KWARATA 5

???? —— 5
Muna shiga ciki tun kafin mu k’arasa inda suke zaune Baba ya fara cewa tou gata nan ku tambayeta kuji, a daidai lokacin da muka iso gabansu.
Ina k’ok’arin durk’usawa Bello yace a , a basai na zauna ba in tsaya a tsaye akwai abinda yake dubawa.
‘Dan b’ata fuska Babana yayi tare da cewa kamar ya kana duba wani abu ? Ai a cikin sharud’d’an babu maganar wani dube dube, dan haka kabar yarinya ta zauna ka wani daina yi mata kallon k’urulla saboda rake ba sa’ar tsoho bane ba, dan koya bada kudin sa ya siya saiya ajiye tunda baida hak’oran cizawa, ya k’arasa maganar cikin sigar duniyanci.
Murmushi Bello yayi tare da cewa, ai zamani tafiye yake da ci gaba ko ba’a tauna ba a tsotsa, d’an b’ata rai Babana yayi tare da cewa, kaga da Allah mubar wannan maganar muyi abinda ya had’amu, ya k’arasa maganar cikin nuna rashin jin dad’in zancen nasu.
Gyara zama Bello yayi tare da cewa, haba Aliyu kasanni fa farin sani, kuma haka nima nasanka ciki da wajen ka, wane dare ne jemage bai gani ba ? Na hau tudu nabi ta gangare, kasan ko inacin kwarika wannan kwaron yayi min k’ank’anta shi yasa kaga bana cin shinge saboda na raina girmanshi duk da kuwa yana da mai sosai nafi gane kura ko da kuwa an soyata babu magi ba gishiri, kalmar dai d’ayace ake kira amma wurin hidimar da banbanci karka samu damuwa yaro ne sabon jini kuma bak’one a harka, yasan dad’in komai a duniya amma har yanzu baisan dad’in mace ba shi yasa kaga inata k’ara dubawa dan bana san a samu damuwa,
Dariyar mugunta yayi tare da cewa , wash ashe na manta malamar Babanta jarumin gaske ne a harkar wasan caca, Shima Babana murmushi yayi amma da ganin murmushi kasan na b’acin rai ne, yace Bello kenan, shiga ramin kura ba abu ne mai sauk’i ba, idan har kaga na fad’i a wasan cacar nan tabbas duk wanda yayi k’ok’arin kusantar min Mama saina ga bayanshi, wannan shine sharadi na,
Bello kuma cewa yayi kar muyi haka dakai Aliyu yaron nan d’an rigima ne, mu daina wannan maganar kawai dai muyi fatan Allah yaba mai rabo nasara, kallona yayi tare da cewa kin amince ? Jinjina kaina nayi tare da kallon Babana sannan nace na yadda………… Dariya Bello yayi tare da cewa magana ta k’are mata tacewa mijinta shege,
Kafad’ar Babana ya daka tare da cewa Aliyu muje, juyowa yayi ya kaleni tare da cewa yarinya ki shirya, idan kinga Babanki tou fa lallai an ciki a wasan caca, idan kuma kika ga Bello tou Babanki ya cinye matashin nan, ganinmu shine zai tabbatar miki Babanki yaci caca mu kuma munzo miki murna ne, suna fad’in haka sukayi gaba abunsu,
Bayan tafiyarsu ina zaune suku suku dani kamar asirin mayya ya tonu, ni ba Babana ne damuwata ba Dikko shine tashin hankalina, yace duk inda nake a gano ni, sai yanzu na gane na tafka babban kuskure dana rubuta suna na a jikin takarda, lallai na cika babban dak’ik’iya.
A b’an garen Dikko kuwa nema na sukeyi kamar rai da mutuwa, babu wanda yasan inda muka koma, daga makaranta prymary babu wanda ya sake jin labarinmu,
Rashin gani na yasa suka fara ba Dikko hak’uri, amma fur Dikko yace wallahi kafin sha biyun dare sai an nemoni idan har ba’a ganni ba zai iya sargafe kanshi ya mutu,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Duk iyakar yanda suka so Dikko ya hak’ura ya k’iya, ba nemoni bane wahala a wurinsu suna tausayin irin a zaftuwar da zanyi a wurin Dikko, dan ya fad’a musu ba mutuwar dokin ya b’ata masa rai ba, d’an marasa tarbiya dana kirashi dashi, bama shine baida tarbiyar ba iyayenshi ne basu da tarbiya abinda nake nufi kenan,sai kuma idan ya fasa shi ba d’an Babanshi bane. Wannan sune munanan kalamai masu muni da suke ta zungurar zuciyar Dikko.
Dikko yana da zuciya sosai, kuma fushin shi baya da kyan gani, idan ya nace akan abu sai yayi babu wanda ya isa ya hanashi, idan yace bayayi babu wanda ya isa ya tursasa masa yayi abinda baisa kanshi ba.
Yau Dikko yana cikin matsanan cin b’acin rai, yayin da ni kuma nake cikin fargaba da tashin hankali, dan yanayin dana ga Dikko d’azu ya bani tsoro,
Duk wanda yaji wannan abun yasan nice bani da gaskiya, domin ni naje har inda yake na jawoshi fad’a, ya Allah ka rabani da Dikko daga yau insha Allah bazan sake janshi fad’a ba, ka mantar mishi dani a rayuwarshi kuma ka bashi hak’uri a zuciyarshi, ya daina nemana,
Misalin 10:45pm Babana ya dawo gida, dashi da abokinshi Bello a lokacin har nayi bacci Baba yasa a tadoni in samesu kofar gida……
A waje na samesu, gaishe su nayi tare dayi musu sannu da zuwa, Bello kad’ai ya ansa amma Babana ya kasa magana, Bello ne ya fara magana kamar haka.
Maryam, wannan shine sunan da Babana ya sakamin, wato sunan mahaifiyar shi, darajar wannan suna ne yake kirana da Uwar masu gida ko yace Mamana, Bello yaci gaba da cewa an samu matsala mahassada suka cuci Babanki bandai san yanda abun ya faru ba gab da za’a fara wasa kwalwarshi ta juya, ba buk’atar dogon bayani kawai dai Aliyu ya fad’i wasa.
Tou idan ya fad’i sai kayi ya ya kenan ? Na tambayi Bello, sai zamu tafi dake wurin wanda ya ranta masa kud’in, dan a can basu yadda da ansar mace ba, sai wani ya buk’ata dan haka ya bada kud’in yace a kawo mishi ke,
Waye shi ? Na sake tambaya, a tak’aice ya bani amsa cewa idan kinje kin ganshi, zan k’ara magana Babana yace Mamana babu abinda zai faru kiyi hak’uri kuje dan bana tunanin akwai wanda ya isa yayi miki wani abu a cikinsu saboda sun san waye ni, na bud’e bakina zan sakeyin magana a karo na biyu, wanda Babana ya sake tare min numfashi na da cewa idan dai har kare zai iya farautar kura tou lallai wani abu zai iya shiga tsakaninku, idan kuwa kare bazai iya ba tabbas zasu dawo dake, dan duk rashin kunyar kare ta gida ce, bishi kuje…. Yana fad’in haka ya juya da zumar shiga gida,
Da gudu nabi bayan Babana na rik’e hannunshi ina kuka nace haba Babana laifin me nayi maka zaka sayar dani ? Cikin kulawa ya kalleni tare da gogemin hawayen da suka zubo saman fuska ta sannan yace, baki sawuwa Mamana saboda nima bada kud’i nasiyo ki ba, haka kuma bakya satuwa tunda Allah shine ya azurtani dake, hak’ik’a kuma baza ki ciwo ba ta sanadiyar wasan caca ko kun tafi sai kun dawo, dan haka ki zama d’iya mai biyayya a gareni,….
Baba…..Mamana ya fad’a kafin nace komai, yaci gaba da cewa, so guda d’aya ne tal a zuciyar ko wane d’an adam, amma shi wannan san a duniya za’a kasa shi kaso mutane so adadin haka, uwa, uba, d’a da kuma mata, banda uwa banda uba, kuma ni Allah bai d’oranmin ciwon son “ya “ya ba, bare mace da ban d’auketa a bakin komai ba, wannan son nawa gaba d’aya kece na martaba ki dashi saboda ki zamo d’iya mai sharewa Babanta damuwa. Sakin hannu na yayi tare da cewa sai kun dawo, yana fad’in haka ya shigr gida.
Inaji ina gani suka tasa k’eyata gaba suka sakani mota mukabar k’ofar gidanmu, tafiya mukayi mai nisa sosai, sannan Bello da abokinshi daya taho dashi suka fara magana,
Bello yace, alhamdulillah na zurashi rami na gama, kasan Aliyu yana tak’ama da tasha ni kuma zan k’ure mishi tashi tashar shi dan abinda yayi min bazan manta dashi ba nima saina rama akan wannan d’iyar tashi daya d’auka san duniya ya d’ora mata,
Bello yaci gaba da cewa nine na bada kud’in nan cas saida na ajiyesu sannan akayi caca, bana asara zan kaita inda za’a bani kud’ina har a d’ora mani riba, ina tsoron wai wai da bayan da Aliyu zaiyi wallahi da nine zanyi mata kaca kaca da rayuwa amma yanzu zan kaita wurin gwamnati idan zai iya yayi fad’a da hukuma in gani.
Ai kaji shi wai Allah baisa mishi ciwon san “ya “ya ba, nima shi yasa ban zab’i ko d’aya daga cikinsu ba dan nasan duk wacce na d’auka abin bazai mishi ciwo ba, nima ina so in dasa masa irin tabon daya dab’a min a zuciyata wanda bansan ranar da zai gogo ba,
Ajiyar zuciya Bello ya sauke tare da cewa da Allah sake kiransu ni fa ba abinda ya dameni da wani fushin banzar shi, dan ba fushi yakeyi ba ko mutuwa akayi mishi ni kawai tafiya zanyi idan munje can ayita ta k’are, abokinsa yace to idan masu gadi suka hanamu shiga fa ? Daina min ma wannan bak’ar fatar taka da Allah, duba min magungunan nan Allah yasa ban zubar dasu ba wurin wancan sakaran, wata “yar k’aramar leda ya d’auko ya mik’a ma Bello tare da cewa gasu nan, dariya Bello yayi sosai tare da cewa kasan bak’one dole saida “yan rakiya,
A daidai lokacin daya fara magana a waya, nifa dama basai yana harkar mata ba, to dama banda abinka duk wanda kaga yana harkar mata ai koya yayi, nifa taimaka min zaiyi kuma na taimakeshi, saurara ka taimaka mana kazo ka shigar damu gidan idan muka shiga duk nasan yanda zanyi da Allah, tou babu damuwa gamu nan isowa ba jimawa, haka yayi wayarshi har ya gama, yakan d’auke maganar sa danjin abinda abokin wayar tasa zai fad’a, yana fad’in haka yaja motar muka tafi.
Ni kuma tunanin abinda Babana yayi masa kawai nakeyi wanda har yasa zaiyi ma Baba ramuwar gayya, ina tunani naji yana dariya tare da cewa an fad’a maka ni sakarai ne ? Ai kaima kasan baiyi cacar ba dan ubanshi dasai yaci, mugu ya saki baki ya lashe kud’i mu kuma muka lashe “yar sa, dariya ya k’arayi sosai tare da kaiwa sitiyari duka yace kud’i na biya malamai suka sa banza wasi wasi……. Amma ai kasan Aliyu maye ne da yayi wasan caca da gaske dasai ya lashe kudin nan kamar yadda karuwa ke lashe sabon harka……….
Ya kuma sabon harka ? Su sai suyi ta magana juyayya wanda sai su “yan bariki kad’ai suka isa su fassara yaren, ina ne nan kuma ? Na tambayi kaina yayin da muka tsaya gaban wani k’aton get, ga jami’an tsaro masu yawan gaske kowa ya kame da bindiga takai tsawo na, za’a fara magana wani daga cikin mota yace barsu su shiga tare muke,
K’arfe ne aka d’age mana muka shige saida mukayi tafiya mai d’an nisa sannan muka tsaya, daidai da daidai kowa yana zaune cikin mota wanda ya shigo damu yace, Bello bana so nayi maka gardama ne kaga kamar wani abu amma na rantse maka da girman Allah Dikko baya neman mata,
Wani irin tashin hankali naji yayin da naji an kira sunan Dikko sai yanzu na tuna da Dikkon da zaici uwata, hankalina na mayar a wurin Bello dake cewa kai ai sakaran banza ne idan zai nemi mata shawara zai maka ? Ai ba’a shedar namiji akan mace, murmushi mutumin yayi tare da cewa Bello na rantse maka da girman Allah har al-qur’ani zan iya dafawa Dikko bai harka mata,
Tsoki Bello yayi tare da cewa muje idan zaka raka mu dare nayi, jinjina kai yayi tare da cewa muje, yana gaba muna biye dashi saida muka wuce get ukku kafin mu isa, kuma duk inda mukaje jami’an tsaro ne har muka isa bakin wata k’ofa, dukkannin mu anan mukayi parking, kulle min ido da hannu Bello yayi bayan mun tsaya.
Rufe motar yayi da makulli sannan suka shiga ciki, wurin zama aka basu tare da cewa su jirashi yana zuwa, sunyi zaman daya wuce mintuna talatin sannan Dikko ya fito cikin tsananin b’acin rai dan har yanzu maganganun Sultana caccakar masa zuciya sukeyi, kuma ma koba komai dama shi Dikko ba ma’aboci sakin fuska bane,
Gaishe shi sukayi, da kanshi kawai ya ansa gaisuwar tare da tsare su da ido, mutumin daya kawomu shine ya d’urkusa gaban Dikko yayi masa magana k’asa k’asa wanda babu wanda yake iya jiyo abinda yake fad’a,
Kallo su Bello Dikko yayi tare da cewa da Allah kuyi hak’uri ita rayuwa sannu ake binta, babu wanda yasan abinda anjima zatayi bare kuma gobe, kar kace zakayi ramuwa akan duk abinda akayi maka wannan ba d’abi’a bace mai kyau, halin mutunan kirki sukan manta da duk wani abu mara kyau da akayi musu, ka zama mai yafiya akan ko wane irin mutum idan yayi maka laifi, kaima sai Allah ya gafarta maka, miliyan nawa ne ka kud’in ? Dikko ya karasa maganar tare da tambaya,
Cikin kwantar da murya Bello yace miliyan biyar ne na zuba, Dikko yace tou kai Sani kuje dashi ka bashi miliyan goma, a rik’a hak’uri kaji bawan Allah, gyara zama Bello yayi tare da cewa kayi hak’uri gaskiya ni ko miliyan d’ari zaka bani wallahi basu ne gabana ba a yanzu kawai so nakeyi ka ramamin abinda ubanta yayi min.
‘Daure fuska Dikko yayi domin duk cikin k’arfin hili yake magana, shi duk duniya babu abinda ya tsana irin mutum yace ya wulakanta shi, danne zuciyarshi ya sakeyi tare da cewa kayi hakuri gaskiya Dikko baya neman mata,
Kayi hak’uri ranka ya dad’e ka ganta ko so d’aya ne nasan zatayi maka, kai jeka taho da ita da sauri, duk Bello ya fad’a ba tare daya bari Dikko ya sake cewa komai ba danshi Dikkon ma harya gaji da magana yayi shiru.
Kamar wata b’arauniya haka ya jawoni har yanzu idona a rufe yake, lallausar kafet in dana taka da wani sanyi mai shiga jiki sai wani irin daddad’an k’amshi mai dad’in shak’a naji, hakan ya tabbatar min an kawoni inda za’aci mutunci na, har yanzu banyi magana ba amma idona ya cika da hawaye dan da ba’a rufemin idona ba babu abinda zai hana na cika d’akin da kuka…..
A gaban Dikko aka durk’usar dani, amma shi ya kauda kanshi gefe d’aya bamu yake kallo ba, hankalin shi yana kan T V danma baya so ya kalli ko wace ce aka kawo dan babu zuciyar wanda shed’an bazaiyi wasa da ita ba,
Bud’e min fuska akayi da sauri na bud’e duk girman idanuwana na fara kalle kalle, innalillahi na fad’a a fili a lokacin da idonuwa na sukaci karo da Dikko tare da fara k’ok’arin mik’ewa,
Har yanzu Dikko bai juyo ba, dan haka nayi shiru dan karyaji magana ta, hijabin jikina suka ciremin da hular da na saka saman kaina, sannan aka turani saitin inda Dikko ke kallo, gaba d’aya kunya ta kamani dan haka na duk’ar da kaina k’asa,
Dikko bai kalleni ba, kuma baiyi magana ba, inaa tsaye a wurin kaina na kallon k’asa hannuwana kuma suna d’aure ta baya na, ina tsaye a wurin shima Dikko bai dainaa kallon T V ba dan har yanzu bai kalleni ba bare na tabbatar daya ganeni ko bai ganeni ba,
Shiru kowa yayi babu wanda ya sake magana har kusan tsawon awa d’aya, Bello ya gaji yace ranka ya dad’e zamu koma, yanzu ma kai ya jinjina ma Bello , matsowa Bello yayi a kusa da Dikko ya ajiye ledar daya zo da ita sannan yayi magana banji abinda yace ba, amma wannan karon Dikko bai ko motsa kanshi ba, fita sukayi suka tafi, shima wanda yayo mana jagora bin bayan su Bello yayi Dikko yace idan ka fita kaja man k’ofar,
Cikin girmamawa yace tou, yana fita yaja k’ofar gam wanda rufeta yasa naji wani irin tashin hankali na saki baki na fara kuka da dan Allah kayi hak’uri kar muyi haka dakai, mugu kenan yaji mugunta dan haka ya fara murmushi, ashe ma yafi kyau idan yana murmushi,
‘Dan wasa yayi da idanuwan shi sannan yad’anyi motsi da kanshi kamar yaji kid’a, saida ya k’ara k’ayataccen murmushi sannan ya d’aure fuskarshi kamar baisan miye dariya ba, ya tsareni da idanuwanshi masu sa mutum yaji yanajin fitsari, da sauri na mayar da kaina k’asa gabana yana ci gaba da bugawa.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }()); Wayarshi ya d’auka yayi danne danne sannan ya k’ura mata ido, d’an tab’e bakinsa yayi a daidai lokacin daya kara wayar a kunnen shi yana cewa duk duniya me mace “yar matshi ya ta tsana ayi mata ? Kallona yayi sosai sannan yace 16 zuwa 17, mai maganar a waya ya dad’e yanawa Dikko bayani, murmushi Dikko yayi har saida kyawawan hak’oransa suka fito sannan yace yayi tare da ajiye wayar,
Mik’ewa yayi bayan ya gama wayar ya kulle k’ofar da makulli ya tafi dashi ciki ya barni anan falo tsaye kamar wata gunkiya,
Bayan kamar wani lokaci mai tsayi ya dawo, inda ya zauna da farko a wurin ya sake zama sannaan yace min zo nan, babu musu naje gabanshi na durkusa kamar yanda naga anayi mishi,
Ya sunanki ? Suna na Sultana, da Allah me kike so nayi miki wanda zai tabbatar miki dani d’an Babana ne, shiru nayi bance komai ba, gyara zamanshi yayi tare da mik’e k’afarshi ya taka saman kafad’a ta, yace ina saurarenki.
Kayi hak’uri don Allah sharrin zuciya ne, to kinga kin kasa ba zuciyarki hak’uri a lokacin dana b’ata miki , ni yanzu waye zai ba tawa zuciyar hak’uri ?
Kayi hak’uri don Allah insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, kayi hakuri don Allah, kwantar da kanshi yayi jikin kujera yana nazari har yanzu k’afarshi tana kan kafad’ata, ba tare daya taso ba yace gaskiya kamar zan hak’ura amma na fasa,
Dan Allah kayi hak’uri, tasowa yayi tare da cewa wallahi bazanyi hak’uri ba yau zan nuna miki cewa ni d’an Babana ne, kuma da kanki zaki sheda ya iya haihu a daren nan zuwa safiya zaki anshi hukunci mafi munin hukunci, zan baki mamaki kuma zan nuna miki Dikko ba sa’an wasan yara bane, zan biga tambarina a zuciyarki za kiyi ta kuka daga yau har zuwa ranar mutuwar ki, yanayin farin ciki ko damuwa duk wanda kika shiga wallahi baza ki manta da Dikko ba a rayuwarki, dani dake kinga saiki fad’amin waye ciwon zuciya zai kama…..
Ka rufamin asiri, ke yarinya ya fad’a tare da takamin bakina da k’afarshi, da sauri na janye fuskata gefe guda tare da goge bakina da kafad’ata, kam balasti kafatace kike gogewa baki ? Tou bari kiji in fad’a miki wannan k’afar tafi ubanki tsafta, tafi uwarki ni kuma nafiki banza kazamiya d’iyar d’an caca, saboda san duniyar da bata da tabbas ubanki ya anshi kud’i ya bada ke, mutunci da ko wace “yar mutunci da iyayen mutunci suke tattalawa amma ke ya siyar dan biyan buk’atarshi,
Da sauri na kalli Dikko raina amatuk’ar b’ace nace gaka babban d’an iska da zakayi fasik’anci dani a cikin gidanku, ni ba fasik’i bane yarinya ki tambaya kiji ni babu mata a tsarin rayuwata shi yasa bana sabgarsu, amma kedai yau sai nayi miki kaca kaca wallahi yanda ko sunan Dikko kikaji sai kinyi fitsari, ya kara sa maganar tare da sake maida k’afarshi ya takamin baki,
Sake janye k’afar nayi daga bakina na k’ara juya kaina gefe, dariya Dikko yayi tare da sauko kafarshi saitin k’irjina ya taka tare da tura babban d’an yatsan shi cikin riga ta sannan yaja da k’arfi, b’earr k’arar yagewar rigata, cika idona yayi da hawaye kuma ga hannu na d’aure ta baya, dan girman Allah kayi hakuri karka ciremin kayana,
Sai k’ara tattakani yakeyi, gajiya nayi da iskancin shi nace sakaran banza kwance min hannuna na kaga yanda zanci k’aniyar ka a daren nan,