Zee Baby Book 1 Page 41

*????????41*
….daket jama’a sukafito dasu babu mai motsi acikinsu jini ya bata musu jiki mahbeer harda wani karfe gefen cikinsa da ya cakesa cikin hukuncin Allah sai ga Ahmed yazo wucewa yaga taro jama’a sunacewa akaisu hospital parking yayi ya fito ya nufi wajan ganin su zee ne abun ya tashi hankalin Ahmed arikice yace” don Allah ku kamamun musasu mota motar Ahmed aka sasu harda mai motar ya shiga yana kuka Ahmed yaja da sauri yabar gun gudun kar akirawo yan sanda wayar Sardauna ya kira, lokacin suna hanyar dawowa gidansu ganin Ahmed ya, daga ko magana baiba yace” Dr kaiyi sauri kazo hospital ya kashe Kiran, yaci GABA da tuki hankalinsa atashe suna zuwa hospital aka taresu aka kawo gadon marasa lafiya aka fito dasu aka kwantar dasu kai tsaye emergency akayi dasu
Ahmed hankalinsa atashe yake Sardauna ya shigo da mota ko parking d’in kirki baiba ya fito Nisha na biye dashi Ahmed ya taresa “Dr kayi sauri kaceto rayuwarsu rike Ahmed Sardauna yayi” suwa ye? ” zainab da Mahbeer ai bai tsayaba ya sakeshi yayi ciki da gudu Nisha ta fara kuka” meye ya samesu? ” hatsari sukayi kiyi hakuri bari kukan muje ki zauna Sardauna kai tsaye emergency ya shiga jikinsa na tsuma sunaga Dr ya shigo suka dakatar gun mahbeer ya nufa kallo daya yamasa, idanunsa ya ciko da ruwa ya kalli Dr Nabeel ” kuje ku ceto ran matarsa bari ni na dubasa, da kaina bai sauraresu ba ya fara ceto ran mahbeer saida ya kwashe awanin biyu ya dinki masa gefen cikinsa da cinyarsa da
sharan fuskarsa da goshinsa da ya tsage wlh ba mahbeer ba Sardauna ma yau abin tausayine ya hada duk maganin da yasan zaiyi Saurin dawo dashi haiyacinsa da kashe masa zafin ciwanka ya saka masa drip ko ina akumbure yake jikin mahbeer lokacin da ya fito yaga yan gidansu cike akofar dakin hankalinsu atashe ghaisha ta nufoshi” Dr ya zainab take da mahbeer don Allah ka fada mana? cikin dakiya yace” ghaisha da sauki zasu warke basu wani jimuba Nisha tana kuka tace” wlh Daddy sun jimu kallo daya idan mutum ya musu bazai sakeba wani mugun kallo ya watsa mata ta sada kanta Daddy da nuhu da kawu saminu suka hada baki”Dr dan Allah ya suke ciki? ” Daddy kuyi hakuri da sauki zasu farfado barima na duba zainab din wajan ummi Raiyan ya nufa tayi tagumi tana zaune” ummi kuyi hakuri
zata farka insha? ” Dr babu komai Allah shine mai iko da kowa da kuma komai a lokacin da yaso Allah ya tashi kafadinsu gurin ya bari da sauri dan da sunsan halin da yake ciki sai sun tausaya masa dauriya ce kawai yakeyi gurin zee ya tafi kanta anade yake an dinki mata gefen da kanta ya bugu saboda bata jimuba sosai saide buguwar kanta bakin gadon ya zauna zuciyarsa na bugawa gatanan bata motsi duk na’urorine jikinta saboda buguwar kanta tashi yayi ya kara, duba lafiyarta da kyau cikin dakiya da jarumta yake komai amma ko alamun motsi batayi ba jikinta ya fada yana kuka saida yayi yagaji dan kansa ya fito ya nufi wani room yashiga ya rufe kansa, yayi alwalla ya shimfida darduma ya tayar da sallahr nafila yana nema musu sauki awajan Allah har baisan adadin awanin da ya daukaba saida ya duba agogon hannusa yaga karfe, daya na dare ya Mike ya fito har yanzu yan gidansu ba Wanda ya tafi tausayi suka bashi
yace “Daddy dan Allah kutafi gida insha Allah zasu farka cikin haiyacinsu mamana kuje gida babban yaya kai sai ka tsaya Kawu Saminu yace” wlh babu inda zamu yanzu muka gama musu Addu’a zasu farka nan kusa gun Nisha ya nufa ya kamo hannuta ya nufi Office d’insa da ita”ya saka key ya bude suka shiga saman doguwar kujera ya kwantar da ita” Nisha ki kwanta ki huta kibar kukan yar uwarki zata farka inshn Allah kinji? kai ta daga kiss ya mata agoshi yaje ya dauko wata jibgegiyar rigarsa. ta sanyi ya lulubeta ya zauna kusanta k’ugunsa ta kamo tana kuka kasa-kasa bayanta yake bugawa har tayi shiru tana sabke ajiyar zuciya saida yaji tayi shiru ya Mike ya fice har yanzu
Yan gidansu ko mutum daya bai motsaba kai ya girgiza dan sasun halin da yake ciki wlh sai sun tausaya masa dakiya kawai yakeyi sai lokacin Sardauna yaga Ahmed da mai motar gurunsu ya nufa Ahmed yace”Dr kabi asannu kaima ba lafiyar zuciyace da kaiba karfa kasa, damuwa aranka don Allah kayi tawakali? murmushi Sardauna yayi ya rumgume Ahmed yana buga bayansa” Abokina karka damu nabarwa Allah ikonsa kaikuma ina godiya da samunka aboki nagari nagode nagode” dan Allah kabarmun godiya kaga bawan Allah nan hankalinsa atashe su Daddy sunce ya tafi sun yafe masa, amma yace sai yaga tashin bayin Allah nan sakin Ahmed Sardauna yayi ya isa gun mutumin ” kaje kawai babu komai Allah ya kaddara bawa baya wuce kaddarasa kaje munyafe maka ni ganinka ya fi batamun rai don girman Allah kaje mun yafema ganin yada jikin Sardauna yake tsumane yasa mutumin tsorata wuff ya fice da niyar gobe sai ya dawo zaune sukayi zuciyarsu da alhini har karfe kusan uku da, rabi na dare wlh idan ka kalli bayin Allah nan sai ka tausaya musu na’uran datake jone ce jikin mahbeer ta fara kuka da gudu wata nurse ta fito Kiran Sardauna arikice yayi ciki mahbeer ya farka sai tari yake jini na fita yana Kiran sunan zeena don Allah karki mutu gwara ni Na mutu ke kirayu da gudu Sardauna yayi kansa yana bashi temakon gagawa, su Daddy ana hanasu amma saida suka shigo daket Sardauna ya samu ya daina aman jinin rumgumeshi yayi yana kuka abinda yan gidansu taba ganin Sardauna yayi ba shine ya karyar da zuciyoyin yan gidansu ghaisha k’asa ta zauna
tana kuka, mahbeer yace”Kenan zeena mutuwa tayi shine kukamun Alluran bacci har aka binneta Daddy ne yazo ya rikeshi Sardauna yace”wlh bata mutuba zako rayu tare itama nemanka take tarin ya sarkeshi ya ruko hannu Daddy” Dadyna don Allah kuyafemun nine nayi sanadiyar mutuwar zee da na nace sai an maida mana auranmu da yanzu tana rayuwarta wlh ina sonta banga anfanin zamana aduniya babu zainaba ba don Allah duk Wanda nabatawa ya yafemun gabaki daya kowa yayo kansa, ghaisha, ta ISO ta rumgumeshi tana kuka”mahbeer mun yafema amma wlh zainaba tana raye bata mutuba Sardauna aje ayi dubara akawota da “to ya amsa dan yasan na’ururin da suke jikinta ayanzu bazai yuba aciresu mutikar fata farka tabbas komai zai
iya faruwa da zee rike hannu Sardauna yayi muryashi tayi k’asa” karku takura kanku ni nasan zee ta mutu saboda naga yada kanta yayi zan tardata muci gaba da rayuwarmu nide kuyafemu ya fada yana shakuwa jini na fita daga bakinsa ahankali yake kalmar shahada Daddy yayi saurin rumgumeshi yana fadin” lailaha illallah Muhammadun rasulullah sallalahu alaihi’wa sallam haka mahbeer ya maimaita har sau uku numfashinsa ya tsaya cak idanu Sardauna ya zuba masa mahbeer na damke da hannunsa jikin Sardauna babu inda baya rawa ghaisha ganin mahbeer ya mutu ta tsayar da kukan cak daddy kansa kasa shafema mahbeer idanu yayi Kawu Saminu ne da Nuhu sukayi jarumta kawu ya shafema mahbeer idanu Sardauna wani irin kukane ya kufce masa ya fada jikin mahbeer ya rumgumeshi yana kuka Nuhu ya janye Sardauna ya rumgumeshi Daddy ya kwantar da gawar mahbeer ya Mike tsaye
ummi zubewa tayi asume gabaki daya Sardauna jikinsa kerrrma yake yana wani irin kuka na fitar hankali gabaki daya ghaisha tama kasa motswa daga inda take tana karkarwa azaune ta tsare gawar mahbeer da idanu Daddy ne yayi kan ummi Ahmad akidime yayi waje ya kirawo likita Dan yasan Sardauna babu abinda zai iya ayanzu tare suka shigo da nurse da Dr Nabeel aka fitar da ita domin ceto ranta daddy ya koma gun gawar mahbeer ya tsugunna ya rike hannunsa”mahbeer yanzu ka mutu kenen Allah nagode maka da ka jarabeni ka daukemin yarona mai son yan uwa mai hakuri mabucin dariya mai son nak’asa dashi Allah na amshi jarabawarka da hannu biyu mahbeer Nayafema duniya da lahira khadijah kizo kiyafema d’anki zai tafi tafiya ta har abadan Saminu ya rike Daddy ya Mike tsaye “haba Abdu muyi tawakali da Allah mu karawa nak’asa damu kwarin gwiwa mana Nuhu ya Saki Sardauna yaja hannusa suka zauna “Faisal kayi hakuri kaga ba lafiyar zuciyaba gareka ba kuma kukanka shine yake Kara tada hankalinsu daddy kalli ghaisha halin da take ciki jeka ka bata baki babu Wanda ya isa ya hana Allah ikonsa duk lokacin da yaso fuskarsa ya goge masa ya ja hannusa suka tafi gun ghaisha Sardauna ya rumgumeta”momy kiyi hakuri kinji rumgume Sardauna tayi ta fashe da kuka “Faisal kaga yayanka yatafi ya barmu ko? Ahmed ne ya amso farin yadin ya kawo daddy tashi yayi ya lulube mahbeer ya dauki waya ya fara kiran yan uwa suna zaune agun sun tisa gawar mahbeer gaba ummi kuwa ba’a samu ta farfadoba sai karfe biyar na asubah tana kuka tana kiran mahbeer da zainaba sun mutu saida aka mata allura barci bayan sallah asubah gabaki dayansu suka dunguma gida har gawar mahbeer zuwa karfe takwas na safe gidansu mahbeer babu masayar tsinke Al’ummmah musulumai sun cika gidan sai koke koke akeyi zainab kanwarsa nan take naguda ta kamata sai hospital batajima ba ta haihu da namiji hadeema ana take yace asa sunan mahbeer yana kuka tamkar ransa zai fita dan bashida abokin da ya wuce mahbeer gashi mijin kanwarsa tana haihuwa ya koma gidansu mahbeer duk inda kake neman tashin hankali to wannan Family wlh sun shiga ga zee bata farkaba Daddy dubi suke itama ta mutu Sardauna boye musu yayi misalin karfe Tara na safe an gama shirya mahbeer za’a kaishi makwancinsa yan uwa gewaye dashi sai Addu’a suke masa ghaisha ta rumgume gawar amma bata kuka”mahbeer halinka nagari yabika na yafema duniya da lahira hafeeza ma rumgume take da gawar tana kuka Nisha ma Najib salma intisar ma tace”Ashe bazan rayu da kaiba nasoka kamar na mutu yaya mahbeer Allah ya jikinka da rahma Sardauna yace” kubamu guru mu daukeshi Ana jiranmu Dan kokarine kawai yakeyi maryama da anty hauwa suka janyen su amma maijidda taki sakin gawar mahbeer tana kuka mai cin rai daket Sardauna ya dauketa cak ya kaita gabansu Daddah suka ririketa su nuhu suka dauke gawar suka fice Sardauna ya rumgume ghaisha” momy idan bakyaso nima ki rasani to kiyi shiru don Allah? ” nayi Sardauna nayi shiru kuje ku kaishi gidansa na gaskiya sakinta yayi ya nufi gun ummi Raiyan ya tsugunna gabanta”ummi kiyi gakuri don Allah wlh nima zaku rasani idan Baku bar kukanba” mun bari Faisal tashi katafi mik’ewa yayi ya fice Ana shirin sallahtar gawar