban Anwar yayi dake zaune kan wata farar kujera.
“Ka same ni a waje”.
Ya Sakai ya fice Anwar yabi bayansa da sauri.
A office ɗin Doctor ya taddashi anayi masa bayani kan batun Yarima Jaleel.
Bayan ya gaishe dasu Mai Martaba yace ya zauna suka cigaba da maganarsu.
“Yanzu wanne halin yake ciki to?”.
“E to yanzu dai munyi masa allurar bacci sai idan ya samu relief ya farka zamu San abinyi domin ya bugu ne sosai har kwayoyin da yake sha sunfara barazanar taba masa kwakwalwa”.
Mai Martaba yayi shiru tsayin wasu lokuta kafin ya buɗe baki yana mai cigaba da faɗin.
“Ya batun Magaji kuma?, yaushe ne zai farfaɗo?”.
“Jikinsa alhamdulillahi ana samun nasara sosai, zai iya farkawa nan da kwana hudu ko biyar idan zuciyar tasa taɗan samu relief sai dai abu guda ɗaya, duk yanda za’ayi dole ne idan ya farka ya fara sanya ido akan abin da yafi so idan ba hakaba za’a iya samun matsala domin ciwon zuciyar tasa ya taka matakin ƙarshe na rayuwa ko mutuwa?”.
“Karka damu insha Allah zamu San abinyi”.
Doctor ya mike ya fice daga office ɗin domin zuwa duba wasu patients nasa ya barsu nan suna tattaunawa da Anwar.
Mai Martaba ya gyara zama yana mai duban Anwar tare da cewa.
“Anwar…!, Ina so ka bani labari akan yarinyar da Magaji yake so bana so ka ɓoyemin komai dan Allah”.
Fudhal ya gyaɗa kai alamun ya fahimta nan ya kwashe komai tun daga farko har ƙarshe bai ɓoye masa komai ba ya sanarmasa.
Mai Martaba ya da ɗe tsayin wani lokaci yana gyaɗa kai tare da jinjinawa al’amarin jikinsa yayi sanyi ainun.
“Haƙƙina nane innemawa Magaji auren yarinyar da yake so…!”.
Anwar duban Mai Martaba yahauyi baki galala cike da murna da farin ciki amma daya tuna ankusa bikinta sai jikinsa yayi sanyi da ƙyar ya iya ɗaga harshensa ya furta.
“Abba ankusa bikinta fa !, Inajin baifi nan da sati guda ba”.
“Kada ka damu zansan abinyi insha Allah Magaji ne mijinta”.
Anwar yaɗanyi yaƙe kawai tare da sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi yinƙurin sake cewa komai ba.
*7:2pm*
Bayan sallar maghriba misalin ƙarfe bakwai da mintuna biyu Umman Aynu da Babanta suna zaune tsakar gidansu suna hira tare da tattauna yanda zasu tafi da al’amuran bikin ɗiyarta tasu tilo.
Aynu na cikin ɗaki kwance kan tabarma kanta na bisa pillow tayi ruf da ciki kai kace bacci take, amma azahirin gaskiya idonta biyu ba zaka tabbatar da hakan bama sai ka lura da kai hannunta da take kan fuskarta tana share kwallar dake taruwa cikin idonta lokaci zuwa lokaci.
Har cikin ranta bata jin son auren nan nata da za’ayi a cikin ranta ba tajin zata iya rayuwa da kowa idan ba Yarima Fudhal ba.
Sallama suka jiyo ƙofar gida Baban Aynu ya sanya takalmansa ya fita domin ganin mai sallamar.
Dogarawan Sarki Ubaiyd ya gani tsaye bakin ƙofar gidan suka gaisa tare da faɗin.
“Sarki Ubayd na da buƙatar ganinka a dai-dai wannan lokaci”.
“To…! Lafiya dai ko?”.
“Koma dai menene idan kaje za kaji”.
Ɗaya daga cikin su ya bashi amsa, Baban Aynu ya gyaɗa kai tare da faɗin.
“Bari inshiga ciki insanarwa iyalina”.
Yana shiga ciki bai ƙarasa inda Umman take zaune ba yahau faɗin.
“Zanje gidan Sarki yana nemana yanzu zan dawo”.
Tsaye Umma ta miƙe tana faɗin.
“Allah yasa dai lafiya?”.
“Amin bari inje inji”.
Ya fice ya barta nan tsaye, Aynu ta fito da sauri domin jin me yake faruwa?.
Suna tafiya basu tsaya ko ina ba sai ƙofar falon Mai Martaba sukayi sallama ya basu izini su shiga.
Suna sanya ƙafa Baban Aynu sakar baki yayi yana kallon falon tare da aiyana irin dukiyar da aka kashe a ciki, suka sunkuya tare da kwasar gaisuwa Mai martaba dake zaune bisa ɗaya daga cikin kujerun dake falon ya amsa tare da basu umarnin su basu guri, ba musu kowa ya fice falon ya rage daga Baban Aynu sai Mai Martaba kawai.
Gyaran murya Mai Martaba yayi tare da gyara zama kafin ya bude baki ya fara magana.
“Nasan zakaji mamaki sosai da kiranka da nayi a dai-dai wannan lokaci, hakan ta faru ne sabida kafiya da naci irin na yaran zamani”.
Yaɗanyi shiru na wani lokaci kafin ya cigaba da magana.
“Ni Sarki Ubaiyd ɗana yaga iri a gidanka yana so, ina fatan zan samu ?, domin aurar da ‘ya a babban gida irin wannan wane zai ƙi?”.
“Ni zanƙi…!”.
Baban Aynu ya bashi amsa bai jira mai zaice ba ya cigaba da faɗin.
“Iri na anriga anshuka harya fidda kai nan da ranar juma’a mai zuwa za’ayi girbinsa zuwa gidan daya dace da ita damu iyayenta”.
A fusace Mai Martaba ya dubeshi.
“Har ni kamata na nemi alfarma a wajeka ka iya buɗe baki kace a’a…! Da matsayina da mulki na waye kai?, mai kataka?”.
“Ni talaka ne kuma miskini, ban taki komai ba sai alkhairi, kayi hakuri amma bazanyi magana biyu inzamo karamin mutum ba ƴata dai aurenta za’ayi ina roƙawa ɗanka samun wacce ta tawa a wajen Allah na barka lafiya”.
Baban Aynu ya miƙe ya fita daga ɗakin cike da ɓacin rai da takaici, shi kuwa Mai Martaba kasa ko motsi yayi sabida ƙuncin da yake ji a cikin ransa, yau rana ta farko a rayuwarsa ya but buƙaci abu bai samu ba, abin da ko da kuɗi zai siya dukiyarsa bazata taba girgiza ba, amma yau talaka ya shigo gidansa har falonsa ya iya kallon tsabar idonsa ya gaya masa magana.
“Mene ya jawo hakan?”.
“Fudhal Kaine sila…!”.
Yayi maganar a fili tare da miƙewa tsaye ya na faman safa da marwa a cikin falon.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdausy Jeebour.
38
Faram-faram Baban Aynu ya shigo gida fuskarsa babu yabo babu fallasa, amma duk wanda ya sanshi ya kuma san yanayinsa yana ganinsa zai san yana tare da bacin rai.
Umma da Aynu suna zaune inda yabarsu cike da fargaba sai ganinsa sukayi ya faɗo cikin gidan da sauri suka miƙe Umma na tambayar.
“Lafiya Baban Aynu?”.
Neman guri yayi ya zauna suma suka zauna tun da yayi tagumi ya shafe tsayin lokuta kafin ya iya motsa harshensa ya bawa Umma amsar tambayar da tayi masa.
“Akan ƴata har akeson nunamin iko da kudi da mulki, na godewa Allah da yasa bikin kwanaki ƙalilan ya rage da bansan abin da zasu zomin da shi ba”.
Nan dai ya kwashe dukkan abin da ya faru tsakaninsa da Sarki ya sanarmusu, Umma shiru tayi ba tare da ta iya furta komai ba, Aynu kuwa fashewa tayi da kuka tamiƙe da gudu ta shige ɗaki.
***
“Assalamu alaikum barkanku da yamma”.
Anwar ya faɗa a dai-dai lokacin da yayi parking motarsa gefan wani shagon da wasu samari uku suke zaune kan benci.
“Yauwa barka dai”.
Samarin suka amsa cikin haɗa baki.
Anwar ya sake dubansu tare da jefa musu tambaya.
“Dan Allah tambaya nake, gidansu wani ana ce masa Ya Sayyadi Umar a nan layin aka cemin gidansu yake”.
Ɗaya daga cikin samarin dake zaune bakin shagon yaɗan jinjina kai yana mai-maita.
“Ya Sayyadi Umar..! Ko wanda aka bashi wata yarinya Aynu bikin saura sati guda ko?”.
“E shi nake nufi”.
Anwar ya basu amsa.
“To ai gida a can ƙasan layin nan yake zaka ganshi flat mai bluen ƙofa”.
“OK nagode sosai sai anjima”.
Anwar yaja motarsa ya wuce su zuwa inda sukayi masa kwatancen.
Yana parking motar kofar gidan ya fito tare da jingina jikin motar yana waigen neman yaron da zai aika.
Can sai ga wani yaro da bai wuce shekaru bakwai ba ya taho yana gara taya da niyar shiga gidan, Anwar ya tsai da shi yana faɗin.
“Zonan dan Allah”.
Yaron babu musu ya tako zuwa inda Anwar yake tsaye yana faɗin.
“Gani”.
Anwar ya dafa kafaɗar yaron kafin yace.
“Dan Allah idan ka shiga kace ana sallama da Ya Sayyadi Umar”.
Yaron ya amsa da “To”.
Ya juya ya shige cikin gidan.
Ya shafe tsayin mintuna goma kafin yaron ya fito ya bashi amsar.
“Wai yace yana zuwa”.
Anwar yace.
“To nagode zoka karɓa”.
Ya laluba aljihunsa babu chanji sai ɗari biyu ita ya miƙawa yaron fuskarsa cike da murmushina yana faɗin.
“Ga wannan kasayi sweet ko”.
“Nagode sosai”.
Yaron ya faɗa yana mai cigaba da gara tayarsa ya fice daga layin.
Kafin fitowar Ya Sayyadi sai da Anwar ya kuma bata tsayin mintuna goma, can sai gashi ya leƙo yana dube-duben ganin waye ke sallama da shi domin ko kaɗan bai kawo Anwar bane a ransa, dan zai iya cewa ya mance da fuskarsa, sai dai yana tunanin kamar ya taɓa ganinsa.
Ganin haka ne ya sanya Anwar ƙarasawa wajensa da sauri cikin sallama, Ya Sayyadi ya amsa tare da mika masa hannu sukayi musabiha.
Anwar ya buɗe baki a hankali ya fara magana.
“Ni sunana Anwar nasan baka shaida ni ba, amma ni nakasance abokine kuma amini ga Yarima Fudhal”.
Ya Sayyadi ya faɗa ɗa murmushinsa tare da sake bashi hannu suka gaisa yace.
“To mu shiga daga ciki mana?”.
Anwar babu musu yabi bayansa har zuwa cikin ɗakinsa dake soro(zaure), ya bashi guri ya zauna tare da kawo masa ruwa mai sanyi yasha.
“Ya Fudhal ɗin yana lafiya ƙalau ko?”.
“E to lafiya ba lafiya ba, domin yanzuma sanadin halin da yake ciki ne ya kawo ni wajenka”.
Ya Sayyadi ya gyara zama yana faɗin.
“To Allah yasa muji alkhairi ina sauraronka”.
“E to gaskiya bazan iya furta komai ba a halin yanzu alfarma ɗaya zannema a wajenka dan Allah dan Annabi inaso ka bini yanzu zuwa asibiti”.
“Amma mai zamuyi a asibiti kuma?”.
“Babu komai kawai ina sone kaje kaga halin da dan uwanka musulmi yake ciki wato Fudhal”.
“Ban fahimci maganarka ba, wai meke faruwa ne?”.
“Koma mene ka kwantar da hankalinka insha Allah idan mukaje zaka fahimta”.
Ya Sayyadi Umar yayi shiru na wani lokaci yana kallon Anwar kafin yace.
“Shikenan tashi muje”.
Anwar ya miƙe suka fito Ya Sayyadi ya rufo ƙofar ɗakinnasa, ya shiga cikin gidan sukayi sallama da mutanan gidan ya fito zuwa waje, Anwar ya kunna motar suka shiga yaja suka fice daga layin.
Bai yi parking motar a ko ina ba sai cikin harabar asibin a parking space ya kashe motar suka fito, Ya Sayyadi kawai bin Anwar yake a baya tare da ‘yan kalle-kallensa har suka isa wani ɗaki Anwar yasa hannu ya murda murfin ƙofar tare da turawa suka sanya kai zuwa cikin ɗakin.
Durƙusawa sukayi suna gaishe dasu Hajiya da Aunty Sadiya dake zaune cikin ɗakin suka amsa fuskarsu babu yabo babu fallasa tare da bin Ya Sayyadi da kallo domin basu San waye ba sun ɗauka ko abokin Anwar ɗinne.
A tare suka miƙe suka ƙarasa bakin gadon da Yarima Fudhal yake kwance domin yanzu anfito da shi mai makon da, da ake ganinsa ta window.
Ya Sayyadi ya jima yana jero masa addu’o’in samun lafiya kamar yanda Manzo Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar damu cewa.
(Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai yace masa;
لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .
La ba’asa tahoorun in sha’al-lah.
لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .
La ba’asa tahoorun in sha’al-lah.
Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda.
أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)
Asalul-lahal-‘azeem rabbal-‘arshil-‘azeem an yashfeek (7).
Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al’arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
Asalul-lahal-‘azeem rabbal-‘arshil-‘azeem an yashfeek (7).
Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al’arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya faɗi wannan (addu’a) sau bakwai face ya sami lafiya)”.
(Allahu akbar ya Allah kasa mu dace kasa mukasance masu koyi da koyarwar Annabi ka kara mana sonsa da ƙaunarsa Amin).
Ya sayyadi yayi musu sallama ya fito daga ɗakin Anwar ya biyo bayansa.
A zaune ya taddashi kan wani benci a wajen asibitin shima Anwar ya nemi gurin ya zauna.
“Amma har tsawon wanne lokaci ya ɗauka bashi da lafiya ne?”.
Anwar yaɗan dubeshi kaɗan kafin ya bashi amsa.
“Kwana huɗu kenan”.
“Kwana huɗu?, amma kamar yayi shekara akwance, me yake damunsa ne?”.
Ya Sayyadi ya sake jefawa Anwar tambaya.
“Ciwon SO ne”?.
“So kuma?”.
“E mana kana mamaki ne?”.
“A a kawai dai nake ganin kamar akwai ciwon da yaja masa hakan bayan Soyayyar”.
“E yana fama da ciwon zuciya gaskiya Wanda ya takama matakin ƙarshe na rayuwa ko mutuwa”.
“Subhanallahi to a bashi abin da yake so mana”.
Anwar yayi murmushi kaɗan kafin yace.
“Wannan kuma aikin kane, Kaine kake da haƙƙin yin hakan domin abin da ya mutu akan sonsa yana wajenka”.
“Kana nufin Aynu yake so?”.
“E nasan kasan da hakan ai”.
Ya Sayyadi shiru yayi yana kallon Anwar ba tare da ya kuma cewa komai ba, can ya nisa yace.
“Zaka iya mai da ni gida, ko in tafi”.
“A a mai zai hana?, ni na ɗauko ka ai, tashi muje in mai da kai”.
Ya Sayyadi ya miƙe suka taka har zuwa Inda sukai parking motar suka buɗe suka shiga Anwar yaja suka fita daga cikin harabar asibitin.
Suna tafiya akan titi shiru babu mai cewa da wani komai, Anwar ne yaɗan dubi Ya Sayyadi ta gefan ido kafin ya buɗe baki ya fara faɗin.
“Zan roƙi alfarma a gareka nazo na ɗauke kane badon komai ba illa kaga abin da zan faɗa maka da idanunka domin ganin ya kori ji inji bahaushe, yanzu wuƙa da nama suna hannunka nasan cewa Allah ke rayawa kuma shi yake matarwa idan lokacin mutuwar mutum yayi babu Wanda ya isa ya ƙara masa ko second ɗaya, kamar yanda Idan lokacin mutuwar mutum bai yiba babu Wanda ya isa ya kashe shi, amma kasan cewa komai yana da dalilinsa da kuma sila Fudhal baki ɗaya ya ta’allaka rayuwarsa akan Aynu ne rasa Aynu a cikin rayuwarsa kamar Fudhal ya rasa rayuwarsa ne, wallahi Allah shine shaida da kuma ni Fudhal nason Aynu fiye da rayuwarsa a iya sanina da ganina ban tana ganin mutumin dake son abin da yake so kamar Yarima Fudhal ba…!”.
Ya katse maganar dai-dai sanda yayi parking kofar gidannasu, Anwar ya sake duban Ya Sayyadin yana mai cigaba da faɗin.
“Ka taimaki Fudhal dan Allah ka ceto rayuwarsa nasan ka fahimci abin da nake nufi”.
“Zanyi tunanin akan hakan, nagode sosai ka gaida gida Allah ya ƙara masa lafiya”.
Abin da yace kenan ya fice daga motar, Anwar ya amsa da
“Amin” yana mai bin bayansa da kallo, aransa yana addu’ar Allah yasa abin da yake ƙoƙarin yi ya tabbata yasa kuma ya fahimci abin da yake so ya fahimta.
“Amin” yana mai bin bayansa da kallo, aransa yana addu’ar Allah yasa abin da yake ƙoƙarin yi ya tabbata yasa kuma ya fahimci abin da yake so ya fahimta.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:- Namesy Phirdausy Jeebour.
39
***
Al’amarin ciwon Yarima Fudhal da Yarima Jaleel sai dai addu’a ba zaka iya cire guda ba a cikinsu wanda yafi sauƙi.
Yarima Jaleel tsayin sati biyu kenan ya zama kamar wani zautacce sai dai a yi masa allurar bacci data sake shi kuwa inya farka ya dinga sambatu da buge-buge kenan har sai Doctor ya zo ya sake yi masa wata allurar.
Fulani Sokoto ita ce a wajen Yarima Jaleel sai sauran ‘yan aikinta da masu zuwa dubiya.
Fulani Bingel kuwa dukkan yaran gidan sun tare a wajen jinyar Yarima Fudhal duk da cewa suna zuwa dubo Jaleel lokaci zuwa lokaci.
Sarki Ubaiyd baki ɗaya abin duniya ya ishe shi yara biyu, duk suna kwance rai a hannun Allah ! kuma duka waɗanda yake ganin sune magada a bayansa kullum ba shi da aiki Wanda ya wuce tuanani da neman mafita.
Shi kanshi yasan mafita ɗaya ce akan ciwon Fudhal yaje ya nemawa Fudhal auren Aynu amma kash hausawa nacewa (Girman kai rawanin tsiya).
Tsananin girman kai da isa, ba zasu barshi yaje ga wadanda yake ganin su maƙas-ƙantane a gareshi ba.
Tsananin girman kai da isa, ba zasu barshi yaje ga wadanda yake ganin su maƙas-ƙantane a gareshi ba.
“Wai Hajiya Mai Martaba ba shi da wani na gaba da shi ne?”.
Anwar dake zaune gaban Fulani Bingel yake tambayarta.
“Akwai mana !, Amma me yasa kake tambaya?”.
“E to gani nayi gaskiya ya kamata a san abinyi tun da wuri, yanzu haka zamu zuba ido akan ciwon Magaji ne?”.
Fulani Bingel tayi shiru tsayin lokaci kafin ta buƊe baki ta bashi amsar tambayarsa.
“Kayi gaskiya Anwar amma sai dai banajin Magaji Saif zai yarda yazo nan garin har yayiwa ƙaninsa sarki Ubaiyd wata magana mai daɗi”.
“Waye Magaji Saif kuma?”.
Suka haɗa baki dukansu wajen tambayar Mahaifiyartasu domin tun farkon tambayar da Anwar yayi mata suka mai da hankali kacokan a kan Fulani Bingel.
“Magaji Saif yaya ne ga Mahaifinku Uwa ɗaya Uba ɗaya, sai dai abin da ya shiga tsakaninsu tsayin shekaru shine yayi sanadiyyar raba zumuncin dake tsakanin Mahaifannaku.
“Mene ya shiga tsakaninsu Hajiya?”.
Wannan karon Aunty Sadiya ce tayi tambayar.
Ajiyar zuciya Fulani tayi kaɗan kafin ta fara magana.
*MUSAB-BABIN GABARSU*
“Abin da ya haddasa gaba tsakanin Mahaifannaku akan abu biyu ne na farko nice na biyu kuma al’amarin sarauta ne”.
“Ni ‘yar asalin garin Bingel ce haifaffiyar can wata rana Mahaifinku da Yayansa sun ziyarci garin namu tare da iyayensu domin halartar ɗaurin auren ɗan sarkin garin wato Yayana, a wannan lokaci ne a cikin hidimar bikin muka fara haɗuwa da Mahaifinku ya baiyanamin abin da ke ƙarƙashin zuciyarsa da sunan yana sona, duk da ban amince ba car lokacin sabida kunya amma washe garin ranar na baiyanawa ƙawata kuma ta sameshi ta bashi amarsa”.
“A ranar ne kuma Yayansa shima yazo min da irin batun da Mahaifinku yazo min da shi, sai dai ban amince ba anan take na baiyana masa cewa ni Ubaiyd nake so, tun a wannan lokaci faɗa ya fara shiga tsakaninsu saɓanin da ayanda suke Mahaifannaku suna son junansu tare da girmama tsakaninsu haka kuma Mahaifinku yanajin maganar Yayansa”.
“Yazo masa da batun cewa sai dai ya haƙura ya bar masa ni ai shine gaba da shi, shi kuma yace bazai yiyu ba hakan ne ya haddasa faɗa atsakaninsu har suka koma gida babu mai yiwa wani magana domin Magaji Saif yafi Sarki Ubaiyd tsananin fushi da zuciya”.
“Ana cikin wannan hatsaniyarne kuma Kakanku ya kwanta ciwon ajali cikin kwanaki biyu yace ga garinku nan, lokacin munzo gaisuwa a ranar majalisa ta zauna domin tan-tance wanda zai zamo Magaji a tsakaninsu , Magaji Saif yayi magana kan cewa”.
“Indai shine za’a bawa sarauta to dole ne Sarki Ubaiyd ya haƙura da aure na ya barmasa ko kuma ya fita yabar garin, shi kuma Mahaifinku yace bazai yarda ba ananma sai da sukayi faɗa haka aka tashi ba tare da samun mafita ba”.
“Sai dai kuma abin da kowa bai sani ba a daren ‘yan majalisa sun sake zama domin kwance wannan ƙullin dake tsakanin iyayenku sunyi shawara kancewa Mahaifinku za’a bawa sarauta tare da aurena inyaso Magaji Saif a bashi waziri domin gudun matsala sabida sun San muddun suka bawa Magaji Saif sarauta duk yanda zasu so bazasu iya hanashi muzanta Sarki Ubaiyd ba, domin irin kalaman da yayi sun San zai aikata fin haka dan baya magana ya sake ta, shi kaifi ɗaya ne koda kuwa zai rasa ransa”.
“A washe garin ranar aka haɗa aurena da Mahaifinku tare da naɗin sarauta da kuma sadakar ukun Kakan ku, nan take Magaji Saif yace baya son wazircin kuma daga ranar Shiba haifaf-fan garin nan ba ne, kada Wanda yace ma ya taɓa saninsa a duniya daga nan ya fice yabar garin bamu sake jin labarin saba sai lokacin da aka fara maganar batun auren Magaji da Gimbiya Safiyya mukaji cewar yana zaune a Sokoto”.
Shiru ɗakin ya dauka tsayin daƙiƙu masu yawa kafin Anwar ya nisa yana mai faɗin.
“Insha Allahu zamu sami nasara, zanje innemeshi zai dawo gida cikin farin ciki kuma zasu manta gabar da suke da yardar Allah”.
“Allah yasa ya ɗora ka akansa, domin shi kaɗai ne nake ganin a duniya Wanda zai iya sanya Sarki Ubaiyd yayi, kuma shine kaɗai zai iya hanashi ya hanu, sai dai kuma meye fa’idar sako shi a zancen?”.
Anwar yaɗanyi murmushi.
“Hajiya kenan kin mance yau saura 2days ayi bikin Aynu kuma duk yanda naso Mai Martaba yaje ya roƙesu yaƙi, duk wata hanya da zanbi insawa Fudhal farin ciki nabi amma babu nasara sai dai inaji a raina wannan ce kaɗai nasararmu in Allah yaso”.
Fulani Bingel ta murmusa tare da faɗin.
“Allah yayi maka albarka Anwar ya baka abin da kake so duniya da lahira lallai ka cika aboki kuma amini na gari Ubangiji ne kaɗai zai iya yi maka sakaiya akan abin alkhairin da kake aikatawa domin mu kuwa bamu da abin da zamu saka maka”.
“Hajiya kibar faɗin haka ai Fudhal a guna dan uwane na jini zan iyayin abin da yafi hakama akansa kedai kawai ki tayani da addu’a”.
“Insha Allahu kada ka damu da wannan”.
Anwar ya sanya kai ya fita daga ɗakin yayin da suka biyoshi dukkanninsu da addu’ar fatan alkhairi.
****
Tun ranar da Ya Sayyadi Umar yaje ya dubo Yarima Fudhal ya dawo baki daya ya gaza samun nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare da shi, ji yake kamar yana shirin aikata bab-ban kuskure ne tare dayin aikin dana sani, sai dai ƙasan zuciyarta na tausarsa da cewa shimafa yana sonta taya zai iya haƙura ya bawa wani?.
Hakan yasa yake samun ƙwarin gwiwa tare daji aransa bazai taɓa iyayin SADAKAR SOYAYYA ba.
Shi kaɗaine a motarsa yake driven yayin da ya sanya kira’ar sudais a motar yana tuƙi yana bi hankalinsa kwance kai kace babu abin da yake damunsa a duniya, sai dai ƙasan zuciyarta cunkuce take da tarin damuwa da tunanin abin da zaije ya tarad duk da cewa yana yiwa kansa fatan alkhairi tare da saran samun nasara domin yasan aikin alkhairi yake shirin aikatawa bare kuma al’amari na zumunci Allah zai bashi nasara.
Ko da ya isa cikin Sokoto birnin shehu ya shafe tsayin a wanni hudu yana fafutuwar neman Magaji Saif kafin Allah ya haɗashi da wani al’amajiri mai wanki da guga shine yace ya sanshi ai shi yake bawa wanki da guga duk sati, gidansa a can (kalan baina) yake yazo suje ya rakashi.
Haka suka tafi yaron na nunawa Anwar hanya shi kuma yana bi har zuwa bakin gate ɗin wani tamfatse-tsen gida sukayi hon gateman ya buɗe ƙofar wangagememan gate din gidan suka sanya kai.
Almajirin yace wa Mai gadi ya sanarwa Alhaji yayi baƙo, ba musu Mai gadin ya wuce cikin gidan da sauri domin sanarwa ahaji dake yasan almajirin sosai, mintuna kaɗan sai gashi ya dawo tare da amsar su shiga yana jiransu.
Su Anwar suka sanya kai zuwa cikin gidan, shi dai Anwar kallon gidan kawai yake domin yasan ko a turai da yayi karatu bai taɓa ganin gida mai girma da haɗuwa kamar wannan gidan ba, faɗin haduwar gidanma ƙauyanci ne sai dai masu karatu ku ƙiyassata a cikin ranku.
Yana zaune falo kan wata luntsumemiyar kujera ‘yar ubansu shaddar dake sanye jikinsa ita kanta kukan kuɗi take bare kuma azo batun takalmi da hula zuwa uwa uba agogon hannunsa, yana zaune a hannunsa kuma news paper ce yake karanta sukayi sallama ya ɗago kai cike da fara’a yana mai amsa musu.
Tsan-tsan kamar Sarki Ubaiyd da Anwar yagani a tare da fuskar Magaji Saif shine abin da ya daure masa kai ainun ya kuma tabbatar tabbas wannan shine Magaji Saif yayan Sarki Ubaiyd.
Suka gaisa Anwar yayiwa almajirin godiya tare da alkhairi mai yawa ya tashi ya tafi.
Yana fita Magaji Saif yabi Anwar da kallo yana faɗin.
“Sai dai ban shaida fuskarka ba, ko zaka iya yimin bayanin waye kai?, mene kuma ya kawoka gidan nan?”.
Anwar yayi murmushi kafin yace.
“Abu mai sauƙi dama hakance ta kawo ni”.
Nan take Anwar ya fara bashi amsar tambayarsa dalla-dalla tare da faɗin abin da ya kawoshi da kuma dalilin zuwansa.
Magaji Saif ya haɗe girar sama data ƙasa tamkar bashi ne yake murmushi ba yanzu sai kace an aiko masa da saƙon mutuwarsa haka ya miƙe tsaye yana mai mid zuwa wajen Anwar tuni hantar cikin Anwar tahau kaɗawa tsoro ya ziyarceshi take ya fara karanto addu’a cikin ransa domin ya gama hasko irin cin mutunci da tozarcin da zai fuskanta yau a hannun Magaji Saif.
KOMA DAI MENENE KU BIYO NI……..! Smile kuna raina fa.
Nagode sosai da sosai da ɗunbin tarin addu’arku a agare ni Allah ya biyaku amin.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITWRS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY PHURDAUSY JEEBOUR.
40
Ganin yanda Magaji Saif yake nufoshi, shine yayi sanadiyyar miƙewarsa tsaye a kasalance suna duban juna ido da ido amma duk da hakan Anwar baiyi ƙasa a gwiwa wajen cigaba da karonta addu’o’i ba a cikin ransa.
Har sai da Magaji Saif yazo daf da Anwar suka shafe tsayin lokuta suna kallon juna ko wannensu da abin da yake saƙawa cikin a cikin ransa.
Sai dai abin da Anwar yaga Magaji Saif ya aikata ne yayi sanadiyyar tsayawar wayoyen jikinsa da dena aiki take lantarkin dake sarrafasu ta ɗauke, murza ido ya hauyi domin tabbatarwa gaske ne ko a mafarki ne?, Magaji Saif ya rungume shi har yana ɗan bubbuga bayansa…!.
Maganar Magaji Saif ita tayi sanadiyyar dai-daituwar kwakwalwarsa.
“Tabbas munyi kuskure a rayuwa nayi nadama bayan wani lokaci, ka sani yau tsayin shekaru ina zaman jirar ranar da zanga wani ya zo nemana, sai gashi Allah ya amsa roƙona a yau lallai dole inyi farin ciki tare da godewa Allah a yau ɗinnan”.
Anwar dai sosoko yayi yana sauraransa, Magaji Saif ya janye jikinsa daga na Anwar fuskarsa cike da murmushi haɗe da hawayen farin ciki, ya cigaba da kallon fuskar Anwar.
Anwar yaɗanyi gyaran murya tare da buɗe baki ya fara magana.
“Amma mai yasa baka je ka nemi ahalinka ba tare da neman gafararsu tasayin wannan lokaci ka zauna sai dai a zo a nemeka, ko kasan cewar Mahaifiyarku ta rasu?”.
“Na sani…!”
Jin amsar daya bayar ya sanya Anwar sakar baki yana dubansa, Magaji Saif yayi murmushi tare da kama hannun Anwar ya zaunar da shi kan kujera shima ya koma Inda yake da ya zauna tsayin da ƙiƙu yana ƙarewa Anwar kallo kafin ya ci gaba da magana.
“Ina gudun wulakanci da tozarci ne shine yasa naƙi baiyana kaina a wajen ƙanina amma batun jana’idar Hajiyarmu tare dani akai hatta zaman makoki nayi dukkan wani motsi na gidan babu Wanda ban sani ba, sai dai abubuwa da yawa suna ɗauremin kai akan Ubaiyd”.
Yaɗan ja numfashi kaɗan.
“Yaushe ne Ubaiyd yazama azzalumin sarki?, taya akai ya zama mai girman kai da izgili? tarbiyar iyayenmu babu wulakantar da ɗan adam, amma ina mamakin yanda akai Ubaiyd ya koyi wasu irin munanan halaye ya sanyawa kansa alhali nasan a da ba haka yake ba, ko kuma Sarautace ta koyamai hakan?”.
Duk wannan tambayoyin da yake jerewa Anwar kawai kallonsa yake yana kuma sauraronsa.
“A sanda nabar gida na tafi ne tare da burin komai daren daɗewa sai na gaji mahaifinmu nayi sarauta, amma akan Ubaiyd naji na tsani sarauta indai haka sarauta take mai da mutum mai munanan halaye bazan taɓa addu’ar Allah ya sake bawa wani jinina ba kai ko barema domin wannan halayen sune matsayin kuɗin siyan wutar jahannama sune za suyi sanadiyyar sayar mana fushin Allah da Manzonsa…! UBAIYD.! UBAIYD..! UBAIYD…! Me yasa haka?, me yasa?”.
Ya kai maganar cike da ƙaraji yana huci harda bugun centre table ɗin dake gabansa.
“Kayi hakuri Abba, amma nake ganin babu abin da yake sayawa ɗan Adam munanan halaye sai dai idan dama can halinsa ne dake ɓoye cikin ransa to idan mutum ya samu wata dama ko wani muƙami sai hakan ya dinga bashi ƙarfin gwiwar aikatawa tunda yana tunanin babu Wanda ya isa ya hanashi bare a taka masa burki”.
Magaji Saif kai ya gyaɗa yana faɗin.
“Haka ne maganarka kayi gaskiya Anwar, yanzu ya jikin Fudhal?”.
“Alhamdulillahi Abba”.
“Masha Allah sai ka kwana anan zuwa gobe da safe idan Allah ya kaimu zan nemi hutu a in da nake aiki sai mu tafi can ɗin”.
“OK Allah ya kaimu”.
Anwar ya faɗa yana mai ƙarewa falon kallo duk hotunan Magaji Saif ne cike a falon ya baza ido iya bazawa baiga hoton ɗa ba bare na wata mace.
“Abba nace Yaran gidan sunyi tafiya ne?”.
Anwar yayi tambayar dai-dai sanda Magaji Saif ya isa wajen freezer domin kawo wa Anwar ɗan lemo.
Magaji Saif yayi murmushi kawai ya ɗauko juice na kwali da cofi ya kawo gaban Anwar ya a jiye yana maganar.
“Babu kowa a gidan nan babu mace taya za’a samu yara?, daga ni sai kukuna sai mai gadi mukenan a gidan”.
“Matarka mutuwa tayi ne Abba?”.
Magaji Saif ya girgiza kai yana duban fuskar Anwar har lokacin murmushin dake kan fuskarsa bai ɗauke ba.
“Ban taɓa aure ba Anwar amma a kullum ina son yi, yanzu ga ɗaki can ka shiga kayi wanka ka huta anjima ka fito daining ni zan shiga ciki”.
Ya miƙe yahau saman bene yabar Anwar nan zaune yana jujjuya maganar Magaji Saif.
“Ban taɓa aure ba Anwar amma a kullum ina son yi..!”.
Ya sake mai-maita maganar.
“To amma mai yahanashi yi?, duk da gashi bai rasa komai ba a duniya, ko da yake aure nufi ne na Allah”.
Yayi tambayarsa ya bawa kansa amsa.
Juice ɗin ya buɗe ya zuba a cofin yaɗan sha kaɗan kafin ya miƙe ya nufi ɗakin da Magaji Saif ya nuna masa.
Ɗakin komai akwai ciki hakan ba ƙaramin daɗi da mamaki yayiwa Anwar ba, kayansa ya cire ya faɗa toilet domin yin wanka.
Yana fitowa dama yayo alwala da yake lokacin sallar maghriba yayi ya sanya jallabiya yayi sallah yana idarwa ya jawo wayarsa yahau neman number Hajiyarsu Fudhal.
Kira ɗaya ta aga tare da sallama, Anwar ya amsa yana faɗin.
“Na samu gidansa Hajiya goben nan zamu taho tare da shi”.
“Kana nufin kace ka sanar dashi komai amma ya yarda zai biyoka cikin sauƙi haka?”.
“Hajiya kenan kin manta da ƙarfin fauwalawa Allah komai da addu’a kuma?”.
“Hakane Allah ya kaimu goben lafiya muna zaman jiranku Allah ya kawo ku lafiya”.
“Amin Hajiya ya jikin Fudhal fa?”.
“Da sauƙi Anwar yau dai ansamu ya iya motsa yatsun hannunsa dana kafa amma bai buɗe ido ba”.
“Kai..Amma naji daɗi wallahi idon ma da yardar Allah zai buɗe Allah ya ƙara lafiya”.
“Amin ya Allah sai da safe”.
Suka kashe wayar a tare yana ajiye wayar akayi knocking ya amsa a shigo.
Wani saurayi ya leƙo yana faɗin.
“Komai ready Yallaɓai na jiranka a daining”.
“OK ganinan”.
Saurayin na juyawa Anwar ya biyo bayansa.
Daining cike taf da abinci kala-kala haka suka ci suka ƙoshi sunayi suna hira jefi-jefi duka hiran akan Yarima Fudhal ne.
Magaji Saif yayi murmushi yana faɗin.
“Shi kuma sai da yaje ya ɗebo wannan zafin ran na banza ko?”.
Anwar shima murmushin yayi ba tare da yace komai ba, suna gamawa Magaji Saif yayiwa Anwar sai da safe ya hau sama, shima Anwar ɗin bai wani zauna ba ya koma aki ya ɗan huta domin ya gaji.
*WASHE GARIN RANAR DA SAFE*
Hayaniyar ce tayi sanadiyyar ta shinsa daga baccin, yana buɗe ido yaga ashe gari ya waye time ɗin 8:20, dafe kai yayi tare da miƙewa daga kan gadon ya zuro ƙafarsa ya sauko ya nufi bakin windown ɗakin dan ganin hayaniyar tame ce take tashi haka?.
Jama’a ya gani cikin harabar gidan damƙam, Magaji Saif na zaune kan kujera gefansa kuma buhu ne na kuɗi sai kayan abinci katan-katan na taliya da makaroni indomie da couscous ga kuma manyan buhunan shinkafa nan ajiye yana ta rabawa mutanan Anwar abin ya ƙara ɗaure masa kai ya shafe tsayin lokuta yana kallo kafin ya shige toilet yayi wanka ya fito ya shirya ya fita daining ya tadda komai is ready yayi breakfast.
ya koma ɗaki ya duba ta window yaga babu kowa kamar anyi shara maganar da yaji ne ta bayansa yasa shi juyawa da sauri murmushi sukayi a tare Anwar ya durƙusa ya gaishe shi ya amsa tare da shafa kansa yana faɗin.
ya koma ɗaki ya duba ta window yaga babu kowa kamar anyi shara maganar da yaji ne ta bayansa yasa shi juyawa da sauri murmushi sukayi a tare Anwar ya durƙusa ya gaishe shi ya amsa tare da shafa kansa yana faɗin.
“Harka tashi ka shirya?”.
“E nagama komai, Amma Abba zakka kayi ne?”.
“A a alƙawari na cika”.
“Alƙawari kuma na me fa?”.
“Duk ranar da Allah ya kawo wani nawa na alƙawaranta cewa zanyi sadaka ta musamman domin nuna godiya ga Allah”.
Anwar yayi murmushi tare da jin daɗin kyawawan halayen Magaji Saif har yana rayawa a cikin ransa dama ace shine ya haifi Yarima Fudhal.
Helloooo…!
Kuyi hkr da wannan sai gobe idan Allah yakaimu da rai da lafiya zaku jini insha Allah.
Byeee