AtikuLabaraiSiyasa

2023:; Ina Mai Rokon PDP Ta Sake Bani Daman Tsayawa Takara

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sanar da kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP aniyarsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023, inda ya yi rokon da a sake ba shi dama.

Ya bayyana kudirin nasa ne a ranar Talata, yayin wata ganawa da shugabannin Jam’iyyar a Abuja. Atiku wanda ya kasance dan takarar babbar jam’iyyar adawar a zaben 2019, ya roki a sake bashi dama domin ya wakilci PDP a zabe mai zuwa na 2023.

Ya yi alkawarin gina kyakkyawar alaka a fadin yankunan kasar idan har aka bashi tikitin takarar jam’iyyar yayin da yan Najeriya za su shaida hakan idan suka zabe shi a shekara mai zuwa.

“Don Allah ku hada hannu da ni wajen gina cigaba a fadin kasar nan domin kowane yanki na kasar nan ya ji ana damawa da shi. “Shugabanni, dattawa, hazikan mutanen wannan jam’iyya tamu mai albarka, ina kira gareku da ku yi hakuri don Allah ku sake bani dama domin ci gaba da duk wasu manufofin jam’iyyarmu domin mu tabbatar da dimokuradiyya, hadin kai, da ci gaban kasarmu.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi godiya ga shugabannin PDP da suka amsa gayyatarsa na halartan taron. A karshen taron, ya je shafinsa na soshiyal midiya inda ya wallafa hotunan ganawar tasu.

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button