NOVELSUncategorized

YARIMA FUDHAL 46-END

*YARIMA FUDHAL*
NA
FIRDAUSY S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
46

Nacin duniyar nan Yarima Fudhal yayi amma Aunty Sadiya tace bata san zancen ba, a kan dole suka tattara suka bar gidan ba tare daya samu ganin Aynu ba zuciyarsa ta cika fam da haushi.
Hakan yasa duk surutun da Anwar ke tayi masa a mota bai kulashi ba domin sosai yau haushin kowama yake ji gani yake kamar ba sonsa suke ba.
Har suka isa gida Yarima Fudhal bai kula Anwar ba haka Anwar ɗin yayi masa sallama ya wuce gida domin shi al’amarin Fudhal ma dariya yake bashi, idan yana abu wani time ɗin sai kaga kamar wani ƙaramin yaron goye.
Anwar na fita Yarima Fudhal ya rage kayan jikinsa ya shige toilet domin watsa ruwa sabida wani irin zafi da yake ji a lokacin, daya fito kaya ya nema marasa nauyi ya saka ya fice daga part ɗinsu zuwa part ɗin Hajiyarsu wato Fulani Bingel.
Da sallamarsa ya shiga falon babu kowa ciki illa Hajiyartasu dake zaune tana kallon tashar Zee world, ta jiyo cikin fara’a tana amsa masa sallamar.
Yarima Fudhal ya ƙarasa inda take zaune ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafuwanta yana faɗin.
“Barka da dare Hajiya?”.
“Muna lafiya, ya ƙarin ƙarfin jikin naka?”.
“Alhamdulillahi”.
“Masha Allah..!, Ina kaje ne na shiga wajen naka baka nan?”.
“E munɗan fita nida Anwar ne”.
“Fita kuma?, daga fitowarka daga asibitin haka FUDHAL ai ka bari kaɗan ƙara murmurewa ko?”.
Fudhal murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya mai da kansa kan TV yana kalla, amma a zahiri ba kallon yake ba baki ɗaya tunaninsa ya tafi akan neman mafita wajen ganin Aynu.
Can dai ya motsa ya dubi Hajiyar wadda itama shi take kallo domin tun shigowarsa taga alamun akwai abin da yake son faɗi amma kuma ya kasa furtawa.
Hajiya tace.
“Yadai Magaji akwai wata matsala ne?”.
Yarima Fudhal ya gyara zama yace.
“Ammmm..dama..dama”.
“Kayi magana mana inajinka”.
Yarima Fudhal ya ɗan dubi Hajiya yau baki ɗaya wata irin kunyarta yake ji haɗe da jin nauyinta amma haka ya daure ya sake buɗe bakin yace.
“Kan maganar Aynu ce Hajiya, naje gidan Aunty Sadiya tace wai…!”.
Sai kuma yayi shiru ba tare daya iya ƙarasawa ba, Hajiya tayi murmushinsu na manya tace.
“E nasan abin da kake son cewa, kayi haƙuri har zuwa sanda aka yanke kaji?”.
Yarima Fudhal ya gyaɗa kai kawai ba tare daya iya cewa komai ba, domin bai zaci wannan amsar daga bakin Hajiyartasa ba.
Haka yayi mata sallama ya koma part ɗinsu ranar ko kaɗan kasa cin abinci yayi sabida shi gani yake tamkar gidan Aunty Sadiya babu tsaro za’a iya zuwa a ɗauke masa Aynu.
***
RANA BATA ƘARYA…!.
Cikin satin nan kullum sai Fudhal yaje gidan Aunty Sadiya amma Allah bai sanya idanuwansa sunga Aynu ba ko da sau ɗaya, gani yakema kamar kawai faɗa akayi Aynu bata gidan.
Rana ɗayane suka kusan haɗuwa.
Ana ijibi ɗaurin auren su jaleel ranar ta shiga kitchen ɗin Aunty Sadiya domin ta ɗora ruwan wanka sun ɗauke nepa tana ɗorawa shi kuma ya shigo kitchen ɗin neman cofi.
Inda Allah ya taimake ta tayi saurin tsugunawa dake irin kitchen ɗin nan ne mai kanta a tsakiya, kuma bai wani tsaya dube-dube ba yana ɗauka ya fice.
Ranar kusan awanta uku a kitchen tana jira ya tafi har sai da Allah ya taimaketa akayi masa waya ya tashi ya fice daga falon aikuwa da gudu ta ɗauko ruwan zafin ta shige ɗaki domin itama bala’in nauyinsa takeji gani take ba zata iya haɗa ido da shi ba.
RANAR JUMA’A DA MISALIN 2:00.
Bayan saukowa daga masallaci aka d’aura auren.
JALEEL DA GIMBIYA SAFIYYA
ANWAR DA SAIMA.
Ɗaurin auren yayi jama’a sosai, Fudhal tamkar shine aka ɗaurawa auren a lokacin, shigarsu iri ɗaya sukayi dukansu su ukun bluen yadi wanda yasha aiki irin na sarauta.
Daka kallesu dole su birgeka hardai Fudhal da Jaleel dasu ke matuƙar kama tamkar ƴan biyu ga kayan ya amshesu sosai duk da shima Anwar ɗin ba baya ba wajen kyau da haiba.
Da dare aka fara hayaniyar kai amare gidajensu, Jaleel da Fudhal dama tuni an gyare musu part ɗinsu nanne za’a kawo musu amaren, Anwar shi kuwa gida ya gina guda acan ƙasan layin gidansu gidane mai kyau da tsari.
Sai da aka ɗauko amaryar Anwar aka kaita gidanta sannan aka wuce ɗaukan nasu Fudhal mutane kaso uku aka rabu wasu suka tafi ɗaukan amaryar Fudhal wasu kuma ɗauko ta Jaleel domin ta baro sokoto tana nan gidan Yayan Babanta, sai kuma wasu suka tafi kai amarya Jalilah wadda tasha kwalliya da alkyabba sai buga kamshi take.
Gidan da Magaji Saif ya danƙawa Mallam Umar nanne aka kai Jalilah gidan sosai ya haɗu dai-dai zaman mutum ɗaya.
Fulani Sokoto ranar tayi kuka mutane sun ɗauka kodan rabuwa da ɗiyarta ta ne, amma a zahiri ba hakan ba ne baƙin ciki ne kawai ace wai ƴarta kamar Jalilah itace yau za’a kai gidan wani baƙirin mutum kuma malamin islamiyya da bai aje komai ba bare ya bayar.
Babu yanda ba tayi da Jalilah ba akan tace bata so amma ƙememe Jalilah ta to she kunnuwanta akan taji ta gani zatayi biyayya ga mahaifanta domin ita yanzu ba zata ce bata son mahaifitarta ba sai dai baki ɗaya halayenta sun cire mata arai, gashi bata da bakin maganar da zata iya yi mata maganar da dazata fahimta.
Sai dai kullum tazo ta ƙaraci bambamin faɗanta ta fita, amma Jalilah bata taɓa zuwa tayiwa Mai Martaba zancen Mallam Umar ba tun ranar da suka kirata suka sanar da ita anɗaura mata aure ko kan bata ji wani ciwon a ranta ba, addu’ama ta dingayi Allah yasa mijin ya sota itama ta soshi suyi zaman lafiya da amana sosai Mai martaba da Magaji Saif sunji daɗin biyayyar Jalilah akansu musamman Magaji Saif da kokaɗan baiyi tunanin hakan ba.
To taya kuma yanzu tashi ɗaya zataje tace musu bata so?, bayan sun bata dukkan nin yardarsu da amincewarta.
DARE
9:30.
Misalin ƙarfe tara da rabi na dare aka kawo amaren gidan Sarki Ubaiyd, Gimbiya Safiyya da Aynu tuni gidan ya rincaɓe da guɗar ƴan kawo amare sai kusan 11 dai-dai sannan kowa ya watse aka bar Amare da ƙawayensu kawai.
A dai-dai lokacin ne angwaye sukayi sallama abokan Yarima Fudhal suka rakashi part ɗin sa na Jaleel ma sukayi part ɗin Jaleel.
Zee na idar da sallah sukayi sallama tayi maza ta naɗe shinfiɗar tana tsokanar wani Mukhtar abokin Fudhal dake ta san shi sosai.
Shi kuwa gogan naka sai faman kwaɗa murmushi yake idanuwansa kafe kan Aynu dake zaune tsakiyar gado kanta lulluɓe da mayafi.
Nan dai akayi siyan baki cikin raha da nishaɗi tare da yi musu nasiha angwaye sukayi musu sallama suka tafi tare da ƙawaye amarya Aynu tariƙe hannun Zee ƙam wai a dole ba zata tafi ta barta ba da ƙyar ta lallaɓeta ta fizge hannun suka tafi.
Haka suma sauran angwaye anyi siyan baki lafiya kowannensu angwayen sunyi musu nasiha sosai mai ratsa jiki kafin kowa ya watse dakin ya rage sai amarya da ango kawai.
Suna fita Yarima Fudhal ya matso inda Aynu ke zaune suna fuskantar juna yasa hannu ya janye mayafin dake kanta fuskarta ta baiyana a fili sai yaga Aynun kamar ba wadda ya sani ba.
Sosai yau kyawunta ya fito fiye da koyaushe duk da ruwan hawaye dake kan kuncinta sai yaga hakan ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba ga kuma uwa uba kamshin turarenta daketa dokar masa hanci.
Tattausan hannunsa yasan ya ya ɗago fuskarta suna kallon juna Aynu ce tayi saurin sauke kai ƙasa yayin da hawaye ya cigaba da bin kuncinta.
Hannu yasa ya sake ɗago fuskarta akaro na biyu yana mai share mata hawayen yace.
“Mene na kuka kuma, ko bakya farin ciki da wannan ranar ne?”.
Aynu shiru tayi kawai ganin bata da niyar bashi amsa yasa shi faɗin.
“Kina da alwala?”.
Kai ta gyaɗa alamun E amma acan ƙasan zuciyarta fargaba ce fal ciki.
Yarima Fudhal ya miƙe tare da cire babbar rigar dake jikinsa ya shige toilet mintuna kaɗan sai gashi ya dawo jikinsa duk ruwa da alamun alwala yayi.
Ya buɗe wardrobe ya ɗauko abin sallah ya shimfiɗa sanann ya sake buɗe wani murfin jikin wardrobe ɗin ya ɗauko mata hijab ya miƙa mata Aynu ta karɓa cike da mamakin hijab ɗin waye ya bata?.
Shi yayi musu limanci suna idarwa Yarima Fudhal ya shafe tsayin lokaci yana addu’a kafin yayi sallama ya kama kanta yayi mata addu’a sosai sannan ya dubeta ya fara yi mata tambayoyi akan addininta kamar yanda yazo a koyarwar addinin musulunci, tana bashi amsa dai-dai da abin da ta sani.
Sosai Yarima yaji daɗin yanda Aynu tasan addini domin shi a rayuwarsa yana son mutum wanda ya san addininsa bare kuma matarsa uwar ƴaƴansa.
Suna gamawa yajawo ledar dake gabansa ya buɗe da ƙwalan kajini kwala-kwala guda biyu aciki sai Freeshyo manya-manya suma guda biyu gefe guda kuma kilishi ne sai tashin kamshi yake.
Yarima Fudhal ya miƙe ya fito zuwa falo kai tsaye kitchen ya nufa ya ɗauko musu plat da kofuna ya dawo, da kanshi ya zuba musu freesh ɗin ya juye kilushin a plat tare da kazar.
Ya yago yakai mata bakinta takau da kai, sai da taga ya ɓata rai sannan takarɓa tana ci a hankali sosai yanda take cin kazar ya tafi da imaninsa ya shagala a kallonta, sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan shima yaci yana gamawa ya kwashe komai ya kai kichen.
Yanda ya barta haka ya tadda ita murmushi yayi kawai ya nufi wardrobe ya ɗauko wata sleepingdress ya miƙa mata ya juya yahau cire kayansa Aynu ta ɗauke kanta da sauri yayi murmushi domin yana kallonta.
Toilet ya faɗa da dukkan nin alamu wanka zaiyi Aynu najin ya shiga tayi maza ta cire kayanta ta ɗauki rigar zaya saka taganta guntuwa iya gwiwa gata shara-shara tsaki tayi aranta tana faɗin bazata iya sawa ba.
Ajiyeta tayi gefe ta mai da kayanta ta koma can ƙarshen gado ta kwanta tare da lullubɓe jikinta da bargo.
Ko da yafito yaga rigar a gefe kallonta ya tsayayi kawai sai kuma yaga ashe tayi bacci dariya ya ɗanyi mai sauti ya ƙarasa jikin mirrow ya shafa mai tare da feshe jikinsa da tuararuwa sannan shima ya ɗauki wani boxer nasa ya saka yahaye gefan gadon ya kwanta tare da janyo Aynu.
Firgigit ta farka Jin antaɓata yanda ta farka ya bashi dariya sosai amma ya kanne yana faɗin.
“Ki rage kayan jikin ki zakifi jindadin baccin zafi ake fa”.
Aynu ta takura waje ɗaya kawai tana sauraronsa murmushi ya sakeyi tare da matsawa inda take ya dafa kafaɗarta da hannu biyu yace.
“Duk wannan tsoron na meye?, ki kwantar da hankalinki babu abin da zanyi miki wallahi kin yarda da ni?”.
Aynu ta gyaɗa kai alamun E.
“OK idan Kin yarda dani da gaske jeki canja kayan naki, idan kuma rigar batayi miki ba ki duba cikin wardrobe ki ɗauki wata duk kayanki ne cike kinji?”.
“To”
Abin da tace kenan tana mai saukowa daga kan gadon Yarima Fudhal yabita da kallo, shi yanda take nuna jin tsoransa ma dariya yake bashi sosai.
*YARIMA FUDHAL*
NA
QURRATUL-AYN.
NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION®.
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
47
Wardrobe ɗin ta buɗe ta dubo wata riga mai ɗan dama-dama ta shige toilet ta saka sai kuma ta kasa fitowa hakan yasa ta ɗaura zaninta akai tare da yafo mayafinta ta fito a hankali ta koma gadon ta kwanta dan tunaninta yayi bacci domin ta ɓata tsayin lokaci a toilet ɗin kafin ta fito.
Shi kuwa yana jinta yana kuma kallonta duk da duhun dake ɗakin dariyarsa kawai yake ciki-ciki.
7:00am
Bata tashi farkawa ba sai ƙarfe bakwai dai-dai da a gogon ɗakin ya buga ta buɗe ido taga haske garin miƙa tayi tare da salati ta ganta lulluɓe da bargo daga ita sai rigar baccin data saka kanta ko ɗan kwali babu bare kuma zanin data san ta ɗaura akan rigar da mayafin data naɗe kanta dashi damm gabanta ya faɗi ta dafe kai tare da salati.
Miƙewa tayi da sauri ta ziro ƙafafuwansa ƙasa ta zauna bakin gadon tana sauraron taji ko yana toilet, jin shirun da taji yayi yawa ya sata miƙewa ta nufi bakin toilet ɗin da niyar bugawa sai kuma taga ƙofar ta buɗe ta leƙa taga babu kowa ajiyar zuciya tayi tana mai cigaba da tunanin abin da ya faru jiya amma ta gaza tuna komai tun daga kwanciyarta kan gado bacci ya ɗauketa bata tuna komai bayan nan.
Ganin tana ɓata lokaci da yawa ya sata shigewa toilet ɗin domin yin wanka tare da alwala.
Ko da ta fito sai gani tayi an yaye zanin gadon an bar shimfiɗar haka ta taka zuwa bakin gadon cike da mamaki jin hayaniyar da tayi a bakin ƙofar dakin ya sanyawata juyawa da sauri.
Su Larai ta gani su uku tsaye bakin ƙofar suna wani cika da batsewa batayi aune ba sai ji tayi sunja hannunta sunyi waje da ita tana turjewa tana komai, bata tashi ganinta ako ina ba sai filin tsakar gidan tana ɗaga idonta ta ganta tsakiyar mutanen gidan kowa na kallonta tayi saurin takure jikinta sabida daga ita sai rigar baccin dake jikinsa kawai aka fito da ita.
“Me kike wani jin kunya bayan kin riga kin gama zubar da mutunci tun a waje, Gimbiya Safiyya dai ta ciri tuta domin ta kawo budurcinta gidan mijinta, sai dai ba muyi zaton Yarima fanko zai aura ba?”.
Cewar Larai kenan, Fulani Sokoto dake tsaye gefe tayi dariya tare da ƙarewa Aynu kallo.
“Waya san ma ina aka shiga aka fita?, domin ni dama tunda Fudhal ya nace nasan ba lafiya ba da walakin goro a miya”.
Tuni sauran bayin gidan suka hau salati da sallallami, zuwan Fulani Bingel wajen ya sanyasu da katawa suna duban ta domin jin mai zata ce.
“Meye haka kukeyi kuma?”.
“Babu komai surukarki dai ta zubar da mutunci da ƙimarta Larai nuna mata”.
Larai ta buɗe farin bedsheet ɗin tana nunawa Fulani Bingel, Fulani Bingel ta dafe kai cike da takaici ta girgiza kai tana faɗin.
“Wai har yaushe ne za’a bar wannan mummunar al’adar ne?”.
“Babu rana kam”.
Cewar Fulani Sokoto kenan tana wani cika da batsewa, Larai ta buɗe bedsheet ɗin ɗakin Gimbiya Safiyya tuni aka hau ihu da murna gurin ya kacame kowa na tofa albarkacin bakinsa a kan Aynu ita kuwa tuni fuskarta ta jiƙe da ruwan hawaye sai shash-sheƙar kuka take.
Tsawar fudhal da sukaji ne ya sanyasu yin shiru tsaye gefansa kuma Anwar ne kallo ɗaya zakayi masa kasan ransa a ɓace yake sosai, takawa yayi har zuwa inda Aynu ke tsaye a takure tana shash-sheƙar kuka sai ji tayi kawai anyi sama da ita ta buɗe ido da sauri sai ganinta tayi ɗauke a hannun Fudhal tayi maza ta sake runtse idonta yayin da hawayen ya cigaba da bin kuncinta.
Bai ajiyeta ko ina ba sai kan gado ya kwantar da ita tare da janyo bargo ya rufa mata sabida ganin da yayi tana kakkarwa, yasa hannu ya share mata hawayen har alokacin bata buɗe idon ba.
Su kuwa suna ganin ya ɗauke ta tuni kowa ya kama gabansa Fulani Bingel tayi murmushi kawai itama ta bar wajen.
Fudhal na fita bai zame ko ina ba sai ɓangaren Fulani Sokoto ya sameta ita dasu Larai anata mai da zance da dariya tsawa ya daka musu yana duban Larai tare da faɗin.
“Ka da in sake ganin ki cikin gidan nan, ki tattara ki fice kafin in dawo”.
Bai jira mai zasu ce ba ya fice daga falon Fulani Sokoto ta bishi da kallo kawai Larai kuwa tuni ta fara tsima tare da hawaye tace.
“Kin gani ko?, Hajiya abin da nayi gudu kenan”.
“Kefa sokuwa ce wallahi Larai shi ai ba shi da iko kan bayina kamar yanda bani da iko akan nasu kwantar da hankalinki babu inda zaki je”.
Yarima Fudhal ya wuce part ɗin Hajiyarsu ya sameta tare da su Anwar zama yayi tare da gaisheta bai kuma faɗin komai ba yayi shiru kowai can dai ya buɗe baki yace.
“Wai Hajiya ba zakuyi magana adaina wannan mummunar al’adar ba?”.
“Taya za’a daina Magaji?, abu ya samo asali tun kaka da kakanni mu da muka zo yanzu meye namu a ciki?”.
Yarima Fudhal yaja guntun tsaki cikin ransa yana mai mid ba tare da yace komai ba suka fito tare da Anwar.
A hanya Anwar ke faɗin.
“Ai duk abin da ya faru laifinka ne fa Fudhal kasan al’adar gidan nan taya zakayi sake har hakan ta faru?”.
Yarima Fudhal yaja dogon tsaki yana duban Anwar.
“Kai nifa ba wannan ne a gabana ba, akwai dalilin da yasa ni yin hakan kawai”.
“Kamar ya..! Mene dalilin kuma?”.
Yarima Fudhal ya tsaya daga tafiyar da yake yana duban Anwar tare da faɗin.
“Ina so in tabbatar wa da Aynu irin son da nake mata, ni zan iya zama da ita har a bada ba tare da wani abu ya shiga tsakaninmu ba”.
Anwar ya bi Yarima da kallon takaici yama rasa mai zaice masa can dai yace.
“Hmmm ayi dai mu gani?”.
“Zaku gani kuwa”.
Fudhal ya bashi amsa suka ci gaba da tafiya suna zuwa kofar part ɗin su Fudhal sukayi sallama Anwar ya tafi gida shi kuma ya shige wajen sa.
Inda ya barta nan ya sameta sai faman takurewa take ya taka inda take kwance da sauri ya taɓa goshinta da wuyanta zafi sosai alamu fever ya kamata.
Yaye bargon yayi tare da miƙewa zuwa gaban mirrow ya dauko man shafawa ya ajiye gefan gadon sannan ya koma jikin wardrobe ya buɗe ya ɗauko mata doguwar riga yellow mai ratsin baƙi ya ajiye gefe, Aynu na kallonsa ya ɗago da ita ya ɗorata bisa ƙafarsa yahau shafa mata man sai da ya gama sannan ya shiga kici-kici zare mata rigar zai sanya mata mai ɗan kauri ta rintse idonta sosai dai-dai sanda taji ya janye rigar daga jikinta.
Sai da yagama sannan ya dubeta da murmushi yace.
“Buɗe idon sarkin tsoro, kinci abinci kuwa?”.
Kai ta girgiza alamun a’a kwantar da ita ya sake yi ya fice daga ɗakin da sauri.
Mintuna kaɗan ya dawo hannunsa ɗauke da jug cike da kunun gyaɗa da soyayyar wainar kwai a plat ya ajiye gefe ya zauna sosai kan gadon ya ɗagota yana mai bata kunun akan dole taci badan ranta naso ba, sai da taƙoshi sosai sannan ya bata magani ya mai da ita ya kwantar ya faɗa toilet domin yin wanka.
***
Saima zaune bisaaya daga cikin kujerun falonta daya sha kayan alatu kala-kala tana kallonta cikin nishaɗi dajin daɗi Anwar yayi sallama ta amsa cike da fara’a tana faɗin.
“Sannu da zuwa” taanyi hug nasa ya nemi guri ya zauna ita kuma ta fara gabatar masa da kayan abinci kala-kala tana faɗin.
“Na dai san cikinka ɗauke yake da yunwa”.
“Kamar kin sani wallahi yau munsha yawo sosai da Fudhal danma na matsa dole abincin matata zan ci, sukayi dariya baki ɗayansu.
Tun randa aka kai Jalilah atsayin matar Ya Sayyadi Umar yayi amanna da irin halaccin da iyayenta sukayi masa ya karɓi Jalilah matsayin mata a gareshi hannu bibbiyu, sun fahimci juna sosai a daren duk da cewa Jalilan bata magana.
Ya Sayyadi Umar kuma yaci alwashin insha Allah zai nema mata Maganii duk a inda yake, domin tashi ɗaya yaji sonta fiye da yanda yaso Aynu domin Jalilah ma ba bayaba wajen ladabi da biyayya da sanin ya kamata ga uwa uba kyau domin zai iya cewa tafi Aynu kyau sabida jikinta a goge yake kuma ita fara ce.
(Tofa..! Masoyan Aynu shin kunyarda da batun Ya Sayyadi Jalilah tafi Aynu kyau kuwa?, kodai ya faɗa ne kawai domin ya rasata?).
*******
Aynu ce keta faman shige da fice domin haɗa musu kayan kalacin safe, Yarima Fudhal na zaune kan carpet da system a gabansa amma baki ɗaya hankalinsa nakan Aynu can dai ya kasa daurewa tana zuwa zata wuce domin shiga bedroom ɗinsu zata ɗauko wani abi yayi saurin janyota ta faɗo jikinsa Aynu ta rufe idonta da sauri domin bala’in kunyarsa take ji sosai.
“Buɗe idonki ki kalle ni”.
Sake rintse idon tayi Fudhal yayi murmushi ya cikata daga riƙon da yayi mata yana faɗin.
“Wai har yaushe ne zaki daina jin kunya ta ne?”.
Aynu ta miƙe da sauri tana murguɗa masa baki ta shige bedroom ɗin da gudu ya biyo ta yana faɗin.
“Idan na kamaki zakiyi bayani”.
Basu tsaya ko ina ba sai kan gado, Fudhal ya hau yi mata wasa mai matuƙar rikitarwa kullum shi aikinsa kenan sai dai yayi wasa da ita son ransa ya rabu da ita , ita abin nasa har ya fara bata tsoro har Zee na faɗin ko ba shi da lafiya ne?.
BAYAN WATA ƊAYA…!.
°°°°
Yauma kamar yanda ya saba ya shafe tsayin lokuta yana wasa da ita kafin ya sauko daga kan gadon yana faɗin.
“Zoki gani Aynu”.
Ta matso da sauri domin ta tsorata ta ɗauka wani abin ne.
Wani ɗan akwati taga ya miƙo mata yana buɗewa zobe ne ya baiyana a ciki sai walwali yake dan kyau.
Murmushi tayi tasa hannu ta karɓa cike da murna.
Yarima Fudhal shima murmushin yayi ya cire zoben daga cikin akwatin ya kamo hannunta ya sanya mata tare da yin kiss ɗin hannun yana faɗin.
“Mai yasa kike gayawa Zee har yanzu babu abin da ya shiga tsakanin mu?”.
Aynu ta rufe idonta cike da kunya yasa hannunsa ya janye hannuwan nata suna duban juna yace.
“Nayi hakanne kawai ba dan rashin lafiya ba, kawai inason tabbatar miki da irin son da nake miki, wallahi Aynu zan iya ƙare tsayin rayuwa a tare dake ba tare da wani abu ya shiga tsakanimu ba sabida soyayya ta dake gaskiya ce amma…!”.
Aynu ce tasanya tattausan hannunta ta to she masa baki kanta na ƙasa take faɗin.
“Na yarda wallahi Yarima, na yarda da son da kake min ba sai ka rantse ba duniyama ta shaida ba ni ba, ina Sonka kuma zan cigaba da sonka har ƙarshen rayuwa..!”.
Kaiii…nima fa gaskiya aradu na antaya kogin soyayyar YARIMA FUDHAL kodai sakin Aynu zansa ayi ni a antaya ni lolll.
Wannan page ɗin nakine SHAFA’ATU UMAR inayinki nima irin sosai ɗinnan wallahi.
*YARIMA FUDHAL*
NA
QURRATUL-AYN.
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®.
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
48.
BAYAN WATA UKU.
Kwance yake bisa doguwar kujera dake cikin falonnasu lokaci-lokaci yana ɗan riƙe cikinsa dakeyi masa ciwo, Safiyya na zaune can gefe hankalinta na kan TV ko kaɗan bata lura ba sai kawai ganin sa tayi ya faɗo kan carpet da sauri ta miƙe ta ƙarasa wajen sa tana faɗin.
“Lafiya Jaleel mai yake damunka?”.
Shi dai ya riƙe ƙam faɗi yake a hankali.
“Cikina.! Wayyo ciki na..!”.
Safiyya ta miƙe da gudu ta nufi wajen Fulani Sokoto a ruɗe ta shiga falon tana faɗa mata halin da Jaleel yake ciki da sauri sukayo waje zuwa ɓangaren su Safiyyan.
Shi kuwa sai faman malelekuwa yake yana ihun cikinsa suka ƙarasa kansa tuni Safiyya ta fara kuka Larai ce dake biye dasu ta sake ficewa a guje zuwa wajen Sarkin gida ta faɗa masa halin da ake ciki tuni ya nufi fada domin sanarwa sarki Ubaiyd.
Sarki Ubaiyd yace a fito dashi a kai shi asibiti, Magaji Saif dake zaune yamiƙe da sauri suka nufi cikin gidan tun zuwansa har yanzu bai koma ba Sokoto ba Sarki Ubaiyd yaƙi bari ya tafi.
Sarkin gida ne ya tallafoshi tare da Magaji Saif Safiyya ta biyosu tana kuka aka ce ta zauna Fulani Sokoto da Magaji Saif sune suka tafi kai shi asibitin.
Tuni ciwon Jaleel ya baza cikin gidan.
Yarima Fudhal kuwa basu san wainar da ake toyawa ba domin ko buɗe falonsu ba suyi ba ranar duk da cewa suna zaune falon.
Aynu na bisa cinyar Fudhal akwance shi kuwa ya dage wai tsifar kai yake mata Zee zata zo tayi mata kitso, suna hirarsu jefi-jefi cikin so da ƙauna abin dai abin sha’awa, bugun ƙofar falon da aka hau yine yasa Fudhal miƙewa yana faɗin.
“Waye?”.
“Jakadiya ce”.
Ta bashi amsa ya buɗe yana faɗin.
“Yadai lafiya kuwa?”.
“Babu lafiya ranka ya daɗe, Fulani ce tace a gaya maka ka shirya zaka kaita asibiti yanzu aka tafi kai Jaleel”.
“Jaleel kuma..! Mai ya sameshi?”.
“Ciwon cikinsa ne ya tashi”.
Yarima Fudhal yaɗan dafe kai kafin yace.
“Ina zuwa bari in shirya”.
Jakadiyya ta koma shi kuma ya juya cikin falon yace da Aynu.
“Bari inyi wanka asibiti zamu”.
Dake Aynu taji komai to kawai tace ya shige cikin bedroom dinsu ya barta nan falon tana cigaba da tsifarta.
Mintuna kaɗan sai gashi ya fito cikin sauri harya shirya yayi mata sallama ya fice zuwa part ɗin Hajiyartasu.
Ko da yaje ta shirya shikaɗai kawai take jira, yana shiga suka fito suka nufi inda motar take suka shige Fudhal yaja suka tafi.
Suna isa asibitin suka tadda Fulani Sokoto zaune gefe tayi jugum Magaji Saif na tsaye sai faman zarya yake, Hajiya ta nemi guri ta zauna Fudhal ya karasa inda Magaji Saif yake tsaye yana faɗin.
“Ina Jaleel ɗin?”.
“Yana emergency”.
“OK”.
Abin da Fudhal yace kenan ya nufi ɗakin shima, domin asibitinsa ne kuma shine babban Doctor.
Bayan shigarsa sun shafe tsayin a wanni kafin su Fudhal su fito wujuga-wujuga dasu ya kalli Magaji Saif yace.
“Yana buƙatar akawo masa Safiyya”.
“Me yasa wani abu ya sameshi ne”.
“Aa adai kawotan tukunna”.
Magaji Saif ya dubi driver yace.
“Yi maza kaje ka ɗauko Safiyya”.
Driver ya miƙe da sauri ya fice domin cika umarnin Magaji Saif.
Yarima Fudhal ya koma cikin ɗakin da Jaleel yake ya zauna kawai yayi tagumi yana kallon halin da dan’uwannasa yake ciki.
Lokaci-lokaci yana duba agogon hannunsa yana jira yaga zuwansu Safiyya.
Magaji Saif ya buga ƙofar ɗakin Yarima Fudhal ya share kwallar dake kawo masa ya miƙe ya fita zuwa wajen har da Aynu ya gani tsaye ta biyo Safiyya.
Fudhal yace.
“Zaku iya shiga dukkan ku”.
Ai kuwa tuni suka ɗure cikin ɗakin zuwa inda Jaleel ke kwance bisa gado abin tausayi.
Ya riƙe cikin sosai Safiyya tariƙo hannunsa tana faɗin .
“Sannu Allah ƙara sauƙi”.
Jaleel ya juya yana kallonta hawaye nabin kuncinsa ya buɗe baki a hankali yace.
“Kiyi haƙuri Safiyya, ki kulamin da abin da yake cikin ki, ni bana da tabbacin zanga abin da zaki haifomin amma inaso ki kulamin da tarbiyarsa a hannunki, bana so ɗana ya taso hannun Mahaifiyarmu domin ina jin tsoron kada ta bashi irin tarbiyar data bamu ni da ƙanwata…!”.
Yakai maganar yana mai kallon idon Fulani Sokoto dake tsaye gefe kunya duk ta cikata da maganar da Jaleel yake.
“Momy kece duk silar halin da nake ciki a yanzu kuma kece silar rasa bakin Jalilah duk nasan wannan, na tabbatar bada ban mugun nufinki nason halaka Fudhal da son a dole ni ne zanyi sarauta ba da duk hakan bata faruwa ba”.
“Yanzu gashi tsananin son kanki mai yaja mana Momy?”.
Magaji Saif ne ya ƙarasa wajen sa ya rufe bakinsa yana faɗin.
“Aa Jaleel mahaifiyarkuce fa kada kace haka ka yafe mata dukkan abin da tayimaka kaji domin nasan tayine cikin kuskure ka yafe mata na roƙeka wannan alfarmar”.
Kai ya gyaɗa alamun to, yana duban Magaji Saif ya buɗe baki a hankali yace.
“Na yafe mata”.
Yakai maganar da murmushi akan fuskarsa, ya sake ɗaga harshe yana salati sai gani sukayi idonsa ya kafe akan Mahaifiyartasa har lokacin murmushin bai ɗauke daga kan fuskarsa ba.
Yarima Fudhal dake tsaye bakin ƙofa yana kallonsa sai yayi maza ya juya masa baya yana share kwalla, bai aune ba saijin mutum yayi a jikinsa yana shash-sheƙar kuka ya buɗe ido yaga ashe Aynu ce ƙara rungumeta yayi sosai yana share mata hawayen.
“Jaleel…!”.
Kowa ya ɗago kai ya mai da dubansa inda sukaji ankira sunan Jaleel Magaji Saif dake rufe idanunsa tare da Jan mayafin dake kan gadon ya karasa lullbeshi yana duban wacce ke magana.
Jalilah ce tsaye bakin ƙofa tayi maganar kowa ya bita da kallo itama sai take kallon kan nata domin jin maganar tayi kamar ba daga bakinta take fita ba.
Ƙarasawa tayi da gudu ta buɗe mayafin da aka lulluɓe Jaleel dashi ganin da tayi baya numfashi hakan ya ƙara tabbatar mata da cewar ya mutu kenan?.
Da baya ta koma ta zube ƙasa tana rusar kuka Hajiyarsu Fudhal ta dafata tana faɗin.
“Kuyi hakuri Jalilah ba kuka zakuyi masa ba addu’a zakiyi masa kinji”.
Jalilah ta share hawayenta tana yiwa Mahaifiyarsu Fulani Sokoto wani irin kallon tsana.
Fulani sokoto dake tsaye ƙame gefe ta kasa ɗaga harshenta tayi magana idonta ya bushe ƙam babu ko kwalla kukan zuci kawai take.
Jalilah ta ƙarasa wajenta tana kuka take faɗin.
“Kin gani ko Momy?, kin gani kinyi silar rasa ɗan’uwa na da munanan halayenki akan duniya kin zaɓi Jaleel ya mutu…!”.
“Ba Jaleel aka zaɓa ba..! Ke aka zaba ki mutu..! kuma tabbas zaki mutu domin burin mahaifiyarku shine, ta raba auren ki da Umar ta raba Jaleel Safiyya ta raba Aynu da Fudhal inyaso Fudhal ya auri Safiyya Jaleel kuma zai zama Magaji a bayan Mahaifinku”.
Larai na kaiwa nan ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya tana mai cigaba da faɗin.
“Boka yace dole akai ruhin Jalilah indai kina so Jaleel yayi sarauta inda dama ma sai a kashe Fudhal ko Hajiya haka kikace ai yanzu zanje infaɗa masa”.
Saita kama rawa a wajen kowa jikinsa sai yayi sanyi aka mai da hankali wajen bin Fulani Sokoto da kallo Jalilah kuwa tuni ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, Fudhal yazo ya ɗauke ta aka kaita can wani ɗaki domin taimakon gaggawa, ita kuma Larai yasa akayi waje da ita.
Domin tone-tone take tayi na irin abubuwan da suka dinga shiryawa Yarima Fudhal amma sai abin ya dinga komawa kan Yarima Jaleel.
Safiyya zaman daɓaro tayi tana risgar kukar rashin mijinta ga kuma wanna mugun jin da kunnuwanta suka jiye mata akan Momynsu Jaleel.
“Yanzu da tuni nine acikin wannan halin?, da tuni nike neman mata da shaye-shaye, Allah yajikanka Jaleel yanzu ga abin da shaye-shayen yaja maka ya illata kayan cikin ka har yayi sanadiyyar rasa ranka”.
Yarima Fudhal keta wannan zancen aransa domin babu wanda yasan abin da yayi sanadiyyar mutuwar Jaleel da gashi dai sauran likitocin da sukayi masa aiki, kuma Fudhal ne ya gargaɗesu akan kasa su faɗa, sabida gujewa halin da zai shiga idan yaji tare da ƴan uwansa sai kuma gashi mai aukuwa ta auku.
ALLAH KENAN..! AISHI BA AZZALUMIN BAYINSA BANE, SUN MANTA DA CEWA YANA GANINSU,KUMA YANA JINSU, SUN MANTA DA CEWAR IDAN BABU DUNIYA AKWAI LAHIRA, ALLAH KASA MU DACE KASA MUFI ƘARFIN ZUCIYARMU AMIN.
*YARIMA FUDHAL*
NA
QURRATUL-AYN.
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®.
SADAUKARWA:-NANESY FIRDAUSI JEBOR.
49.
Nan dai aka fice da gawar Jaleel aka tafi kai shi gida domin ayi masa wanka akaishi makwancinsa.
Gimbiya Safiyya tayi kuka iya kuka domin iya kacin kwanakinta da Jaleel sun shaƙu fiye da tunanin duk inda tunanin mutum zai kai.
Magaji Saif kuwa hankalina gaza kwanciya yayi daga abin da Larai ta faɗa hakan yasa yana fita daga asibiti bai wuce gida ba sai wajen wani malami da yasani masanin fiƙihu sosai ya zaiyane masa dukkan abin da ake ciki, malamin yace idan da dama suje yaga Jalilah .
Babu musu Magaji Saif ya ɗauki Malam har cikin ɗakin da Jalilah ke kwance asibitin suna shiga malamin ya ƙare mata kallo yace.
“Tabbas gaskiya suka faɗa, amma ka kwantar da hankalinki insha Allahu babu abin da zai faru daga gareta”.
Malamin ya nemi guri ya zauna ya buɗe alqur’ani ya fara karantawa Magaji Saif ya nemi guri ya zauna, malamin ya shafe kusan awa guda yana karatun kafin ya rufe Qur’an ɗin ya buɗe jakarsa ya ɗauko wani ruwan rubutu ya nufi inda Jalilah take kwance ya zuwa rubutun a hannunsa ya yarfa mata sau uku saiga wani Koran hayaƙi na fita daga jikinta yana gama fita ya kuma watsa mata tayi wata irin atishawa tare da ajiyar zuciya.
Malamin ya dubi Magaji Saif yace.
“Insha Allah babu abin da zai faru, sai dai a gaya mata ta dage da azkar da tsayuwar dare tare da yawaita salati ga Annabi Muhammad (S. A.W)”.
“Domin da yawanmu mu mutane muna shagala da duniya sosai mu manta abin da Allah da Manzonsa sukace, waɗannan abubuwa dana lissafa ba karamar kariya bace garemu, ga kuma dumbin lada da zamu samu bayan wannan ta dalilin yinsu sai ka ka samu aljana Allah dai yasa mu dace”.
“Amin ya Allah”.
“Mungode sosai malam muje in ajiyeka gida zan wuce jana’izar Yayanta ne anata jirana”.
“Aa muje tare mana, inyaso na koma ni kaɗai”.
Ko da suka isa anyi masa wanka da komai, su kawai ake jira suna zuwa aka sallaceshi aka ɗaukeshi zuwa gidansa na gaskiya gidan da dukkan wani mai rai dole ne sai ya shige shi.
Su Zee dasu Baba ta Sallah Umman Aynu da Babanta duk tawowa sukayi gidan domin zaman makoki, Aynu tayi kuka sosai da mutuwar Jaleel, Fudhal kuwa zan iya cewa yafi kowa damuwa musamman inya tuna ata dalilin ƙiyayyarsa da Fulani Sokoto keyi masa ya rasa ransa yakanji duniyar tayi masa zafi sosai danma ana tausarsa sabida shima Gawa taƙi rami ne.
Har Jaleel ya cika kwana uku amma Fulani Sokoto bata umm bata um-um, Jalilah ta warke garas abinta sai dai baki ɗaya ta bar part ɗin Mahaifiyarta ta koma wajen Hajiyarsu Fudhal, Hajiya tayita yi mata faɗa akan ta daina fushi da mahaifiyarta sai dai kawai tace.
“Ni ba fushi nake da ita ba kawai banajin daɗin ganin halin da take ciki ne”.
Har akayi sadakar bakwai kowa ya watse ranar Magaji Saif ya shirya meeting da dare baki ɗaya mutanan gidan kafin masu aure su tafi gida.
Magaji Saif yayi musu masiha sosai nasiha mai ratsa zuciya babu Wanda bai yi kuka ba a wajen musamman ma Jalilah wanda duk nasihar akanta ne sabida fushin da take ga mahaifiyarta take aka sanya ta ta nemi gafarta duk da cewa Fulanin bata magana.
Taro ya watse cikin jin daɗi sosai duk da cewar mutuwar Jaleel ta zame musu wani babban giɓi a garesu amma nasihar Magaji Saif yasanya zuciyoyinsu samun nutsuwa da hakuri tare da salama.
***
BAYAN WASU WATANNI.
Gimbiya Safiyya ta haifi ɗanta namiji an sanya masa sunan Yarima Jaleel, ba’ayi wani taron suna ba sabida yanda haihuwar yaron da sunan da aka saka yake tunawa da dukkan ƴan gidan rasuwar Jaleel, shiyasa Mai Martaba yace babu taron da za’ayi azo a zauna ana faman koke-koke, yasa aka ɗauki Safiyya aka kai gida domin tayi wanka a gida.
Al’amarin Fulani Sokoto sai abin da yaƙaru yanzu bata magana ko kaɗan sai dai kawai ido, ɓangarenta ya ɓaɓe yanzu duk taron jama’ar nan babu sai ƴan ragowar masuyi mata shara da ɗan goge-goge, idan ka ganta yanzu a bar tausayi tayi wani irin baƙi da rama kwalliyarnan duk babu, danma Jalilah na zuwa lokaci-lokaci dubata.
Yanzu kuma gashi cikin Jalilah ya tsufa sai dai Aynu ita ke zuwa kullum tayi mata dukkan abin da take buƙata ta dawo part ɗinta.
Yanzu tsakanin Saima da Aynu wani zumunci ake mai ƙarfi Saima ta ƙara tabbatarwa Yarima Fudhal na Aynu ne dole dukkan mata su haƙura duk da irin ƙaunar da suke masa kuwa, domin shi babu wata mace dake gabansa wacce ta wuce Aynu.
Ansanya bikin Zee wata huɗu masu zuwa tare da wani malamin makarantar primary dake can ƙasan unguwarsu, murna agun Aynu ba zata faɗu ba domin dama ita burinta ayanzu bai wuce taga auren Zee ba.
Magaji Saif wani danƙareren gida ya bawa iyayen Aynu suka koma ya buɗewa Babanta ƙaton shago cike da kayan masarufi yana siyarwa.
Ashe a rasuwar Yarima Jalil Magaji Saif yaga Babarsu Zee yaji tayi masa zai iya aurenta kasancewar Mahaifinsu Zee ya daɗe da rasuwa tun suna yara kuma ba ta sakeyin wani auren ba sai yanzu da Magaji Saif ya ganta ya koma nace aurenta zaiyi.
Nan da nan aka sanya aure sati biyu masu zuwa tare da taimakon shawarwarin Umman Aynu domin da Baba ta Sallah ƙin amincewa tayi sai da Umman Aynu tayi ta mata nasiha sannan tace ta amince ya turo.
Anyi bikin girma da karamci Baba ta Sallah ta tare a cikin gidansu Magaji Saif wato gidan sarauta Aynu ba ƙaramin daɗi hakan yayi mata ba yanzu gata ga nata a kusa ai dole tafi kowa jin daɗi, gashi bikin Zee ma anan za’ayi sabida baki ɗaya suka dawo gidan ko yaushe Aynu na tare da Zee suna bawa juna shawarwari a tattare da su.
Yarima Fudhal ya mai da hankali sosai kan aikinsa, idan ya dawo kuma yakan zaunar da Aynu yana koya mata abubuwan da bata sani ba na addini da na boko ganin tayi zurfi sosai shi kuma aiki ya sakoshi gaba yanzu ya yanke hukuncin samo mata mai yi mata lesson kafin ya sanyata School, domin so yake kafin ta shiga tasan komai data shiga akaita SS 2 ko 3 sabida tayi exam nan da nan ta wuce university.
Hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba kullum ta zauna labarin kenan makaranta Zee tace.
“Nifa labarin skull ɗin nan ya fara isa ta mudai kawai muji labarin ‘yan takwaye”.
Aynu tayi dariya yana faɗin.
“Ba yanzu ba sai mum morewa amarcinmu”.
Suka sanya dariya baki ɗayansu, Yarima Fudhal dake tsaye bakin ƙofa yayi sallam tafi nawa basu ji shi ba suna hira shima dariyar yayi.
Dariyar tasa sukaji suka juya Zee tace.
“Au ashe kana tsaye?”.
“E mana duk inajin hiran taku ai”.
Sukayi dariya dukansu Zee tayi musu sallama ta fice, Yarima Fudhal ya riƙo Aynu tare da rungumeta yace.
“Nima fa inason yaran nan da zaki ce ba yanzu ba so nakema tashin farko ki haifamin ƴan uku”.
Aynu ta zaro ido waje.
“Haba dai uku ƙaramata dani ina laifin ɗayan ma”.
“Ohh kinaso kema kenan?”.
Aynu ta sanya kanta cikin ƙirjinta alamun kunya.
Dariya yayi yana mai kai bakinsa cikin kunnenta yace.
“Zo muje in baki yau tunda kin shirya”.
Aynu sai ji tayi ya ɗauke ta cak sai other room
ALHAMDULILLAHI….!.
Nan muka kawo ƙarshen wannan book mai suna YARIMA FUDHAL.
Abin da muka faɗa dai-dai Allah yasa ya amfani al’umma, wanda mukayi kuskure kuma Allah ya gafarta mana amin.
GODIYATA A GAREKU.
Mungode sosai sosai abisa ƙoƙarinku agaremu na ganin ci gaban kungiyarmu Allah ya saka da alkhairi ya biya Ku amin.
MaryamulAbdul Kwaiseh
Adda Benaxer
Hauwa m. Jebo.
Aunty lubie mai tafsir.
Firdausi sodangi.
WANNAN BOOK SADAUKARWANE AGAREKI DUKA.
NAMESY :-FIRDAUSY JEEBOR
ALLAH YA BAR ƘAUNA.
MASOYANA.
A ko ina kuke ina miƙo gaisuwata tare da ɗumbin ƙaunarku nima kamar yanda kuke nunamin.
Zaku ji cigaban book ɗin YARIMA FUDHAL cikin BOOK mai zuwa muku nan da wani lokaci mai suna ZUCIYA DA HAWAYE wanda Document zai zo muku basai kun jira post ba.
NAGODE BYEEE.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button