FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

FR21

Way to school

Ranar jumua da yamma can gabanin magriba wasimé tana zaune tanata wasa har aka kira sallah bataji ba sai wasanta kawai takeyi…taher ya sauko yanata kallonta baice mata uffan ba ya wuce masallaci haryaje ya dawo bayan ishai tana wajen bata tashi ba..

Yana yaye labulen kofar falo ya hangota, motsin takunshi dataji daga bayanta yasaka ta juyowa adan razane suna hade ido cikin sauri tabar abubuwan datakeyi ta mike tsaye sum sum tayi da kanta kasa zata bar wajen,binta da kallo yay baice mata uffan ba harsaida tayi nisa ta soma takawa kan step
Zata nufi daki.Daga bayanta taji sautin muryansa yana cewa kina gamawa kizo kisameni a daki…

Tsayuwar dole tayi dan Bakaramin faduwa gabanta yy dataji yace hakan ba, A sassarfe
Ta juyo ahankli ta kalle shi snn ta amsa shi da toh ta wuce sum sum ciki cikin sauri duk tana tsarge tsoro ya gama cika mata zuciyarta. tana idar da sallah ko cire hijabi batayi ba ta nufo waje tana waige waige.

Wani kauri kaurin kunan wuta ta dingaji ayayin da take saukowa daga matakala,wani irin tsananta bugu kirjinta yay.,kamar ance mata ta daga ido ta duba kayan wasanta aikuwa taga ankwashe su tasss babu ko daya a inda ta bari.

Wani irin bugawa zcyarta yay atake gabanta ya fadi idanunta suka cikka da ruwan hawaye Haka kawai jikinta ya soma bata wani abu Da mugun gudu ta karasa saukowa kasa ta bude kofar waje cikin hanzari ta leka kadan,a can taganshi yana famar É“abbaka wa babynan rubbernta da sauran kayan wasanta wuta….

ragwabewa tayi wajen tanaji kamar an cakkawa zucyarta mashi, rushewa da wani irin tokarriyar kuka tay, da mugun gudu ta koma cikin gidan tana rusa ihu tana kiran sunan bilti a gigice,kusan a raxane bilti ta fito daga wanka batare data shirya ba Hankli tashe take cewa ‘innalillahi Wasime lpya kuwa? wasime meyasameki…

Akasa ta turmusa tana kallon bilti da shagwababben yanayi ta dinga ihu tana birgima tana wulla kafafun ta”wayyo Allah na na higga uku, kayan wasa na, baby na baby na…

Bilti tace ikon Allah wasime toh meya same su?

ACikin kuka Tace “Ba yaa dahiru bane ya konamin kayan wasa na, Wayyo Allah na ni wallahi saiya biyani abuna.Bilti batace mata komi ba.

Wasime ta rungume kanta tana gunjin kuka tana surutai duk ranta a dagule”Yanzu hikenan salamatu ta mutu?(sunan favrite toy dinta kenan salamatu)

tana kukanta tsakani da Allah harda jajjan majina ta cigaba da cewa “wayyo hikenan ni yau naga mutuwar salame..,
yaa dahiru makashine,ya kashemin salame wayyo salame na…na higga uku…”tafadi a kasa ta rike kai cikin yanayin zabura mai ban dariya
Wani tsalle tay ta tumu “..Wayyo Allah na fatima ma tana cikin wutan,hikenan fatu,fatu sa’i yayi, ya Æ™onata wallhi bilti kije ki gani wallhi ya cannata acikin wuta.
…yanzu kodan aminatu bazai barmin ba?. .dazun nan fa nayi ma salma wanka nasaka mata kaya mei hegen kyau… wiii wiiii ta cigaba da kukanta Kamar xata tsaga kanta tana yi tana bori tana cillo kafafuwanta akasa tanaji kamar zata haukace…

Bilti ta tsaya agabanta emotionless duk sai ta rasa mexatayi kwara daya,shin dariya zatayine koko kuka?dan abun wasimen gaba daya ya rikirkita mata hankli…
Kukan nata abun tausayi amma surutayyan nata kuma abun dariya.

Tana cikin fetsa maganganunta caraf taji kamar motsin kofa ta bayanta a rikirkice ta mike tsaye ta hadiye kukan mel tayi shiru kamar ba ita takeyi ba.
Kallon kasa ta dingayi kamar marar gaskiya

Ahankli ya turo kofar dakin ya tsaya daga can bakin kofa yana kallonta,
Ya hade rai yce ihun waye nakeji Haka?

…kafin bilti ta amsa caraf wasimé ta cabe maganan muryanta na rawa rawa tace “

“Ummm ba ihu bane fa. Dama Salame ne da fatiti da amina da salma suka rasu shine nake gaya mata,shine kawai naji tausayinsu, shine kawai na ga kuka yafara xubomin saina farayi..sai gaka nan ka higgo,kasa daurewa tayi ta rushe da wani uban kuka mai ban dariya tanayi tana goge hawayenta ahnkli dan kar yagani,cikin shessheka take cewa “Allah ya jikan su salame…wayyo Allah na hikanan salame ta mutu tabarni…inama zan iya da saina bita lahira…

Ta cigaba da hawaye duk tsoro ya gama rikirkita mata yanayinta is like bata ma san tana furta wayannan maganganun ba.

Bilti mezatayi inbanda dariya,..ta lura bakaramin drama queen bace wasime…she look so funny and serious at same time har wani sharrr tayi takoma kamar
Wata wanda takecikin matsanancin halin makokina gaske.

Dada harde ransa yy yaja tsaki mai tsayi, yi yy kamar ma bai gane me take nufi ba “yace suwaye kuma salame?..
Bilti ta cigaba da dariya ganin wasime ta dora hannu akai sai gunjin makoki takeyi tana jimamin babynan robanta batama ji meyace ba..,bilti tace
“wai kayan wasanta ne tacemin ka konasu awaje…Bai jira ta karasa maganan ba ya dada harde rai yace ohh,da wani matsiyancin harara yabita snn ya zare mata idanunshi yace”ke?bakida hankline will u Comon get out of this place?akan dan wann abunne kike bude wa mutane baki?nace akan wannan shirmen kike cika mana kunne.

Rungume kanta tayi tana ja baya baya cikin girgiza mai kai

mtsw…yaja tsaki ciki ciki yace..”stupid,sai shegen son wasan banza,ke Bance miki kizo daki ki sameni ba?toh Uban me kika tsaya yi anan.

Hawaynta ta goge da kyar cikin shshekar kuka cikin tura baki tace “kace”..ai ina zuwa.

Harararta yay snn ya sake kofar yana cewa
“Dont waste my time, be fast.

Yana barin wajen bilti ta juyo ta kalleta cikin sauri tace toh kiyi maza ki share hawayenki kibishi
Hala zai sayamiki wasu kayan wasanne wanda sukafi wayannan kyau .

Tana famar share idonta da sukaki dena bulbulo da ruwan hawaye ahankli tace “Allah ko bilti?gyada mata kai kawai bilti tayi tanamai dafata,can tayi shiru sanda ta samar makanta nitsuwa snn ta fice ta doshi hanyar dakinsa

Taheer kuwa tunda yabar dakin yake tsintar kansa dayin tsaki musamman ma inya tuno da shirmen data dingayi agabansa”

Sallama tayi ya amsa snn ta turo kofan ta shigo suna hade ido taga kamar ya dan hade ransa

Tsugunawa tayi har kasa cikin ladabi da biyayya sann tace yaa dahiru gani nan nazo!

Shiru yy saida ya gama ja mata aji snn yace jeki kicema bilti inta gama abunda takeyi ina son ganinta yanzun nan.

Mikewa tay cikin sanyin yanayi babu musu tay waje cikin zcyarta tana ta kukuni,sai yaje har daki bazai iya gayama bilti yanason ganinta ba saiya aikeni?Gabaki daya ranta abace yake da shi tana tafiya tana tura baki ta samu bilti harta gama shirin kwanciya taja ta tsaya “Uhmmm bilti cewa yay waikije ki same shi yanzu yanzun nan

Bilti ta juyo cikin dafa kafadunta da sigar tsokana toh yaya akayi baice miki komi akan su salame bako?

Kamr jira take bilti ta furta hakan” bata gama rufe bakinta ba ta Rushe da wani sabon kuka.
“Allah Nide ancuceni kawai ankahemin su salame,Wallahi Allah ji nake kamar inyi zage zage.
..a zuciye ta karashe maganan tana stressing dinsa kamar wata yar daɓa tana huci, Bilti ta fashe da dariya sosai hartana rike cikinta..
Acikin dariyar Tace wasime wato ji kike kamar kiyi zage zage ko?

Gyada kai tayi tana sharban kukanta dagske

Bilti tace yoh kimayi kigani, wallhi babu ruwana kika sake kika yi wani abu yaukam sai taheer ya soyaki a magyada.

Ki gwada budan bakinki kice zakiyi wani abun rashin kunya kiga.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button