FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 36-40

FR36.

Desperate13:busted

“me zan gani haka najaha?ubanme kikeyi min anan..
Arazane najaha ta juyo tare da miÆ™ewa tsaye adan daburce tana cewa..babu,babu,saikuma ta dan dakata taja numfashi “kai wasime meye zaki wani dakamin tsawa kamar wata yarki mtss ji harkin wani tsorata ni.

Fuska a matukar dore wasime ta hantsalo cikin kitchen din suka tsaya gaba da gaba suna kallon juna, wani dan uban harara takebin najaha dashi daga sama har kasa tanai musu kallon debar albarka daga ita har kayan girkin dataje ta sissiyo.

A dake cikin harara tace
“Yaushe kikaxo gidan nan bansani ba, kuma uban Meye wannan kika kawo nan?uban waye ya baki izini ?

Wani rolling idanu najaha tayi a makirce cikin kadadi da rigima shareta tay tanamai bata keya kamar ma bada ita takeyi ba,sai can acikin shan qamshi ta juyo,murya ciki ciki tace”As u can see,shoping najeyi na abunda zamuci yau agidan…”kinma san abunda zaki dafa kuwa?

Zonan ta jawo hannunta ta kawota har gaban ababen data siyo snn tace “look carefully,tana fadin haka ta jawo kayayyakin data siyo ta ajesu agabanta tahau nuna matasu one by one tana cewa wannan ledar kayan hada cole slaw ne,wann kuma nikakken nama zakiyi masa meat balls dinki mai shegen dadin nan,snn pasta italiano zakiyi shine as main meal da dan tuna fish sauce inkin gama gabaki daya saikiyi ganishing din abincin da meat balls din..

Dama so nake in shishhriya miki su kafin sai inje na kiraki kizo kifara yin aikin ki yanzu,And yes,lest i forget dan Allah wasime kidaure kina dan rage barkwano wallh Jiya bakiga yadda yaya na yakeyi da bakinsa ba ne wai Kashe shi zakiy ne?
Tana maganan ne with confidence irin ta samu wajen nan, tanawani kadadi da yanga tana giggila kai kamar itace oga madam din gidan gabaki daya.

wasime dake kallon ta da mamaki bata san lokacin da idanunta sukayi wani ja ba, ranta gabaki daya ya hargitsa ya baci,wani irin Runtse idanunta tay tare da dunkule hannayenta da suke mata kaikayi duk jikinta na rawa zuciyarta na mugun tafarfasa da kyar ma ta bude rikitattun idanunta ta saukesu akan najaha

Karkada kafafun ta tahauyi Cikin tsananin jin haushi snn ta daka mata tsawa”tace ke najaha wai intambayeki ni yar aikin ki ne…gwalo ido waje najaha tay ni yaushe nace miki haka..
bata gama rufe bakinta ba taji an wani cakomu wuyarta an shaketa cewa take amsa zaki bani jaka makaryaciya Yaushe kika dauke ni aiki a gidan nan da zakina bani dokoki??ko nan gidan ubanki ne da zaki wani xo kina mana mulki ga wani dan iskan karyan da kika samu sarar gundumawa wa yayana akaina najaya ashe ke babban munafuka ce kullum sai inyi girki kice inbaki zaki kai ashe karya kikeyi munafurta na kawai kikeyi..kinsa yaya na yanamin kallon wata shashasha.

matsiyaciya kawai ince kinayi ne don yana baki kudi?ai bantaɓa sanin bara da roko yakawo ki gidanmu ba,dan tsabar rashin kunya gida banaki ba harda karban kudin cefane waike gaki sarauniyar sanin hanyar kasuwa ko, hamshakiya me yimana jefanen gida.kin wani maidamu yan iska toh wallh baki isa ba,nafi karfin makircin ki,yau din nan karyan ki zai ƙare kuma saina tona miki asiri babban munafuka kawai.

Bude baki Najaha tay idanunta har sunyi jaa zatay magana wasime ta wani turmusa wuyanta yanayinta a mugun zafafe fixgo hannunta tayi a walakance tana mai tunkuduta kamar wata yar akuya takai ta har waje can bakin gate sann suka tsaya kowannen su na huci suna kallon juna.

“Wasime meyayi zafi?
Najaha ta furta hakan muryan ta na rawa idanunta cike taff da hawaye

A fusace wasime ta hau karkada kafafunta da sigar rashin mutunci da dabanci,bala’i da masiface zalla a cikin kwayar idanunta

tace ince dai waje na kikezuwa kuma dama ni na bukaci hakan,dan haka yau na sallameki karki Æ™ara zuwa wajena kije can gidanku kicigaba da makircin da karyanki anan,snn ki tarkata mulkinki kije kibaza ma tsohuwarki a gida amma ba anan ba…get out and dont ever come back…ta kara turata can waje a mugun fusace tunkan najaha ta bude baki tay wani magana har wasime ta hargitsa ta rufe kofar gate dinsu gararau ta danna masa lock ta ciki kamar wata mahaukaciya

Zubewa awajen najaha tay, tsoron wasime fall cikin ranta ta tuma akasa taci kukanta ya ishe ta sann taja kafafunta ta isa gida,anan ma tana isa ta zube a tskar gidan su tana rabza kuka Can saiga maman ta ta fito daga wanka akanta ta tsaya da sigar mamaki tace ke najaha Waime ya sameki haka kiketa kuka wani abu ya farune?

Cikin bori da kuka ta juyo tace mama ba wasime bane tay min korar kare a gidansu Cewa take wai nazo ina musu mulki da karya shine tajani har waje ta koreni korar kare tace wai karna ƙara xuwa.

Kyabe baki maman tay ta ce “ita din ne ta gaya miki haka…gyada kai najaha tay cikin kuka,”murmushi maman nata tayi snn tace ke da Allah share hawayenki ki tashi mu shiga ciki waye kuma wasime da har zaki kyaleta zo muje Ai inta san wata bata san wata ba,,wata rana tana zaune haka zataga an kawo ki a matsayin amaryan yayan ta anan ne kuma zataga bakar mulki,jeki dauko min wayata kizo kiga wani abu itace zatasha kunya yau Intaga yayanta ya dawo dake gidansun dakanshi kin zauna daram, sai inga kuma ta inda zata kara samun daman koraki.

Share hawaye najaha tahauyi tanajin dadin abunda mamanta take furtawa,zcyarta cike da karfin gwiwa ta shiga daki ta dauko mata wayar ta kawo..

Scrolling tay zuwa tex messsage ta bude wani
Unknwn number daya turo mata da sakon lambar wayar taher

Copyin number tay ta mika ma najaha wayar tace wannan lambar wayansa ne kiyimin saving da sunan sa anjima kadan daf zai dawo kituna min saina turamai sako amma zanyi masa kamar kece kika rubuta kinji?.

Cike da mamakin salon mamn nata tace mama nikuma?to me zakice masa kenan..mama karkiyi abunda yay taheer zai ganomu kinsan shi ba baida mutunci wallh

Dariya maman ta saki cikin tsareta tana cewa kibarmin wannan yata
Kedai tashi ki shiga daga ciki ina zuwa yanzun nan zanzo in sameki sai mu rubuta saƙon tare.

Najaha batace uffan ba ta mike tayi ciki jikinta a matukar sanyaye

A fannin wasime kuwa Komawa cikin gidan tay tana tafiya fuuu kamar zata tashi sama, ranta ya mugun baci,a hargitse ta shigo bata tsaya koina ba direct ta wuce kitchen tahau yin firo da abubuwan da najahar ta sissiyo tanakaiwa waje

Abun baimata bama ta kwashe kayan duka taje ta watsasu a dustbin ranta ya baci sosai sai tanajin kamar ma ta tsane ganin fuskan najaha na har abada.

Bambami ta dingay ita kadai tana cewa
Yar iskan yarinya dan taga ina son koyar abu a wajenta ne shine zata na rainamin wayo tana hadamin munafurci tana wani bani oda nida da gidan mu?kut man uba lallai ma najaha ta balain raina min wayo taci kasuwarta akaina,amma wallhi saina nuna mata cewa badaga kauyen yaya kare na fito ba..nima ai na iya karya da munafuccin…tsaki ta dingaja tana huci dan wasime akwaita da zazzafan zuciya da riÆ™o.
Har wani tukikin haushin kanta takeji da tunda can bata dauki wani mataki ba tanamai jin mugun nadaman jawo najaha.

Duk tarasa me zatayi dan zuciyar ta ya dan sassauto yay sanyi tsintsiya da mopper ta dauko kawai ta Kara tsaftace gidan ko ina yay tsaf snn ta fetsa ma gidan turare.

Can anjima da ranta yadanyi sanyi sai ta dawo kitchen din ta fere doya ta tafasa snnn ta daka tayi musu wani hadadden brown yam balls mai flaked fish sann ta dafa yellowshi fried rice dinta dan dai Ta soya chicken wings
Din daya rage a frdge ta dora akai tay zobon dayaji kayan qamshi ta zuba a glass jug kominta ta kammala on time.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button