Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 48

Lokacin da Sardauna ya isa gidansa karfe daya na dare nisha na zaune hankalinta a tashe Sardauna bai dawo ba yana shigowa ta nufi gunsa amma ganin yanayin da yake ciki ta tsorata ta fashe da kuka ta rungumeshi tana tambarsa nan ya fada mata zainab ta bace tayi mutikar tsorata da lamarin. Alwalla yayi ya fara sallah Nisha dakinsa ta bishi ganin yana sallah itama tayi alwalla take tadako abaya ta bishi sunayi. Bangaran zee baby kuwa karfe takwas bata yiba su isa Kano gidan Turk suka nufa masha Allah kallo daya zakama gidan kasan balarabene ya hadu sosai. saide zee ta Kafa musu rigima akaita gun baby daket suka shawo kanta taci abunci suka bata maganin bacci matar Turk nada kirki ita tayi ta kula da ita har tayi bacci Turk ya zaboma zee abaya mai kyau da tsada wacce zatasa gobe sun gama shirya tafiyar gobe karfe shabiyu na rana jirginsu zai tashi dama passport biyu yasa aka masa da na ummi da na zainab yazo dasu cikin farin ciki ya kwanta shima Dan yasan maganin baccin da tashi bazata farka ba sai washe gari burinsa ya kaita babbar hospital ta saudiya tasamu sauki ta dalilinsa yasan zata daina fushi dashi zai janyo diyarsa jikinsa ya zabama zee miji ya kashe auran da dangin ubanta suka mata Dan yanzu yana bukatar jikokinsa ahaka har bacci ya dauke sa. Family su Sardauna yanda sukaga rana haka sukaga dare babu Wanda yayi bacci sun dage da sallah suna rokon Allah ya baiyana zainab yasa tana cikin koshin lafiya aduk inda take har asubah tayi ba Wanda ya rumtsa wlh kallo daya zakama ummi Raiyan taba ka tausayi.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Ana sallah Asubah Sardauna yayi shirin tafiya gida Nisha ta fara kuka ya tafi da ita Dole ya tafi da ita Dan Sam shi maganar ma bayason yi sai Dole. aparlo duk suka samesu ana jimami Nisha ta nufi gun ummi ta rungumeta tana kuka. ” Aisha kiyi hakuri Allah zai biyanata insha Allah Sardauna ya gaishesu yaje ya rungume dadinsa ya lumshe idanunsa bayansa yake bugawa tuwusai da minata sai kuka sukeyi kawu Saminu na basu hakuri daddy yana shafa bayan Sardauna yana lallashinsa shiru yayi baiyi magana ba daddah tace”don Allah Sardauna kayi hakuri kar ciwo ya kamaka zainab zata fito insha Allahu. Aisha kema kiyi shiru ba ason mai ciki tana damuwa sosai ya kamata ku karfafawa Raiyan kwarin gwiwa ba kusata tana yawan kuka ba. haka sukayi jigum jigum har rana ta fara babu Wanda yayi yinkurin sakama cikinsa wani abu.

***
Da misalin karfe 11:50.am su zee suna Airport sanye take cikin abaya mai masifar kyau tayane kanta da mayafi sai murna takeyi saboda sun mata wayo sunce babyna na cikin jirgi yana jiransu zasu tafi gun mahbeer Turk na tare dasu sun bata waya wai ta babynta ce yana ciki da sun shiga ta bashi sai dariya take. Shabiyu daidai aka fara sanarwa matafiya su shiga jirgi Abu Rahman ya kama hannun zee suka nufi gun jirgi tana waiwayar Turk da Sauri yabar gun Dan yarinyar tabashi tausayi kuma yaji sonta ya kamashi zee baby tunda suka hau matatakalar jirgi kanta ya fara juyawa har suka shige ma’aikatan jirgi suka nuna musu kujerasu Dan alayin manya Abu Rahman ya saya zama sukayi zee tana ta zaro idanu inda zataga babynta ganin haka ya kalli wayarsa ya karanta abunda Turk ya rubuta masa yace” yana toilet bari zai fito kai ta daga tana hawaye ahaka har jama’a suka gama shigowa jirgi ya fara shirye shiryen tashi. Bayan minti goma jirgi ya fara tafi asannu sannun har yakai gunda zai cira da karfi yayi sama aikuwa yana cirawa zee wata irin hajijiya ta dauketa ta rinka ganin jiri tana ganin motar da ta bugesu da mahbeer Abu ya rikota wani irin gigitaccen ihu tayi da karfin gaske Wanda jama’a suka fara lekensu. tace” wayyo Mahbeer mota zata kashemu…nan take numfashinta ya dauke cak ta zube jikin Abu Rahman Asume Wanda yayi mugun tsorata zufa sai keto masa takeyi Dan zatonsa zainaba mutuwa tayi ma’aikatan jirgin ne sukayo kanta da gudu………… ✍????????????♀

 

 

*ZEE BABY*

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button