BABU SO 54
Typing????
*_????BABU SO....!!????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
BABU SO????????AREWABOOKS
54
………Ƙara riƙo hanun yay da ƙyau idanunsa masu kaifi na saukar mata da kasalar data mantar da ita wanzuwar su aunty Sakina a falon. Dama haka yake buƙata, ta manta da wanzuwar tasu ya samu damar isar da gargaɗinsa garesu batare daya samu wani tangarda daga gareta ba.
“Dama haka ake bama miji abu?”.
Ya faɗi maganar a salon daya nema ɗauke numfashin Anaam na wucin gadi, dan muryar da yay mata magana da ita muryace da zata iya rantsuwa bata taɓa ji daga garesa ba. Da ƙyar ta iya ƙwato kanta, tai ƙoƙarin ajiye masa kayan a hanun kujerar da janye nata idanun daya sargafe a nasa dan ta gama yanke shawarar barin wajen kafin a samu matsala yaga rauninta. Tana daga kafa ya riƙo hanunta tare da jawota sai gata ɗaram a cinyarsa tamkar walƙiya. Kafin tunanin wani abu ya risketa har ya yimata zobe da hanunsa ta hanyar ɗorawa a saman cikinta ya manne bayanta da ƙirjinsa kansa bisa wuyanta yana shinshina da fara magana cikin kunenta da wani salon daya saka tsigar jikinta tashi.. “A haka ake bama miji abu ba’a tsaye ba”.
Saukar wata mulmulalliyar ashariya cikin kunnuwansu ta tilastata ƙanƙamesa babu shiri dan da gaske ta tsorata dama gata a tsakkiyar wani firgicin. Harga ALLAH ta manta da su a falon, saɓanin shi da duk abinda yakeyi domin su ɗinne dama. A firgice ta ɗaga ido zata kallesu ya hana hakan, dan kuwa hanunsa ya tura cikin rigarta sai dai akan cikinta ya tsaya.. Ɗan matsawar da yay ta sata saki ƙarar ruɗewa dan a bazata abin yazo mata kuma taji zafi……
Rige-rigen fita aka farayi tsakanin Hajiya Luba da Aunty Sakina, saboda ƙarar Anaam ɗin fassara daban suka bata. Aunty Sakina ma harda gwara kai a jikin garu lokacin da suke turereniyar ficewa.
Hanunsa da taketa faman kaima mintsini ya janye, ta mike zumbur daga cinyar tasa idanunta taf kunya. Riƙota ya sake yi fuskarsa ɗauke da murmushin ƙeta. “Malama nace na gama n….”
Hararar data wulla masa ce ta hanashi ƙarasa faɗa ya saki dariyar data ƙara ƙular da ita tana jin zafinsa har cikin maƙoshinta. Sake fisgota yay ta dawo saman cinyar tasa. Ya haɗe hannayenta duk biyu dake son turesa ya danne akan cikinta. “Idan idanunki suka cigaba da harararta daga yau sai na miki haɗiyar ɗan sululu a gidan nan fitsararriya”. Mutsu-mutsunta ta cigaba dayi na son ƙwacewa yaƙi bata dama. Saima lanƙwansota yay ta kwano jikinsa ya kai goshinsa kan nata ya haɗe. Yawu ta fara kokawar haɗiyewa da sauri-sauri ganin yana daidaita lips ɗinsu.
“Please Yaya dan ALLAH kar kayi bana so”.
Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya, “Fitinanniyar yarinya minace zanyi to?”.
Bakinta da take faman karewa da hannu tatura gaba da ƙoƙarin kauda fuskarta ya tare da hannunsa, tare da janye nata hanun ya manne lips ɗinsu. So take ta turesa, amma tasirin abinda yake matan a cikin jini yana barazanar hanata kowanne irin yunƙuri, daɗin daɗawa ya riƙe hanunta ta yanda bazata iya ko motsashi ba. A karon farko ta fara maida masa murtani a yau dan tasirin salon nasa jinin jikinta ya fara amsarsa da ƙarfin gwiwa da wani sirrin ɓoye dake can ƙasan zuciyarta da ita kanta har yanzu bata san da zamansa ba tattare da ita. Hakan tamkar ƙara zugane a garesa da dukkan haƙurinsa, dan kai tsaye zuciyarsa ta fara ingizasa ga kaiwa inda bai gama shirya kai kansa ba. Ring na wayarsa ne ya dawo dasu duniyar da suka jima da yin nisan barin cikinta da lissafi irin na masu hankali. Sakinta yay, zaram ta miƙe kamar wadda take a tsinin allura. Da sassarfa ta bar falon ko waiwayensa taƙi tayi. Da kallo ya bita yana sakin kakkauran numfashi da murmushi, a hankali yakai bayansa jikin makarin kujera ya kwantar yana mai lumshe idanunsa da sake sakin ajiyar zuciya a jajjere yana kai hanunsa ya shapo lips ɗinsa….
Tun fitowarsu take faman kaikawo a harabar gidan, dan ko sashen Fadwar sun gagara komawa tsabar mamaki da jinjina ƙwarewar iskancin Shareff ɗin a yau. Yaron da ko ido bai cika ɗagawa ya kalla mutane ba shine yay musu wannan baƙin iskancin. Ina bazata iya haƙuri har sai sunje gida ba, dole ne ta kira Mommy kam ai. Takai wayar kunenta tana faman kaɗa ƙafafu da jijjiga jiki na tsantsar bala’i. Cikin sa’a aka ɗaga mata gab da zata tsinke.
“Sakina har kun isa gidanne?”.
Mommy ta faɗa tunkan aunty Sakinar tace wani abu. Aiko cikin matuƙar ɗacin murya ta tare numfashin Mommy din da faɗin, “A dole Mustapha kam yafi karfinki wlhy Yaya Nafi! Dan tabbas babu makawa an wanke an basa ya sha.”
Ƙirjin Mommy ya buga da ƙarfi, sai dai kafin tace wani abu Aunty Sakina ta cigaba da bata labarin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Ta ƙare da faɗin, “Zama dai kam bai gammu ba dan wannan yarinyar tafi uwarta hatsabibanci. Nan gaba babu makawa zaima iya cewa kwanciyar aure zaiyi da ita a gabanki saboda ya tabbatarma duniya shi ɗin tantirine na gask……” Ƙitt!! Wayar ta yanke. Tai saurin cirota a kunenta tana kallo a tunaninta ko kuɗine suka ƙare. Ƙoƙarin siya tai ta banki ta ƙara kiran Mommy ɗin. Sai dai kuma number busy ake nuna mata alamar waya take ko kiran wani…..
Ring ɗin wayarsa ne ya sake sashi buɗe idanunsa da har yanzu ke’a rufe. Ya kafe fuskar wayar da kallo tamkar mai tsoron ɗauka ganin sunan First Luv ruƙu-ruƙu na yawo. Rabon da suyi koda waya ne harya manta, ya kuma tabbatar gargaɗin da yayma su Aunty Sakina ya risketa ne matsayin saƙo. Bazai iya ƙin ɗaga kiranta ba koda yana jin tsoron dukkan wani furuci daga bakinta, kimarta da girmanta sun wuce a musalta a cikin idanunsa da zuciyarsa. Hannu ya kai ya ɗaga tana gab da tsinkewa, yakai kunen nasa cikin ƙarfafa kai….
“First luv barka da safiya”.
“First ubanka ba first luv ba. Al-Mustapha wlhy ina gab da jamaka kalmar ALLAH ya i…..”
“Please First luv, abeg kar kice haka dan girman ALLAH.”
“Idan ka sake kirana da sunannan ALLAH sai naci ubanka. Kuma kazo ina nemanka idan ba hakaba ka bari na tako ƙafata gidanka da kaina yarinyar nan na a ciki wlhy wlhy wlhy kadaiji na rantse ko! Sai na jamaka ALLAH ya isa da manyan baƙi no-no na daka sha dan bakai kaɗai na haifa ba balle ka ɗauramin hawan jini”.
Harshensa har sarƙewa yake wajen faɗin, “Shi… Shike nan naji zanyi, zan zo, amma kimun alfarma Mommy dan ALLAH sai gob…….”
“Alfarma ubanka, Al-Mustapha ni kake son tozartawa a idon maƙiyana dai ko? Kana nunama duniya mace ta fini daraja da kima a idonka?”. Ta faɗa tana fashe masa da kuka. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi, ya girgiza kai tamkar yana a gabanta. “Mommy wlhy babu wata mace da darajarta zata ko kama ƙafarki a wajena. Dan ALLAH ki fahimceni Mommy ina a tsaka mai wuya……”
A fusace ta yunƙuro zatai magana Gwaggo ta fisge wayar. “Nafisa wai kin rasa hankalinki ne halan?! A tunaninki wannan butsutsun naki akan Mustapha shine mafita ta ƙarshe da zakibi wajen raba auren?!!……”
Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da lumshe idanunsa ya saki wayar a jikinsa batare daya ƙarasa jin abinda Gwaggon ke faɗa ba. Dan kuwa tabbas a wannan gaɓar ta taimakesa taimako irin wanda bakinsa bazai iya maimaita faɗa ba, sosai al’amarin Mommy ke daɗa tayar masa da hankali, ya rasa ta inda zai kama domin shawo kanta akan wannan aure. Har yanzu yarasa gane minene takamaimai laifin su Abie a gareta da take musu irin wannan ƙiyayyar (Niko nace Shareff a haka ta tashi, tun tana ƙaramarta an riga an cusa mata ƙinsu. Haka ɗan adam yake, a duk lokacin daka koyar da shi wani abu ƙyaƙyƙyawa ko mummuna yakanzo ya fika iyawa. Iyaye tabbas muna kuskure, kuskuren da shike saka ƴan ubanci a zukatan ƴaƴanmu tsakaninsu da ƴan uwansu. A kullum baki da aiki saina aibanta kishiyarki gaban ƴaƴanki, baki da aiki sai na zaginta da nuna cutarki take zaluntarki take bata sonki, bata ƙaunarki, maƙiyarki ce kuma a gaban ƴaƴanki. Tayaya kike tunanin bazasu tsaneta su tsani ƴaƴanta fiye da yanda kike tsanarta ba, saboda ke ra’ayin ƙinta ya shigekine da girmanki da hankalinki, idan kin so zaki iya yaƙarsa, suko kin raini zukatansu ne akan wannan ƙiyayyar, dolene su dawwama da ƙinta da ƙin duk wani abinda ya shafeta koda bata aikata musu komai ba na ƙi ɗin. ALLAH ka gafarta mana ka gana damu gaskiya koda bazata mana daɗi ko zuwa dai-dai da son zukatanmu ba).
Anan falon yabar lap-top ɗin da takardun ya fice, koda ya fito su Aunty Samira sun wuce dan baiga motarsu ba. Motar ya shiga shima ya fita a gidan, dan yana buƙatar yin nesa da su har zuciyarsa ta huce. Haka yake baya son yanke hukunci cikin fushi, ya gwammaci yin nesa da abu a duk lokacin da zuciyarsa ta harzuƙa. Asibiti ya nufa wajen Dr Jamal, sai da ya shigo cikin asibitin sannan ya kira wayarsa..
Daga can Dr Jamal yace, “Ka shigo mana, ni kaɗaine ma a office”.
Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yanke wayar, bai cika san buɗe cikinsa ga kowa ba. Amma dai mutane biyunnan sun wuce abokai kawai a garesa aminaine na gaskiya. Daga Dr Jamal har Fharhan abokansa ne tunna ƙuruciya, koda yabar ƙasar kuma basu yarda juna ba. Basu da abokin shawara sama da shi, duk da shi yakan jima basuji nasa cikin ba saboda yanada zurfin ciki matuƙa. Na ukunsu kuwa shine Khaleel, duk da kasancewarsa ƙani a garesa hankalin yaron da nutsuwarsa kansa ya kallesa tamkar aboki, sannan shima Khaleel ɗin bashi da wani amini sama da shi duk da yana amsa sunan yayansa ne.
Sai da yay knocking aka bashi izinin shiga sannan ya shiga. Dr Jamal na zaune a kujerarsa ya amsa masa sallamar da yay fuskarsa da murmushi. Cikin danne kishin rashin Anaam yace, “Ango kasha ƙamshi”. Harararsa ya ɗanyi ya ɗauke kai, ya zube cikin kukerar dake gaban desk ɗin Dr Jamal ɗin yana furzar da iska mai nauyi. Dr Jamal dake binsa da kallo danya fahimci damuwa a fuskar abokin nasa ya miƙa masa hannu sukai musabaha.
“Wai yana ganka haka kamar mara lafiya? Ko jikinne har yanzun?”.
Kai ya girgiza masa, sai dai baice komai ba. Dr Jamal ya tsura masa ido na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe ya ɗakko masa ruwa. Baiyi musu ba ya amsa, murfin ya ɓalle ya kai bakinsa. Tass ya shanyesa yana dire robar da lumshe idanu ya sake lafewa a kujerar yana sauke numfashi. Kusan mintuna uku suna zaune a haka shiru, kafin ya buɗe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya canja ya kalla Dr Jamal daya tsura masa ido…
“Kai kurwana da ɗaci irin wannan kallo haka”.
Dariya Dr Jamal ya kwashe da shi. “Ɗan wulakanci, inda ni maye ne ALLAH kamun kaɗan a ci ɗan iska kawai”.
Murmushi yay a karon farko da gyara zamansa. “To zama mayen mana kaga idan zan ciwu a wajenka mara mutunci”.
Dr Jamal yay dariya kawai. Sai kuma ya miƙe daga kujerar zamansa ya dawo inda Shareff ɗin ke zauna shima ya zauna suna facing juna. “Mike faruwa? Damuwa ta kasa ɓoyuwa a kan fuskarka my Dude”. Nannauyan numfashi ya sauke da ɗan ɗage kafaɗa, “Bani da wata damuwa kawai dai nace bari in gaisheka”. Idanu Dr Jamal ya tsura masa fuskarsa na canjawa zuwa jin haushi……..