FITAR RANA 1
Alhamdullahi rabbil Aalameen.This is a short, hopely amazing story of a witty-smart girl wasimé Aliyou in her love_hate relationship with her biggest critic yet wildest fantasy,i hope u’did enjoy it.thanks!😘
BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.
6:15pm Bunu: Shammo cluster,east language of kainji,toro L.G.A bauchi state.
Lokacine da almuru ya ƙeto gab gabotawar sallahn magriba. wata ƙibabbiyar matace wacce a shekaru bazata haura sama da arba’in ba, kalar fatar jikinta ɓaki kirin ta ƙife irin fallen zanin atamfar dake jikinta akanta tayi lullubi dashi har saman idanunta tamkar wacce bataso a kalli tsananin munin fuskarta, dauƙe take da man fetur da kuma ashana ahannunta, ta tsaya a ƙofar wani matsaikaicin gida ginin blo dayajima sosai duk ya balangwaje ya tsofe ginin ya karsashe wanda ana taɓa bangon ƙasane kawai ke zuba.
Daga cikin gidan Babu abunda ke tashi acikin dan tsurkukun dakin nasu sama da zautaccen bugun sautin wahalallaleyar numfashin mace wacce amonsa tayi kama da kamar ranta ake zarewa acikin tukikin ciwon naƙuda mai azabtarwa da kuma radadi,ita kadai sai murƙususu takeyi acikin dakinta tana tauna laɓɓanta tana wayyo Allahnta amma kashh!! shiru kakeji babu wanda ya kawo mata doƙi.
Bisa Kallo daya kayiwa matar zaka fahimce cewa bazata wuce kimanin shekaru arbain da takwas a haife ba,murmurarreyar mace ce mai ginannen jiki wanda duk da alamun wahala da talauci dayayi mata naso ajikinta da kangon dakinta bazai taba hanaka kallon kyakkwar surar halitta da Allah yay mata ba.,ba kuma ina nufin tsantsar kyauna kwatantacin siffar ƴayan aljanu ba,a a, .ina nufin itama baqace sidik original melanin beauty, mai dauke da natural skin na matanmu na mutan biu(a jahar maiduguri) tabbas matar nan ta mallaki sulbabben sheqin fatar su mai kyau da daukar ido,game da dirarren shape da baƙin suman kai dai dai cikon misali.
Har kwatankwacin Misalin tara na dare amma haryanzu shiru,iska ne ya cigaba da kadawa sakamakon yanayin damina ne duhun inya rufa har ba a iya kallon hasken tafin hannu.
Matar can tana waje,mai naƙudar nan itama tana cikin gida tana kkrin fidda nishi,kuma Dukkansu basu rusuna akan qudurorinsu ba.
Duk wani addua daya fixgo kanshi cikin bakinta da zucyarta yinshi kawai takeyi danta samu saukin azabar naƙuda datake sha ajikinta dan kuwa yau Shekarunta 30 kenan da yin aure a duniya amma bata taɓa samun haihuwa ba sai a wannan ƙaron da jiki ya riga ya ragwabe tsufa kuma yaxo mata rayuwa ya kuma musu tsanani ita da mijinta malam hassan(aliyu) denge a hannun muguwar amaryasa Anmuna.
Maimunatu garba,
wacce akafi sani da Anmunah mayya yar gidan garba maye ta kasance tamkar wata mujiya ce acikin alummar shammo ta kabilar ribinawa a jihar bauchi, kasancewar zargin da akeyiwa mahaifinta nacewa shi mayene Shekara da shekaru bacin duk wani alamu sun nuna hakan amma rashin ƙwakkwarn shaidu shi ya hana a gurfanar dashi.Qaddara shiya janyo aure tsakanin anmuna da malam hassan mijin badiatu wanda tunda suka ƙafa alƙalmin tarihin zaman auren su basu taba sabawa juna ba,mutane ne masu tsantsar hkuri da juriya tare da takantsantsan da rayuwarsu gameda kyakkwar zuciya,a tunanin su kawo anmuna cikin zamantakewar su zai iya jawo musu albarkan haihuwa bayan tsawon shekaru da sukaja basu samu ɗa ko ƴa ba,anmuna takai shekaru sama da arba’in babu wanda ya taba taya aurenta sabida halin mahaifinta na maita,acikin tsangwama tay rayuwarta,malam hassan da badiatu ne kawai suka tausaya mata, amma sai abun yazo musu da sabuwar qaddara wanda basu tabayin tsammanin cin karo dashi ba.
Dan kuwa tunda anmuna ta shigo cikin gidan su da sunan aure yau shekaru goma kenan malam hassan da matarsa badiatu suke cikin tasƙon rayuwa mai tsanani.
Duk wani albarkan Rayuwarsu saida tayi fatali dashi,ta talautasu ta muzanta su,tayi zaman diris akan dukiyarsu sannan ta sassaka musu ciwuka kala kala ajikinsu.
Tunda badiatu ta same wann cikin yakasance malam hassan bayada wani kwanciyar hankli
Yaushine nan gobe shine can duk dan ya ƙare matarsa badiatu daga mummunan kaidin anmuna,ahakan ma da ikon Allah ne kawai sukaci nasara dan kuwa tasha alwashin dauƙar ransu duka inhar ya sake badiatu ta haihu mata acikin gida.
Yau tun safe ya fita neman taimako awajen wani babban malamin addini dake taimaka musu sosai wajen ƙaresu awani dan kauye,duk hanklinshi baijikinshi, ya tafi yabar badiatu cikin ciwon ciki yasan izuwa yanzu ta galabaice,yana amsar magungunan da malam ya damƙa masa ya kamo hanyar gida cikin gaggawa,tafiya yake kamar zaici da baki tsabar sauri amma sai yaga kamar ana komar dashi baya, ko yayi lalume yaga ya ɓata a jejin,gaba daya saiyaga ya ruɗe hanyar ya bace mishi baiya fahimtar inda ya dosa,ko haka kawai yaji ya firgita,wani sa’in ji yake anai masa maganganu marasa ma ana masu kuma firgitarwa da tsaki mai ƙauri acikin kunnen sa,Ahaka dai ya danne xuciyarsa bai karaya ko yaji tsoro ba,Adduoi ya dingayi har Allah ya kawo sauƙin abin sannan ya soma fahimtar hanyarsa harya gabato ixuwa gida.
Goma shaura dot na dare saigashi ya iso kusa da kofar gidansa inda baifi taƙu ashirin haka yakai inda matar can take ba,kirjinshi na tsananta bugu duk jikinshi na rawa cikin sauri ya hau warware kullin dake hannunsa kamar yadda malamin ya umarceshi daya shafa turaren dake ciki ajikinshi kafin ya gabatota hakan kuwa yay babu ɓata lokaci,shiyasa harya xo ya wuceta suduk cikin duhun dare bata ganesa ba..
Tari take tana zage zage ita kadanta “Durun uwa!!! wannan wani irin kazamin turarene haka?
Da addua abakinsa ya shiga gidan ya samu badiatu tana kwance cikin jikata harta fara ɓarin jini,tana ganinsa ta soma kkrin miƙa mai hannunta dake rawa rawa cikin kakkalallen murmushi mai mugun rauni ta riƙosa tace “Aliyu”..Aliyu harka dawo?..raunatattun hawayensa ne suka soma gangarowa bisa kuncinsa yanamai gyadamata kansa yanacewa “eh”,agabanta ya durkusa bisa gwiwonsa duk gabobin jikinsa sun nakarkashe jikinshi baida wani sauran laka,wani malalaciyar numfashin tausayin kansu suka sakar ma junansu.
Rungumeta yay ajikinshi
Tsammm yana maida ajiyar numfashi muryansa can ƙasa sann yace “sannu…kiyafe ni Badi’atuh na..kiyafeni daya kasance bana tare dake a wann lkcin dakike matukar bukata…sannu kinji..Allah ya sauƙeki lpya yar aljannata…kanta kawai ta iya gyadawa cikin ciwo…Ya dauƙi shauran turaren ya shashhafa mata ajikinta itama,yabi ya hada ruwan maganin daya amso awajen malam ya bata tasha wasu ya wanketa dashi dan malam ya gaya masa aljanu ke azbtar da ita ba zallan ciwon naƙudar ba,Aikuwa tana shan maganin gadan gadan saiga ciwon naƙuda ya tasomata babuji babu gani,da murƙususu da komi haka badiatu ta sauka lpya cikin ikon Allah ta haifo lafiyayyar ƴa mace
Wacce ta debo kamannin uwa da uba batada nakason komi.
Malam hassan(aliyu)tuni ya zauce wajen kallon yarinyar dake cikin jini rauntattun hawayensa na diga yuuuuuuuu akanta tamkar koramar datayi ambaliya,bakinsa dake karkarwa babu abunda yake furtawa sai Allahn sa “Alhamdullahi rabbil samawati wai al’ardi…ya rabbil alameen,anta noorul samawati wama fi hinn,Rabbil arshill azeeem.Allah maiyi duk yadda yaso a kuma lokacin dayaso,yah Allah nagode maka!!Allah nagode maka,ya rungume yariyar tsam ajikinshi yana mai fidda sautin kukansa mai cike da gamsuwa da ni’imar da Allah ya saƙa musu dashi daya azurtasu da haihuwa sakamakon hakuri da juriyarsu tsawon shekaru 30 da aure.