AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 73-74

??73 and 74??

Via OHW????

Yana karasawa asibitin yadaukota dukta bata masa motar da jini,

Yana shiga da ita wasu nurse suka ganshi da sauri aka janyo irin gadon nan mai taya aka azata akai, hilal yarike gefen gadon anan gudu yana kiran sunan ameelah,

Sai abakin kofar shiga emergency room sannan suka dakatar da shi,

Ba a son ransaba yatsaya, yana kuka ya jingina kansa a jikin ginin dakin da ameelah take ciki,

Kusan mintinsa goma a haka, kuka kawai yake, duk yarasa meke masa dadi, da wanne zaiji, bala in ameelah ko kade mutum dayayi,
A yanzu zuciyarsa cike take da zargin ameelah akan tana cutarsa, kuma tana cin AMANAR AUREn sa,

Cen bayan wasu yan sec yaji an tabashi ta baya, yana juyowa a kasale, suka hada edo da wadda tatabashi, ya rungume matar data tabashi yana kuka yace “umma ameelana zata mutu”

Ummansa ta taji tausayinsa sosai, tadago kansa… amma hilal yakasa bude edonsa domin idan yabude jiri yame gani, tace “garin yaya haka takasance, ina zaune gida hajna tazo tasanar dani cewa taga kadauko ameelah cikin jini”
Hilal ya bude janjayen edon dasauri yana kuka yace ” ummana zuciyata tana zargin ameelah akan tana cin amanata, amma kuma saina karyata zuciyata, ummana idan kuwa hakane Ameelah tanacin amanana, umma…..”
Tunkafin yakarasa maganar shock ya dibesa zube kasa a some,

Umma da hajna tare sukazo asibitin, dasauri suka kira likita shima hilal aka bashi gado acikin asibin,
*** *** ***

Acen kuwa gefen gidan su afham, tun bayan da abba yabar gidan lokacin da suka sami takardar afham ta barin gari,

Yana fita gidan mahaifin amal yanufa yasanar dashi komai dake faruwa mahaifin amal yayi jimami sosai,

Abban afham yace shifa haryanzh yananan kan bakarsa ta dauren auren amal da afham idan mahaifin amal zai amince a yanzu su daura musu aure, dan aure shedu kawai yake nema kuma gasu nan,

Abban amal bazai iya musawa abban afham ba amma baason ransa ya aminceba,
Anan abban afham yazare kudin sadaki, kamar yadda addina yatanada yabawa mahaifin amal,

Mahaifin amal yace abari yafita waje yakira koda limaman unguwane,

Abban afham ya amince da hakan,
Mahaifin amal yafita yaje yakira limaman unguwa da dattjiwan unguwa suka fita a harabar gidan su amal anan aka dauka auren AFHAM DA AMAL..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button