AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 79-80

??79 and 80??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Ameelah ce take yunkurin kasheka,

Duban kowa a dakin yadawo kan hajna,

Momy tayi saurin dago kanta tace ” karki shigo cikin maganar mu keme kika sani”

Hajna tashare hawayen tayi taku takaraso kusa da momy tace ” ai kuwa ninasan komai, domin kuwa ni yarki take gayawa komai kuma a yanzu zantona mata asiri, nagaji da ganin yadda take cutar dan uwana, zumuncin dake tsakanina da hilal yafi wadda yake, tsakanina da ameelah..,

Hilal yada mata hannu yace “kar inji kinfadi komai anan “

jinkalaman hilal yasa hajna tasaka kuka tana cewa ” yaya hilal saidai kayi hkr amma wlh saina fada domin nagaji da daganin yadda ameelah takecin AMANAR AUREN ka, ameelah tana chart da samari a wayarta, tun kafin tayi aure, kuma datayi aure saita kasa dainawa, hatta ranar da aka kai ameelah dakinta har A ranar saida ameelah tayi chart har kusan karfe biyun dare, ta charting Suka hadu da wannan mutumen, wadda tayi save din Number shi da hmm, soyayya sukeyi, kuma ta nunan masa cewa ita ba matar aure bace, shikuwa saurayin yayi matukar kamuwa da sonta,
Wata rana naje gidan ameelah a ranar tasanar dani cewa

Mutum da take tare dashi a chart yanada hadari sosai.

Hajna Tajuya gefen da hilal yake wadda tun alokacin data fara magana ya gazgata ta,

Suka hadu edo ita da hilal taci gaba da cewa “ya hilal idan bazaka mantaba kwana ukku da suka wuce naje gidanka, to aranar ne ameelah tasanar dani komai akan saurayin, domin kuwa shi saurayin yasanar da ita cewa shifa baa yaudararsa kuma duk maccen data yaudaresa to hukuncin kisane akanta,

Aranar nabawa ameelah shawar wari dadama akan tadaina chart da maza, amma taki ji daga karshema cemun tayi, tayi wani sabon saurayi hadande wai ko sunansa AFHAM kuma dan abuja ne..

Hilal ya zare ido?? yana kallon hajna, bakinsa na rawa yace Afham”

Momyn ameelah kuka take sosai tace “wallahi karya take, ameelah bazata iya yin wannan abunba, kazafine take mata”

Zuciyar hilal tadau zafi da karfi yadakawa momy tsawa “ya isah haka,”

Saida momy ta zabura, ganin yanayin edanunsa sunyi ja yasa takame bakinta, jikinta yadau rawa ta tazana sosai, har mamaki tarika yi a zuci “ayya kuwa wannan hilal ne, ba aljannu suka shiga jikin saba

Hawaye tab a edon hilal umma ma haka, hajna tana tsaye, tana kallon hilal habar bakinsan har wani rawa take,

Da karfi hilal yaja jikinsa, yafita waje, umma na kiran sunan sa amma yaji tsayawa,
Dataga baidawo ba, tabi bayansa ita da hajna da abban ameelah,

Dakin da Afham yake ciki ya nufa harya karasa bakin kofa, wasu likitoce da suke tsaye a bakin kofar suka hanashi shiga,

Tsawa ya daka musu saida dayan yafadi, bashiri suka bashi wuri kofar yabude ya shiga dakin…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button