BABU SO 51

★★
Kusan ƙarfe takwas ta farka. Ganin har yanzu shi barcinsa yake hankali kwance sai ta koma ɗayan ɗakin tai wanka ta shirya a can. Ganin har lokacin baida alamar tashi saita nufi falo ta gyara duk da ba wani datti bane ba. Yunwa takeji matuƙa, dan haka ta haɗa tea ta dawo falon tai zaman sha tana buga game a waya. Koda ta kammala a falon ta cigaba da zama tana game ɗin har kusan ƙarfe tara.
“Wai mutumin nan bazai tashi bane? Koya manta yau monday akwai office?”.
Ta faɗa tana kallon agogon dake falon, miƙewa tai kanta tsaye ta nufi bedroom ɗin. Mamaki ya ƙara kamata ganin har yanzu dai a kwance yake, (Lallai babu lafiya) ta ayyana a ranta tana ƙarasawa gaban gadon, dan ita dai a sanin datai masa na rashin wasa da aiki inda ƙalau yake babu yanda za’ai yakai yanzun yana barci. Fuskarsa ta ɗan tsurama ido dan kwance yake a rigingine. Lumshe idanu tai da sake buɗewa a kansa, ita shaida ce Shareff ƙyaƙyƙyawa ne, ƙyawu irin na masu kwarjini da cikar haiba bawai na fitar hankali ba. ALLAH ya bashi dukkan kamala ta cikakken mutum tamkar wani babba. Baida yawan hayaniya, sannan bai da yawan fara’a. Mutane da yawa kance mata yanada sauƙin kai da daɗin zama, sai dai ita har yanzu bata ganinsu tattare da shi, dan zata iya bugar ƙirji tace babu wadda yatsana a rayuwarsa ƙila sama da ita, ta rasa minene laifinta a gareshi. Ta taɓe baki da juya idonta, a fili ta furta “Yo karya soni ɗin nima ai ba son sa nake ba humhh”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki ta juya zata bar wajen a bazata taji an riƙota. A firgice ta juyo dan ta tsorata, sosai idanunta suka firfito waje dan batai zato ko tsammanin shi ɗin bane tunda taga barci yake. Idanunsa ya ɗan rufe ya sake buɗewa a kanta tare da fisgota ta faɗo kansa…..
“Wayyo Yaya zaka karyani ne?”.
Komai baice mata ba, sai dai kafeta da idanunsa dake a yanayin wanda ya tashi barci. Ƙoƙarin son zame jikinta take a nasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora hanunsa a bayanta ya tallafeta da ƙyar a saman jikinsa, fuskarta dake a gab da tashi ta kautar gefe saboda yanda yake kallonta tsigar jikinta har tashi take. Ɗayan hanunsa yasa ya maido fuskar tata a saitin tasa har yana jin saukar numfashinta.
“Kina yin miye tsaye a kaina?”.
Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta tura baki da ƙara ƙoƙarin janye fuskarta dan bazata iya jurar kallonsa ba. “Ni to mizanyi? Kawai nazo tadaka ne dan naga lokacin office yana wucewa”.
Agogon dake ɗakin ya ɗan kalla tare da maido idanunsa a kanta lokaci guda. “Dama ango na zuwa office ne?”.
Sosai ta yatsine fuska tamkar wadda aka faɗama wani mugun abu. sai kuma ta taɓe baki da sake yunƙurin barin jikin nasa……..✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????